Sashe 77
Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tana shigowa falon taga kulan abinci a aje budewa tayi taga Koh ci batayi ba sallama ta Soma Mata Amma shuru ba amsa bkin kofar taje ta tsaya tana Kiran Amina,Nishi dataji Yana tashi shiya mugun d'aga Mata hankali,haihuwane gadan gadan janta tayi sukayi bayan gida wahala iyya wahala Amina tajishi har Allah ya dauketa lafiya ta haife yaranta tagwaye kyawawa masu Kama da mahaifinsu sak hatta skin nasu Basu dau hasken taba.
Bayan badawiyya ta Gama kimtsa yaran kwantar dasu tayi ta taimakawa Amina tayi wanka bayan fita da tayi taje part nata ta daura ruwan zafi tazo ta kimtsa ta da yaranta,Allahu Akbar lokacin da badawiyya ta sanar da haihuwar Amina duk da Muzammil baya kaunar Koh ganin Mai Kama da Amina amma jini yafi ruwa kauri,Saida ya taka kafarsa har dakinta ya dau jariran sosai jikin familyn Alhassan yayi sanyi ganin yaranda Amina ta Haifa like father like son,anan take muzammil ya d'au yaran ya Kai har dakin mahaifin su,da hannu ya nunawa muzammil ya nuna Masa yaran, facing nasa yayi ya nuna Masa yaran a take hawaye ya cika Masa Ido,tare da Mika hannu daga kwance dayake ya karbi yaran ya kwantar dasu duka a kirjinsa,a hankali ya bude bakin sa ya Soma magana"muzammil kiramin Amina"da mugun mamaki muzammil ya mike Yana cewa"Abbi magana kake kaji sauki"?gyada Masa Kai Alhassan yayi da gudu muzammil ya fita Kiran Amina cikin gaggawa duk da Bata da karfin jiki Kuma hutu take bukata amma hakan bai hanata gaggawar mikewa zuwa Kiran mijinta ba.
Tunda ta shigo dakin ta fashe da kuka ganin yanda Alhassan ya koma in baka Masa kyakkyawan sani ba bazaka ganesa ba,daga tsaye da take yasa hannu ya rike nata tare da jawota kadan ta zauna a bakin gadon har lokacin yaransa na jikinsa sai bacci suke yatsan su a baki"Amina na gode da wannan kyautar da Allah ya Mana ke Kuma Kika Haifa mini, Amina Koh a yau na mutu Banda asara tunda har Kika haifamin yara a tsotsonki,Ina sonki Amina Allah ya Miki albarka ga yara Nan na musu huduba da Sunan Hassan da Hussain Kamar yanda nake nida dan uwana"Kuka ta fashe dashi tana rufe Baki sai Kuma ta zamo bakin gado ta Soma rukon sa gafaran abinda ta Masa, murmushi kawai yayi yace"Niya dace na nemi yafiyar ki Amina na cutar dake na aureki na dole badon ranki naso ba Baki tabamin wani Abu na bacin Rai na kwanta dashi ba ba tare da na yafe Miki ba Amina ki yafe min..........Bata Bari ya karasa ba ta rufe Masa Baki da hannu tana hawaye tace"babu abinda kamin bare ka nemi yafiyata Alhaji Allah ya baka lafiya"Ameen ya amsa Mata Yana lumshe idanunsa dake cike da hawaye.
Addayiya ne ta shigo dakin tare da Muzammil dasu Umar daman sumayya(goggon katsina) ma na gidan,karasowa sukayi Jin muzammil yace muzu Alhassan na magana Aiko gashi sun ganewa idanunsu Zama sukayi Suka kewaye sa saiga Hussain ya Shiga dakin shida matarsa Hawa Kan gadon yayi ya rike hannu dan uwan sa cikin tsananin tausayin sa,suke Masa sannu hannun dan uwansa ya Kara damkewa a nasa,a hankali alhussan yasa hannu ya d'aga yaran akan kirjinsa shima ya rikesu a hannun sa,gyara kwanciyar sa Al'hassan yayi ya Soma magana Kamar haka"Umar ya Kira sunan babban dansa da Sauri Umar ya matso kusa dashi hawaye na cika Masa Ido,nuna Masa jariran yayi yace"Umar Koh bayan Raina zanyi Alfahari dakai mundin karike min y'ay'ana ka Basu tarbiya ka kularmin dasu Kamar yanda kake kula da yaranka,gasunan Amana na bar maka"kuka Umar ya fashe dashi Yana cewa mahaifinsa bazai mutu ba insha Allah zai tashi da kansa zai kula da yaransa.
"Ah ah Umar banajin haka a jikina muzammil jafar inaso kumin alkawarin Koh babu Ni banason ku Ware yaran Nan a cikin ku Koh ku nuna masu banbanci, Alhussan ga Umar da kannen sa na barmaka ragamar kula dasu a hannunka ka zame musu uba tamkar kaika haifesu duk abinda kaga sunyi ba daidai ba ka sawatar musu,gabaki dayan ku Allah ya musu albarka duk abinda kuka min Wanda na sani da Wanda ban sani ba duk na yafe muku duniya da lahira yayana nima kuskuren dana muku kuyi hakuri..............Bai karasa ba sumayya tace"babu abinda ka Mana Abbi insha Allah babu abinda zai sameka, Addayiya Kam kuka take lokacin da taji mijinta na cewa ya yafe Mata duniya da lahira itama ta yafesa,sosai Alhassan ya karya musu da zuciya kuka Kam shi suke Alhussan kasa hakuri yayi har Saida ya zubada kwalla karban yaran Alhassan yayi daga hannu Hussain ya kwantar akan kirjinsa Suma yaran Koh kuka basuyi ba Suna bacci,shima baccine ya daukesa Yana kankame da yaran,ganin haka yasasu Fara fita dakin d'aya bayan d'aya Kama Amina badawiyya da sumayya sukayi Suka fitar da ita a dakin aka Kira likita har gida tazo ta dubata tare da daura Mata ruwa.
da misalin karfe 1 na rana Addayiya ce ta leko a Karo na uku tun baccin Alhaji da yaran Nan Bai farka ba har yanzun,Hassan(Lahab)ya farka sai kuka yake yasata shigowa hannu tasa a hankali zata dau yaron tana mamakin wani irin nauyin baccine ya d'auke mijinta yaro na sanyara kuka amma baiko motsa ba bayan Kuma tasan sa da yawan ji Koh bacci yake mutum ya shigo dakin sai ya farka, janye hassan(Lahab)daga jikinsa tayi sai taga hannun dayasa ya rungume yaron yayi baya ya sake Yana Lilo a Bakin gado waro Ido tayi jikinta na bari ta Soma maimaita kalmar innalilahi wa'inna'ilahu raji'un sai Kuma tasa hannu ta dau Hussain (Rahab) shima ta kwantar dasu a gefen gadon Aiko take ya farka suka Soma kuka su duka biyun a tare da Sauri tasa yatsanta biyu a bulin hancin Alhassan (mahaifinsu) sai Kuma ta sulale a kasa ta sake wani marayan kuka.
*********************
Allahi Akbar rayuwa kenan yaudai Alhaji Alhassan Muhammad dogo Mai naira ya zamo tarihi,Allah daya hallice abinsa yau ya dau kayansaAlhassan an kaisa gidan sa na gaske,mutuwar Nan tayi mugun dukan Amina ashe haka rayuwa take Koh baka kaunar mutum Randa aka waye gari babu shi sai kayi alhini bare ita dake kyautata masa sosai ta Shiga wani irin Hali na atausaya Mata,dole tasa inno zuwa akan zata tafi da ita kauye Amma Umar ya Hana yace ta zauna a dakin ta tayi wankan jego,Aiko dole tasa inno zama a gidan tana kula da 'yarta.
Amina ta Zama abin tausayi sosai tayi sanyi bana Wasa ba tayi nadamar abubuwan da tayi Masa a rayuwa,Allah sarki duk irin kiyayyar da aka nuna Mata a gidan Albarkacin y'ay'anta ta samu sassauci sosai suke nuna kaunar yaran nata bana Wasa ba,kullum matar Alhussan haka zatazo ta daukesu su wuni a part nata no-no kawai ke dawo dasu wajen uwar su.
Tunda Alhassan ya rasu shikenan lafiya tazamo sai a hankali a wajen dan uwan NASA sosai ya Soma ciwace ciwace na ba gaira babu dalili yaje asibiti likitoti sun gargadesa akan damuwar da yasawa ransa ya rage,Amina ta kammala jego cikin koshin lafiya Amma babu zacen barin gidan Umar yaki inno ta koma kauyen su,tabarta anan,shekaran Yaran d'aya Allah Yama Alhussan rasuwa,rasuwar da ya tada ciwon mutuwar Alhassan mutuwar ya zamo musu sabo fil,don shikadai ya rage musu suke kallo a matsayin uba,Amma ya Suka iyya babu Wanda yake ja da hukuncin ubangiji.
Bayan rasuwar Alhassan, badawiyya ta Soma laulayi Ashe rabo ya shiga duk tsawon shekarun Nan Bata taba koh batan wata ba,sai bana dahar sun cire tsammani Allah ya Bata taso ace kafun mijinta yabar duniya yaji wannan albishir amma harya bar duniya baisan da cikin ba......................
🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀
*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*
Page 98&99
Bayan rasuwar badawiyya Amina taso ta cigaba da shayar da yarda badawiyya ta Haifa ta rasu ta barta aka maida Mata sunan mahaifiyarta ana kiranta da Amrat,Amma su Yan uwan badawiyya sunki sun nuna Akan zasu rike yarinyar a wajen su Tasha Madara,Kuma ba musu aka barmusu yarinyar a wajen su.
Bayan Amina ta yaye yaran ta anan tace zata koma gidan su don rasuwar mijinta shekara biyu kenan,gadon su Lahab a kallah yakai million biyar biyar Koh wannen su ga gidaje biyu biyu da Suka tashi dashi,da gonaki,Amina an Bata kasonta Saidai na yaranta ta barma Umar a hannun sa,ya sanya Dana muzammil Yana juyawa a cikin kasuwancin sa kudin na dad'a habbaka,ta dau tata gadon ta ta koma garin su, y'ay'anta ta barsu a hannun Addayiya ita tacigaba da kular Mata dasu.
Hassan da Hussain wa'inda aka lakabawa Lahab da Rahab har sunan su na ainahi ya buya don kowa kunyan Kiran yake sunan iyayene,yaran sun tashi kowa da halin sa, Lahab yarone Mai hakuri ga Wasa ga saurin yafiya ga rawan Kai dogon hakuri farfar da mutane babu ruwan sa talaka Koh Mai kudi shikam duk daya suke a gunsa Amma akwai rigima da taurin kai,sabanin Rahab daya tashi da sanyin Hali amma akwai zuciya ga riko ga saurin fusata gashi d'an ba ruwana ne sai yaga dama yake shiga harkan mutane in baiga dama Amma akwai yawan gaisuwa kam, Lahab akwai Wasa fara'a rawan Kai hakan yasa yafi Rahab yawan jama'a da wuya kaje unguwan kace Lahab wani baice yasan Saba.
Amina na komawa garinsu Daman sulaiman ya kammala makarantan sa babu aiki haka yaci gaba da kiwo a kauyen su,zuwa lokacin ya hakura da zancen Amina Amma Bai Kara zancen aure ba dawowar Amina ita ta sake tada Sabon sonta a ransa,Suka cigaba da soyayyarsu suka daura daga inda suka saya.