← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 122

Sashe 113

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Toh Wai me yayi ne"?wannan Kuma sai kin biyomu zakuji"Kai officer dakata wani irin wulakanci ne wannan da baza'a Mana bayani ba toh wallahi Babu Mai tafiya dashi"muzammil yace don haryau Bai koma ba,gyada kai dayan yayi kana yace"yayi alwashi ga wani yaro Nabeel na ikirarin ganin bayan sa,kana case in kisan da aka taba shariya dashi ya taso sabo iyayen yaro sun daukaka Kara don haka zaku bamushi dole"kaga dakata officer wannan yaro Nabeel da ake magana kowa yasan Nabeel da Lahab haka zalika Lahab bazai taba cutar dashi ba zafin mutuwa ne yasashi furta wannan kalaman maganan case na Abraham Kuma yanzun baida isheshen lafiya so bazamu badashi ba har sai yaji sauki"

Mika musu hannu Lahab yayi baiyi magana ba tsawa Abbu ya buga Masa Yana cewa"Kai Lahab kanka daya kuwa koka haukace ne da zakayi surrender"dan Allah yaya kayi hakuri ku Bari su tafi Dani Kamar yanda doka ta umurta Kuma a shiga kotu na amince da duk wani hukunci da za'a yanke a kaina" Abbu ya wankesa da Mari daidai lokacin Mami ta shigo gidan don itama yanzun kullum cikin zuwa take saboda farin cikin d'anta,har cewa tayi ta yafe Masa duk lokacin da Allah ya bayyana yarinyar zata karbeta hannu bibbiyu,Kuma ta basa dama yanemeta,amma Lahab a lokacin da tayi maganan Nan Koh annuri bataga ya wanzu a fuskar Saba bare ya d'ago Kan nasa daga duke.

Karasowa tayi tana tambayar lafiya shikam Lahab gaba yayi yaje ya Shiga motar tasu aiko sunga hauka Mami bala'i babu Wanda batayi ba Amma Koh kulata basuyi ba haka Suka shiga Suka tafi da Lahab..

**************
Wata sabuwa inji dan caca,zance ya karasa gari akan abinda ya faru kowa zagin Nabeel ya Fara aka abinda ya aikata wasu Kuma Suna cewa ya musu daidai,Abbu yadau lauya akan case na Abraham zancen Nabeel an ajesa gefe dan karamine shikam,in an shiga shariya duk lokacin da akayi zaman kotu Lahab baya magana sai lauya yayi jawabi in ance hakane Koh ba haka ba anan zaice musu hakane babu Koh musu abinda ya Kara Kona ran family sa kenan don sun fahimci so yake ya mutu shima,Mami da Addayiya sunyi kuka harsun godewa Allah jarabawar da Allah ya jarabcesu kenan dashi a shekaran nan Suna Addu'an Allah ya Basu ikon cinyewa.

RANAN TONON ASIRI
Ayau akayi Zama na karshe Babu Wanda Bai hallanta a kotun Nan ba harda peace (Mai aikin su Nnenna da aka Kai prison)family Lahab danasu Nabeel ganasu Abraham Kai jama'a a kotu makil Adewale ne kawai Babu shi Inna sunzo da mubeena Kuma tasa Nabeel ya janye Karan daya daukaka Akan Lahab don shima yanzun yayi kudi sosai Wanda ba'a San daga Ina ba,jinsa yake daidai da uban kowa shiyasa Koh Zama aji ya gagaresa"badon ransa yaso ba ya janye sai don kuka da Inna ta sanya Masa tana cewa zata tattara kayanta ta gudu ta barsu kafun ya janye zancen aka Kama na Abraham kawai,an gama gabatar da shaidu da hujoji Kuma Lahab ya amsa laifinsa na cewa dasa hannun sa aka kashe Abraham kamar yanda ake zargi.

"Abisa duba da hujojin da lauyoyi Suka gabatar, da amsa laifinsa damai laifin yayi wannan kotu Mai adalci ta yankewa Hassan Al'hassan dogo Mai naira hukuncin........................................Ina daja ya Mai shariya"kattafanin kotun sukaji Amon muryar mutumin daya shigo cikin kotun ga Adewale na binsa a baya"mikewa tsaye Alhaji sulaiman yayi jikinsa na wani irin Bari sakamakon ganin Wanda ya shigo cikin kotun yace"kaiiii buba meya kawoka nan haka mukayi dakai baka tashi bayyana ba sai a irin wannan Rana tsawon shekarun nan..........................................

*Naga complain na mutane akan mutuwar Rahab Amma fa kuyi hakuri littafina na riga na tsarasa akan hakan ne,Kuma Inna bite na cire wannan bar wannan daga baya Zan rikice ne kawai in ban mantaba shekaran jiya nayita samun magana akan character in Lahab wasu sunce zasu bar karantawa saboda Babu Wanda Lahab yakejin tsoro kaza kaza kana jiya ance kunci zaima Lahab yawa* 🤧🤧🤧 *

*Kunga ai Inna sake nawa na Kama naku karshe nazo na makale a hanya Ina zare ido Daman shi rayuwa ba kome akeso ake samu ba Daman haka rayuwa take aka rasa uwa ma Kuma mutum ya hakura*

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*

Wani irin murmushi Lahab ya sake yana gyada Kai ganin Wanda ya Jima yanason gani ya bayyana a bayan Ade wato abokinsa Barrister khamal najib,tsawa alkali ya buga da guduman sa don da yawa sun mike tsaye cikin su harda ummu da Addayiya,natsuwa kotun ta danyi kad'an kafun sulaiman ya mike Wai hawan jininsa ya tashi zai koma gida hanasa fita akayi a ciki code in ganin Kamar akwai bayani a bakin Wanda ya shigon,Koh zaka sanar da kotu Kai wanene da Kuma dalilin shigowarsu a irin wannnan lokaci ana tsaka da Sharia"Zama Ade yayi mutumin da sulaiman ya Kira da buba sai Brr daya gabatar da kansa a matsayin lauya Mai zaman kansa Kuma mataimakin lauyan dake Kare Wanda ake zargi,kotu sosai yayi tsit sai ummu dake da zufa sai yanko Mata yake"Kara natsuwa khamal yayi ya gyara zaman rigansa kana ya nemi izinin Fara gabatar da hujojinsa na Kare Wanda ake tuhuma"an baka dama"shine abinda alkhali yace"nagode ya Mai shariya sai Kuma ya juya yace"Kiran buba yayi ya fito ya tsaya a inda masu bada shaida Koh masu laifi ke tsayuwa tambaya Brr ya Soma Masa Kamar haka"Malam Koh zaka iya sanar da kotu cikekken sunan ka"eh Sunana Adamu ja Amma anfi kirana da buba ja"Masha Allah Koh zaka sanar da kotu menene alakanka da family dogo Mai naira da Kuma son halartar shariya tayau daka nema"?

Kamar yanda nace Sunana bubaja Ni ainahin dan nijar ne kamar yanda kowa ya gani Ni buzune,Neman kudi ya kawomu NAGERIA nida iyalina,bamusan kowa a kasar Nan ba tunda mukazo wahala mukesha sai dai mu samu bayan shago Koh gida mu rabe mu zauna muna kwana Ni Kuma Ina Saida shayi.

A hakan wata Rana Allah ya hadani da Alhaji Alhassan Harya daukeni aikin gadi a gidan sa nida iyalina mun koma gidan sa da Zama Kuma Babu abinda Muka nema muka rasa rayuwa ta Mana dadi dayake matar Alhassan macece Mai fada Amma tana da kyauta hakan yasa Muka kashe zuciyar mu dagani har matata Muna cin harziki harda yaron mu.

Nafi shekara ishirin Ina gadi a gidan Alhaji hatta makarantan d'ana shike biya,mun Zama Kamar Yan uwa,yayansa sun giggirma har wasu sunyi aure.

Bayan wasu shekaru zuwa lokacin gidan ya Kara cika ga aure da Alhaji ya Kara ya auro Amina,tunda Alhaji ya auro Amina kullum sai sulaiman yazo kofar gate yayiita min magiya Akan na Kira Masa Amina Koh Kuma ga wasika na Kai Mata amma Koh daya ban amince ba duk yanda yayi ta hadani da Allah naki,ana haka sai kanwarsa ta Fara zuwa gida tana baiwa Amina wasika daga baya Allah ya tona asirin abin Alhaji ya ganosu shikenan sai yasa security a gidan tsaro ya ninka nada.

Shikenan tun daga lokacin bankara ganin sulaiman ba Ni harnama manta da labarin sa,kwasam wata rana saiga yarona ya shigo gidan da gudu ya Kama hannu na Dana mahaifiyarsa Muka nufi sashin mu don yanzun mun Jima da barin bakin gate,hankalin mu ya tashi da abinda ya sanar damu kwata kwata bamu taba kawo hakan a ran mu ba cameran daya dau kome ya bani kana yace in nunawa Alhaji,Kuma ya Kamata mu gudu mubar gidan don Sun gansa dumu dumu Yana musu vedio"shin yanzun kana tare da kemeran ne tsahon shekarun Nan Koh yaya Kuma ya Kamata kama kotu bayani dallah dallah suwa dan naka ya gani"?

Eh dama Yana karatun jarida ne da Alhaji yadau nauyin sa yace min wata Rana sun fito makaranta Suka biya gidan abokin su zai dubasa kutsam sai yaga Khadija(ummu)ta shiga wani gida dake unguwan shikuma yayi zaton Koh gidan Yan uwantane yace Bari ya shiga ciki ya gaidasu saiya bita cikin gidan Yana kokarin bude kofar dakin ya shiga sai ya Fara Jin magana na tashi Nan ya zagaya ta window yasa hannu ta baya ya bude labule wa'inda ya gani a ciki yasa sa daukar camera sa yayi record na kome Yana tsaka da daukane Mutumin ya gansa harma da matar suka bisa shine ya fito a cikin gidan.

A ranan yarona yabi ya rikice akan mubar gidan nace Masa Ni sai na nunawa Alhaji Kuma na Masa sallama bazaiyu nabar gidan baby sallama ba kuma in Muka koma nijar Banda sana'a Koh wani aiki Amma hakan yaron Nan yace sai dai mu tafi shi haka kawai yaji tsoron Zama a gombe,mahaifiyar sa tace ya shirya kayansa zata tafi dashi in yaso inya samu natsuwa sai su dawo in Kuma Basu dawo ba Nina bisu,haka Koh akayi a ranan Suka bar gidan,nayita jiran ganin fitowar Alhaji Amma bansamu ganawa dashi ba Ina zaune Khadija ta dawo tazo ta shiga gidan.

Washe gari abin mamaki saiga Alhaji ya tashi da ciwon kafa hankali na ya tashi naso naje na sanar dashi Amma Kuma saina kasa Koh shiga cikin falon gidan a hakan yayita ciwo wata da watan Ni duk lokacin da na yunkura Zan sanar dashi sai na kasa, har Allah ya dauke rayuwar sa, a Randa ya rasu na tattara kayana bamma kowa bankwana ba nabar gombe na koma kasarmu Amma abin ciwo iyalina Basu zo kauyen muba na tsorata sosai hakan yasa na dawo cikin gombe Babu irin yawo da banyi ba Amma bansame suba duk Inda nasan Zan gansu na duba Amma bangansu ba hakan yasa na Kama shago Ina xama a ciki Ina dan sana'a,maganan camera Kuma memory na saya Ina chanja record na vedio duk bayan shekara biyu duk abin kallo daya fito na yayi saina saya na tura a ciki na aje don nasan wata Rana xai min matukar amfani.
Chapter 113 · 0% Book details