← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 122

Sashe 69

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da Sauri ta Mike tsaye ganin zai fita a dakin a shagwabe tace"toh Ni yaushe nace maka bana sonsa Kuma ai Vance a sauke sarti ba"?juyawa yayi ya kalleta cikin Serious yace"nifa na gama magana mundin sadeeq ya kirani yace Baki kirasa ba wallahi tallahi saina gayawa Abbu,Bai saurareta ba ya fita a dakin ya maida kofar ya rufe.

Washe gari Lahab ya d'au Kaya yakai dinkin duka kala ukun sa ya baiwa Adewale da Nabeel nasu Suma Suka Kai dinki don kowa da telan sa saboda yawan rikicin su da teloli daman Nabeel telan matane vana maza ba,zancen Ruky da Ahmad har manya sun shiga iyayen Ahmad sun kawo kudin goro naira dubu 50 cicib aka saka musu sarti Nan da wata biyu masu zuwa Nan take ahlin gidan su Ruky da Ahmad Suka Soma shirye shiryen biki,mubeena data tsinci zancen zuciyarta ne kawai Bata hadiye ta mutu ba amma har ciwo Saida ta kwanta na kwana biyu tsabar damuwa.

kuma rukyn ce ta tura Mata message ta what'sApp akan an saka ranar auren ya zancen anko da zasu fitar, Bata Mata reply ba sai ma blocked inta da tayi don ita gani tayi Kamar cin fuska Ruky ke Mata, daman sun riga sun kammala exam nasu Suna hutu yanzun.

*******************
Yau Alhamis saura kwana daya a Fara biki gidan su Lahab cike yake tam da jama'a bakin da sukazo aure abinka da d'aga bikin farko a family sosai Yan uwa ta kowani kusurwa Suka allara gida ya cika makil da Yan uwa Mata,Lahab ne ke shirga kayan sa a jaka zai bargidan saboda karancin dakuna da sukayi kadan dan su hudu suke kwana a dakin ga mata a sauran dakunann Koh bacci basa iyawa saban surutun jama'a daga asuba dana kuke kuken yara daman shi Anwar tuni ya koma gidan sa tare da zugan abokan sa don har sun Fara program na biki umaima ne sai gobe laraba za'ayi kamu.

daukar jakansa yayi Rahab dake zaune a gefe mikewa yayi ya dau NASA daya jima da hadawa,fita sukayi Suna ratsa jama'ar dake falon Suka fitowa tsakar gidan matane make tirim sai muneera dake zaune a gefe ga dukkan alamu kuka ta gama ga idanunta a kukkumbure,yafitota Lahab yayi da hannu ba tare daya tsayaba ya fita kofar gida.

Biyosu tayi har waje kallon ta Lahab yayi sannan ya tambaye ta meya faru wani kuka ta sake da karfi tana cewa"toh ba mamu bane ta aikeni tun safe Ina Kai katuna gidan kawayen ta shine fa ban samu lalle ba har Mai lallen ta tafi kafun na dawo, Kuma nacewa ummu ta ban kudi naje saloon Amin tace Wai bazata bayar ba.

"yanzun ke da girmanki Zaki tsaya kina kuka a gaban mutane amma wallahi kinji kunya duk yanzun ba wannan ba nawa ne kudin lallen"?cikin murna tace 3k ne uncle hannu Lahab yasa ya zaro 3k ya Mika Mata da murna ta karba tare da juyawa ta koma cikin gidan da Sauri zata dau mayafinta.

Gidan su ya jafar Lahab suka nufa don su nanne ma duk sun zo gidan su maza ne kadai a gidan ya jafar in, jakansa kawai Lahab ya aje Suka Shiga gari da Majid dinkin sa yaje ya karbo daga Nan Suka wuce cinima sai kusan 6 na yamma suka koma gida,abinci Suka samu an turo musu daga gidan biki Mai Rai da lafiya bayan sunyi dinner ne Majid ya kallli Lahab sannan yace"Lahab yaufa akwai casu"cikin rashin fahimtar Lahab yace kamar ya akwai casu ban gane ba"? murmushi Majid yayi ya mike tsaye tare da bude wardrobe nasa ya fito da wasu arnan jeans da longsleeve tare da wani jacket Mai uban kyau ya wurgawa Lahab a fuska Yana cemai"yau za'a Yi partyn ferry za'a kwana ana shashewa da Yan Mata Kai yau akwai casuuuuu

da Sauri Lahab yace"kana nufin yau za'a ayi partyn auren nata"?kwarai ma kuwa shiyasa na Mana shopping ba tare dana sanar da Kai ba gasu maza by 10 o'clock Muna hotel.

Mikewa tsaye Lahab yayi zai fita a dakin da Sauri Majid yace Ina Kuma zaka bayan nace maka karfe goma zamu fita yanzun Kuma Ina zaka"bazan Jima ba waje zanje Ina zuwa yanzun Nan,Yana karasa maganar ya bude kofa ya fita,da Sauri ya zaro wayar sa lalubo number Anwar yayi jikinsa har wani rawa rawa yake, ya Kara a kunne amma Harya tsinke Anwar bai d'auka ba Kara Kira yayi again har Saida Yama Anwar five miss call kafun yaji an d'au wayar abokin sane ya d'auka yace Yana wanka amma inya fito zai kirasa..........................................

🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*

Page 88&89

Komawa cikin gidan Lahab yayi ya samu har Majid ya shiga wanka, agogo ya kalla 8:30 ne na dare fitowa majid yayi Yana goge kansa yake cewa Lahab"kaga kayi Sauri wallahi tara yayi muna cikin gidan Nan fita zai Mana wuya kasan Daddy dasa Ido"?girgiza Kai kawai Lahab yayi ya bude bandakin ya Shiga Bai Jima ba ya fito Kaya ya sanya Suka fito har lokacin Anwar bai kirasa ba bini-bini sai ya duba wayar sa har Majid ya kasa hakuri ya tambaye sa meyake dubawa a wayan sane Wai"?akwai Wanda zai kirani ne Kuma har yanzun bai Kiraba"toh Kai ka kirasa Mana"na Kira baya d'auka ne"oh kawai Majid yace Yana tura gate in ya rufe tsallake titi sukayi,motar dake Parke a gefen titin Majid ya bude baya ya shiga shima Lahab budewa yayi ya shiga mutum biyu ne a ciki saurayin da ranan yazo ya dauke su sai wata budurwan dake zaune a gefen sa Tasha wanka cikin English wear.

tafiya suke Majid da abokan Shashancin sa sai Hira suke akan party yau da kayatuwar da zaiyi,wani kayatatten Hotel Lahab yaga sun nufa gate aka bude Suka danna hancin motarsu ciki,tun Kan su Isa parking space sukejin yanda kide-kide ke tashi Kamar ba dare ba ga matasa na shigowa da mota wasu da machine harda Wanda masu xuwa da kafa ma, parking sukayi suka sassauka dukansu nufar Hall in sukayi Lahab na binsu a baya har Suka danna ciki wa'iyyazu billah Mata da mazane shakude ansha wanka cikin banzan Kaya bama Kamar matan Wanda Rabin tsiraicin su ke waje,Zama su Lahab Sukayi don ita uwar gayyar Bata shigo ba.

Tsabar kid'an dake tashi shiya Hana Lahab Jin ringing in wayarsa dake Aljuhu,mikewa tsaye matasan sukayi suna ihu ganin shigowar farida cikin wasu shegun Kaya wando damamme sai riga da kwata kwatansa kasan kirjinta ga Rabin mamata ta sama a bude kannan yasha attachment ga eyelashes fuskar nan d'auke da makeover,tafiya suke ita da saurayinta da akayi birthday partynsa ranan hannun su cikin na juna da Sauri Lahab yasa hannun sa a Aljuhu ya zaro wayarsa sai a lokacin yaga miss call in Anwar,vedio ya Soma Mata har sukaje suka zauna har lokacin hannun su a cikin na juna sai wani lillikewa a jikin juna suke saving in vedio yayi ya mike da Sauri ya fita a Hall in.

Saida yayi nisa da hall in yanda zaiji abinda Anwar zaice Masa Kiran Anwar in yayi bayan yayi picking yace Masa"Lahab ka kirani d'azun Ina wanka dana fito muhsab yake cemin ka Kira Niko ban kiraka ba sai dazun baka d'auka ba ince dai lafiya"lafiya Anwar don Allah kana Ina"?

da mamaki Anwar yace"kace lafiya Kuma kana tambaya ta Inda nake"Kai dai ka fadamin kana Ina yanzun"?kallon agogo Anwar yayi yace Ina gidana"ok toh ayya in baka wani Abu zanzo akwai maganar da zanyi da Kai"dan shuru Anwar yayi sai Kuma yace"a daren nan zaka fito? kadai Bari gobe da safe kazo Mana"nidai dan Allah kace min eh babu ruwan ka da dare yayi"shikenan sai kazo,katse wayar sa Lahab yayi da Sauri ya nufi gate Keke ya tsayar tare da fada Masa unguwan da Anwar yake.

Sauka yayi a keken ya zare 500 ya Mika ma maikeken tare da bar Masa changen gate na gidan ya tura yaji a rufe hannu yasa ya ringa dukan gate in da karfin gaskiya don unguwan sabuwar unguwa ne ba mutane sosai,bude kofar akayi Anwar ne tsaye Yana kallon Lahab dake kallon sa shima"Wai da gaske zakazo Lahab"?

"Eh man Anwar da gaske nake yana maganar ya bi gefen Anwar ya shiga gidan Anwar ma bayan sa yabi,juyawa Lahab yayi ya dawo wajen gate in yasa hannu ya bude babban kofa ya wangale,zaro Ido Anwar yayi yace Wai kanka daya kuwa ana Neman karfe 10 kana wangale gate Aiko da Rana ba'a irin wangale wannan"Ina key motan ka"?shine tambayar da Lahab ya Masa"wani banzan kallo Anwar ya Masa yace kana nufin abinda ya kawoka kenan kazo ka amshi mota a daren nan toh wallahi badani ba bazaka jazamin masifa a wajen yayunka da Addayiya ba.

Had'a fuska Lahab yayi yace"ba Aron mota nazo ba zuwa nayi in d'auke ka muje wani wajen da zaka Sha mugun mamaki"hararan sa anwar yayi yace kaga nifa yanzun haka a kule nake fa"meya faru toh Lahab ya tambaye sa"d'an tsaki yaja sannan yace"waifa Saida muka gama arrangements na kome farida tace Wai bazatayi bidi'a a auren taba taki yarda da kamun da za'ayi gobe,gashi na tara friends.
Chapter 69 · 0% Book details