← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 122

Sashe 18

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D'akin su lahab ya nufa hannu yasa ya tura kofar kaman yanda ya tsammani basu rufe ba, shiga yayi ganin dakin da duhu yasa sa lalubar makunni ya kunna wutan d'akin, katifar Lahab ya nufa, yasa hannu ya d'ana masa duka a baya ji kake dom.

Innalilahi Rahab yace da sauri yana mikewa zaune cikin Al'ajabi yake bin uncle in nasu da ido, uncle lafiya?

Uwarka ne tashi ka sanya kaya mu fita jogging?

Ni kuma Uncle?

Eh koh akwai wanda nace wane bayan kai?

Amma uncle ai naga l.....

Bai bari ya karasa ba ya daka masa tsawa, mike nace koh jikin ka ya gaya maka.

Mikewa yayi cikin magagin bacci don shi baima fahimci katifar ba tasa bace da sauri ya nufi wardrop nasa, ya d'auko wando da riga na basketball ya sanya toilet ya shiga ya wanke bakin sa.

Fitowa yayi tare da marairaice murya Ayya uncle nifa banason jogging in nan Lahab nefa ke zuwa.

Zaro ido muzammil yayi yana tambayar Rahab, wani Lahab in bayan kai kuma, ni zaka mannawa hauka d'an iska?

Wallahi uncle bani bane ga lahab a kwance.

Make masa keya muzammil yayi, shige muje banason karajin wata magana a bakin ka, shasha sha kawai kullum musu a cikin ka, watoh na fita jogging kafun na dawo ka sa kafa kabar gidan koh? shige nace.

Tsamo-tsamo haka Rahab ya ringa binsa a baya ga sanyi kamar yayi me sai yanzun ya gano Abinda lahab ya masa especially daya taba kansa yaji ba gashi.

Lahab dake kwance yana jinsu jin sun fita yasa sa kyalkyalewa da dariya don daman tunda Uncle ya shigo yake matse dariyar karta fitoh,dawowa katifar sa yayi, gyara kwanciyar sa yayi yaci gaba da baccin sa.

Rahab kam a gaba Uncle ya sashi suka ringa zagaye tun daga unguwan su har round about suka sake bin bayan layin su basu suka gangaro gida ba sai 5 In mutum yaga Rahab sai ya tausaya masa gabaki d'aya ya shanja yayi wujiga-wujiga dashi.

Suna shiga gidan a lokacin jama'ar gidan keta Alwalan asuba,umurni ya bawa Rahab akan yaje yayi wanka, ya basa 5 minutes shap-shap yana maganar yana shigewa d'akin sa dake gidan.

Rahab na shiga dakin daidai lokacin Lahab ya fitoh toilet sanye da gajeren wando da gani Alwala ya d'auro, shakosa Rahab yayi cikin masifa yace, me yasa Lahab zaka aske mini gashin kai?meyasa zaka maidani shimfidar ka meyasa? yana maganar yana girgiza sa da karfi.

Turesa Lahab yayi cikin shekiyan ci yace"kowa kai yake so, kowa kai yake gani a matsayin nasa, ni babu mai sona a gidan nan hatta mamin mu kai tafiso dani, a wannan karon kaima zansa kaji yanda nake ji"

Nina hanaka ka zama na kirkine koh ninace karsu soka?tayama zasu soka a haka, yace yana nuna lahab da yatsa.

"Ok shikenan gani gaka kaima sai ka d'an d'ana abinda nake ji" ya karasa maganar cikin bagu ya taka har bakin katifar sa ya zauna ba tare daya saka kaya ba.

Da sauri Rahab yayi wanka ya fitoh jallabiya yasa fari sai hula shima fari silifas yasa a kafarsa ya fita a d'akin yabar Lahab har lokacin zaune akan katifar sa.

Ganin ya fita yasa lahab mikewa da sauri bude tasa wardrop in yayi ya zaro jallabiyar sa fara kal sabuwa irin na Rahab dan daman koda yaushe in za'a sai musu kaya iri d'aya ake saya, indai na sawa ne a baiwa kowa nasa, amma shi sai dai ya ajesu yasai irin nasa, saka jallabiyar yayi ya d'auki hula ya saka irin na Rahab ya sanya takalmin sa irin na d'an uwan nasa.

Murmushin mugunta yayi sai kuma da sauri ya fita a d'akin jin uncle na kwala masa kira a falo, fitowa yayi ya kalli Uncle in, "ah ah uncle barka da asuba Lahab fa ya fita masallaci yanzun nan"?

Ok toh muje Rahab na d'auka koh bai fita bane ai d'an banzan yaro sai nayi da gaske kafun nabar gidan nan, don naga su yaya sun zuba masa ido yana abinda yaga dama.

Da sauri lahab yace"wallahi kam uncle koh school baya zuwa"

Karka damu ai yau kafata kafarsa har makaranta d'an iska, sawa zanyi a shanja masa aji bazai zauna da abokan shashancin nan nasa ba.

"Hakan ma yayi uncle"ya karasa maganar daidai da isar su bakin masallaci, shiga sukayi aka tada sallah.

Ana idarwa suka fifito daga masallacin sai kuma su Abbu suka bisu da ido cikin mamaki ganin su yau sak iri d'aya, uncle ma zaro ido yayi kai menene haka yau kuka sanya kaya iri d'aya?sai kuma ya nuna rahab kai shige muje.

Zaro ido Rahab yayi wallahi uncle bani bane ga lahab nan, da sauri lahab ya nuna sa da ido, "kai lahab ka shiga taitayin ka banason iskanci fa, uban wa yasa kasa kaya irin nawa"

Kama baki Rahab yayi bangane ba bani na fara fita a d'akin na barka zaune ba?..

Kafun ma Lahab yayi magana da sauri Uncle yace d'an banza watoh kaika fara fita ka barsa a dakin kenan, dashi mukazo masallaci shige muje nace maka koh?

Ba yanda Rahab ya iyya haka yabi Uncle a baya yayin da Lahab yabi su Amma cikin natsuwa, kamar na Allah suka nufi babban falo yayin da uncle ya wuce da Rahab garden.

Suna shiga ya tsunguna kamar yanda Rahab keyi ya gaida Abbu sauran yaran suka gaggaishe sa gaida Addayiya yayi dasu mamu kafun ya wuce d'akin su, kwanciya yayi abinsa har bacci ya d'auke sa.

Da misalin karfe 7 Rahab ya shigo d'akin jikinsa duk tabo Alamu dai gyaran flowers sukayi kafa yasa da karfi ya tunkude Lahab dake kwance, mikewa yayi da sauri ya kalli Rahab sai kuma ya ruga da gudu yayi toilet saboda Agogon bango daya gani, wanka yayi ya fitoh yana kallon Rahab"sannu biyu na zoka wuce kaje kayi wanka,

Tsaki kawai Rahab yayi ya wuce toilet, mai Rahab ya shafa a jikinsa ya d'au uniform nasa ya saka, wando ne nevy blue sai riga fari tas mai dogon hannu, neck-tie nevy blue ya d'aura a wuyansa, socks ya d'auko baki ya zauna a bakin katifar sa ya sanya, sai boot nasa baki mai igiya ya d'aura a kafar sa, agogo ya d'aura shima baki sai jakan makarantan sa shima baki ya rataya turaren Rahab ya fesa da sauri ya ruga yayi waje jin motsen d'an uwan nasa na kokarin fitowa daga toilet.

Yana fita a d'akin daidai lokacin tirmizi ya fito a d'akin su uzaifa, harda uzaifan ma da sauri lahab ya kwala masa kira kamar yanda Rahab keyi"kai angon addayiya wannan wanka duka nata ne"?

Hade fuska tirmizi yayi aini uncle babu ruwa na da kai, tunda dai jiya kuka koreni a dakin ku?

"Ayya ango kayi hakuri kaji ni babu ruwana"

Amma ai uncle Lahab ne, meyasa baka masa magana ya barni ba kana gafa har son dukana yayi?

"Yi hakuri zo muje daining koh"koh bazaka daina fushi dani bane"?

Na d'aina uncle, yace yana kama hannun lahab suka fita a falon su zuwa babban falo, gabaki d'aya mutanen gidan ne zazzaune a daining inka cire matan gidan dake zaune a falo suna cin abinci, sai Rahab da uncle da basu fitoh ba, da sauri Lahab ya gaida Nabeela harda kiran ta da aunty nabeela, amsa masa tayi tana yabon hankalin sa.

Zama yayi akan kujera zulaihat ta zuba masa breakfast nasa ya soma ci duk a tsammanin su Rahab ne.

Uncle muzammil ne ya fitoh cikin shirin jamfa da riga harda hula, da sallama ya shigo falon Amsa masa akayi duka aka sake sabon gaggai sawa, bin falon yayi da kallo har idanun sa suka sauka akan lahab dake zaune hankalin sa kwance yake yagar kazar sa yana ci, kai Rahab ina d'an uwan naka.

"Wallahi uncle yana ciki taima baza shi makarantan bane"

Da sauri mamu tace, aiko wannan karamin aikin sa kenan daman ba zuwan yake ba aini nagode Allah na godewa muzammil.

Gyada kai muzammil yayi ya juya ya nufi kofar falon su Lahab, yana shiga lokacin Rahab ke sanya uniform nasa, ai uncle na zuwa ya rufesa da masifa yana tsaye har ya gama kimtsawa gabaki d'aya hawaye ya cika masa ido, shidai ya shiga uku ace wai jama'a bazasu iyya gane saba koh banban tasa da lahab.
.
A gaba Uncle yasa sa har falo zama sukayi akan kujera suka soma karyawa, kallon Lahab zulai tayi, uncle Rahab ina assigment ina.

Da sauri Rahab dake gefe yasa hannu a jakan sa zai d'auko takardan Zukaihat duk da bashi ta tambaya ba amma yasan shi ta baiwa takardan ta, yana sa hannu kawai yaga takardu da ba nasa ba budesu yayi dakyau koh shakka bayayi takardon lahab ne.

Mikewa yayi tsaye hade da kallon lahab dake mikawa zulai takardan ta, lahab wallahi wasan kwaikwayon nan ya isheni haka ka bani takardu na, koh na maka mugun duka agidan na.

"Kallon sa lahab yayi, wai menene haka lahab tun asuba saice mini kake wai nine kai menene riban ka tsakani da Allah fa"?

Wani irin fusata Rahab yayi da mugun haushi ya sake takardun makarantan sa ya nufi lahab, don yana ga duka kawai zai iyya masa yaji sanyi a ransa, kai mara kunya????yaji uncle yace cikin bacin rai, wallahi lahab ka kuskura ka tabasa saina mugu-mugun saba maka munafuki daman ka aske masa kaine don kayi basaja.?

Tsayawa kawai yayi yana bin kowa dake falon da kallo, sai kuma kawai ya sabi jakan nasa ya nufi barin kofar, kiransa Uncle yake amma yaki juyowa, da sauri muzammil ya bisa yana kokarin fita a falon ya fizgosa wanke masa fuska yayi da lafiyayun mari wanda yasa gaban Lahab dake zaune faduwa bai d'auka abin zaikai harga duka ba amma dai baice kome ba.

Kai karamin d'an iska ina maka magana kana tafiya saboda kaje ka hadu da yan iskan abokan nan naka ku shiga gari koh? toh yau kafata kafarka har makarantan naku abincin ma bazaka ciba.

Shuru kawai Rahab yayi yana dafe da kumatun sa yana kallon d'an uwansa yana mamakin Faruwar Al'amarin.

Suna tsaye har aka gama karyawa Uncle ya durasu a mota dukan su rahab ne lahab ne muneera da zulaihat, yaja motar suka nufi school nasu.....
Chapter 18 · 0% Book details