← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 122

Sashe 56

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abbu yaje office in likitan ya nemi sallama duk da Dr baiji dadin haka ba amma yanemi alfarman shi zaina zuwa duk safiya kafun ya fito clinic yazo ya dubasa afternoon zaizo Koh da evening,ba musu Abbu ya amince sanan aka sallame sa,dakin ya shigo yana cewa muneera ta hada kayan dakin zasu tafi,kallon ta Lahab Yaya yace"Kinga akwai garden a hospital Nan inkin fita akwai Kaya dake shanye guda biyu wando da riga na mata dana Maza sai abaya baki,kallon sa duka Yan dakin sukayi har Mami ta kasa hakuri harta tambaye sa,kayan mace Kuma meya hadaka da kayan Mata Kuma,shuru yayi bai bata amsa ba har muneera ta fita a dakin,turo kofar akayi nurse innan ce ta shigo wanda koh sunanta bai sani ba, gaida su Yan dakin tayi kafun ta kalli Lahab tace,Hassan ya jikin na....makalewa maganar yayi lokacin da Rahab ya fitoh daga toilet in da Sauri ta kallesa ta kalli Lahab,d'aga Mata gira Lahab yayi Yana murmushi,bude Baki tayi zatayi magana Lahab ya rigata da cewa"Hussain sunan sa"Hussainin ka?ta Kara tambayar da?

Zuwa Rahab yayi ya zauna kusa dashi baice ma nurse in kome ba sai Addayiya data nuna Mata mami"ga maman su Ni Kuma matar baban suce saida na tsufa mijina ya aureta ga y'ay'an su shararren dan kasuwane in gaya Miki yaran Nan tun Suna kanana Allah yama mahaifinau rasuwa Allah sarki,murmushi kawai nurse in tayi ta kalli Mami, gaskiya hajiya kin iyya haihuwa Allah ya rayasu nima kisani a Addu'a Allah ya ban tagwaye irin su masu Kama wallahi Suna ban sha'awa?

Insha Allah kawai Mami tace juyawa nurse in tayi tana kallon Lahab tare da tambayar sa jiki.

"da sauki sister amma sallame mu"zaro Ido tayi da mamaki tace,an sallame kafa kace Hassan?amsa ya bata"eh an sallameni za'a cigaba da dubani a gani,sai Kuma ya dau waya da abayan ta ya Mika Mata harda sallaya,gashi mungode sister Allah ya bar zumunci"hannu tasa ta amshi wayar tace,kabar sujud in da abayar na bar mata.

"Ah ah ki amsa sister ai ta riga ta tafi"da mamaki tace,ta tafi Kuma Hassan tafiya babu sallama? murmushi yayi ya shafa kansa a hankali yace,tafiyar ce tazo babu tsammani,Mika Masa wayarta tayi ungo kasamin layinta sai muyi zumunci,amsar wayar yayi yasa Mata layin sa don baisan me zaice Mata ba karbar wayar tayi ta musu sallama ta fita Y'an dakin Kam sai mamaki suke don su basu gane wa ake nufi ba Amma Basu ce kome ba,har bakin mota nurse da Dr Suka rakasu,kallon Abbu mami tayi tace,yayan su nace Koh Zan wuce da Lahab Ina kula dashi a wajena daidai yaji sauki?

Wani kallo Abbu ya Mata amma baice kome ba sai Addayiya ce tayi magana,lallai Amina Baki da mutunci harmu Zaki nunawa son d'a da iyya kula dashi watoh mu bazamu iyya ba kenan Koh me?toh bara na tuna Miki inkin manta tunda Kika yaye yaran Nan Kika dawo Mana dasu nake kuladasu dani da yarana sai yanzun Kinga ya samu matsalan Kashi Zaki wani jajubo jiki Wai a baki shi kiyi jinya toh baza'a bada ba,hannu tasa ta tura keyar Lahab da karfi tana cigaba da masifa,wuce muje bazaka bita ba Shi dayake binta yaje can yayita bin nata kaidai bazaka ba munafurcin banza da wofi, baki ummu dasu muneera Suka sake Suna kallon ikon Allah kasa hakuri Abbu yayi cikin alhini yace,haba Addayiya itace fa ta haifi abinta ta fimu iko da yaranta tana da ikon tafiya da Lahab ta kula da lafiyar sa don haka ki barsa ya bita.

tsayawa Addayiya tayi amma har lokacin bata sake Lahab ba saina rike Masa kafadu da tayi da kyau Kamar xa'a kwace ta a hannunta tace,wallahi bazai bita ba ai da mahaifinku zai bar duniya yasan da Amina a duniya ai yace Kai ya baiwa amanar y'ay'an sa ka kular Masa dasu, toh akan me zaka barsu a gidan uban wasu wallahi bazan bayar ba ai Ni da Y'ay'ana aka barwa yara ba wata b'akutuwa ba tana karasa maganar ta Kama marfin mota tana kiciniyar budewa amma saboda bala'i tama kasa budewar shidai Lahab baice kome ba Kuma bai tayata budewa ba sai da ummu ta bude Mata Suka shiga Mami Kam kala batace ba ta bude motar ta ta shiga ita dasu mustapha Suka bar asibitin.

Parking Abbu yayi Suka bubbude kofar motan Suka fiffito har lokacin Addayiya batayi shuru ba sai mita take,in ma bakin cikin kajin da za'a kakkawone take hassada tace zatayi jinyar Lahab, kashinsa da fitsarin sa lokacin da nake dawainiyar su Ina ita Aminar take da uwarta sai da yara Suka kawo Kai za'a nuna muna fin karfi,badai Wanda ya kulata shikaran kansa Lahab baice kome ba har Suka Shiga cikin gidan, ba kowa a falo har lokacin Addayiya na makale da kafadar sa,bude kofar dakinta tayi Suka shiga su Abbu Suka zauna a falo,Suna Shiga dakin da Sauri ta sake sa tasa hannu ta rufe kofar harda makulli bude wardrobe nata tayi ta Ciro Sabon zanin gado ta feffesa Masa turare ta yaye nakan gadon ta shimfida Sabbi tana chanja pillow tace,ai gwara na canja Kar azo dubaka aga zanin gadon ba yanda yake tana gama shimfidawa Lahab ya kwanta, sake share dakin tayi ta feffesa turare,matsowa tayi kusa da gadon tace,Kai lahabu Mai Zan dafa maka Naman kazane Koh ganda Koh kifi Zan maka kasan ance in mutum ya samu matsalan Kashi so ake a ringa dafa Masa nama Amma karfa kaci Kashi?

Shuru Lahab bai amsa Mata ba leka fuskar sa tayi taga yayi bacci fita tayi a dakin taja kofar ta rufe tare da nufar kitchen dake babban falo,har yamma mamu da yaranta basu shiga sun duba Lahab ba sai Anwar daya fake idanunta ya shigo ya duba Lahab in tare da Masa ya jiki yayi zaman sa a bakin gadon Yana daddanna wayar dake hannun sa jifa jifa Suna Hira da Anwar in,Addayiya ce tayi sallama tare da leko cikin dakin amma bata shigo ba,had'a Ido sukayi da Anwar sai Kuma ta had'a fuska tare da turo kofar ta shigo hannun ta d'auke da food flask Mai shegen kyau guda biyu ajewa tayi akan table dake dakin ta had'a rai ta zauna akan kujera tana hararan Anwar tace,Ni don Allah tunda mutum yazo dubiya Kam basai ya duba ya tafi ba me na Zama Kuma zai sawa mutane Ido aka abincin ma mutum bazaici ba sai an wani zuba Masa na mujiya salon ya kware,murmushi Anwar yayi ya mike tsaye yace,toh Addayiya basai kince na tafi bakison naci amincin da Kika Masa ba ai shikenan Yana maganar ya bude kofar ya fita,kallonta lahab yayi kafun yace"Wai ke Addayiya menene haka"?

Hararan sa tayi tana d'auko kulolin tana ajewa akan gadon tace,uwarka ce amsar da ta basa kenan tana bude kula babban tuwon shinkafa ne fari tass gashi ya dawo sosai laida biyu ta dauko ta bude tare da ajewa a plate in dake gefe karamin kulan ta bude lumshe Ido Lahab yayi,kazane tayi ferfesun sa sai kamshin citta da tafarnuwa yake zubawa tare da tsokokin a kwanon Miya,ta aje a tsakanin su tare da mikewa ta taro ruwa a roba ta Mika Masa,hannun sa yasa ya wanke a roban kafun taje ta zubar ta dawo ta zauna kusa dashi Suka Soma cin abinci hankalin su kwance.

mami na barin hospital in bata tsaya dasu mustapha ba duk da yaso su tsaya ya sauka amma Mami tace ah ah sai dai ya bita suje gidan ta,Suna shiga gidan dukan su suka sauki a motar sukayi cikin gidan zaune Alhaji yake da yaransa a falo Suna Wasa da sallama Mami ta shigo falon yaran na binta a baya gaggaisawa sukayi Rahab da mustapha Suka zazzauna gabaki d'aya Rahab so yake ya koma gidan su,amma ya rasa ta Yaya Yana son Zama da dan uwansa waje d'aya,hijab Mami ta cire tayi cikin kitchen Alhaji ma mikewa yayi yayi part nasa yabar su a falon mikewa Rahab yayi ya shiga kitchen in ya dauko musu kayan marmari ya dawo falon ya aje musu shida mustapha...

Abinci Mai Rai da lafiya Mami ta dafa miyan ganda ta dafa da tuwon rogo,tana gamawa tadau Sabon kulanta Mai kyau ta zuba abincin a ciki ta rufe ta dau sauran ta jera a falo,wanka tama yaranta Suka shirya tsab harda shi Alhaji Kiran sallan azahar da akai shiyasa sasu wucewa masallaci bayan sun dawo ne Suka zazzauna a dinning Sukayi lunch gabaki dayan su.

Bayan sun gama ci hijab Mami ta daukowa wasila da mufeeda Alhaji na rike da Yusuf sai mahzar dake d'auke da kulolin abincin da Mami tace ya dauko a kitchen,mota biyu Suka shiga d'ayan mami keja daya Kuma Alhaji Suka nufi gidan su Lahab.

************************
Adewale basu Suka dawo church ba sai kusan 12:30 Suna dawowa kwanciya Adewale yayi Yana maida numfashi don harga Allah ba lafiya bane dashi turo kofar mama tayi ta shigo dakin ganin sa a kwance yasa ta karasowa kusa dashi tasa hannu tana taba jikin sa tace,Wai Adewale bansan meke damun kaba jikinka zafi gashi yanzun kome sai kanayi a sabule what wrong with u?matsowa yayi ya daura kansa akan cinyarta hannu tasa ta shafa Kan nasa tace,Wai har yanzun dai akanta ne Koh Hala?uhmmm har yanzun mama bansan matsayina a gunta ba?

Murmushi tayi tace,in baka shawara son?gyada Mata Kai yayi baiyi magana b kara shafa kansa tayi ta soma magana,ur too young sosai yanzun ace ka Fara soyayya a dan wannan shekarun naka karatu ya dace kayi ka samu ka Zama cikekken mutum kafun ka Fara maganar mace?kaga yanzun zaka b'ata future naka ne a banza Kota amince da soyayyar ka auren ta zakayi?

d'ago kansa yayi ya kalleta yace,toh mama basai ta jirani na gaba makaranta ba sai muyi auren Koh Kuma keda papa kumin aure sai mu cigaba da rayuwa tare?

Dariya abin ya baiwa mama amma batace kome ba don tasan komame zatace bazai fahimce taba saboda so ya rufe Masa Ido ita Kuma bata San me zata ce Masa ba.
Chapter 56 · 0% Book details