← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 122

Sashe 46

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***************
Nnenna na fita a bakin asbitin ta samu wani shagon Kaya shiga ciki tayi ta zabi riga da wando kala uku na Lahab sai itama ta dauko wando kala biyu da riga biyu sai vest ta saya Masa da boxes ita Kam bata samu vest na Mata ba towel ma duk ta saya mikawa Mai shagon ATM nasa tayi yasa a POS ya cire kudin sa wani shagon dake gefe ta shiga tasai maclen brush da soso harda sabulu da turare abinci Kam tama rasa wanne zata sai Masa wajen Mai shagon bakin asibitin taje ya had'a Mata shayi a flask Kofi biyu sai kwai daya soya Mata, tasai bread sai doya soyayye data musu takeAway,komawa cikin asibitin tayi hannunta Niki Niki da Kaya ta tura kofar dakin ta shiga kwance yake Kuma Sarai yaji shigowar ta amma bai wani motsa ba Yana kwance a yanda tabarsa,aje kayayyakin hannunta tayi tare da daukar laidan suturar da ta sai musu ta matsa bakin gadon"Lahab ga kayan na sai maka ka duba Koh ya maka"?

Kala baice Mata ba sai mikewa da yayi daga zaunen da yake sandal Nata yasa a kafarsa ganin haka yasa ta saurin dauko Sabon silifas Inda ta sayo ta aje a gaban sa,cire sandal in yayi yasa silifas in,mikewa yayi a hankali ga hannu an daure harda igiya aka daura Masa a wuya zuwa hannu saboda hannun kada ya ringa Lilo sauka yayi a gadon ya finciko laidan hannun nata da hannunsa Mai lafiyar wando ya d'auka da vest ya Kama hanyar toilet in da Sauri Nnenna ta kallesa sai Kuma tace"Amma dai ba wanka zakayi bako"?

Har lokacin baiyi Mata magana ba sai kokarin bude kofar da yake da hannun sa na hagu Yana jinta Sarai yaki tamkawa,"Lahab kasan ba'a wanka in aka samu rauni irin wannan Koh"?

Bauuuu kakeji ya maida kofar toilet in da karfi ya rufe shuru kawai Nnenna tayi takoma ta zauna sai Kuma ta Mike da Sauri Jin Karan faduwar a toilet tare da ihun mutumin nata.........

Page 57&58

da gudu ta shiga bandakin zaune ta gansa akan tiles kayan daya shigo dasu a watse a kasa tsayawa kawai Nnenna tayi tana kallon Lahab dan sauke ajiyar zuciya tayi ganin babu abinda ya samu hannun nasa dan ita tama tsorata ta d'auka Koh hannun ya samu matsala ne"menene ya faru kake ihu"?

dan dagowa yayi ya watsa Mata wani kallo cikin masifa-masifa yace"oho ban sani ba yanzun a yanda Kika gannin Nan Har kina tambayar meya faru? Koh ma meyafaru aikece sila".

Shuru kawai tayi bata kulasa ba har lokacin tana tsaye"bazaki kamani na tashi bane"?da mamaki take kallon sa Jin abinda ya fada Wai ta kamasa matsowa tayi a hankali ta duka a gabansa ta sanya gwuwuwinta a tiles in hannunta ta zura a hakarkarin sa a hankali,dan zabura yayi don wallahi sai yaji Kamar jakulkule ta Masa"ya haka malama Zaki wani ciccibeni Kamar Zaki d'aga dan yaye Kama min hannu zakiyi"Lahab yace cikin d'an rawa rawan murya don dan tabasa da tayi yanajin wani iri a tattare dashi.

Nnenna bata kulasa ba unexpectedly ta dagosa daga zaunen da karfin Allah,zaro Ido yayi"keee Wai Naman jaki kike cine Koh me mutum sai karfi Kamar shariya Kamar ba mace ba haba "

tura Lahab in tayi Kamar xai Fadi sai Kuma tasa hannu ta rikosa tare da pushing nasa ya zauna akan toilet sit,ba musu Shima Lahab in baiyi kokarin tashi ba sai hannun sa na hagu daya sa Yana kokarin cire vest in jikin sa amma ina ya kasa saboda hannun sa dole sai dai a yaga vest in"Wai tsayuwar me kike ne da bazaki taimake Ni ba Koh jira kike na Kwabe kayan nayi wanka a gaban ki"?Lahab ya karasa maganar yana hararanta.

Hhhh dariya Nnenna ta sake a karon farko shima yaga dariyar ta sosai dariyar ta Mata kyau ga wasu cute white teeth nata da suka bayyana,girgiza Kai tayi cikin dariya ta fizgo vest in jikinsa har sai da ya barke ihu lahab ya sake Yana ce Mata"Wai menene haka ke Baki da hankali ne ki natsu Mana"Amma Ina zare Masa yagegen vest in tayi Lahab Kam da hannu daya yake ta Kare jikinsa Yana daka Mata tsaka ganin tasa hannu ta Kwabe botul in wandon jikinsa tana kokarin zaresa d'aga waist nasa,jikinsa har wani irin rawa yake yasa hannun sa Mai lafiyar ya fizgota har Saida ta fado a kansa"wash yace Yana Kara sa hannu ya mannata a jikinsa sosai Yana wani irin sauke a jiyar zuciya akai akai.

Jinta a jikin namiji a karon farko a rayuwar ta mutumin da take sakewa dashi fiye da mahaifinta da ace wanine ya rungumetan Nan da sai wani ikon Allah badai Shiba,dan muskutawa tayi tana son tashi d'aga jikin sa Jin yanda gemun dake fuskarsa ke taba Mata wuya gata dama-dama akan kirjinsa Mai d'auke da kwantancen gashi baki duk da bamai yawa bane sosai amma ga dukkan alamu shekaru yake jira su dan Karu Shima ya Karu saboda kallo daya Zama ma Lahab kasan irin mutanen Nan ne masu halittan gashi da yawa a jiki"so kike kimin tsirara da gaske"?Lahab ya tambaye ta Yana kwantar da kansa a wuyanta.

Kokarin turesa take amma Ina ta kasa saboda da karfi sosai ya riketa,cusa hannunsa yayi ta wajen cikinta ya zagayo dashi bayan ta tare da rike waist nasa,ihu ta sake tana cewa ya sake ta ya saketa amma Lahab gam ya riketa sosai Yana dad'a mannata a jikinsa.

ganin da gaske bazai saketan ba yasata dan sake jikinta kadan a nasa tare da dago kanta ta kalli fuskar sa hannu ta d'aga a hankali ta shafa fuskar tasa da Sauri ya lumshe idanunsa Wanda tun dazon yake kanta,dan bude Ido yayi Yana kallonta itama kallon nasa take"yunwa nakeji"Lahab yace Yana Kara bin fuskarta da kallo.

Uhmmm kawai tayi ta lumshe idanunta kafun ta basa amsa"nida Kai wa aka rike?

"Ke kike rikeni"ya Kara amsa Mata Yana dan shashafa Mata waist,hannunta tasa akan nasa tana turewa"ka sakeni Mana sai kayi wankan kaci abinci kaji"?

Dan muskutawa yayi yace"so kike na sakeki watoh Kinga Banda hannu ki kwabemin Kaya Koh"?

"ah ah Wasa nake maka mezaisa na Kwabe maka Kaya a gabana Kuma ai saina makance"

Jin abinda tace yasa sa sa hakorin sa yadan ciji kafadarta da dan karfi"Jesus ka kasheni"tare da ture hannunsa ta sauka a jikinsa tana shashafa wajen tsungunawa tayi ta kwashe kayan daya shigo dashi bandakin suka zube a kasa ajewa tayi a bandakin cikin boket da Sauri ta bude kofar ta fita shikam da Ido ya bita Yana dan murmushi,bata jima ba sai gata ta dawo da wani Sabon wando da rigan harda towel ajewa tayi ta ciki ruwan dumi a boket in ta aje Masa a gabansa tare da daukar karamin towel tasa a cikin ruwan hade da bude sabulu ta aje Shima juyawa tayi zata bar wajen,hannunsa yasa da Sauri ya rike nata,tsayawa tayi bata juyo ta kallesa ba ganin hakan yasa sa Kwabe fuska"kizo ki Kama min wando ki cire wallahi kafar baya fita sai da laida"(kaji iskanci dazun da za'a cire mekace😏)

Juyawa tayi ta kalli kafar wandon ta sake kallon fuskarsa"Wai menene haka kike wani kallona toh ma waya raunanani ne ai kece don haka ki kula dani malama"kala batace ba Shima mikewa yayi ya zare wandon a kugunsa ya saukar kasa rumtsa Ido tayi da karfi ganin boxes nasa a waje ga cinyoyin sa masu tsoka gasu bakikkirin ga gashi a kwance akai"kijamin kafar wandon Mana hai"?

tsungunawa tayi ta kamo kafar Lahab in ta daura akan cinyarta kallon yatsotsin tayi gasu dogaye tsirara dasu ga kafar Mai tudu da nama Kamar kafar mata hannu tasa ta Kama wandon tana ja ja take da karfi amma Ina wandon pencil Kam yaki fita sam"Wai menene amfanin sayan wando Alhalin Kai Mai kudin baka huta ba ace ka sai wahala da kudin ka Wai da sunan gayu"Nnenna tace tana Jan wandon da karfin gaske Wanda har lahab dake zaune ya biyo wandonsa Suka zubu a kasa daga shi har Mai cire masan"innalilahi wa'inna'ilahu raji'un wayyo hannuna yace kamar irin ya bugen Nan cikin tashin hankali ta Mike tana dubasa"sannu sannu Lahab Inga hannu Jesus hannu Mai ciwo.

sassake jikinsa Lahab yayi yana wani irin narkewa Kamar maijin jiki,da Sauri Nnenna ta Mike ta nufi kofar"bara na Kira likita suzo su dubaka hannunka ya fame"kizo ki gyaramin jikina bazan iyya ba sai mu fita a bandakin kafun kikirasu"dakatawa tayi Jin abinda Lahab yace da Sauri ta dawo ta taimaka Masa ya tashi ya zauna bucket in ta jawo sai Kuma ta fita da Sauri ta dauko laida Baki da aka sa Mata su soson wankan a ciki ta dawo bandakin ta tsunguna a gaban Lahab ta sanyawa kafarsa a laidan kafun wandon ya fita aje wandon tayi a gefe ta tsoma hannunta a bucket In ta tsamo towel dake ciki ta matse sosai kafun ta sanya towel in a gadon bayan sa tana goga Masa lumshe Ido Lahab yayi,a sannu sannu tayi ta goge Masa jiki sai dai bata goge kafa ba iyya sama kawai ta wanke, hannu tasa ta lakace sabulu tana goga Masa a fuska a hankali gudun Kar ruwa ya taba Masa hannu har lokacin idanunsa a rufe Yana ji tana tattaba Masa gashin fuska wanke Masa fuskar tayi tasa towel ta goge Masa fuskar sosai take kallon fuskar NASA gashin gemunsa ya jike tare da sajensa ya wani irin kwantawa gwanin sha'awa.

Aje towel in tayi"ka karasa sauran da kanka Zan jira ka a waje kayi Sauri abincin na sanyi"ta fita a ban dakin ta barsa.

kallon abin wankan Lahab yayi sai Kuma ya cire gajeren wandon sa ya karasa wankan da kansa towel ya daura ya fitoh a bandakin,mikewa Nnenna tayi ta bude laidan kayan ta Mike Masa karba yayi ya koma bandakin ya sanya wando dogo na roba vest Kam bazai Shiga ba saboda yanayin hannunsa fitowa yayi ya aje rigan dake hannunsa ya zauna a bakin gado"meyasa baka saka rigan ba Koh vest"?sai naje na Kira Dr ya duba hannun tunda ka fame.
Chapter 46 · 0% Book details