← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 122

Sashe 89

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lahab bai koma gida ba sai kusan 10:30 na dare babu Wanda yace Masa kalallahu haka ya shiga ya kwanta,sannu sannu kwana nesa su Lahab harsun kammala exam nasu Suna jiran result har yau Lahab baije gidan su mubeena ba Kuma bai hadu da itaba haka zalika bai yarda yaje wajen Mami ba in ma yaji tazo baya fita nukuwa yake a daki harta tafi sosai yake Jin shakkar haduwar tasa da ita dan baida amsar da zai bata,duk lokacin da take son kallon Nnenna Yana rokon Ade ya d'auko Masa ita, in Kuma yaji Yana son Jin muryarta wayar goggoji yake Kira ta hadasu sosai soyayya Mai zafi da tsafta ya shiga tsakanin su daidai da rana daya Lahab bai tabajin dana sanin tarayyar su da Nnenna ba Yana sonta bana Wasa ba duk da kalaman soyayya har yanzun bai shiga tsakanin su ba Amma akace labarin zuciya a tambaye fuska.

Abbu ya kirasu yace su ukun Nan su fada Masa school Inda suke son shiga a abroad uzaifa ya kammala degree insa a gombe zai Kama Master's shima a abroad Abbu yace su nemi kasa d'aya takamemme, Rahab yace India shi Kuma uzaifa yace Canada shidai Lahab shuru yayi Yana jinsu Suna da CeCe kuce har Abbu ya gaji yace suyi applying na school biyu duk Wanda akayi accept nasa shiken,Aiko Lahab yaji dadin zabi biyun Nan duk da baiyi magana ba ya rasa ya zaiyi da ransa wallahi baison tafiya yabar Nnenna gashi result nasu yayi kyau gabaki dayan su harda Ade,wanka yayi ya fita a gidan directly gidan su Ade ya shiga da yake yau lahadi ne iyayen sa Suna church,zaune ya samu Ade a falo Yana karyawa Zama yayi Suka Soma magana"ah yanzun Lahab bakajin kome ne Wai kayi aure gidan ku basu sani ba Kuma Koh a jikinta"?

d'aga kafada Lahab yayi yace"nikam Koh a jikina wallahi yanzun ma duk ba wannan ne ya dameni ba"da mamaki Ade yace wata sabowa meya sameka Kuma"?badai Akan matsalar yarinyar Nan Bako?dariya Lahab yayi yace"wallahi kasamin Ido na rantse da Allah toh akanta ne"?hararansa Ade yayi yace zaka mutu akan ta wallahi"in mutun Mana Ina ruwan ka"babu ruwana Kam Lahab Ashe na manta"in serious Lahab yace"ya maganan makarantan mune Wani kasa ka zaba"?dan shuru Ade yayi sannan yace "Kai wanne kake so?na bar maka zabi "yace yana jiran yaji me Lahab zaice"tunani ya shiga kafun yace Ina son zuwa University of Canada Koh Kuma London a cikin biyun Nan nake son daya Rahab yace India uzaifa yace Canada zashi Ni Kuma banida burin tafiya school dasu dukansu biyu nafison na tafi da Nnenna abroad bana tunanin Zan iya barinta a kasar Nan bansan halinda zata shiga ba bayan babu Ni"wani banzan kallo Ade ya Masa kana yace kana nufin kacemin wai da yarinyar Nan zaka bar kasan Nan Ina ka samu kudin da zaka biya Mata kudin jirgima bare na tafiya"?

Balance Lahab yayi yace"wallahi Ni Karan kaina na rasa Ina Zan samu kudi ban damu da kudin kome ba irin jirgin da Zan biya Mata shine na yanke shawara Koh zanje na samu Abbu a cikin kudin gadona yaban million daya"da Sauri Ade ya mike cikin masifa yace amma wallahi da zakayi haka kaf duniya babu Wanda ya kaika rashin ta Ido, mutumin da tun kuna yara har kawo yau da kudinsa yake d'aukar d'awainiyar ka bazakaji kunyar tambayar sa gadonka a yanzun ba? wallahi kaban mamaki kabi a hankali Lahab kada makauniyar soyayya ta kaika ta baroka a banza"shuru Lahab yayi har Ade ya Gama masifar sa ya koma ya zauna Yana huci sanan yace toh Ade ya zanyi yanzun dan Allah dai?kawai ka barta anan mu tafi karatun mu shine kawai magana"amma Ade a halinda take cikin Nan tana bukatar kulawa na musamman duk da nasan goggoji zata riketa Amana harna dawo, amma duk da hakan ma gaskiya banjin Zan iyya barinta"da haushi Ade yace toh saikayita fama Allah ya baka sa'a sannan ya mike yabarwa Lahab falon gabaki daya,mikewa Lahab shima yayi ya wuce gida.

Washe garin da safe saiga Adewale yazo wajen Lahab shidai Lahab baice kome ba,wuri Ade ya nema ya zauna kafun yace"nama papa maganan Inda nake son karatu kasan abin mamaki ashe Wai yasa an Masa bincike anji xaku tafi India karatu shine yace na xabi Koh Ina amma Banda India"hhhh dariya kawai Lahab yayi yace shikenan saimu wuce London"gyada Kai Ade yayi yace gaskiya Lahab bai Kamata mu tafi mubar Nabeel ba kasan shi har jamb yayi baici ba kasan abin sa'a ne"d'aga kafad'a Lahab yayi irin I don't care innan yace,"kaga yanzun ta kaina nake bata wani Nabeel ba abinda muka Masa a baya Allah ya saka Mana amma yanzun bazan iya ba in kaga zaka iya Bismillah kayi"

Da lallama Ade yace,haba Lahab gaskiya hakan bai dace ba tare fa muka tashi Kuma kome muka saya sai mun raba tare,da masifa Lahab yace"Wai gidan uban wa Zan samu kudin da Zan biya Masa karatu a London Harya gama ne kanaga kudin da Zan biyawa matata ma bandashi kudin jirgi kawai"da mugun mamaki Ade ke kallon sa Yana mamakin Al'amarin Lahab Baki a ciki bako Jin kunya Wai matansa,ai sai yanzun na ganoka watoh tunda Nabeel yace ya tsani Nnenna Naga gabaki d'aya ka chanja Masa wallahi wata rana har tambaya ta yake Mini, Wai ya kasa gane kanka kwata-kwata yanzun baka shiga shirgin sa"tsaki Lahab yayi baice kome ba Ade ya Kara cewa"Wai Lahab nace Koh zaka ma Abbu magana Koh zai dau nauyin Nabeel kasan Ni Koh hauka nake bazan Fara gayawa papa haka ba,kaga inya yarda Ina da dan million daya a account nawa saina biya Masa Koh kudin flight ne"wani harara Lahab yake ma Ade cikin harzuka yace"Kai Ade kaje Kama Abbu da kanka karka sake cewa na roke kowa kudi babu ruwana an maidani wani dan iska kome Ni ai abbun yafini sanin abinda ya dace in yaga zai iya biyamar ya biyamasa in yaga bazai iya ba bazansa bakina ba"karshe dai haka Ade ya hakura da maganar Nabeel.

After few weeks Lahab ya samu gurbin karatu a London shida Ade amma ba tare da ya fadawa kowa ga kasar da yayi applying ba har Saida yaji Rahab nacewa Abbu zai musu visa kowa ya kawo passport NASA abin mamaki Bai gama kashe Yan gidan ba Saida Lahab yace shi a London ya samu makaranta da mamaki Rahab yace kana nufin ba India zamu ba kenan ranan na tambaye ka kace wajen zaka har uzaifa ya hakura shima ya nemi Nan?Lahab shuru yayi baiyi magana ba Abbu Kam sai kallon sa yake Ido cikin Ido da Sauri Lahab ya sunkuyar da Kai"kai dawa zaku London in"?Abbu da Adewale ne"gyada Kai Abbu yayi baice kome ba sai nuna Masa da yayi ya aje passport in,Aiko take Rahab ya dire yace shima sai London Saida Abbu ya nuna Masa jan Ido kafun ya hakura amma ya zage Lahab Kam iya zagi ya kirasa munafuki duka Lahab Bai kulasa ba dan yasan bai kyautawa dan uwan nasa ba dan tunda Suka tashi sutura wannan Rahab yafison yasa irin NASA shine ke kin yarda suyi anko haka ma makwanci da Lahab baya bacci sai ya Mannu dashi daga baya ne Lahab ya ringa gudun sa har Suka raba shimfida.

Alhamdulilah su Lahab visa insu ya fito saidai su Rahab zasu riga su Lahab tafiya tun saura sati su Rahab su tafi gabaki d'aya ya birkice yace ya fasa tafiyar shi bazai tafi yabar Lahab ba daker aka samu ya natsuwa amma haka kawai inya zauna sai kaga ya buga tagumi ya Fara tunani Wasa Wasa ya Soma ciwo yau ciwon Kai gobe zazzabi kullum Yana like da Lahab Dole aka d'aga tafiyar tasu har yaji sauki,yau saura kwana uku tafiyar su Rahab Lahab Kuma sai Nan da sati daya,wanka sukayi tun safe yau Kaya iri daya Lahab ya yarda Suka saka jamfa da wando yau harda hula,motar Shareef Lahab ya karya su uku harda uzaifa Suka shiga Suka Soma bin gidan Yan uwa Suna musu sallama, lokacin da sukaje gidan ya jafar 100k ya baiwa Koh wannen su nanne ma ta dan Basu wani Abu daga Nan gidana Anwar Suka biya sun samu Aisha na fama da laulayin ciki Anwar ma ya basu kudi har 30k Koh wanne suka Masa godiya daga Nan Suka ringa yawon sai kusan yamma Suka Isa gidan Mami.

tunda Suka shigo da Lahab ya gaidata Bata Kara bi ta kansa ba sai Hira take da uzaifa da Rahab sun dan Jima a gidan lokacin da sukazo tafiya, ta saidasu ciki ta shiga sai gata ta dawo da laida manya manya biyu ta mikawa uzaifa daya daya ta mikawa Rahab tana cewa zata zo ranan da zasu tafin insha Allah godiya Suka Mata sai Kuma Rahab ya kasa hakuri yace Mami Ina na Lahab wani mugun kallo data Masa Bai sake cewa kome ba Suka bar gidan haka Suka ringa yawon gidan Yan uwa sai goshin mangariba Suka nufo gida har sun wuce kofar su Nabeel da Sauri Rahab yace Lahab dan dakata Bara na shiga gidan Inna na Mata sallama rabona da gidan su bazan iya tunawa ba?ba musu Lahab ya tsaya dukansu Suka fito a motar cikin gidan Suka shiga da sallama.
Chapter 89 · 0% Book details