Sashe 57
Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mikewa Adewale yayi ya shiga ban daki Bai jiba ba sosai ya fito ganin mama tabar dakin yasa sa daukar key in machine nasa ya bar gidan akan machine in roba-roba direct gidan su Nabeel ya nufa Harya share kwana sai Kuma ya tsaya ganin Shareef tsaye a bakin rumfar kayan marmari dake kusa da tsallaken layin su Yana sayan kankana,Jan Machine NASA yayi zuwa Inda Shareef in ke tsaye da sallama ya faka machine in hade da mikawa Shareef hannu,juyawa Shareef yayi ya kallesa sannan ya kalli hannun kin bawa Ade hannun sa yayi sai amsawar da yayi a gatseñe Yana kokarin barin wajen.
danne zuciyar sa Ade yayi yace,Shareef yakake?lafiya klau kawai yace Yana kokarin bude motarsa da Sauri Ade ya sauka a machine in ya nufesa yanace Masa,ayya nace Koh anji labarin Lahab Koh Inda yake?
shekeke Shareef ya tsaya sai Kuma ya bude motar ya shiga yaja kofa ya rufe kafun ya sauke glass yace ma Ade dake tsaye har lokacin Yana binsa da Ido,eh ya dawo Yana gida baida lafiya,da Sauri Ade ya matso kusa da glass in har Yana tuntube yace,ba lafiya meya samesa,oho kashin hannunsa ne ya tsage daga haka yaja motar da Sauri Ade ya matsa gudun karya taka masa kafa, machine nasa ya hau ya gangara gidan su Nabeel paka Machine in yayi a kofar gidan ya cire key tsayawa yayi a bakin kofar gidan Yana kwada sallama.
Nabeel dake Kan Keke sai dinki yake don yau tun da safe Banda sallah babu abinda ya dagasa akai sai cin abincin Rana da yayi ya samu ya dinka riga yanzun ma siket yake dinkawa yaji muryar Ade Yana sallama amsa Masa yayi,ka shigo Mana sai kace Bako,turo kofar gidan yayi ya shigo kansa a kasa,sai Kuma ya dago Kai da Sauri Jin Karan Keke da mamaki ganin Nabeel akai yace,yau wani Rana Nabeel dinkin wace Mai sa'a ce hake kake dinkawa?mtwsss kaga ga kujera zoka zauna bana son wani surutu gabaki d'aya mutane Basu da adalci gabaki d'aya kunsa min Ido,dariyan karfin hali Ade yayi ya juya kitchen Jin muryar Inna na Masa magana,ah ah wa nake gani Kamar bayarbe kwana biyu nace Koh Lagos kuka nufa ai?
Ah ah inna Ina Nan wallahi bandaiji Dadi bane sai yau ya gida?
Alhamdulilah Adewale ya jikin naka Ina labarin lahabu bawan Allah
Wallahi Inna nima yanzun Nan na hadu da dan yayan sa Shareef nake tambayar sa labarin sa yake cemin Wai an gansa Yana gida ya samu tsagin Kashi a hannu zaro ido Inna da Nabeel sukayi kafun suyi magana sukaji Karan Abu a bayan su gabaki dayansu suka juya mubeena ce ta fito wanka daure da zani a kirjin kanta da jikinta naaaaaa...........................
🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀
*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*
Page 71&72
Kwandon soso dake hannun tane ya Fadi dukansu kallonta sukayi, tana had'a Ido da Adewale da Sauri ta juya ta koma ban dakin tana tsaki batasan zata fitoh ta gansa ba da Bata fito a hakan ba,sunkuyar da Kai Adewale yayi Yana Jin abinda Inna ke cewa,kee mubeena kin haukace ne Koh me?Kai Kuma bayarbe garin Yaya abokin naku ya samu wannan rauni haka?
Wallahi Inna ban sani ba shiyasa ma na biyo tanan muje mu dubasa da Nabeel, Adewale yace Yana sauraron abinda Nabeel zaice, Ade mu Bari zuwa dare sai muje mu dubasa,da mamaki Inna tace wani irin a bari sai dare Nabeel meyasa baka da mutunci ne Lahab nefa baida lafiya kace sai dare zaku?Kai Inna sofa nake na gama dinka wannan kayan daman Mai kayan taban kudin dinkin rabi Inna Kai Mata sai taban sauran Kinga saimu samu mu sai Masa koda kaza ne.
Murmushi Adewale yayi yace,kaga Nabeel in zamuje mu dubasa muje mu dubasa maganar kaza Koh abinda zamu Kai wannan bazai hanamu zuwa ba kaga saimu koma da daren,gyada Kai Nabeel yayi yace shikenan muje in ba matsala. Sauka yayi akan keken NASA sukayiwa Inna sallama Suka fita a gidan Suna fita mubeena ta fito daga bayin fuska a hade tare da dukawa ta dau sosonta daya Fadi ta kalli Inna da har lokacin tana Kan taburma tace,nifa gaskiya Inna bana Jin dadin abinda yaron Nan yake Mana?da mamaki Inna tace ke mubeena meya Miki da har baki Jin dadi bansani ba Kuma Ni gani nayi yaron Nan baida matsala.
Murguda baki tayi tace nifa gaskiya Inna banson Yana shigowa gidan Nan Kai tsaye irin haka duk abinda zaiyi Koh yakeso ya tsaya a waje Nabeel in ya fita ya samesa acan Akan me zaina shiga haka Kai tsaye yanzun fa wanka na fitoh fa a haka dagani sai zani na gansa a tsakar gidan Nan hakan ya dace kenan Muna barin wannan arnen Yana Kare Mana.
Rike baki Inna tayi cikin mamaki tace,lallai baki da mutunci mubeena yaron Nan sama da shekara goma Yana zuwa gidan Nan sai yau kikasan ya Fara Kare Mana kaji Mara kunya?
Yanzun dai duk ba wannan ba Inna yaushe zamuje mu duba Lahab in,wani kallon mamaki Inna ta Mata tace,keee na hanaki zuwa ki dubasa ne Koh yanzun kikeso shiga ki kimtsa kizo ki wuce nidai sai gobe da safe zani,wucewa kawai mubeena tayi ta shiga daki batace kome ba.
********************
Bude kofar gate in Mai gadi yayi Alhaji sulaiman ya danna hancin motar sa zuwa cikin compound in na Mami na binsa a baya, parking sukayi gabaki dayan su suka fito,tsayawa Alhaji yayi da mustapha a parking space Mami da sauran yaran sukayi cikin gidan tura kofar Rahab yayi suka kusa Kai ciki,babu kowa a falon nufar kofar sashin su Lahab Sukayi har Mami zata bude kofar aka rigata uzaifa ne ya fitoh da fara'arsa ya Soma gaidata,amsa wa tayi tana tambayar sa jikin Lahab,ai Yana dakin Addayiya baya Nan ku Isa, kofar falon Addayiya Suka nufa tura kofar sukayi da sallama babu kowa a falo kofar dakin Suka nufa gabaki dayan su suka tsattsaya a kofar dakin Rahab yasa hannu Yana bubbugawa Yana kwada sallama, Addayiya dake zaune ana yagan kaza Jin ana bubbuga musu kofa kamar Kuma muryar Rahab yasa ta Fara masifa,Kai haba karka ballamin kofa Mana ka jira azo a bude maka banason gaggawa haba?mikewa tayi tana tsude hannu tazo ta bude kofar,waro Ido tayi sai Kuma ta washe baki tace,ah ah wa nake gani Kamar hajiya wasila?
Nine Addayiya Ina wuni?matsawa Addayiya tayi ba tare da ta amsa gaisuwar ba tace ku shigo Mana kin tsaya a tsaye,shigowar dukansu sukayi Suka zazzauna aje kulan mahraz yayi ya matso kusa da dan uwan nasa Yana Masa ya jiki,Mami ce tace, Addayiya da Alhaji mukazo Yana waje zai shigo ya duba Lahab,hijab Addayiya ta d'auka tasa tare da cewa, Bismillah ya shigo fita Rahab yayi yashigo dashi,su Mami basu tashi barin gidan ba harsu Nabeel ma Suka shigo sosai mutane keta shigowa abin sai ya baiwa mutum mamaki duk da kowa baijin dadin Lahab amma Allah ya Masa farin jinin mutane kuma duk Wanda zaizo saiya riko Masa Abu kulolin kaji Kam yafi biyar aka cikawa Addayiya a daki sai yamma sosai Mami Suka tafi amma Rahab bai bisu ba,bayan wucewar su kasa hakuri Lahab yayi ya tambaye Rahab"Wai Rahab lafiya Kam Naga gabaki d'aya kana Nan uncomfortable yau innan meke faru tunda na dawo Banga umaima Koh Shareef sunzo sun dubani ba Koh basa gidan ne"?
Shuru Rahab yayi ganin Addayiya ta shigo dakin shiya hanasa magana,kallonta Lahab yayi yace"Wai Addayiya Ina Yaya muzammil ne Koh fushi yake dani har yanzun bai shigo ya dubani ba haka ma Aunty nabeela"?uhmm ajiyar zuciya ta sauke tare da Zama a bakin gadon ta had'a giran sama da kasa ta kalli Rahab tace,malam fita ka bamu waje zamuyi sirri don Ni yanzun bani ba kai.
Waro Ido Lahab yayi yace"Kai Addayiya Rahab nefa kike kora Koh idanun nakine Suka samu problem"?zanci mutuncin ka lahabu?Jin abinda tace yasa Rahab Hawa Kan gadon ya kwanta Aiko da masifa ta Mike tana cewa sai ya fitar Mata a daki ya tashi ya fita amma haka yaki fita ta gama nacinta da masifarta kafun ta d'ale Kan kujerar dakin ta kwanta harda filo ta daura a kanta Kara tambayarta Lahab yayi ganin bata basa amsa ba"Addayiya Ina uncle ne yau kwata kwata ban gansa ba"
Ya koma tace Masa,zaro ido yayi cikin happy yace"ya koma fa Kika ce haba dai da gaske ya koma Amma Baya ce sai bayan auren su umaima zasu koma ba"?
Eh haka yace amma abinda dnn uwanka ya Masa shiya fusatashi ya tattarasu da sassafen Nan suka koma Inda suka fito,Kama baki Lahab yayi Kamar mace yace"bangane ba Addayiya meya faru meya hadasa da Rahab Kuma"?gashinan a kusa da Kai ka tambaye sa?juyawa yayi ya kalli Rahab dake kwance yayi Kamar baijin abinda suke cewa maka Masa kafada Lahab yayi yace"Kai tashi ka fadamin meya faru"?