← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 122

Sashe 118

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da Sauri security Suka kamota sai kokuwa take dasu su barta ta Isa wajen Lahab sai cewa take ita fan nasa ne,so take suyi photo dan dakatawa Lahab yayi Jin Amon muryarta daya cika wajen muryar so familiar to him waro Ido yayi lokacin da Suka had'a Ido da yarinyar,nuna wa security yayi da hannu su barta ta karaso,Aiko Suna saketa da karfin cin tuwo ta ruga ta nufi wajensa shidai tsayawa yayi kawai Yana ganin ikon Allah a casa'in, kafarta kawai yake kallo dake cikin boot tana zuwa har zata rungumesa sai Kuma ta saya cikin fara'a tace"Ni Ina daga daga cikin fans naka ne Koh da yaushe Ina kwallon wasan ka ba Wanda yake wuceni dan Allah muyi hoto,gyada Mata Kai yayi da Sauri tasa hannu zata dau wayarta a Aljuhunta sai Kuma ta zaro Ido ganin Babu waya,Fara dube dube tayi Wanda hakan yasa Lahab yafito Ade dake tsaye nesa dasu tashi Ade yayi ya shigo wajen dan tsayawa yayi Yana bin yarinyar da Ido sai Kuma ya waro Idon ya kalli Lahab.

Zaiyi magana Lahab ya girgiza Masa kai hannu kawai yasa ya amshi bag NASA budewa yayi yadau wayarsa ya Mika Mata gashi toh ki dau hoton da wayata in yaso inkinga taki saiki tura ki bani tawa,da Sauri ta amshi wayar tsayawa tayi sai Kuma ya mikawa Ade tace"pls brother Amana hoto"amsar wayar Ade yayi Yana murmushi yayi musu kala biyu Suma Yan jarida sai daukar moments nasu suke,juyawa yarinyar tayi tabar filin,shikam Lahab na tsaye harta mule Masa.

***************
lahab na Shiga motar sa Adewale ma ya shigo harsunyi nisa Lahab ya amshi wayar Ade ya Kira wayar sa Saida yayi five miss call kafun ta d'auka cikin ihu take magana Hello bamai wayar bane tace cikin larabci"Hassan Lahab ne nace kin koma gidane ya maida Mata maganar da turanci"da Sauri yaji tace ba ma fito a cikin stadium in ba"ok toh ga munan a waje kizo"sai Kuma ya yanke wayar kallon driver yayi yace ya koma baya"shidai Ade Bai Kara yunkurin magana ba.

Aiko tun daga nesa Suka hangota tana dube dube,tsayawa motar tayi a gabanta Dan ja baya tayi sai Kuma ta matso kusa da motar ganin Lahab a ciki kawai ta bude motar ta Shiga shima Lahab baice kala ba yace direban yaja,tafiya suke yarinya Koh a jikinta wayar sa dake hannun ta take daddan nawa saiji tayi sunyi parking kallon Inda suken tayi sai Kuma ta waro Ido cikin zazzakar muryarta tace"ah Ina ne Nan Kuma Nan fa ba gidan mu bane big brother"?kala baice Mata ba ya bude motar ya fita shima Ade budewa yayi ya fita itama budewa tayi da gudu ta nufi gate na gidan da niyar barin gidan da gudu Kamar giftawar Ido Lahab ya damkota kamo hannun nata yayi duka biyu,ihu tasa tana cewa ya saketa itakam gida zata koma daman ummen ta bata San ta fita ba ya rufa Mata asiri ta had'asa da Allah koh sauraronta baiyi ba fiiiiiiiiiiii ya jata tare da bude kofar falon ya turata ciki fuska Babu walwala.

Saura kad'an ta Fadi sai Kuma ta fashe da kuka ta zauna a kasa tana cewa"nifa fan's naka CE wallahi daman tunda Aunty Esha ta ganka a TV tace da gani Kai mugune Ashe shiyasa Al'ameen baya kaunar ka Kuma yace shi ba Fan's naka bane,baya sonka"shut up rufemin baki nonsense kawai"shine abinda Lahab yace Mata cikin tsawa Yana shigowa falon,Ade na bayan sa,kuka ta Kara fashewa dashi da karfi da Sauri Ade ya shigo falon Jin kalan kukan da take Kamar an yankata dagata yayi daga zaunen da take tana ihu duk ta cika gidan da kara......................

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*

Keee rufemin baki Koh yanzun na Saba Miki"? jiki na rawa ta rufe bakin Nata maida kofar falon yayi ya rufe da key kana ya matso kusa da su don har lokacin Ade na kusa da yarinyar fizge wayarsa yayi ya nufi daya daga cikin dakunan,mikewa Adewale yayi yabi Lahab cikin daki zaune ya samesa ya tallafe kansa"Lahab mekake ne haka"?uhmmm Adewale don Allah don annabi ka kalli shigen dake jikin yarinyar Nan ace yarinya tana by this age a barta babu suturan kirki haka mukayi da Labiba?don ita Bata sallah nace ta barmin yara haka kara zube ne"?

Waro Ido Ade yayi cikin mamaki yace"Wai Lahab ban gane ba daman kasan yarinyar ne Koh me"?wani banzan kallo ya maka Masa cikin haushi yace"yanzun Kai fisabililahi saina fada maka Kai daga ganin yarinyar Nan baka ga alama ba"cikin danne dariyan sa Ade yace"alaman me ranka ya dade"?tsaki kawai Lahab yayi ya mike ya fita a dakin yana Jin zancen da Adewale ke Masa Akan ya Kamata a maidata gida Kar hankalin iyayen ta ya tashi,shi kuma Lahab ya Kulla Niya a ransa sai uwarta ta duri ruwa yau,yana fita tsawa ya daka Mata hade da karbo abinci ya Mika Mata yace taci ba musu ta karba ta Kama ci da mamaki yace yanzun ci take bataji tsoron cin abin hannu mutane Koh Kuma damuwa na rashi komawa gida ba?abin haushi amsar da ta basa shine ai kwara ta mutu a koshe data mutu tana Jin yunwa.

Fita yayi Bai Jima ba ya dawo da Kaya dogon rigane na Arab gown sai hijab ya Bata yace ta canja na Jinkin taje tayi sallan mangariba, masallaci yaje ya dawo yace ta tashi tayi sallah a idon sa ya gani,tana kunkuni ta tashi sosai ya yaba da ibadar nata ajeta yayi ya zauna shima Yana cin abinci Yana Mata tambayoyi ta fannin addinin koma sosai yaga alamu yarinyar ta samu koyarwar addini,sunan ta ya tambaye ta Wai sunan ta "Meera Hassan Lahab Amma Sunana na gaskiya nazeefa Kuma in gaya maka saban sonka da nake har cewa ake Wai Muna Kama shiyasa nakewa yaran ajin mu karya nace Kai yayana ne"gyada Kai yayi yace meyasa bakice musu Ni Abien ki bane"?

Wani kallo ta Masa sai Kuma ta rufe fuska tana dariya hararanta yayi ba Wasa yace toh dariyan me kike Kuma ke kin sannni kuma"ah ah kawai dai dariya nake Taya zance wa kawaye na Kai abie nane D'an wannan dakai"ai gwara uncle Usman shidai Zan iya cewa babana"murmushi Ade daya karaso wajen yayi ya zauna kana ya jefo Mata tambaya"toh ke Ina baban ki tunda wannan abie ya Miki kadan"uhmmm babana dai Bayanan Koh rasuwa yayi Koh guduwa yayi Ni ban sani ba ummi batason mu Mata tambaya a kansa kullum ai tace Mana wata Rana zaizo Kuma haryau baizo ba"Aiko Kisha kuruminki yazo Kam"waro Ido tayi da kyau tacewa brother ka sanshi ne"?

Gyada Mata Kai yayi Nan fa tadi ya barke a tsakanin su shidai Lahab nasa Ido har kusan 11 na dare kafun Suka kwanta amma Lahab ya kasa bacci bini-bini saiya mike ya fita a dakinsa yaje ya leka yaga Koh tayi bacci gabaki d'aya gani yake Kamar inya kwanta zai farka yaga mafarki yake Koh ya tashi yaga ta gudu.

Washe gari da safe suna karyawa yarinya gabaki d'aya ta sake jikinta dasu Babu wani tsoro Koh kewan gida abin Yama Lahab ciwo gani yake kamar Nnenna bata Basu tarbiyar daya dace ba,mace ace tabar gidan su tun jiya amma Bata damu ba,Suna kammala karyawa Lahab ya tasata agaba Suka nufo gidan su Meera harda Adewale,tunda Suka nufo unguwan suke jinjina kudin da mamallakan gidajen kedashi wani hamshakin gida Suka nufa Wanda Meera ta nuna musu a matsayin gidan su gidane Mai kyaun gaskiya,horn Suka danna wani security yazo ya leka ganin Meera yasa shi saurin bude gate in Suka kusa Kai ciki.

Akallah gidane da za'a Kira unguwa guda Mai girman gaske dauke da part part masu zafi Kuma iri daya a kalla security dake kewaye da gidan sunfi hamsim ga police da Suka gani a gidan sai jama'ar dake tsattsaye Suna magana da police in sun Kai su Sha biyar gabaki dayan su Suka juyo Suna fuskan tan motar su Lahab bude motar Meera tayi da gudu tana Kiran ummi ta nufi wajen jama'ar,matar da Lahab ya gani a wajen meeting ita yaga ta Mike cikin tashin hankali fuska a kumbure alamun kuka Tasha bana Wasa ba ta nufi yarinyar da Sauri,yarinyar na Isa ta rungume ta fizgo yarinyar tayi ta wanketa da Mari Mai zafi ba Wasa a fuskar ta tana cewa zata kasheta ne tasan halinda ta sata a ciki yanzun inta Bata me zata cewa mahaifin.................makalewa sauran maganan yayi ganin Lahab da Ade da Suka sauko a motar.

Gabaki d'aya mutane tsakiyar gidan da mamaki suke kallon Lahab,maza samarin kam tuni Suka matso kusa Suna basa hannu, sake fuskar sa yayi ya duka har kasa yana gaida mutanen dake wajen,sai Kuma sukace ya shigo falo sai ayi magana a ciki,binsu yayi Suka shiga ciki zazzaune suke akan kujera Lahab Kam Yana zaune a kasa sai Deyana data shigo hannun ta damke cikin na Meera tazo zata giftasu kwala Mata Kira Jaddu(kakan Nnenna ta wajen uba) yayi yana cewa Ina zata tazo ta zauna maganar daya shafeta ne suje Ina bayin Allah Nan Suka same ta"girgiza Kai kawai tayi tabar wajen.

Shigowa wani kyakkyawan balarabe yayi fari tas dashi sak Deyana(Abbas Ali)Zama yayi Lahab ya Kara gaidashi da murmushi ya amsa kana yace Hassan Koh"ba mamaki Lahab ya amsa don yasan yanayin aikin sa shiyasa mutane ke yawan sanin sa"Masha Allah yace kana ya nuna Lahab wa Yan falon a hankali yace"wannann shine mahaifin Abulkhari da Meera"da Al'ajabi jama'ar falon Suka Soma mamaki Suna cewa daman dan wasan kwallon nageria da suke gani a TV kullum shine mahaifin su Abulkhari Ashe ba abanza Meera keson sa ba,sun Kuma nemi dalilin kin fada musu da ba'a Yi ba sai yanzun Suka sani, Kuma sunsha mamakin ganin dan 31 dauke da yara Yan 13 year's,ana tsaka da maida magana saiga wani babban mutum a kalla zaikai 40 hannun sa rike dana wani yaro fari kyakkyawa Kamar dai Meera sun shigo daga ganin su hankalin su ba'a kwance yake ba dukan su biyu.
Chapter 118 · 0% Book details