Sashe 84
Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya Ade yayi yace ka duba WhatsApp na tura maka hoton ta kaga halinda naje na sameta a ciki zuciyar Lahab Saida ta buga cikin tsoro yace meya sametan,baidai basa amsa ba kawai ya katse wayar,jikinsa har rawa yake ya bude data ya shiga WhatsApp zubewa yayi a kasa ya zauna tabas saban shock Nnenna ya gani kwance Kamar gawa Ido a rufe jikinta gabaki d'aya ya sauya daga fari zuwa yellow sosai ga bakinta yayi jajer dashi rabin fuskarta har wajen wuyanta jijjiyoyine bakekkerin Suka fito rudu-rude jikinsa ne ya cigaba da rawa ya fita da Sauri wayar Ade ya Kira Yana d'auka ya Soma Masa magana"Adewale mutuwa tayi ne meya sameta"kaga Lahab karka sa kanka a matsala nidai goggoji tacemin yau kwana biyu kenan da Fara ciwon Nan nata sun tsorata ainun don numfashin tane kawai zai tabbatar maka tana da rai"innalilahi wa'inna'ilahu raji'un kawai Lahab yace ya katse wayar da gudu ya fito daga ban dakin wardrobe ya bude ya fito da kayansa sakawa yayi ya zaro takalmi zai sa yaga Rahab ya shigo da mamaki yace"Lahab sai Ina zaka a haka Kuma"?
"da Sauri Lahab yace fita zanyi"fita fa kace wani irin fita kake nufi Koh ka manta ne baka da daman fita a gidan Nan yanzun"da Sauri shima Lahab yace Ina da Kai Koh ka manta ne dan Allah Rahab kaje ka kwanta a matsayi na Ni Kuma na fita a madaden ka ka taimaka min wallahi akwai babban matsala"wani kallon tuhuma Rahab ya Masa sannan yace wani irin matsala kenan?
Nidai ka taimaka min kin taimaka Masa Rahab yayi daker ya samu ya shawo kansa kafun ya amince kwanciya yayi akan katifar Lahab yayin da Lahab Kuma yasa Kai yabar dakin Yana zuwa compound na gidan nasu security Suka tashi shiga mota yayi Suma Suka shiga aka jasu suka Soma tafiya gidan ya jafar Lahab yace a kaisa Suna Isa yace su tsaya a kofar gidan basai sun Shiga ba bude kofar yayi ya shiga gidan da Sauri ya nufi falo gashi yammane Kuma goshin mangari ba falon ya bude da sauri ya Shiga babu kowa sashen su Majid ya nufa Yana bude kofar yaga babu kowa Kamar falo sai kida dake tashi a dakin Majid bude dakin yayi da Sauri Majid ya juyo ya kallesa sai Kuma ya juya yaci gaba da rawansa.
Xama Lahab yayi a hankali yasa hannu ya kashe mp in a kufule Majid yace"kaga Rahab banson surutu tashi kabar min daki da Allah"Majid Lahab ne"zaro Ido majid yayi yace kana nufin kaida aka sawa Mari Kaine ka fito"?nidai ba wannan ba taimakona zakayi security na kofar gida so nake ka taimaka nabar gidan Nan ba tare da sun sani ba"kallon sa Majid yayi da mamaki yace"so kake nayi fiffige da Kai mu tashi ta samane Koh yaya Ni ta Ina Zan iya fiddakai"?
"Shuru Lahab yayi sai Kuma yace back door ka taimaka min"d'an dakata Lahab nifa karkazo ka sani a matsala munddin aka nemeka aka rasa Ni za'a zarga karka kiramin ruwa babu ruwana wallahi"dan Allah Majid ka taimaka min Dan Allah nace fa"dan shuru yayi sai Kuma yace Ina zuwa fita yayi a dakin Bai Jima ba sai gashi ya dawo da key yana cewa Lahab ya bari a Shiga sallan mangariba.
Ana shiga sallan mangariba backdoor Lahab ya nufa da Majid bude Masa yayi ya fita harda waya Lahab ya karba a wajen sa Yana barin layin Adewale ya Kira akan ya fito gida Yana bayan GRA,Bai wani Jima ba saiga Adewale daga Nan gidan su goggoji Suka nufa da yake darene babu Wanda ya gane Lahab Shiga gidan sukayi har dakin da Nnenna ke kwance abin tausayi gabaki d'aya kammanin ta sun sauya ta chanja hannu Lahab yasa ya bude kwayar idanunta Saida ya koma baya da Sauri saboda yanda jini ya taru a idanun tim goggoji ya tambaya garin Yaya ta Soma ciwon"wallahi Lahab kwana uku batacin abinci a kwana na hudun ne na matsa Mata akan saita d'anci abinda na kawo daga gidan ku daga saka abinci a Baki Koh hadeyewa bata gama yiba Naga ta damke makogoronta tana amai harda jini a ciki shikenan ta yanke jiki ta Fadi Ido ya rufu har yanzun bata budewa kwana biyu kenan.
Mikewa yayi da Sauri ya nufi kofar gidan Keke napep ya tare sannan ya dawo gidan da Sauri ya ciccibi Nnenna da jikinta ya bushe ta sandare,da Sauri Ade dasu goggo Suka Soma tambayar sa lafiya Ina zaije da ita gudun kada a ganeta a Kamata,kala baice ba yayi kofar gidan da Sauri Ade da goggoji Suka Shiga keken Suma aka bar faruq a kofar gida a tsaye,wani private hospital na kudi Lahab ya kwatantawa Mai keken directly Suka karasawa asibitin ya d'auketa sai ciki ganin halinda take ciki yasa likitoti rufuwa a kanta.
da misalin karfe 12:30am na dare Lahab da goggoji ne a asibitin don Ade tun 9 na dare papa ya kirasa yanata masifa akan ya dawo gida,likitane ya Kira su vayan sun shiga office nasa ya Soma musu tambaya Koh akwai abinda ke damun tane daya shafi iska-iska girgiza Kai goggoji tayi shidai Lahab shuru kawai yayi Yana Jin abinda Dr ke cewa Wai Basu gane Kan cutar ba sun saka Mata ruwa ma ruwan baya gudu haka Allurar ma sun saka amma ruwan yaki shiga a jikinta,su d'auketa kawai jinyan Nan bana asibiti bane,mikewa Lahab yayi da gudu yayi dakin da aka kwantar da ita Yana zuwa kuka kawai ya fashe dashi ya zauna a bakin gadon hade da kamo hannun ta Yana hawaye.
Goggoji ce ta turo kofar ta shigo ta zauna akan kujeran tana kallon Lahab sai Kuma tace"Lahab yarinyar Nan ta Fara bani tsoro gaskiya mezai Hana ta koma wajen danginta kaga halinda take ciki fa"hawaye ya share sanann yace"gaskiya goggoji bazan iya barinta a halinda take ciki ba gaskiya tunda yace abar musu hospital nasu da safe sai mu kaita wani"?
Kaga Lahab Kai suspect ne haka ma ita nasan dai ba kowa bane zai gane Nnenna tunda ita gabaki d'aya jijiyoyin fuskarta sun sauya Mata kamanni bai Kamata ana ganinka haka barkatai ha bugu da Kari Kuma halinda yarinyar Nan take ciki bana asibiti bane gobe in Allah ya kaimu sai muje nida faruqu kauyen mu akwai wani babban malami acan gaba da kauyen, insha Allah koma menene zai kawo karshen sa,d'an shuru Lahab yayi sannan yace"muje dai tare goggoji shi faruq ya zauna a gida bai Kamata na bar Miki d'awainiya haka ke kad'ai ba"
amma Lahab baka gani akwai damuwa na barin gari yanda tsaro yayi yawa a kankan Nan"?karkiji kome goggoji Allah ya kaimu goben"ameen ta amsa,washe gari tun asuba Lahab Suka bar cikin gombe Kuma cikin hukuncin ubangiji Basu samu wani matsala a tafiyar tasu ba,haka zalika baibi takan Kiran da Majid keta danna Masa ba sosai suke ta shiga cikin kauyuka wasu kauyukan ma da machine suka shigesa kafun su Isa kauyen da zasu Saida Suka hau kuran shanu kafun Suka iso wani rugan Fulani.
Zaune suke a gaban wani dattijo ne babba sosai tsohone ga farin gemun shi,Lahab da goggoji ne a gabansa a cikin bukkan sai Nnenna da aka shimfidar akan wani taburman kaba,magana ya Fara a hankali cikin nutsuwa yace"Alhamdulilah Ramatu naji dadi matuka da yanda Kika taimake wannan baiwar Allah Nan ba tare da kinsan wacece ita ba haka zalika Kai Lahab kayi matukar kokari Allah ya saka maka sannan ya kalli goggoji yanzun Ramatu inaso ki sanar dani menene ya faru da ita Koh Kuma me tayi ta Soma ciwon"a hankali goggoji ta rusuna tace abinci kawai na takura Mata taci"wani irine abincin"?shinkafa ne da Miya"a nutse yace dakwai nama a ciki"?gyada Kai tayi ganin haka yasa Lahab saurin cewa ai batacin nama"da mamaki goggoji tace Koh shiyasa Inna Bata abinci Mai nama sai takici amma Bata taba fadamin ba ranan ma nina matsamata taci bata gama hadewa ba abin ya faru.
Mikewa tsohon yayi ya nufi Kan Nnenna masowa yayi sosai yasa hannu ya bude kofar idanunta"sai Kuma ya girgiza Kai tare da d'auko wani magani ya bude xamxam ya juye a ciki ya zuba magani Addu'a yayi sosai ya tofa sannan ya Kira goggoji taxo ta Kamata ya bude bakinta ya Soma zuba Mata maganin tana Sha wasu na zuba sai kawai sukaga ta zabura ta Mike ta Soma aman jini babu gaggautawa harda guda-guda sai Nishi take amai tayi bana Wasa ba,har lokacin idanunta a rufe komawa tayi ta kwanta shi Kuma ya mike ya d'auko magani ya kwaba da man shanu yace ta shafa Mata aduk Inda jijiyar ya fito,Dole tasa Lahab ya fita waje shida dattijon don jijjiyar daga fuskarta ya gangara har wuyanta har Kan kirjinta na hagu ya sauka har kafarta na hagu,fita sukayi goggoji ta gama shafa mata kafun Suka dawo gaushi aka kawo a kasko ya zuba magani a ciki maganin na turnuke dakin Nnenna ta Mike tana wani irin ihu da surutai da Sauri goggoji ta Fadi kasancewar tana da marabai,ya aike Lahab ya Kira wasu sukazo Suka fita da ita shi Kuma ya cigaba da fama da Nnenna Harya samu ta natsu sannan ta koma ta kwanta Lahab kam na bare a waje duk abin duniya ya damesa ya kasa nutsuwa yasan war haka ana neman sa.