← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 122

Sashe 53

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inka fasa jamin Allah ya isa Kai shege ne Nabeel yace Yana maida 30 in cikin aljuhun sa,da Sauri Inna ta Mike ganin Mai bairon ya juya jiki a sanyaye ya nufi kofa,Kai yaro tsaya Inna tace tsayawan yayi ita Kuma Inna matsowa kusa da Nabeel tayi tasa hannu a aljuhun sa ta zaro kudi da Sauri shima yasa hannu Yana kokarin Kama hannunta amma Ina ta rigasa d'auka,kudine akalla zai Kai 5k gayan 1k da 200 100 duk a Ciki,naira 100 ta d'auka ta mikawa Mai bairon ihu Nabeel ya sake Yana wallahi Inna ki ban kudina bana so wallahi Inna karki basa dari na,mikawa Mai bairon tayi da Sauri shima ya karba tare dajan bairon sa da gudu yabar gidan cikin Jin dadi.

Zama Nabeel yayi a Kan dutsen dake kasan wajen Yana ma Inna wani kallo tare da Mika Mata hannu ba tare da yayi magana ba,itama dongora masa sauran kudinsa tayi tana surutu,wallahi Nabeel karin ga Jin tsoron Allah Kai Koh tsoron ace an barka da Allah bakaji Koh a jikinka indai akan Allah ya isa ne, Wai a Ina ka Sami wannan mugun haline nacin abin Allah ya isa?

Mtwwwss wallahi Inna ki daina min irin wannan banason sheshege ke babu halin Kiga Ina magana da mutane sai kinsa baki?

Nasa Nabeel nace nasa don kaniyar ka Ina fa rabaka da abin Allah ya isa don wallahi wata rana zakaci abinda zai dameka,Oho dai yanzun ba wannan ba menene yasa ka dauko keken ka ka dawo dashi cikin gida Koh mutuwar zuciyar ce yasa ka dawo dashi gida tabbacin ma babu cigaban zuwa shago kenan Koh?

Kinga Inna nifa ba haka bane abinda yasa Kika ganni ogana ne ya sallameni a shago Kuma fa Inna wallahi tallahi aiki najeyi kinsan nace Miki daga yanzun Ni zanna biyawa Aunty kudin makaranta amma wannan d'an wahalan malam sadam(ogan sa).

Kama baki Inna tayi Jin Nabeel ya Kira ogan sa da wahalalle,amma in ana Neman Mara kunya in an sameka an gama yanzun Koh tsoron Allah bakaji kake ganin tsabar idon rana kace wa sadam wahalalle lallai nabeel?

Nidai duk yanzun abar maganan nan so nake kije ki basa hakuri yayi hakuri na koma shagon kinji inna ta.

Hararan sa tayi kafun tayi magana,Kai Nabeel babu Inda zani bakace Masa dan wahala ba sai ka nemi uwar da zataje ta basa hakuri tana karasa maganar ta nufi bucket in kamunta ta cigaba da tatanta bata ma kara bi ta kansa ba,shima mikewa yayi ya gurgura keken nasa da ker zuwa cikin dakin sa gudun Kar azo ayi ruwan dare,mubeena Kam har lokacin tana zaune a taburma batace musu komai ba.

washe gari da sassafe mubeena na tashi ta kammala aikace aikacen gidan na safe Koko Inna ta dama musu Nabeel ya sayo musu kosai Suka karya dashi kayan wanki mubeena ta fitar duk da jikin nata babu dadi amma haka ta daure take aikace aikace gudun Kar tasa dan uwanta da Inna a damuwa tunda suma basa iyya sakewa mundin tana cikin damuwa,Kuma hakan ya musu dadi dukan su don Nabeel na tashi bayan sun karya keken sa ya fitar tare da wasu zanuwan daya saya musu kayan aiki baiyi dinkin ba ya dauko Yana dinkawa ga mubeena a gefen rijiya tana dauraya yayin da Inna ke kwance a taburma tana fifita da mafici a hannunta.

***********************
da misalin karfe 8 na safe Nnenna ce ta fitoh daga ban daki ta canja Kaya bayan tayi wanka ta wanke kayan jikinta,rike bucket in tayi ta fita a dakin,tsakar asibitin ta fitoh zuwa wajen garden Inda ta Shanya kayan su na jiya cire kayayyakin tayi ta shanja sabo ninkesu tayi ta dawo dakinta aje,har lokacin Lahab bacci yake bai farka ba kudi ta d'auka ta fitoh bakin asibiti takeAway ta musu,mutumin dake kusa da shagon Saida abincin sosai yake binta da kallo sai Kuma ya zaro wayarsa da Sauri ya Kara kallon screen in ganin ta tsallako titi zata shiga asibiti yasa sa binta a baya shima har yaga dakin da ta shiga sai Kuma ya fitoh da Sauri ya tare Keke napep yahau.

Nnenna na shiga dakin àje abincin tayi ganin Lahab zaune matsowa tayi kusa dashi tana kallon sa gabaki d'aya ya sauya hatta fuskarsa ta kumbura hannu tasa ta taba goshin sa shidai sai Ido dayake ta binta dashi,da Sauri ta dau brush nasa tasa maclen "kazo muje kayi brush sai ka samu kaci abinci kasha magani time na wucewa"mikewa yayi Kamar yanda tace a hankali ya nufi bandakin binsa tayi a baya Suna shiga ta basa brush in yayi ta goge Masa jiki tare da fita ta barsa ya karasa sauran da kansa.

Zaune suke Suna cin abinci kowa da tunanin da yake bare Lahab dake ta Sakuran abinci don shi gabaki d'aya yau Innan so yake ya gansa kusa da mamin sa yaji kewanta da son ganinta ya samu ya fada Mata abinda ke damunsa Koh zaiji sauki a ransa,aje spoon in hannunsa yayi ya kalleta"Labiba ki karbo min Aron wayan na Kira gidan mu.

ba musu ta Mike tsaye dan kwalin abayan nurse in ta d'auka ta yafa zata fita a dakin sai Kuma ta tsaya Jin abinda Lahab yace"karki karbomin na Dr Nan ki karbomin na nurse in dake yawan shigowan Nan"?

Ok tace ta fita a dakin bata wani Jima sosai ba sai gata ta dawo da rantsatsen waya Mai kyau touch screen Mika ma Lahab tayi ta koma ta zauna,jujuya wayan yayi a hannunsa Yana tunanin number wa zai Kira yaso yasa na mamin sa ya kirata amma daya tuna yanda Suka rabu akan maganar farida sai yaji shakkan kiranta,dan murmushi yayi ya Soma sanya number dan uwansa ya Kara a kunne tare dakai dubansa ga Nnenna dake cin abinci batama kallon direction nasa.

********************
Rahab bayan sunci abincin dare da mustaph kwanciya sukayi tun mustapha na Masa Hira har bacci yadau mustapha Rahab Kam na kwance idanunsa biyu abinda ke damunsa ya hanasa bacci Koh Ina Lahab ya shiga ga Kuma abinda ya faru a gidan su abin yazo ya damesa Sam baiji dadin abinda Yama muzammil ba duk da muzammil nacin zalinsu Amma fa soyayyar sa ta gaskiya da gaskiya ne duk Wanda zakayi ba daidai ba ya hukunta ka yagama maka kome amma shi ransa ne ya baci Sam baijin dadin abinda yayan NASA kema mamin sa.

Sai can dare ya samu bacci ya dauketa,washe gari da safe salamatu ta Gama musu dumamen tuwon nasara miyan karkashi gashi daman Rahab baison miyan yauki a rayuwar sa tada Masa da zuciya yake dayake salamatu tasan halinsa tun Yana yaro yasa ta aikan mustapha ya sayo Masa dan wake,ya kawo Masa Rahab yaso yakici amma yasan bazasu ji Dadi ba don tun jiya sai rawan kafa suke dashi Suna haba-haba dashi suke yasan in yakicin abincin su baza suji Dadi ba Sam hakan yasa sa karban dan waken yayi yaci sosai Suna Gama karyawa yabi mustapha garejen su Zama yayi Yana kallon yanda suke ta aikace aikacen su na Neman halak sosai yaji zuciyarsa ta tsinke daman haka talakawa suke Shan wahala lallai Allah ya musu gata Koh Basu da mahaifi a raye sun samu gata zasuci zasu Sha sutura Mai kyau makwanci Mai kyau,amma ga wasu da iyayen ma suke nema wa kansu abinda zasu sa a bakin salati tagumi yayi Yana bin jama'an wajen da Ido daga dai ka gansa kaga yaron masu hali Wanda bai Saba da wajaje irin wannan ba.

Wayar sane tayi Kara hannu yasa a Aljuhu ya zaro wayar tasa kallon number yayi ganin new number yasa sa kin dagawa ya maida wayar aljuhu.

tsaki Lahab yaja ganin ya jerawa Rahab har 3 miss call Amma yaki dagawa"Kai Allah ya kyauta maka ace mutum bazai dauki Sabon layi ba Kamar wani dan film sai kuma ya tura Masa sako Kamar hauka"ka dau wayar Nine"

Jin Karan shigowar sako yasa Rahab budewa"ka dau wayar Nine"sosai ya kurawa message in Ido Yana nazari da Sauri Kuma ya Kira layin,dan murmushin Lahab yayi ganin Rahab ya kira, picking in call in yayi yasa a kunne.

Assalamu Alaikum,Rahab yace kamar Mai son tabbatar da abinda yake zargi,shuru Lahab yayi bai amsa ba,mikewa Rahab yayi Jin shuru ba'a amsa ba yasan babu Mai Masa wannan abin sai abokin haihuwar sa, Lahab nasan Kaine Kaine Dan Allah kayi magana Lahab?

"Rahab...... Lahab ya Kira sunan sa ta cikin wayan,jikin Rahab har rawa yake ya Soma magana,laaa dan uwa Kaine Ina ka shiga kasan tashin hankalin da ka samu a ciki kuwa kana Ina ne?

"Ina makama hospital"Lahab ya basa amsa.

What??? hospital fa kace Lahab meya faru dakai meya Kika hospital Kuma na shiga uku.

"Kaga ka kwantar da hankalin ka ba wani abuba ne tsagen Kashi na samu shekaran jiya"

Waro Ido Lahab yayi Wanda yasa mustapha dake gefe Yana gyaran mota ya taso ya taho gare sa,Jin Rahab na cewa,eehh kace tsagen Kashi ka samu innalilahi wa'inna'ilahu raji'un.

Katse wayar Lahab yayi Jin dogon salati da rahab ke zabgawa,ta bangaren rahab Kam tambayar sa mustapha ya Fara meke faruwa ne rahab meya samu Lahab in amma Ina lalubo number Mami yayi ya Kira tafiya ya tsoma Jin number nata na ringing,sai Kuma yaji ta d'auka sai muryar ta tana sallama........

🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*

Page 67&68

Mami dake zaune a tsakar compound na gidan ta ita da yaranta da mijinta Suna buga basketball gabaki dayansu sanye suke da sports wear nasu,yaranta da Alhaji ne suke ball itakam zaune take a gefe Kan cafet Inda ta shimfid'a tana amsa wayar Rahab,sai Yusuf dake zaune akan keken sa na yara,mikewa tsaye tayi cikin zumudi tace, na'am Rahab meka ce?ta bangaren Rahab sake maimaita mata yayi,Mami Lahab ya kirani.

Wai meya ce maka daya kira kan,Wai Ina yake?

Yana hospital Mami ya samu tsagan kashi ne.

Subhanallah tsagen Kashi Kuma garin yaya,tukunna ma kana Ina ne Kai in yanzun?

Ina garejin su mustapha ne yanzun Zan wuce asibitin.
Chapter 53 · 0% Book details