← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 122

Sashe 54

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da Sauri Mami ta dakatar dashi,karka hau Keke ka jirani ganinan zuwa yanzun zanzo na d'auke ka a wajen karka tafi ka jirani bata jira Mai zaice ba ta katse wayar tare da nufar flat nasu,bata ma sanar da Alhaji ba dama hankalin su baya kanta kwata kwata Yana ga kwallo da suke bugawa.

tana shiga cikin falon sai Kuma ta tuna bara ta sanar da yayan su babba(Abbu) number sa ta Kira ta Kara a kunne Yana dagawa Suka gaisa tare da sanar dashi Lahab na asibiti shima sosai yanuna alhinin sa tare da cewa shima gashinan zuwa,wanka Mami tayi ta sauya Kaya daga wando da rigan jikinta zuwa atamfa riga da siket,hijab nata ta jawo ta rufa tare da d'aukar key in mota da Sauri ta fitoh,dai dai lokacin Alhaji sulaiman Suka sakaita da ball in Suna hutawa dukan su akan cafet Inda ta tashi,nufosu tayi tana magana,Abbin mahraz zani hospital yanzun yanzun Rahab ya kirani Lahab na asibiti ba lafiya?

Subhanallah meke damunsa haka mamin yara?ya tambaye ta.

Wallahi Wai ya samu tsagen Kashi bazai wuce a filin ball bane.

toh ai dakin tsaya kin jiramu saimu shiga mu kimtsa mu tafi duka da yaran mu duba jikin nasa?

ah ah bazan iyya jiranku ba kudaiyi hakuri in yaso kuje ku dubasa da yamma Koh da daddare bazan dawo da wuri ba mahraz ya dafa muku spaghetti tana basa amsan ta juya zata nufi parking space nasu,ihu Yusuf ya kurma ganin mamin sa da hijab Kuma ta nufi hanyar waje,kin sauraron sa tayi don tasan daga zaran ta fita a gidan zaiyi shuru ganin tane yasa yake kuka,Kinga dawo kizo ki d'auke sa don Naga kwanan Nan kin tsiri fita kina barin sa a gida Alhaji yace Yana mamakin irin sonda Amina kewa yaranta akan yaranta bata da kawaici especially tagwayen ta don sonda take musu Bata ma yaransa shi.

ba musu tabi umurnin mijinta dawowa tayi ta karbi Yusuf in tare da bude motarta ta shiga ciki aje Yusuf tayi a sit taja tabar gidan hanyar garejin su mustapha ta nufa.

tsaye yake a bakin titin garejin Yana bin mototin dake tahowa daga nesa yayin da mustapha ke zaune a cikin garejin nasu ya sauya Kaya daga na aiki zuwa Mai kyau shima zaibi Rahab asibitin su dubo Lahab,haka zalika shima ya Kira baban sa ya sanar dashi asibitin da Lahab ke.

tun daga nesa Rahab ya hango motan mamin sa fadada murmushin sa yayi Yana daga hannu Kamar wani Bako, murmushi mustapha yayi d'aga cikin garejin ya Masa magana,toh ka hango goggo Aminan kenan?gyada Masa Kai kawai Rahab yayi, parking Mami tayi da Sauri Rahab ya matsa kusa da motar ya bude gaba yadau Yusuf ya shiga ya zauna ya daurasa akan cinyarta Yana Masa Wasa mustapha ma ya bude bayan motar ya shiga rufewa yayi Mami taja motar.

Ina kwana Goggo Amina?

Lafiya mustapha ya aiki?

Mungode Allah,ya Bata amsa kallon Rahab tayi Kai Kuma bazaka gaidani bane Koh me?
murmushi yayi Kai Mami na wallahi zumudi ne kiyi hakuri Ina kwana?

Shuru tayi bata amsa ba shima bai sake cewa kome ba Suka cigaba da tafiya.

*****************
Abbu Suna gama waya da Mami ya mike yad'au Kaya ya sanya a jikinsa fita yayi a dakin tare da shiga dakin Addayiya da sallama,amsa Masa tayi bayan ya zauna yake sanar da ita Lahab na asibiti,sosai ta tsorata tana salati tare da daukar hijab nata have Sunnah tasa tare da gyele ta yafa a kafada tana Masa magana,tashi Maza umaru muje mu duba sa muga ya jikin nasa Allah sarki dan maraya Koh garin yaya hakan ya faru ne?

Abbu daya mike tsaye yace Mata,nima wallahi bansani ba shiyasa nake son naje naji yanzun-yanzun naji garin yaya,kinsan nima uwan nasu ce ta kirani tace min itama dan uwansa ne ya kirasa.

Muje-muje Maza muga ya jikin nasa fita sukayi babban falo yaran ne zaune da iyayen su mata dayake ranan hutune Kuma sunyi baccin su harsun gaji suka fiffito falo Suka zauna,da mamaki suke kallon Abbu da Addayiya ganin su cikin Shirin fita kasa hakuri mamu tayi ta tambaye Abbu,lafiya kuwa Abbu na ganku haka cikin Shirin fita?

Koh amsa Mata Abbu baiyi ba don har yanzun haushin ta yakeji na abinda ya faru jiya,Uzaifa ne ya Kara magana ganin baban nasu da Addayiya na kokarin fita a falon, Addayiya sai ina?

Sai uwarka Kai asuwa da zan fita kace Ina zani?

Haba Addayiya sofa nake nima na biku don nasan fita da Abbu Alkhari ne yayi Mata dadin baki don ta samu ta fad'a musu,Abbu Kam Harya fita a falon Addayiya ta washe baki,Kai Uzaifa Maza zo mu tafi dan albarka bappan ka Lahab ne Yana asibiti ba lafiya zamuje,ai Jin haka yasa muneera mikewa da Sauri daman akwai gyale a jikinta takalmi kawai ta d'auka tabi bayan Uzaifa dayabi Addayiya a baya da Sauri.

Mikewa umaima tayi da dankwali a hannunta zata dau hijab nata akan kujera da niyar binsu daka mata tsawa mamu tayi,uwar Y'an iyayi sai Kuma Ina Zaki?

Jiki a sanyaye tace,mamu Zan bisu muje duba Uncle ne?

Uban kine shi ba uncle ba Yar iska Mara zuciya watoh abinda uwarsa tamin jiya harkin manta Zaki bisu kuje toh babu Inda zaku daga ke har Anwar da Shareef in,tsaki ummu taja ta Mike ta shiga dakin ta tad'au mayafinta tazo ta wucesu a falon tabi bayan mijinta da yaranta tabar na mamu a falon Wanda kallo daya zaka musu kasan suna son zuwa babu yanda Suka iyya ne,munafukar banza zai Kare a tsuliyan ku keda yaran naki ai indai Amina ne Muna Nan dake a gidan Nan Zangan ku a Rana kina binta a gindi a gindi babu uwarda take tsinana Maki,ita dai ummu Koh takanta bata biba ta fitoh compound lokacin Abbu da su muneera duk sun cika motar sa harzasu fita a gate sai gata ta fito tana d'ago musu hannu tsaya sukayi ta bude gaba ganin uzaifa yasata rufewa ta bude baya tare da Zama kusa da Addayiya don muneera ce ta gefen kofa Addayiya a tsakiya itama ta zauna a gefen Addayiya Abbu yaja motar Suka bargidan.

********************
Adewale yau tunda ya tashi da safe bai Fara karyawa da kome ba sai da bala'in papan sa ta Inda yake shiga ba tanan yake fita ba daga yace Masa ya shirya zasu tafi Church,shine Adewale yace bazashi ba baijin dadi,shikenan papa ya Soma ruwan bala'i daman baison zuwa church yaran hausa people na zugasa yabar addinin sa,Jin abinda yace yasa Adewale kasa hakuri ya tamka Masa,haba papa wannan wani irin magana ne haka Ni tunda nake da abokai na basu taba zagin addinina ba Koh suce wani Abu a ciki ba daidai ba Koh na daina.

Rufemin baki Wawa kawai stupid kawai Wanda baisan ciwon kansa ba yanzun ace duk yaran Christian basu isheka abota ba saika had'a da Yan iskan yaran?

Komawa Ade yayi bakin gado ya zauna papa na tsaye Yana jaddada Masa ya tashi ya shirya amma Koh gixau baiyi ba hakan shiya Kara kular da papa Harya sashi mikewa ya fizgo Bell in Ade dake yashe a kasan d'akin ya nufesa ai da gudu Ade ya mike ya rufi kofar bayangida binsa papan yayi tsabar rudewa kasa bude kofar yayi ganin papa ya kusa kamasa yasa sa nufar kofar dakin da gudu ya bude ya falfala a guje yayi falo,maman sa ce dake kwashe kwanuka a dinning ta nufosa tana tambayar sa lafiya? tsayawa yayi ya tsoma magana idanunsa nakan kofar dakin sa ganin har lokacin papa bai fito bama,mama nifa kaina na ciwo bazan iyya zuwa church ba this week gaskiya?

uhmmm haba Ade Kai duk weekend saika kirkiro abinda zai hanaka zuwa church kafasan dole ran papan ka ya baci Yana matsayin pastor ace d'ansa guda bai zuwa church abin zai Zama abin magana Koh ana cewa kafi karfinsa hakan baida kyau ka tashi kaje ka shirya shap-shap kazo mu tafi?

Zama yayi akan kujeran ganin papa ya fitoh Yana maida numfashin gudun da yayi daga dakin Ade zuwa falon,nifa kaina ciwo yake fa mama?

duk naji amma ka tashi haka zaka daure mu tafi abinda by 12:00 ma zamu tashi.

Kai mama har 12:00 Ina zaune ai sai ciwon ya Karu,tsawa papa ya daka Masa ganin sai lallabasa mama take shi Kuma sai botsarewa yake,Ade Zan mugun Saba maka a gidan Nan fa wallahi yau Koh zaka mutu sai kaje church.

Mikewa maman nasa tayi ta kamo hannun sa ta nufi dakin sa dashi Bata tsaya ba har toilet ta shigar dashi kafun ta basa umurni babu Wasa a fuskar ta,kaga Ade kayi wankan Nan na baka 15 minutes ka shirya ka samemu a falo wallahi in ba haka ba Zan Saba maka kanason ka jawa mahaifinka hawan jini Koh?

Kaya ya Soma cirewa ba tare da yayi magana ba hakan ya nunawa maman tasa zaiyi wankan kenan,fita tayi taja Masa kofa,bayan yayi wankan ya shirya Saida ya bata lokaci sosai don mama kafarta uku a dakin sa kafun ta samu ta fitoh dashi,anan ma Saida akayi daru don Ade 3quiter yasa papa Kuma yace bazashi church Yana d'ansa da gajeren wando ba daker dai aka samu ya canja,mota papan ya fitar Suka shiga sai church.

**********************
Lahab na sauke wayar a kunnen sa Nnenna ya mikawa"gashi kema ki Kira gidan ku"yace Yana Kara Mika Mata.

Mikewa tayi ta matsa kusa da jakanta tana harhada kayanta da takardun ta tana basa amsa"ban haddace number kowa a gidan mu ba"

dan zare Ido yayi kafun ya sake tambayar ta cikin dariya"hhhh kina nufin kaf gidan ku babu wanda Kika haddace number sa"?

Wani harara ta maka Masa tana rufe zip na jakanta tare da matsowa kusa dashi tana Mika Masa hannu"ban wayar na maida Mata innazo fita akwai Kaya a garden basu bushe ba,Mika Mata wayar yayi tayi Kamar zata karba sai Kuma yayi baya da wayar tare da Kama hannunta ya rike Yana bin fuskarta da kallo ya Soma magana a hankali"tafiya zakiyi ki bar patient"

Fizge hannunta tayi,"toh ba ka Kira Yan gidanku ba me Kuma Zan tsaya Yi maka"?
Chapter 54 · 0% Book details