← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 122

Sashe 8

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****************
Lahab bashi ya farka ba sai kusan 11 na rana, mikewa yayi daga kwancen ya d'auko laptop na Rahab ya kunna data, har 12 yana dakin jin muryar su rahab a falo yasa kasa mikewa da sauri ya kashe system in ya mayar ya aje.

Fita yayi a d'akin ya wucesu a falo babba suna xaxxaune Ana hira, kitchen ya nufa yana bude kofar kitchen in sai kuma ya tsaya ganin gogoji mai aikin su tana duke Tana kuka.

Harya karaso cikin kitchen in bata ma san ya shigoba shima dukawa yayi a tiles in kamar yanda yaga tayi, ya dafata tare da kiran sunan ta"gogoji"?

Da sauri ta d'ago tana kallon lahab sai kuma da sauri ta kama goge hawayen ta da bakin dankwalin ta.

"Gogoji tun da safe nasan akwai abinda ke damunki, Amma haka kika boye mini dana tambaye ki kikace lafiya, ke ba'a mai aiki na d'auke ki ba kawai a gidan nan, a matsayin uwa nake kallonki tunda nayi wayo na bude ido na ganki a gidan mu, koh zan manta da hidiman kowa wallahi baxan manta dake ba kin mana goma sha tara wanda koh mahaifiyar mu bata kula damu ba kamar yanda ke kika kula damu, don Allah ina rokon ki ki sanar dani abinda ke faruwa"?

Shuru tayi tana kallon lahab sai kuma a hankali ta kamo hannunsa, lahabu bawai banason fad'a maka bane nasan halinka ne shiyasa?

"Insha Allah babu abinda xai faru waye ya zageki koh wani abin aka miki"?

Lahabu babu abinda aka mini a gidan nan daman yarona kuda d'aya da Allah ya bani ne yana da sikila tunda aka haifesa yake fama da jinya ba'a wata biyar sai an daura masa laidodin jini, duk Albashina a jinyansa yake karewa Kanaga dai Abinci ma na gidan nan nake ci natafi masa da nasa.

"eh sai mai yafaru gogoji"?lahab ya kara tambayar ta jin tayi shuru.

Shine wannan karo koh wata biyu baiyi ba daga jinya aka sake bukatar wani jinin don tun jiya yana asibiti gashi bani da wasu kudin a guna, shine nacewa Mamun ku akan tamin magana da Alhaji ina son magana dashi don Allah.

Shine ta tambaye ni meyasa nakeson magana dashi saina gaya mata akan inaso ya taimake ni da kudin aikina na wata biyu zan ma d'ana jinya in ya samu lafiya saina cigaba da aikin har na gama na wata biyun ma.

Shine tace wai baza'a bayar ba kuma na kuskura na gayama Alhaji a bakin aikina tunda daman ita ta d'aukeni aiki, kuma bazan tafi ba saina gama aikina nayau, ta karasa magana cikin kuka.

"Ran lahab a bace yace, kenan yanzun d'anki na asibiti kikazo kina aiki kika barsa"?

Don Allah Lahab karka nema mini magana kabar maganan nan kawai na yafe insha Allah zanje na samesa lafiya.

"Wani irin koshin lafiya bayan kin zabi aiki sama da d'anki, taya zaki amince da abinda mamu ta fad'a bayan kinsan Imani bai wadace taba"?

Don Allah lahab kayi shuru ka daina magana da karfi kar ajimu, yanzun innaje naxo na rasa aiki fa a ina zan samu wani aikin da zan tallafawa rayuwar d'ana?

"ki tashi ki fita a gidan nan ki jirani a kofar gidan su adewale ina zuwa"ya karasa maganar da mikewa tsaye.

Da sauri gogoji tace, mezakayi lahab na rokeka karka jawowa kanka wani rigimar kuma? kadai san mamu akwai iyya munafurci abinda bakayi bama tana kitsawa ta fadawa Alhaji bare kayi.

"Karki damu gogoji kedai ki jirani kawai ina zuwa inta tambaye ki ina zaki kice Kiranki akayi daga asibiti jikin yaronki ya tashi kuma karki kuskura ki tsaya koh tana miki magana ne, muje oya"yace yana kama hannunta suka fita a kitchen in, bayan ya kashe gas data ke girki dashi..

Bai saketa ba saita suka zo mahaden falo ya sake mata hannu tare da nuna mata hanya ba tare da yayi magana ba, itama ba musu ta d'auki hIJAB nata ta wuce falon.

Shikam sashin su Mamu ya wuce tura kofar sashen yayi a hankali yana bin koh ina da kallo tsarin gininsu ba irin nasu bane duk da suna flat d'aya, amma an tsara musu bangaren su, kofofine guda uku a falon tura kofar mamu yayi ya shiga ciki.

Bincike ya fara mata daga akwati har wardrobe, drower koh ina sai da ya bincika amma ina shuru bai samu koh sisi ba zagin mamu yake a ransa na mako irin nata ita kullum saidai ta samu a jikin Abbu amma baxata ci nata ba.

Jakan hand-back nata ya d'auka ya bude ATM ya gani har guda uku, zaban master card nata yayi ya soka a Aljuhu tunawa da yayi ranan ta aiki Rahab bank dashi, kuma yaji Rahab na tambayar ta ta waya menene pin in ATM in a lokacin suna d'aki.

Da sauri ya fita a d'akin maimakon yabi hanyar falo babba, sai yabi baya wata kofar ya fita a falon su mamu, sai ya bi kofar lambu ya fita a flat in ta baya, ya zagoyo ya fita ta get da sauri ya nufi gangaren layinsu har kofar su Adewale, aiko gogoji na tsaye tana jiran sa.

"Gogoji muje koh"?.

Ina xamuje Lahab?

"Kekam muje mana bakin yiwa mamu sallama ba"?

Eh na mata sallama dayake ma Alhaji na falon bata tambaye ni ina zanje ba, danace mata zan koma gida tace ba damuwa.

"ok muje to"ba musu ta bisa har suka tsallake titin unguwan nasu sai da suka iso wani shagon POS, mika ATM in yayi tare da fadar Pin in yace kuma a cire masa dubu dari uku a ciki.

Ba musu masu Pos suka cire masa kudin dakad'an kadan har suka gama a take ya mikawa gogoji, data sake baki tana kallonsa dubu 150k"gashi gogoji ki masa jinya karki sake dawowa har sai yaji sauki in ma kin dawo ta koreki sauran changen ki kama sana'a dashi Allah ya basa lafiya"

Kuka ta sake Ah ah lahab Aina ka samu kudin nan, dakake bani karfa kaje kasa kanka a rigima nasan halinka?

"Ba wani rigima kudina ne danake tarawa duk randa aka d'auke mu ball a kasar waje sai na tafi dashi"

Toh Allah yayi Albarka na gode maka Allah ya rayaku Lahab ya rage maka fitina

"Kai gogoji zafa mu samu matsala dake tunda kema irin su mami zaki zama"?

Ah ah d'an gidana ba'zama ayi haka ba, kaga tafiyata.

"Am gogoji d'an tsaya don Allah nace ba karki fadawa kowa na baki kudi kinji"?
.

Toh saboda me ?

"Nidai na fada miki, in ba haka ba zaki saka kanki a matsala ehen" kawai yace ya juya ya kara gaba ya barta tsaye agun tana binsa da ido.

Lahab bank ya wuce yasake maida sauran kudin daya cire a Account nasa, master card nata kam wurgarwa yayi a kwalben abinsa bai koma gida ba, ya wuce shagon su nabeel don yasan war haka baya gida, aiko bai samesa a shagon ba, wai Adewale yazo sun fita tare.

Komawa gidan su Nabeel in yayi ya kwanta a dakin sa, bai saurare masifar inna ba kona mubeena.

Bacci yayi sai kusan azahar suka dawo, anan suke sanar dashi ai sunje gidan su ance musu bayanan gashi kamar yan gidan ma neman sa suke, sai kawai suka wuce gona.

"Me kuka samo a gonar"?

Rakene sai yalo, Nabeel ya basa amsa

"lallai fa ai gwara da banje ba yanzun ina abinda kuka sinkon yake"?

Yana tsakar gida inna tace sai dai mu fitar mata dashi a gida bazataci kayan sata ba.

Aiko ku tashi muje wajen audu mai rake ya saye su koh zamu samu na kashewa

"allah ya sauwaka nafi karfin 10k yanzun bare wani banzan rake sai kun dawo"?

Shuru sukayi suna kallon lahab tunda suka ji yace haka sunsan ya nada kudine, shiyasa ba musu suka fita su biyun suka sabi rake da tunben buhun yalo sukayi kofar gida, inna sai kutuma musu zagi take mubeena na tayata.

Suma basu dawo gidan ba har yamma sai kusan 3:30, a waje suka hadu da Lahab daya fitoh masallaci, dukan su a gidan su nabeel sukayi wanka suka shanja kaya zuwa na ball inda suka saya jiya gabaki d'ayan su sanye suke da jese fari sai takalmi baki da socks na ball fari daya kai musu kusan gwuwa, wayar Lahab sai kara take Amma yaki d'agawa harsu Adewale na tambayar sa dalili Amma shuru ya musu, ya kashe ya aje a dakin nabeel

Ball lahab ya rike a hannunsa suka fita a gidan, Kekenapep suka hau zuwa filin ball inda ke tsallaken unguwan su a cikin wani makarantan gwannati don ball zasuyi da yan ungwuwan.

***************
Nnenna na duke a cikin daki tayi kuka harta gaji jikinta sai rawa yake, jin An banko kofar falon yasata mikewa da sauri.

Nnenna !!!! Nnenna come Out?

Jikinta na rawa ta fito a dakin cikin kuka tazo tayi lingdown a gabansa, had'e hanneyenta tayi tana rokonsa, Amma ina kwasheta yayi da kafa ta fadi warwar a kasa kafun ta mike ya rufeta da duka, cikin masifa yake cewa kin cuceni ada ban yarda da duk abinda za'ace mini ba akanki, saboda babu wanda ya taba kamaki kinyi kisa da hannunki sai yau zakije ki kashe yar mutane? banace miki karkije kogi ba ashe sai da kikaje, finzgota yayi ya maka da jikin gini a take bakin ta ya fashe jini ya soma dalala ga glass nata daya fadi a kasa.

Cigaba da dukanta yayi, ashe kece kika kashe onyebuchi yau chukwudi ya farka yake sanar da iyayen sa ke kika ma onye Alkawarin mutuwa shegiyar yarinya duk kin sani a bala'i nayi dana sanin sanin ki wallahi a duniya kin rabani da kowa nawa.

Kuka kawai Nnenna keye tana kare dukan, da gudu wata tsohowar mata ta shigo dakin nasu cikin tashin hankali tazo ta amshi Nnenna a hannun papa kallon sa tayi rai a bace tace.

Mr Obinna duka bashi bane zai gyara kome kuma ina so kasan cewa yarka bata da laifi kai koda tana dashi yau bai kamata kaima ka nemi halaka taba, toh bara kaji yanxun haka yan kauye suna tinkaro gidan ka da niyar kashe yarinyar nan kai ya dace ka taimaka mata.
Chapter 8 · 0% Book details