Sashe 24
Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lahab dole nace haka kaga yarinyar ulcer ne ya kamata tana zama da yunwa, koh nace ana mata horo da yunwa don ba yanda za'ayi mutum najin yunwa yakicin abinci har ya masa illah haka, a kalla rabon ta da abinci Almost 24 hour's kenan, bataci kome a cikin taba kuma tana jin yuwa banda hakan ma, tana zama da yunwa sosai gashi ulcer ya mata mugun kamu.
Lahab kam"subhanallah kawai yace yana mamaki ace yarinya za'a iyya sata a school nasu amma ace a binda zataci ma y gagare ta gashi daga gani kaga yar manya ba wahalalliya bace.
"toh yanzun likita ya za'ayi principal yace min ya kira mom nata har yanzun batazo ba nima ina tantama anya a wajen iyayenta take kuwa"?
Will yanzun dai zata iyya farfado wa zuwa karfe 3 koh 4 so anason daga ta tashi in aka zare mata ruwa a samu a bata wani abun taci mai d'an ruwa ruwa bamai nauyi sosai ba, don hanjin nata ya murde dole sai an samu abu mai sauki-sauki an bata daidai yad'an warware.
Lahab dake sauraron sa yace "toh likita kamar me dame zan sai mata kake ga wanda ya dace taci"
Eh kaidai abinda baida nauyi sannan baida yaji baida sanyi kuma baida tsami zaka iyya bata.
Da sauri lahab ya mike ya fita a clinic in kama hanyar cafe yayi cikin hanzari jin ana kiran sallan azahar kawai saiya nufi masallaci Alwala ya tsunguna yake sai ga Rahab da mamaki yake kallon d'an uwan nasa har ya matsa kusa da shi, Lahab daman kana cikin school inne?
"Oho shine amsar daya basa, yamike yayi cikin masallaci a ciki ma ya hadu da nabeel amma kamar bai gansa ba, ana idar da sallah ya nufi cafe hannu yasa a Aljuhu zai taba wayan da sai yaji wayam"subhanallah da sauri ya nufi gona yana Allah-Allah kar wasu sunje wajen sun kwashe masa waya a kasa.
Aiko yayi sa'a kamar yanda yabar wayar haka ya dawo ya same sa harda jakan Nnenna da glass nata daya fadi, duk ya d'auko bakka jakan yayi yafi toh a wajen, direct cafe in ya wuce yana tura kofa suka had'a ido da Adewale dake zaune akan kujeran daining dake wajen shida nabeel, d'aga masa hannu kawai lahab yayi ya nufi wajen mai abincin.
Ordern ferfesun kaza yayi sai fruit salad da kwai dafefe a take Away duka tare da ruwan gora mara sanyi, sai kuma yayi ordern doya dafeffe da zaici da miyan kazan shima.
kudi ya biya ya karbi laidodin ga jakan makaranta a bayan sa, yazo zai fita a cafe in mikewa Adewale da Rahab sukayi sukabi bayan sa, da sauri suka tsaida shi suna tambayar sa lafiya laidodin hannunsa nan fa, ga jakan mata a kafad'ar sa bangaje su yayi ya wuce abinsa dukan su suka bisa da ido harya mule.
Yana isa clinic in, direct dakin da aka kwantar da ita ya nufa yana d'aga labule idadunsa suka sauka akan ta, ita kadaice a dakin tana kwance akan gado tana bacci an cire mata takalmin kafarta aka bar socks, rigan ma an zare mata na uniform daga ita sai vest gabaki d'aya gashin kanta a wargaje sai fuskar ta dayayi fayau fari tas.
A hankali ya karaso bakin gadon aje boron yayi a kasa sai abincin daya aje akan drower kusa da magangu nan ta, zuciyar sa na bugawa ganin ta a haka yasa sa d'aukar zanin gadon dake nade a gefe ya lulubawa kafafunta zuwa kirjinta ya kara gudun fankan sanin da yayi saboda zafine taima ba'a rufeta ba.
Zama yayi a gefe koh abincin ya kasa ci, bayan awa d'aya likita yazo ya kara dubata sannan ya cire mata laidan ruwan dake hannunta.
Sai kusan 4:30 har Lahab yaje sallan la'asar ya dawo ya zauna kafun nan Nnenna ta farka, Alhamdulilah tana farkawa bata farka da tari ba, a hankali ta bude idanunta tana yawo dasu asaman silif na dakin, ganin duhu-duhu take, hakan yasa ta taba idanunta taji ba glass da sauri ta fara yunkurin mikewa.
Lahab dake zaune ganin ta farka kuma tana son tashi yasa sa mikewa da sauri ya iso bakin gadon yana mata sannu cikin turanci.
Gyada kai kawai tayi bawai don tana kallon saba, harta mike zaune, yaye zanin gadon tayi ta zauna ta jingina da gini kafafunta na lilo a bakin gado, tare da dafe kirjinta jin har yanzun nauyi yake mata.
"Sannu ya jikin naki"
"A hankali a karon farko ta basa Amsa da sauki"
Allah kara sauki yace, yayin da ita kuma tayi shuru batace ameen ba don ba haka ta saba ba.
"Pls help me, ka bani glass nawa in yana kusa"
Glass in ya d'auka ya mika mata hannu tasa a hankali zata karba by mistake hannunta ya taba hannun nasa da sauri ya sake glass in jin wani bakon Al'amari mai kamar shock da special feeling.
Subhanalalh yace yana kallon glass in ganin fashewa yayi a tiles"am sorry wallahi glass in ya fashe fa"?
"What kana nufin kace min Goggles ina ya fashe kenan? Shika d'aine dani fa haka kakeso na ringa tafiya bana kallo sosai"
"Kiyi hakuri in aka sallame ki zan sai miki wani"
"Toh kai wanene bansan kaba sannan nan inane na ganne akan gado gashi ina jin warin asibiti"
"Asibiti na kawo ki baki da lafiya"
Shuru tayi tana tunanin lokacin da take gindin bishiya tana tari tadai san akwai mutum agun amma batasan wanene ba, kallon sa tayi duk da bata kallon nasa tass sai yama-yama"ayya jakana"?
"Karki damu jakanki na nan" ya karasa maganar da mika mata roban takeAway dake d'auke da ferfesun kaza.
Hannu tasa ta amshi roban da sauri kuma ta maida masa tare da girgiza masa kai idanun ta na zubar da hawaye.
Da mamaki lahab yace"menene tsoro kike zan cutar dake koh me"?
Ah ah banason wannan ne kawai tana maganar tana nuna kwanon dake hannunsa da yatsa.
"Ikon Allah bakin ce baki gani sosai ba? ya akai kika kare wa kwanon kallo har kikasan meke ciki"?
Ai ina da hanci kuma yanajin kamshi, ta basa amsa tana mamakin kanta da surutun da take, kamar ba Nnenna Obinna ba.
Aje roban yayi ya d'au na fruit salad ya mika mata da sauri ta karba ta soma sha a hankali bai wuce shukali uku tayi ba ta yamutsa fuska ta aje roban a gefe, shima bai tambaye taba illa bare kwai dafefen yayi kuda uku yasa a marfi ya aje mata a kan cinya.
Komawa yayi ya zauna jin yunwa na neman hallaka sa bude doyan yayi ya zuba miyar kazan a ciki yadau shukali ya soma ci.
Kukan kule da motsen da jakan Nnenna keye a kasan tiles ne ya basa mamaki, "ke menene a jakan nan naki"? Ya tambaye ta.
"Oh my god cat nawa ne a ciki"
Cat?yasake maimaita tambayar cikin mamaki yasa hannu ya bude zip na boron da sauri ya koma baya ganin kulentan nan haka kawai suna had'a ido yaji tsikar jikinsa na tashi gashi kulen shi sam baima masa kama da fuskan kulen gaskiya ba, ganin fuskar kamar zubin fuskar mutum.
Da sauri kulen yayi jump daga cikin jakan ya fitoh da gudu yayi kan kwanon abincin lahab baki yasa zai d'auki naman, cikin zafin nama lahab yasa kafa yayi shoot dashi sai da ya had'asa da jikin ginin d'akin, wani irin kara kulen ya sake kamar ba kukan dabba ba ya fade tim a kasa, a take yamike kwance kamar wanda yayi dogon suma.
Kara Nnenna ta sake tana kokarin sauka a gadon tana tambayar lahab meyake faruwa meya sami kiki.
Kin magana lahab yayi ya barta tayita zagayen dakin tana neman kulen amma bata gane inda yake ba, kuka ta sake da karfi wanda yasa Nurse's dake zaune a station nasu sukayi saurin shigowa dakin suna tambayar lafiya?
Itace ta basu amsa tana neman kulenta yayin da lahab ya koma yayi zaman sa yana cigaba da kallon abin al'ajabi koh yunwar da yake ji ma sai yaji bazai iyya cin abincin da kule yasa baki zaici ba.
Da mamaki likita ya shigo yana kallon ta lallai jikin mara lafiyar mu yayi kyau harma neman kule take, ita dai batace kome ba sai da nurse ta d'auko kulen ta mika mata mata, tattabasa tayi sai kuna ta kara fashewa da kuka jinsa a longobe kamar sumemme.
Lahab kam cikin jin haushi yace"Dr asallame mu kawai naga kamar taji sauki gashi yanzun kusan 5 ake nema na yamma "
Ah ah lahab jikin dai da saura ka bari na d'aura mata karamin ruwa bazai wuce 1 hour ba.
Ok kawai yace yana mikewa tsaye ya fita a dakin itama da taimakon nurse ta koma kan gado ta zauna, shinfid'a kulen tayi a gefe ta kwanta kusa da shi.
Lahab na fita shop yaje ya sai mata sabon glass,yana dawowa ruwan na karewa bata glass in yayi ba musu ta karba cikin murna ta sanya a idanunta tana masa godiya.
Sallamar su likita yayi lokacin 6 yayi na yamma ana ma shirin kiran mangariba gabaki d'aya hankalin lahab na gida yasan dai yau baisan wace karyar zai suburbud'a ba bare ma yanda ya ringa ganin call na jama'an gidan su, amma yayi biris bai d'auka ba harda na muzammil.
Rigan ta Nnenna ta saka tare da d'aukar kulenta lahab yad'au mata jakan suka fita a d'akin shidai sai binsa take da kallo, koh ba'a fad'a mata ba tasan musulmine, koh yaushe ana sanar dasu musulmai mugaye ne, amma ita mutum biyu ta hadu dasu masu kyawawan halayya suna taimakon ta.
Makarantan ba kowa shar kake ji sai maigadi hatta malamai babu.
Haka sukazo suka wuce suka fita get, tsayawa sukayi a bakin kwalta lahab ya tsaida keke, tambayar Nnenna yayi don shifa har yanzun bawai sanin sunan ta yayi ba,"baiwar Allah wai a wani unguwa kike ne"?
"Ka bar kudin ka kawai nagode zan iyya zuwa da kafa"
"Oh lallai ki tashi daga gadon asibiti kice wai zaki taka, bawai fa kinji garau bane Dr yace gobe ma zaki amshi ruwa"
"Nace ka bari zan iyya zuwa"
"Mtwss kinsan Allah kina bata mini rai ki shiga keke mu tafi"