← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 122

Sashe 39

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mubeena hannu tasa ta share hawayen fuskarta insha Allah kuwa Ruky,sannan ta cigaba da Bata labarin,toh ganin sonsa sai dad'a ninkuwa yake gaba d'aya,bangaren Ahmad Shima Yana mutuwar Sona duk irin wulakancin da Zan Masa haka ya nace mini,d'aga karshe dana zauna nayi tunanin Mai zurfi saina gano lallai Ahmad najin zafin abinda nakeji taima ma Harya fini tunda Ni so kawai nake Ina hauka na Ni kadai shi kuwa ya furta Amma bai samu karbuwa ba?

Hakan ne yasa na basa dama,tun a farko da zancen aure yazo hakan yasa na Soma Masa kolo kolo nace saina gaba secondary bayan na gama ne ya sake tada maganar akan shi yanzun Yana son aure ne,Nan ma nace saina juna gaba da secondary saboda irin son da yake min yasasa amince wa duk da kullum Yana sanar dani mahaifiyar sa na nuna Masa bacin randa akan kin Saida maganan auren sa da baison Yi.

gashi yanzun na samu shiga college duk Kuma a cikin Aljuhunsa kome nawa shike min Kama d'aga kudin makaranta suturu duk shike saimin in Kika cire Inna da itama tanamin daidai gwargwado Amma Yan uwan babana dana mamata basu San Koh a sallah su saimin turmin zani ba.

Amma fa ki sani har gobe son lahab na d'awainiya dani Kuma ganin da nayi mundin na aure Ahmad shikenan Zan daina ganinsa,shine dalilin na na kasa baiwa Ahmad daman aure na har yanzun,ga Kuma Adewale daya bullo Wai Yana Sona Kuma na tabbatar Lahab zaisan maganan Nan saboda duk wani Abu da Ade zaiyi saiya shawarce Lahab sama da Nabeel Yaya zanyi Rukayya wallahi kirjina zai fashe zuciya ta ta kasa mini Adalci taso abinda bazata samu ba taso abinda zai Bata wahala wayyo Allah na,tana maganar tana kuka ita kanta Ruky Saida hawaye ya cika Mata a ido.

Handkerchief nata ta d'auka tasa a fuskar mubeena tana goge Mata hawaye kafun a hankali ta fara Mata magana,mubeena da ace Lahab da Adewale sun dai 25 ko 30 kinsan shawaran me Zan Baki?

girgiza Mata Kai mubeena tayi.

toh da sai nace Miki ki hakura da Lahab kiyi accepting na Adewale Koh don saboda soyayyar ki dake ransa zai Zama sular musulun tansa in Yana da rabon musulunci,Kinga kema kinyi jahadi,Amma Kinga Lahab baisan kinayi ba sannan baisan kina sonsa ba ga aminin sa na sonki kinsan da wuya ya amince,nidai Zan Baki shawara karki kuskura kiyi Wasa da daman ki sama sau daya yake zuwa wa mace na zaben mijin da taga dama tana so daga xaran shekaru sunja sai dai fa a koma Addu'a Allah ya bada mijin Koh ma yayane.

Kin gannin Nan mubeeena a shekarun baya ba irin sonda Nazeer Bai nuna mini ba yasoni Kamar hauka Amma kullum cikin wulakantashi nake yasha turo abokansa suzo su min magana akan irin tsananin son da yake min Amma na kekashe kasa naki kememen na nuna bana kaunar sa Amma Sam ba haka bane a cikin zuciyata Ina sonsa na Kuma kasa sanin me yasa bana nuna Masa son.

A karshe wata cousin nasa ya aura Wance ta fini kyau da kuruciya nayi bakin ciki nayi kunci,gashi yanzun Koh da kudi aka basa akace ya aureni bazai yarda ba gashi nima yanzun babu wani tsayaye gajiya da zaman gida yasa mahaifina sani a college,gashi haryau babu Wanda yake zuwa da sunan Sona a kofar gida sai dai samarin online.

Ki dubi malamar mu Nan ga ilimi ga kyau ga kudi Amma babu miji,sannan naji labarin ta a wajen aunty laure tace min lokacin da suke Yan Mata baiwar Allah Nan tayi farin jini Kamar na hauka kowa yazo tace sai boko ita bazatayi sure ba wasu sun yarda zasu aureta ta cigaba a gidan ta Amma taki,ki dubeta a yau ta haura 30 da wani Abu Amma babu miji.

don haka kima kanki karatun ta natsu tun duniya Bata Miki ba karkice Zaki biyewa kawa zuci ta kaiki ta baroki in ba rashin tunanin ba Ina ke Ina Lahab bare Ade Suna da abinda zasu rike kansune bare su rike ki? duk da Suna yaran masu kudi Koh dangin su zasuyi maraba dake?in Kuma kikace Zaki jirasa sai ya girma toh shi Kuma a lokacin zai zabo santaleliyar yarinya ya aura a barki da dana sani.

Dan Allah Rukayya ki dakata ya haka kina ta zancen lokaci lokaci karfa ki manta aure nufin Allah ne duk wayo Koh sakaci Koh dabara baya Hana aure baya saka aure don haka kawai in zaki bani shawara ki bani Kuma har yanzun akan bakana nake Ina son Lahab tamkar numfashina Kuma ba'a haifi Wance zata rabani dashi ba muddin Ina numfash.....kafun ta karasa sukaji faduwar mutum a bayansu ji kake timmmmmmm

******************
ta bangaren gidan su lahab daman tun da su muneera suka dawo makaranta ba Lahab muzammil ya tambaye su sukace yaje school Amma da aka tashi yabi su Nabeel Sam sunki fadawa kowa gaskiyar abinda ya faru.

principal na makarantan su Lahab ne ya Kira muzammil akan gobe Yana son ganin su shida kanin sa a school day safe,hakan ya tabbatar wa da muzammil lallai akwai babban abinda Suka aikata kenan tunda gashi har yamma lilis bai dawo gida ba.

Wasa wasa har mangariban ba Lahab hakan yasa hankalin Abbu tashi don yasan duk yawon Lahab baya dare a waje, waya ya d'auka ya Kira Mami Amma tace Lahab baya wajen ta,take ya tuna toh Koh gidan jafar yaje, muzammil ne ya d'aga waya ya kira ya jafar Kuma ya tabbatar Masa Lahab nagun su yaso a daren yaje ya dauko sa Amma jafar yace ya barsa ya kwana da safe yazo ya d'auke sa.

Washe gari misalin karfe 7 na safe a gidan jafar ya samesa amma Ina ya makara kafun yazu ma Lahab ya Kara gaba abin ya Kara kula muzammil sosai ya cika tim gashi yazo yaji labarin sunje party sun kwana a bakin Hashim don Hashim daman haushin su yakeji kaf familyn su su ukun Nan sun ishesu Amrat Majid Lahab,Kuma yanajin dadin yanda muzammil kecin ubansu sosai.

muzammil da kansa yaje har gidan Mami lokacin mijinta baima fita ba Suna karyawa a dinning da yaransu ya shigo Alhaji kawai ya gaishar don daman basa shiri da Mami sam,Amina Ina Lahab?

Wani kallo Mami ta Masa Jin tambayar da ya Mata yasa ta kin kallon sama, sai mijinta daya basa amsa, muzammil Lahab Bai zo ba Allah dai yasa lafiya Koh?

Juyawa yayi fuuuuuu ya fita a gidan mami kam da dogon tsaki ta rakasa dashi.

*************

A makaranta yau Nnenna tayi ta zuba Ido da tsammanin ganin Lahab Amma shuru babu shi babu alamar sa gashi itama yau ta zubo Masa abincin gidan su ta kawo da zimmar zaizo.

A office in principal Muzammil ne da pastor baban Adewale sai bappa Ado,gabaki dayan su babu Wanda yazo da students in nan guda uku hakan ya Kara kular da malaman a ganinsu tunda har su Lahab basa Jin maganar iyayen su babu amfanin a bar musu su Lahab a makarantan.

Principal ne ya mike Rai a bace yace tunda har abin ya koma haka Ni d'aga yau bana son ganin yaran Nan a cikin makarantan naaaaaaaa

**************
Lahab na kwance Yana sharara bacci bashi ya farka ba sai kusan 10:30 na safe Nan ma yunwa ce ta tashesa bawai don ya koshi da baccin bane a hankali ya mike zaune Mika yayi a tsaye tare da hautsana gashin kansa Mai yawa da laushi,agogon dake dakin ya kalla,ganin 10 yasan yanzun babu kowa a gidan sai Mami hakan yasa sa fitowa a dakin d'aga shi sai wando 3quiter dake jikinsa bude kofar yayi ya fito falon Yana kaikaya gashin kansa.

Mami dake zaune akan kujera tana feeding na yaron ta Mai kimanin shekara 1 fari Sol dashi kyakkyawa, Lahab ne koh dai ba Kai nake gani ba?

"Dan tsayawa yayi sai Kuma ya shagwabe fuska yace nine mami"

Kardai kace min a gidan Nan ka kwana na bunu yayan ka yazo neman ka nace baka Nan?

"Matsowa yayi kusa da mamin ganin kaninsa dake Kan cinya ya sake no-no Yana ihu Yana Mika Masa hannu Wai ya d'auke sa,sa hannu yayi ya dauki yaron ya wurgashi sama ya cabe ai a take ya shiga babbaka dariya har hakoransa guda biyu na kasa suka bayyana.

Murmushi Mami tayi,kasan Yusuf ya d'auka Rahab ne harda marmarin ka dagasa,don kai dai bantaba ganin ka d'auke sa ba da sunan Wasa.

"Aikam Naga alama Mami na Yana maganar Yana Kara wullah yaron sama.

Kai Lahab ban yarona karka zoka kadamin shi a banza,tace tana kwace yaron,dariya yayi kawai ya zauna akan daya d'aga cikin kujeran da Yusuf a hannunsa don yaki sakema mamin shi,itama kitchen ta nufa abinci ta Iba ta kawo wa yaron ta Kuma dan farinta Mafi soyuwa a ranta,sarkin rigima Lahab,Jan center table dake tsakiyar falon tayi zuwa kusa da kujerar da Lahab ke Kai ta aje masa.

gyara zama lahab yayi da Yusuf a kafan sa ya soma cin taliyar da mami ta aje masa, itama mamin zama tayi a gefen lahab suka soma hira na tsakanin d'a da uwa, wai lahab meka yiwa muxammil ne yazo yana nemanka a fusace, Lahab kai me kake so ka zamane da bazaka natsu kamar dan uwanka ba?ka duba yanda kowa ke maganar rashin jinka Sam banajin dadin abinda kake,ga taurin kai ga kin zuwa makaranta.

Kwarewa yayi garin zai baiwa Mami amsa da Sauri ta mike ta ibo masa ruwa da kanta ta kafa masa kofin a baki, hannun sa ya daga ya daura akan hannun nata yana sha,Yusuf dake kan cinyansa hannu yasa akan plate in taliyan ya dumbula wai zaici, dan janye bakinsa akan cup in lahab yayi ya kama hannun Yusuf in.

Zama mami tayi ta aje kofin ruwan hade dasa hannu ta karbi Yusuf in tana cewa lahab, maza kaci abincin saika amsa min meka yiwa muzammil.

dan shuru yayi sai kuma ya aje spoon in hannunsa kallon mamin yayi a hankali hace"mami nasan kaf duniya koh zan fadi Abu Aki gaskatawa indai gaskiya ne na tabbata zaki yarda dani koh"?

Kwarai kuwa Lahab, Mami tace

"toh mami na fada miki wani Abu"?

Eh fadamin naji Lahab.
Chapter 39 · 0% Book details