← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 122

Sashe 120

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"dan Allah ka bari wallahi ban shirya d'aukan ciki a gidan mu ba dan Allah dai"?au aikin fi karfina ne yanzun Koh kikace"ah ah dan Allah kayi hakuri ka bari banaso dan Allah dai kokawa Suka Fara a hankali ta koma ta kwanta tana hawaye ganin da gaske yake son kasancewa da ita,yayin da ita Kuma bata shirya karbar sa a wannan lokacin ba,sallama da ake kwad'awa a bakin kofar shiya dakatar da Lahab daga abinda yake,a hanakli ya mike zaune gabaki d'aya jikinsa Babu kuzari mirginawa yayi ya kwanta agefen ta.

Itakam murna fal cikinta mikewa tayi kayanta ta sanya da Sauri ta bude kofar dakin,nazeefa ce Wai Uncle Nabeel(Ade) yace Lahab yazo su tafi masallaci ana Kiran mangari ba"nufar hanya tayi tare da cewa su mike suzo su tafi kin binta sukayi kai da fata,karshe dai haka ta tafi Babu Shirin don Bata son Lahab ya fito ya sameta mikewa Ade yayi ganin ana kokarin tada sallah Lahab bai fitoh ba har lokacin gashi nazeefi yayi Alwala shi kawai suke jira dakin ya shiga anan ya gansa kwance har lokacin bai mike ba girgiza Kai kawai Ade yayi tun lokacin da yaga kwayar idanun sa sunyi mugun rinewa gashi gadon kaca-kaca shiyasa shi juyawa kawai yabar dakin.

Washe gari Lahab Suka nufi NAGERIA Koh sanar dasu Abbu basuyi Suna zuwa ba Rabon Lahab da NAGERIA an Jima sai yau lokacin da suka iso ba karamin mamaki familyn Lahab Suka Sha ba gashi gidan ya Zama daga Abbu sai Addayiya data tsofa sosai sai Mamu don ummu tana fita a gidan yari Abbu ya sallame ta, yara kuma kaf nasu sunyi aure hatta zulai auta itama ta Jima da auren ta.

dangin Lahab sunyi matukar farin ciki na ganin walwalan Lahab ta dawo kowa na dangin su Saida Suka zo kallon yaran Nan kowa yazo, saiya Yaba da tarbiyar yaran ga saurin Shiga Rai,Mami lokacin da tazo kuka ta sake don yaran sun tuno Mata da d'anta Rahab Allah sarki da shima yanzun yayi aure kila.

Lahab ya mayar musu da yanda akai harma dakin auren su da dangin Nnenna basayi Kuma suka nuna akan bazata dawo dakin taba,Abbu da kansa shida Mami sukaje har Libya amma jaddu yace Ina zance dai d'aya ne Nnenna bazata dawo nageria ba an buga an buga Abu yaki haka Suka hakura Suka dawo,shikam Lahab makaranta yasa y'ay'an sa suka cigaba da karatun su shima ya zauna a kasarsa abinsa Yana kula da yaran sa Babu abinda Suka nema Suka rasa.

Esha(cousin na Nnenna) Adewale ya Fara soyayya da ita yarinyar bazata wuce 17 ba ba karamin mamaki Lahab yasha ba ganin tsawon shekarun Nan Adewale baya zance wata mace Saida ya hadu da eshat Ashe shikam tuni sun Soma tsula soyayyar su lokacin daya tare sa da zancen mubeena budar bakin Ade yace yanzun mubeena tafi karfin sa rai bace Lahab yake cewa shida yake da Mata age mate nasa meya samesa, Kuma a haka Yana son suci gaba da rayuwa tare Bai taba Jin sha'awar wata ba.

Amsar da Ade ya bashi shine aisu sunci kurucciyar su shifa? Kuma da ace shima mubeena ta nuna Masa so da har gobe bazai kalli wata ba Ada yayi hakuri Amma Banda yanzun Kam, murmushin takaici kawai Lahab yayi don yasan har gobe mubeena na zuciyar abokin nasu don yayi bincike sosai ya gano Adewale yaci gaba da biya Mata makaranta harta kammala karatun ta har matakin digree aikin da take ma shiya nema Mata kuma duk wata sai ya tura Mata da sakon Kaya Koh wani Abu,amma da sunan Lahab yake amfani Wai Lahab ke Mata sako, don tuni ya gane Wanda mubeena keso shiyasa shima ya sanyayawa zuciyar sa hakuri ya Zama Yana kyautata Matane saboda Allah da Kuma abotar su.

Lahab yadau yaransa har wajen mubeena ya kaisu Allah sarki so ranan sosai tayi Kuka bama kamar daya ce Mata zai aureta don ta matukar basa tausayi gabaki d'aya unguwan su Babu macen data kaita girma a budurwan sai ita kadai,gaskiya so bala'i ne wani lokacin.

Auren Adewale da eshan ya tashi wannan Karo jaddu yace bazai bada eshan ga tubabbe ba Amma eshan tayi fito na fito da jaddu iyayen ta Kuma suka Goya Mata baya don jaddu kakan tane ta wajen uwa Nnenna Kuma ta wajen ubane,Yan uwan Ade Cristian ne shiyasa su Abbu suka tsaya Masa a zancen auren nasa sai dai duk abinda ake anayi ne da izinin iyayen sa papa girma yazo Kuma Ade ba karamin kudi yake dashi ba don yanzun gidan su ma abin kallo ne ga kauyen su daya koma yana d'aukan yara Yana zuwa Yana sasu a makaranta wasu boarding Koh day Suna karatu sosai,wa'inda suka kammala karatu ba aiki duk Yana nema musu aikin yi hakan yasa kiyayyar da suke Masa a dalilin musuluntar sa tuni ya washe a idanun su daman akace kyautatawa tana rage kiyayya.

Zacen auren Ade daya tashi Saida mubeena ta kwanta ciwo sosai ta gane kuranta a rayuwar tayi kuka tayi kuka daga karshe tafawwalawa Allah kome Kamar yanda ta Saba,don zaman gidan bappa Ado ba dadi ne dashi ba sai d'an Karen bakin ciki, yanzun Addu'a take Allah ya Bata Miji komai ruwane(garuwa) tayi aure ta huta itama ta samu zuriyar da zasu debe Mata kewa,Allah sarki mazan jiya su Nabeel(real)an Zama tarihi da farida rayuwa kenan duk abinda ka shuka shi zaka girbe Inka biyewa zuciya zata kaika ta baroka kayi Wasa da Daman ka na rayuwa.

***************************
An daura auren eshan da Ade Ade sai rawan Kai yake an aure balarabiya lokacin da akazo za'a d'auki auren eshan mutanen NAGERIA guda bakwai ne Suka je maza uku sai Mata biyu d'aya goggon sa dayar kuma goggon su Lahab sai ango da abokan sa uku cikin su harda Lahab sai su Abbu da Suka karbi auren,a lokacin jaddu yace Deyana ta tashi tabi mijinta Allah ya Basu zaman lafiya Kuma yaji dadin biyayya data masa ubangiji ya Basu zaman lafiya Kai ranan nan Deyana tayi kuka Kam bana Wasa ba kafun Suka rabu da iyayen ta daman yaranta tuni suna nageria Lahab baki har kunne aka karkato naija.

Hadadden dinner aka had'a a washe garin ranan da Suka dawo da daddare Ade yaso Lahab ya shiga cikin dinner ayi dasu amma Lahab yace dashi da matar sa sun girma, Addayiya ma daker tabar Nnenna (Deyana) taje dinner don tace baza'a tare ba sai Lahab yamata Sabon gida gidajen sa na naija sun tsufa Nnenna tafi karfin su Kuma ya Mata lefe.

Zazzaune ake akan kujerun ga jama'a Kamar me an cika Hall in dam Adewale ne Akan floor da Amaryar sa Esha kyakkayawar yarinya ajin farko, saidai fa Bata Kai Deyanan muba,Lahab na zaune a Inda aka tanadar wa Baki shida matar sa sai yayan su dake zaune kusa dashi daman table ne Mai daukar mutane hudu abokan su tunna secondary school duk sun hallara harda na London duka,hall innen yayi shuru sakamakon sanarwa da MC (Dj) yayi ayi shuru akwai wani abin mamaki da za'a nuna musu,yaye labulen dake jikin gidan hall in akayi.

Farin kyelle ne ya bayyana sai Kuma abinda mutane bazasu zata ba hoton Lahab ne tsaye da Rahab sunyi ne a cikin gida su a wancan shekarun,Nan wa'inda Basu San Lahab tagwaye bane suka Soma tambaye wannan Kam shine dan uwan sa kenan,hoton ne ya bace aka nunu na Lahab sanye da uniform sai Nnenna da itama tana sanye da uniform a jikinta tsaye suke a unguwan su Basu ma San anyi hoton ba,sai Kuma hoton Lahab da Adewale da Nabeel na ainahi,sai Kuma hoto na gaba shine Randa Suka kammala secondary school sukayi hotuna dukan su da mate nasu harma da coper dasu Lahab Suka duka.

Abin Al'ajabi sai ganin vedio dauren auren Lahab akayi sai Kuma aka Kara nuna hoton Nnenna da Lahab again lokacin da take da ciki,kana aka sake Nuno hoton su dayaransu harda Ade a cikin hoton,sosai mutane ke jinjina soyayyar dake tsakanin su, Ada sai gulmar su ake tunda Suka zauna Amma tunda aka ga hoton sai jikin mutane yayi sanyi hotona sosai aka yita nuna wa, mubeena da tayi karfin Hali tare da ma kanta ALKAWARIN insha Allah zata zo bikin Ade Koh don d'awainiya da yayi da ita a boye don taje ta samu Mai kawo Mata kudi da sauran abubuwa tsawon shekarun nan tace ya fad'a Mata tsakani da Allah wake d'awainiya da itan Nan yace Mata Adewale ne.

Hawaye ne ya cika idanunta a hankali ta Mike tana kuka ta fita a Hall in Babu Wanda ya hankalta da fitar ta sai Lahab shima baisan tana hall in ba Saida tazo fita ya ganta,a hankali ya mike tsaye tare da cewa Nnenna Yana zuwa fita yayi a hall in Yana bin bayanta ganinta yayi zaune ta kifa kanta tana kuka,sosai jikin sa yayi sanyi gabaki d'aya ya rasa meyasa yanzun ya damu da lamarin mubeena sosai ya damu akan lamarinta ace mace har 33 Babu aure gaskiya abin a tausaya Mata ne,tsaye yake akanta yafi minti goma amma mubeena bata sani ba a hankali yasa hannu yad'au purse nata data Yar a kasa daga Ido tayi Suka had'a Ido murmushi yayi kana yace inkin gama kukan ki goge hawayen naki ya Isa haka mubeena kiyi hakuri da rayuwa aduk yanda tazo Miki nasan tabbas kina Jin ciwo a ranki amma hakuri ake kome zai wuce.

Dole nayi kuka Lahab Dole ne rayuwar da nake ciki a yanzun ban taba tsammanin Koh hasashen Zan taba shige ta ba,Babu duka Babu zagi sanan Ina da albashina Mai tsoka sai dai rashin aure yamin cikas ka duba fa ka gani Ranan kawai Na fito gida saiga Yar Ahmad (14year's)Wai hartana nuna Ni Wai ga budurwar baban ta har yanzun batayi aure ba sai Kuma ta sake kuka da karfi don harga Allah yanzun so take tayi aure Amma tunda aka ganoo abinda Nabeel ya aikata ta nemi manema ta rasa.
Chapter 120 · 0% Book details