← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 122

Sashe 41

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Toh ki Shiga ciki ki Kwabe kayanki ga abincin ki Nan saiki zo ki d'auka.

Toh Inna shine amsar da mubeena ta bata tana shiga dakin Kwabe kayan jikinta tayi ta daura fellen zani a kirjinta ta fitoh a dakin kitchen ta shiga ta dauko kwanon abincin nata ta zauna a gefen taburman da Inna ke zaune akai bude kwanon tayi dan wake ne yaji burkono da Mai gaurayawa tayi tayi Bismillah ta soma ci a hankali bawai don tana ra'ayi ba sai gudun kada Inna ta zargi wani Abu,ta danci kadan kafun ta rufe kwanon alamun ya isheta.

Badai Harya isheki ba mubeena?

Wallahi Inna na koshine.

Wani irin kin koshi mubeena abincin da kikafi sone fa na girka Miki sannan Koh shokali biyar lafiyayye bakiyi ba kicemin kin koshi?

Mikewa tayi ta dau bucket ta nufi rijiyan dake tsakiyar gidan ta zura guga tanajan ruwa ba tare da ta baiwa Inna amsar taba itama innar bata Kara magana ba sai binta da kallo da take gabaki d'aya yarinyar ta susuce ga tarin damuwa a fuskar ta amma tasan halin mubeena da zurfin ciki shiyasa bazata sake tambayar ta damuwar taba sai in tayi ra'ayi da kanta ta fada Mata, bucket in na cika ta shiga daki tadau kwandon sosonta ta sabe bucket in tayi cikin bayan gida.

Bappa Ado ne ya doko cikin gidan Koh sallah babu tsabagen yanda ransa ke bace,ah ah Ado menene haka ya kana girma kana Kara shiga daji aka sallamar ma ya gagara zaka Fado Mana cikin gida Kai tsaye.

dan Allah Inna kiyi hakuri raina ne duk a bace.

In ranka ne a bace Ado sai ka shigo waje ba sallama,Zama yayi agefen ta wajen da mubeena ta tashi tare da cewa Inna,wallahi Inna yaron Nan Nabeel ya raina mu?

Meya faru Kuma me yayi akace maka a makarantan?Inna ta tambaye sa.

Inna Wai kinji abinda shugaban makarantan su yace Ashe Nabeel da Yan iskan abokan San Nan Suka hadu Suka bugi malamin su.

Da mamaki Inna ta ce,dukafa kace Ado Kai Amma wa'innan yara anyi marasa kunya shi Kuma Nabeel ShaShaSha su duk abinda Suka aikata Suna da gata shi Kuma fa Ado kana ganin kudin makarantan su yaron Nan dubu darine fa duk tam(team) su suke biyan Masa maimakon ya tsaya ya more su yayi karatun sa saiya tsaya shashanci su sukiyi Shima yaki.

Gyara Zama Ado yayi,wani irin karatu ma Inna bayan an koresu.

An koresu fa kace Ado?

Kwarai ma kuwa anan ya fada Mata duk yanda akayi da principal sosai Inna tayita mita kawo Ado sallama yayi Mata ya tafi abinsa.

Nnenna Kam kuka ta sake sosai ganin halin da Lahab ke ciki sai had'a zufa yake Yana dafe da daya hannun nasa yama kasa Koh mikewa zaune,da Sauri ta matso wajensa tasa hannu ta dagosa zaune, customers dake cikin restaurant in gabaki dayansu hankalin su ya tashi ganin halinda Lahab ke ciki ga kukan da Nnenna keyi su Karan kansu ma'aikata sun tashi hankalinsu ganin wani ya Shiga matsala a cikin shagonsu.

Mutumin dake zaune kusa da table in su Lahab ne ya mike a hankali ya nufi Nnenna ganin mutanen wajen sai zaginta suke akan kome ya samesa itace sanadin kome harda cewa su fitar musu a shago,karasowa yayi kusa dasu yasa hannu ya dago Lahab tare da kallon Nnenna dake ta kuka jikinta sai rawa yake harga Allah Bata bugi hannunsa da niyar cutar dashi ba mutumin da ya taimaketa a rayuwa yau an waye gari ita ta cutar dashi,dau jakanki muje asibiti don ina tunanin ya samu matsala a hannun sa,shine abinda mutumin yace Mata Yana tafiya da Lahab bayan ya tallafesa.

Da Sauri tadau jakanta tabi bayan mutumin daya riga ya fita waje,amma abinda ya bata mamaki shine tana fita kawai ta nemi mutumin da Lahab ta rasa,hankalinta a tashi ta Soma tambayar mutanen dake tsatsaye a bakin restaurant in Koh sunga wani mutumin sanye da farin jamfa da wando Yana rike da wani dan makaranta?amma kowa cewa yake baigansu ba dawowa tayi cikin restaurant in ta tambaye su Koh mutumin bai fita bane amma Suka tabbatar Mata ya fita Mana harma tabi bayan sa,dafe kanta tayi da karfi jikinta na rawa sai Kuma ta Mike da mugun gudu ta fita a cikin restaurant in.................

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*

Page 51&52
Sosai ta rikice tana bin wajen shagon da Ido sosai jikinta na rawa kallon wani Forest dake gefe da shagon tayi,da Sauri ta nufi dajin tayi cikin bishiyoyin kaman ance ta dubi damanta kawai taga mutumin nata Sauri da Lahab Kamar ma baya hayyacinsa,da wani irin mugun gudu ta nufi mutumin unexpected tasa hannu ta bangajesa har Saida Lahab Shima ya Fadi timm a Kan wasu ciyawe wuyan mutumin ta shake da karfi sosai ta had'a bayansa da jikin wani bishiyan zaiti,sosai ya shaku Wanda a take kamanninsa Suka Fara sauyawa zuwa na wannan tsohon sosai jikinta ya Kara d'aukar rawa Shima sai kokarin kwatar kansa yake a wuyanta ga tari na caarkesa Kamar xai mutu,ki taimaka karki illah tani ki sakeni ki sakeni Zaki cutar dani akan wannan yaro,shine abinda tsohon yake fada har lokacin ya kasa kwatar wuyansa.

Hawaye ne sun cika idanun Nnenna ta soma magana"na maka gargadi na sake na maka gargadi akan Hassan ka fita daka hanyan sa amma kaki na fada maka kabar zuwa Masa a mafarki kaki sannan yanzun ka koma farautar sa"?

Jin abinda tace yasa sa zabura cikin zafin nama yasa kafa ya tunkudeta sai da ta Fadi a kasa a take ta Mike tsaye tana binsa da mugun kallo,tabbas dole na bibiye sa tsawon shekaru muna baki kariya akan me rana tsaka zaizo ya chanja Maki zanen kaddarar ki d'aga tsarin mu zuwa nasa.

"rufemin baki ku kun Isa ku zanamin kaddarar rayuwata kun Isa babu Wanda ya Isa ya tsara wa mutum abubuwanda zai faru dashi bace abinda God ya tsara wannan karyane"

Bari kiji bazamu lamunce Hassan a rayuwar ki ba bazamu lamunta ba tsawon shekaru kin rayu bisa tsarin mu baki Isa ki kauce ba ata dalilin sa ba ki kaurace Masa muddin kina sonsa a raye.

"taya Zan rabu dashi tunda nake bantaba samun Wanda ya damu da damuwa ta ba ban tana haduwa Koh Samun Wanda yakeson kasancewar dani a tare dashi ba,sai yanzun Hassan ya rabeni ya nuna min tausayi shida shayibu mundin kanason kanka da lafiya ka fita harkan sa ka fita harkansa ka fita wannan ne gargadi na karshe da Zan maka na rantse ka Kara rabarsa nice ajalinka kaji ka fada musu iyya wuya Ina tare da shi"tana karasa maganar ta tsunguma ta cicibi Lahab abin mamaki ba tare da ta wani ji nauyinsa ba abayanta ta goyasa ta dau jakanta ta juya tana tafi ba tare da ta sake kallon Inda tsohon yake ba har ta bar Forest in.

Maharbi dake tsaye tun d'azun a cikin wasu ciyawe da Ido yabi Nnenna Harta bace sannan ya dawo da kallonsa ga tsohon amma Ina baigansa ba girgiza Kai kawai yayi yaci gaba da tsintar maganin sa.

Nnanna har bakin titi ta fitoh da Lahab a bayanta Keke ta sayar Mai keken tsayawa yayi Yana tambayar ta Inda zai kaita ganinta d'auke da mutum a bayanta ga hannunta rike da jaka.

"Asibiti nake so ka kaini" Nnenna tace cikin turanci.

Ke in zakiyi hausa kimin hausa.

Shuru Nnenna tayi don bata fahimce me yake nufi ba gashi bata iyya hausan ba,Mai Keke Kam Jan kekensa yayi ya Kara gaba ya na masifa.

Ta Jima a wajin kafun ta samu wani Mai keken dan niga-niga dashi,tace Masa asibiti zai kaita.

Cikin dan gaya gayan turancin sa yace mata meya samesa naga baya motse.

Kawai malam ka kaimu asibiti,shine abinda tace kenan tana kallonsa.

shiga muje,a hankali ta sa Lahab a cikin keken itama ta Shiga,wani asibiti Zan kaiku?Kowan ne ma maikyau sannan don Allah kayi Sauri.

Karki dawo da gudu ya fege keken bai tsaya Koh Ina ba sai wani Private hospital ya faka.

Sauka Nnenna tayi tare da rokonsa ya Kama Mata Lahab su shiga ciki.

dazun waya d'auka Miki shi da yanzun Zaki wani ce na rike Maki shi da Allah ban kudina na Ware.

Waro Ido tayi sai ma yanzun ta tuna bata da ko sisi a hannunta,kaga ka taimaka ka Kama mini shi mushiga saina karbi kudinka na baka,cikin masifa yace daman kudin nawa bake Zaki bani bama kenan?

Shuru tayi taki kulasa Shima cikin haushi yazo ya Kama hannun Lahab da Sauri ya zabura domin hannun ne Nnenna ta buge Masa,"Kai malam menene haka nace maka hannunsa zaka kama ne"

don Allah rufemin Baki Yar banzan inyamura In ba hannu ba Ina kikeso na Kama Masa,Bata kulasa ba tasa hannu ta cicibi hakarkarin sa ta cirosa a keken wani cleaner ne yazo da gudu ya taimaka Mata ganin Kamar zata fadi.

Cikin asibiti Suka shiga da gudu akazo aka karbi Lahab akayi wani daki dashi,Zama tayi a hall in Mai Keke sai masifa yake akan ta basa kudin sa kin kulasa tayi har hankalin mutane ya dawo kansu wani mutumine ya tambaye sa kudin sa yace 200 ne yasa hannu a Aljuhu ya zaro 500 ya Mika Masa.

Canji Mai keken ya basa Amma yace Masa ya bari kawai, sosai Mai keken yayi ta godiya ya juya ya tafi,kallon ta mutumin yayi,Kinga Yaya karki Kara shiga abin mutum in baki da kudin biyansa hakan babu kyau gwara ki roka ya kawoki a kyauta kinjiko?
Chapter 41 · 0% Book details