← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 122

Sashe 13

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shayibu na dawowa ya tawo mata da kyakyawar Albishir yau wuni yayi yana binciken gidan Coulis kuma ya samu a kasan GRA yake har kofar gidan yaje sai gobe in Allah ya kaimu zai kaita da safe.

Nnenna murna sosai tayi ba kad'an ba har Allah Allah take gari ya waye tabar gidan nan, da dare ma Albarkacin shayibu ta samu dan tuwo ta saka a bakinta.

***************
Lahab da jama'an gidan sune zaune a babban falon gidan kowa na sha'anin gaban sa, Lahab ne zaune yanacin Ferfesun kifi da tuwon gurka(akoro),a kwano d'aya shida Addayiya suke zaune a tsakar falo suna ci suna fad'a, wai Addayiya na shan miya Ah ah tana cin kifi da yawa.

Sai fad'a suke yayinda abbu ke zaune a kujera yana karanta jarida sauran matan hira suke yayinda Su Anwar ke zaune da laptop a hannu munira kam Assigment nasu suke, Umaimah ne ta kalli Abbu sai kuma ta marairaice murya, Abbu Na ayya nace ba?

Zare glass in idanunsa Abbu yayi yana kallon umaimah toh mamata menene fadi ina jinki?

Yauwa Abbu daman Ina son a bani kudi ne xanyi abu?

Wani kudi zai baki yar batalon uba, uwarki bazata baki kudin da zaki yiwa saurayin ki cefene ba sai ubanki ya baki tsabar makon uwarki, Addayiya tace cikin masifa.

Hade fuska umaimah tayi, toh Addayiya ina ruwanki nasa bakin ki a ciki ne?

Kul mamana banason haka yaushe kika fara zama mara kunya mamar tawa kike fadawa haka?

Shuru tai sai kuma ta mike cikin fusata tayi hanyar falon su.

Zo nan mamata?Abbu yace

Dawowa tayi ta tsaya a gefe, ki shiga falona akan center table akwai ATM nawa ki d'auka in Allah ya kaimu gobe lafiya sai driver yaje miki kasuwan don banason yawo.

Cikin murna tace thank you Abbu na.

Shima dariya kawai yayi, yana kallon Rahab dake ta fama da haddansa na Alkur'ani a gefe koh shiga sabgar su baiyi hankalin sa naga abinda yake.

Tsaki Addayiya tayi cikin fad'a fad'a tace kaidai ka jiyo umar da sakarwa y'ay'an ka kudi sakaka har Atn(ATM) kake basu su cire abinda sukaso batare da ka ka'ide musu ba.

Kiyi hakuri Addayiya Ummu tace yayinda Mamu ta hade fuska sosai jin yanda Addayiya keta zazzaga masifa, don an baiwa Umaimah card.

Kallon Lahab Addayiya tayi d'an kusan wa ka tashi ka karo mana miyan, duk kazo ka kanainaye mini abinci gashi duk ka cinye mini kifi kabar kayuka d'an kwad'ayi kawai.

"Wallahi bazan karo ba wani irin na cinye kifi?Ai naga dai Abincin gidan mune kene ma zan ma gori miji ya mutu anki a koma inda aka fitoh"

Nashiga uku nida gidan d'ana dan uwarka ina zanje kaida uwarka ta kasa zama daku tayi auren ta abinta, ta watsar daku badon niba ai da yanzun kun watse.

"Wallahi badai mu watse ba sai dai ki watse"

Ungo naka Lahab wallahi zanji maka tashi ka karo mata miyar, bana son shirme Abbu yace yana ma Lahab gargadi da yatsa, ba musu lahab ya mike da kwanon miya a hannu yana zuwa kitchen ya aje kwanon abinsa ya wuce sashen su bai karo miyar ba.

Daki ya wuce abinsa yayi wanka ya chanja kaya, ya kwanta wayan sa ya d'auka ya kunna data ya shiga groups nasu na whatsApp suna hira da Abokan sa, har kusan10:00 sai da Rahab ya shigo d'akin kafun ya kashe wayar suka kwanta tare kamar kullum.

Washe gari da safe yaran gidan gabaki d'ayan su sun tafi aiki wasu kuma sun tafi Office in aka cire Anwar da baiya zuwa saboda ciwon sa, Lahab ma tun safe daya karya ya fita bai dawo ba.

**************
Ta bangaren Nnenna ma da safe bayan ta gama aikace aikacen gidan tayi wanka tama yaran ma'u, suka tafi makaranta tana karyawa ta cicibi kulenta ita da shayibu suka fita a gidan.

Bakin titi suka nufa Nnenna na rike da laidan kayan ta, da Shayibu yasai mata jiya, Tare musu keke napep yayi suka shiga.

Kwatance yama mai keken har unguwan GRA daidai kofar wani gida mai kyau sosai, amma irin gidan nan na Christian ne ba'a kewaye flat in ba gashi gidane mai kyau gidan sama da kasa gashi yasha glass na Ameniun sai shuke-shuken flowers sai karafuna da aka kewaye gidan dashi, karnuka ne manya manya kwakwance a tsakar gidan wasu na shawage.

Nufo get in karfen dake rufe sukayi suna taba get in karnukan suka mike da gudu suka nufosu cikin haushi........

**************

Umaimah da kanta taje kasuwa tare da driver tayi sayayya sosai, saboda saurayin ta da zaizo yau tare da iyayen sa, za'azo tambayan Auren ta, amma sai gobe iyayen zasu shigo gidan don har bauchi suke kuma in suka iso a yau zasu sauka a hotel su huta sai gobe zasu shigo, Amma Angon yace mata zaizo wajen ta da yamma.

Sayayyya tayi sosai harda wanda gobe za'a dafa musu, ba ita ta dawo ba sai 11 tana, ta tsunduma akan girkin da kanta ba ita ta kammala ba sai la'asar, wanka tayi shafshaf ta zauna ta fara tsantsara kwalliya.

Lahab da suka fitoh yawo tun safe ga yunwa gidan su Adewale suka fara biyawa Amma basu shiga ciki ba gudun masifa don iyayen sa sun tsane su, gani suke duk taurin kan Adewale su lahab ke koya masa, Abinci ade yaje ibo musu Amma momin sa ta koro sa akan bazata basu ba har dashi ma baxaici ba.

gidan Inna suka biya Amma basu samu ba, karshe dai gidan su lahab suka nufo don lahab baida koh sisi a hannunsa bai fita da kudi ba bare su sai abinci, suma basu da koh sisi a hannu a waje suka tsaya shi kuma ya shige cikin gidan, yana shigowa direct kitchen ya nufa.

Kuloli ya gani a jere sai kamshi ke tashi bubude kulolin yayi Abinci ne mai kyau da kayatarwa a ciki, da sauri ya sabi babban kulan mai d'auke da Rice sai d'ayan kulan dake dauke da Soyayyen kaxa da miya.

D'aukar guda biyu yayi da sauri ya fita a kitchen in, nufar falo yayi zai fita sukayi kicibis da zulai, da sauri ta tsaya tana kallonsa sai kuma tace uncle kulanda ka d'aukan nan fa abincin Aunty umaimah ne tama Yaya sadeeq yau xaizo.

Hararan ta yayi cikin masifa yace "wallahi ki ban waje na wuce kona bangajeki yar banza mai gulman tsiya, a gidan uban wa sadeeq in ya zama yayan ki kalen dangi koh"ya karasa maganar da tureta sai da ta fadi akan 2 sita.

Ihu ta sake tana kwalama umaimah kira, wayyo Aunty ga uncle lahab ya d'aukar miki kulan Abincin yaya Sadeeq, mamu kuzo kuzo zai gudu.

Ai jin haka yasa umaimah rugowa a guje daman yanzun take kokarin fitowa ta tarbo sadeeq dake compound, ai da gudu ta kwala kara ta bude kofar da sauri, tana kiran mamu.

Jin muryar umaimah yasa Lahab rugawa a guje da kuloli a hannunsa yayi kofar gida yayinda Sadeeq ke jingine a jikin motar sa, da sauri ya tashi tsaye daga jinginar da yayi ganin mutum ya banbaro a guje yayi kofar get, sai kuma ya juya da sauri jin muryar wance ta bisan tana had'asa da Allah ya da...............

✨Ruqeenjalal✨

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🤹🏿‍♂️ *ALKAWARIN MASOYA* 🤹🏻‍♀️
~ Na ~

🍃 *Rukayya Ibrahim*🍃

Free page🤧

*EXQUISITE WRITER'S FARUM*

page1⃣9⃣&2⃣0⃣
Akan dan Allah ya dawo, Amma ina Lahab koh juyawa baiyi ba harya fita a get, yayinda Umaimah ke tsaye a bakin baranda kamar ta hadiye zuciya ta mutu,haka ta ringaji bare ma sai yanzun da taga sadeeq gabaki d'aya ta manta yana compound ta biyo lahab.

Murmushin dole ta kirkiro hade da karasa wa kusa dashi, tana tsunkuyar da kai suka gaisa irin na masoya tambayar ta yake mai ya had'ata da Rahab yau koh tsayawa baiyi sun gaisaba.

Cikin yake take ce masa su shiga ciki pls,bata basa amsa ba, ba musu yabi ta a baya hanyar da suka saba zama, watoh garden xama sukayi da sauri ta turawa Rahab dake cikin gida sako akan Lahab ya d'aukar mata abincin bako ya taimaka ya fita ya sayo mata shinkafa da miya da kaza a restaurant.

Yana dawowa aka juye a wani kulan, mai aiki takai musu garden, Amma cika kam Mamu da umaimah sun shaka, jira kawai yau mamu take Abbu ya dawo ayita ta kare ta gaji da hakuri da Halin Lahab.

Lahab yanda ya fitoh a guje haka su nabeel suka rufa masa baya don sun sam tabbas akwai abinda ya b'aro kenan shiyasa ba tambaya, gudu yake da kuloli suma suna binsa a baya har suka shari kwana, kafun Lahab ya tsaya aje kwanukan yayi yana maida numfashi.

Kai menene haka duk kabi ka d'aga mana hankali ka sakamu gudu kaman barayi?

kallon sa Lahab yayi sai kuma ya kyalkyale da dariya"aiko wallahi barayin ne don sato mana abincin umaimah nayi saurayin ta zaizo ta masa delicious"

Habba Lahab meyasa zaka d'aukar mata?kai shikenan kullum gidan ku ana case naka.

Tsaki lahab yayi yana bude kulan shinkafan yace"don Allah rufe mini baki munafuki in zakaci kazo kaci banason munafurci"

Zama koh sukayi a wajen ruwan fanfo suka tara suka wanke hannunsu, had'a miyar yayi a shinkafan ga kaji suka soma ci hankali kwance.

Abinci sukaci dayake ba kad'an bane har suka rage ga kaji duka, Almajirai Lahab ya gani a bakin titi ya kirasu ya juye musu sauran Abincin.

Kulan ya sab'a su Adewale suka rakasa har get na gidan su ya kwalama mai gadi kira.

yana fitowa ya basa kulan ya shigar cikin gida shikam baici ta shiga gida yanzun ba.

*****************
Nnenna bata gudu ba tsayawa kawai tayi tana kallon karnukan dake tinkaro ta yayinda shayibu ya ruga a guje ya koma kwanar layin ya tsaya yana kwalawa Nnenna kira akan ta gudu.

Kin gudun tayi ta tsaya don ita ba tsoron kare take ba sam, abune da sun riga sun saba dasu duk da wa'innan mazajen karen, ta fahimci suna da fad'a da zafin nama.
Chapter 13 · 0% Book details