Sashe 17
Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alwala yayi suka zauna har aka kira sallah kafun yan gidan su suka fito tun daga nesa suke gulman lahab suna dariya ganinsa zaune samo samo kamar na Allah.
Ana idar da sallah suka shiga gidan da sauri lahab ya nufi kofar falo, tsawa muzammil ya daka masa, Lahab dawo nan ban sallame kaba?
Ba musu ya dawo ya tsaya a jikin motan kaman yanda yaga uncle in yayi, bude kofar motan Muxammil yayi ya shiga hade da basa umurni ya shiga.
Shiga yayi yaja motar suka nufi barin gidan, suna fita shagon aski suka nufa tunda lahab yaga anyi packing a bakin shagon yaji ransa yayi mummunan tashi ba shakka yau gashin da yake ta kashewa kudine za'a cire masa.
Fita yayi a motar yabi bayan muzammil cikin shagon, sun samu layi dole tasa suka zauna har akai isha'i, sukaje sallah a masallacin bakin shagon suka dawo kafun layi yazo kansu, nuna ma mai shagon kan lahab uncle yayi tare da ce masa ya aske kan kwalkwal a cire gemu.
Ihu lahab ya sake kamar an burma masa Allura"wallahi uncle ban yarba ba haka kawai a aske mini gashi kamar wani kafuri kwalkwal,kuma a cire mini gemu duka? ai gemun sunnah ne manzon Allah ne yace abar gemu.
Mikewa muzammil yayi lokacin da lahab ke surutun ji kawai yayi an wanke masa fuska da mari mai azaban zafi, dafe kuncin sa yayi yana mai duban uncle in nasa, da tsananin mamaki wai shi lahab har yanzun ake duka.
Kallon mai shagon yayi, aske masa kamar yanda nace, kallon uncle mai asken yayi pls oga kayi hakuri nad'an rage masa gashin sosai yayi daidai, gemun kuma a bar masa don Allah yace cikin d'ari-d'ari fahimtar da yayi ran sojane ya baci, ba tare da muzammil yayi magana ba ya basa izinin yayi hakan da hannu.
Zama Lahab yayi akan kujera har lokacin hannun sa dafe da kumatun sa, mai asken ya fara aikin sa.
Gashi mai tsawon nan duk an aske yayi daidai da kan nasa sai gyaran goshi da aka masa sosai askin ya masa kyau ba kad'an ba, muzammil dai sai kallon mai kaman harara yake masa.
Ana gama askin suka nufo gida, bayan sun tsaya uncle ya sai gasheshen kaza kusan biyar, suna isa gidan da sauri lahab ya balle marfin motar ya nufi kofar falo, kwala masa kira Muzammil yayi akan yazo ya d'auki laidan kazan ya shigar ciki, Amma lahab koh juyawa baiyi ba kuma sarai yasan uncle yasan yajisa.
Yana turo kofar falon, family ne zaune a tsakar falon ana ciye ciye harda Nazeefa matar muxammil da yaransu Tirmizi da islam, nufar kofar sashen su kawai yayi koh amsa wa matar muzammil dake masa magana baiyi ba, don daman ba shiri suke da ita ba, kamar yanda baya shiri da mijinta, dariya 'yan falon suka sake da karfi ganin kan lahab yau a aske sai gashi kad'an, don kan Rahab ma yafi nasa gashi.
Yana shiga d'akin akwatin sa ya d'auka ya aje a kasa tiles, ya fara iban kaya a wardrobe yana zubawa a ciki, don Wallahi gudu zaiyi ya koma wajen yaya jafar nasa haka kawai ya zauna wannan mugun soja ya kashesa a banza bai isa ba, don wallahi mami batace masa jika ka gani ba.
Turo kofar akayi da sauri ya soma boye kayan gudun kar wanda ya shigo yagani, amma ina kafun ma ya boye har an shigo, tsaki yayi ganin Rahab ne.
Da sauri ya karaso kusa dashi, Lahab lafiya yana ga kana had'a kaya a jaka?
Kallon biyun nasa yayi da kyau hatta magana in sunayi iri d'aya ne,"wallahi rahab bazan zauna a gidan nan ba, sai muzammil yabar sa ya wani ibo 'ya'yan sa da shegeyar matar san nan zasu zo su sani a gaba"
Yanzun lahab tafiya zakayi ka barni ni kadai kenan?
"Tafiya kam kaman nayi na gama babu uban da ya isa ya hanani"
Sai dai in bana gidan nan?sukaji magana daga bakin kofa, da sauri lahab ya sake kayan dake hannun sa ganin wanda ke tsaye a kofar ga dukan alamu ya jima a tsaye.............
✨Ruqeenjalal✨
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🤹🏿♂️ *ALKAWARIN MASOYA* 🤹🏻♀️
~ Na ~
🍃 *Rukayya Ibrahim*🍃
✨Tsokaci ALKAWARIN MASOYA na kudi ne gamai bukata naira 300 ne kacal ki tuntube ni ta layin nan whatsApp only 07044407979👌
Free page🤧
*EXQUISITE WRITER'S FARUM*
page2⃣3⃣&2⃣4⃣
Uncle nasu ne fuska ba walwala ya karaso tsakiyar d'akin, kallon lahab yayi da kyau, amma wallahi ka bani mamaki dom na damu da rayuwar ka kake zagar mini mata da shege ya?
Dam-dam haka yaji kirjinsa ya buga amma bai nuna ba"nifa bada kai nake ba wallahi uncle"
Kala baice masa ba illah nuni da yayiwa lahab da hannu akan ya wuce su fita a dakin, ba musu yayi gaba uncle na binsa a baya, daining zaka nufa.
Aiko daining in ya nufan yana isa ya nemi kujera yaja ya zauna hade da zuba tagumi ya kurawa waje d'aya ido.
Muneera!!! Muzammil ya kwala mata kira.
Yes uncle, tace tana mikewa ta taho wajen su da sauri ta tsaya tana kallon su.
Ki zuba masa abinci, da sauri ta d'auki plate ta zuba masa aje masa tayi a gaba shima uncle ta zuba masa nasa ta aje, shukali kawai lahab ya d'auka ya soma cin abinci duk wanda yaga fuskar sa yaga tsantsan bacin rai harda na sai dawa.
Addayiya dake zaune a falo tun d'azun sai kallon su take fuska a hade don gaskiya abin na muzammil yayi yawa taya zai sawa amanar ta a gaba haka?kuma babu halin magana.
Abinci ne dai sai da ya cinye tass, kafun ya barsa ya tashi mikewa yayi ya nufi dakin su yana shiga wanka yayi ya sanya kayan bacci zama yayi yana zullumin yanda zai bullowa lamarin uncle, take ya sake murmushi watoh yasan abinda zai kulla musu ai in sun san wata basu san wata ba.
Takardun Rahab ya d'auko yana dudubawa, sai kuma ya aje da sauri jin wayar sa na ring, d'auka yayi ya dube mai kiran nabeel ne ke kiran sa, picking yayi ya kara a kunnen sa.
"Hello nabeel"
Ta d'aya bangaren aka amsa masa, kai shegen ba nabeel bane .
Oh Adewale uban me kake da wayar nabeel kuma war haka"?
Yazo tayani kwana ne shine nace koh kaima zaka fatso mu kwana tare?
"Amma dai baka da hankali wallahi tunda nake da kai na taba yawon mangari ba"
Amma ai naga gidan mu zakazo koh?
"Toh Bazan zo ba "
Jin Amsar da lahab ya basa yasan lallai akwai matsala, guy lafiya kuwa koh file naka aka girgiza ne?
Harya bude baki zai sanar dashi muzammil yazo sai kuma yayi shuru, wallahi yanda yaji a jikinsa suma sai sunji a jikin su, shuru zaiyi Allah yasa gobe suyi gangancin xuwa gunsa suma su kwashe rabon su.
Misalin karfe 10 cif Rahab ya shigo d'akin tare da Tirmizi, kallon yaron Lahab yayi cikin zare ido yace"kai ina xaka ka shigo mana daki"?
Uncle a dakin ku zan kwana?
Ai jin amsar da tirmizi ya basa yasa sa mikewa da sauri, Allah sarki yaron na ganin haka dayake ya saba da gudu ya ruga ya nufi kofar d'akin cikin gudu ya bude kofa yafita.
Koma wa lahab yayi ya kwanta a shimfidar sa, Rahab kam girgixa kai kawai yayi baice kome ba gudun masifa don yasan yanzun D'an uwan nasa a cike yake dam jira kawai yake a tabosa ya sauke.
Wanka yayi yazo ya kwanta, amma baiyi bacci ba har kusan 11 ganin da gaske Lahab ba kwanciya zaiyi ba yasa Rahab tambayar sa, lahab bakajin bacci ne?
"Kaga malam kayi baccin ka kawai ni ba yanzun zan kwanta ba"
Kamar ya ba yanzun zaka kwanta ba, lahab bayan mun saba kwanciya tare kuma bama kai warhaka?
"Yau kuma nace banaji koh? ka rabu dani mana"
Kwanciya yayi tare da kashe wutar dakin, amma bai kwanta ba ganin lahab a xaune yana danna waya.
Har 12 yau basu kwanta ba tun lahab na d'aukar abin da wasa, Rahab keyi harfa ya fahimci da gaske yake, in bai kwanta ba shima baxai kwantan ba, kwanciya yayi hade da rufe jikinsa ya kashe wayar yayi likimo kamar yayi bacci, aiko ganin haka yasa Rahab shima gyara kwanciyar har bacci ya d'auke sa.
Misalin karshe 1 na dare wanda yayi daidai da nauyin baccin rahab, mikewa lahab yayi da sauri ya kunna wayar sa ya haska lahab don kara tabbatar wa yayi baccin da gaske.
Toilet ya nufa da sauri ya d'auko abubuwan aski, zama yayi a gefen Rahab daman shikam akwai nauyin bacci d'aga kansa yayi kad'an yasa clever yana aske masa gashin kai, sosai ya rage daidai irin nasa, gemun ma ya gyara sa sosai kamar yanda tasa yake yana gamawa da sauri ya maida kome toilet.
Jan Rahab yayi ya maida shi kan katifar sa ya lulube sa, ya d'auko jakan Rahab ya juye takandun sa a nasa boron, ya sanya nasa ana Rahab, sai kuma ya kakkabe katifar rahab ya kwanta akai.
***************
Nnenna ce zaune akan gado ta fifitar da kayan makarantan ta tasa a gaba tana kallo, koh abincin dare bata ciba ga gajiyar aiki da tasha, amma ta kasa bacci ji take kamar inta kwanta ta tashi da safe za'ace mafarki take.
Turo kofar akayi tare da Neman excuse, riganta ta d'auka da sauri ta saka jin muryar Abraham ne, tana sanyawa ta amsa masa ya shigo, kallon ta yayi ya sake kallon kayan sai kuma yayi murmushi yazo ya zauna a bakin gadon, beauty hope kayan sun burgeki?
Gyada kai tayi kawai tana tattara kayan tana ajewa a gefen gadon cikin zumudi shima baice kome ba, sai kallon ta yake sai kuma ya mike tsaye ganin ta sa hannu ta kashe wutar dakin ta kwanta ba tare da tayi masa magana ba, yana fita ta rufe kofar ta kwanta har bacci ya d'auke ta.
*****************
Misalin karfe 4 na asuba Muzammil ya farka kamar yanda ya saba, daman lokacin tashin sa kenan, mikewa yayi ya sanya kayan sport a jikin sa.