← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 122

Sashe 45

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mikewa tayi da Sauri ganin mubeeena bata bata amsa ba tabi mubeenar cikin daki,samun ta tayi zaune ta Kwabe hijab in jikinta abinka da farin fata lokaci daya idanun ta da fuska sunyi jawur ganin Inna ya sata Kara fashewa da kuka,jikin Inna har bari yake ta matso kusa da mubeena,ke mubeena menene meke damunki?saurin rungumarta mubeena tayi tana wani irin marayan kuka ita Karan kanta Inna ta shiga damuwan tunda take bata taba ganin mubeena cikin wannan tashin hankalin ba don Koh rasuwar iyayen ta bata da wayo sosai,don Allah mubeena ki natsu nasan ke yarinya ce Mai zurfin ciki Ni na haife mahifinki Kuma Nina raine ki tun kina da shekara biyar a duniya mahaifanki Allah ya musu rasuwa keda dan uwanki duk a hannuna kuka tashi ban rareku da kome ba duk abinda na samu bana Fara sawa a bakina har sai Naga ku kunci meyasa meyasa mubeena Baki d'auke Ni a matsayin wance zakiyi shawara da ita ba wance Zaki fadawa damuwan ki kuyi Alhini tare tun kina yarinya Koh Abu na damunki baki fadamin sai dai Inna gane nayi kokarin magance Miki Amma bazaki fadamin da bakin kiba sai Kuma ta fashe da kuka Mai tsuma rai tana Zama a bakin gadon tasa bakin zaninta ta rufe fuskar tata.

da Sauri mubeena ta sake rungumar Inna cikin kuka take magana,kiyi hakuri inna bawai haka bane wallahi kaf duniyan Nan bani da Kamar ki na tabbatar Koh iyayena ne Suka dawo bazan musu son da nake Miki ba dake na Saba Ina boye Miki damuwa tane don gudun sakaki kema a damuwa.

in dai bakison sani a damuwa toh mubeena ki daina boye mini damuwar ki hakan na mini zafi gani nake Kamar akwai wani abinda nake Miki Wanda yasa kike gudun naji sirrin ki.

girgiza Kai mubeena tayi sai Kuma a hankali ta soma magana hawaye na bulbulowa,Inna Ahmad ya rabu dani s...sa...saboda.......sai Kuma ta kasa karasawa saboda kuka daya ci karfinta,mikewa Inna tayi cikin bacin rai tace,kaii badai akan wannan yaro kike zubda hawaye haka ba tukunna ma maiya hadaku daman duk son da yake gwada Miki na shekaru duk karyane munafukin Allah toh wallahi babu Wanda ya Isa ya yaudari jikata ya kwana lafiya tana karasa maganar ta gyara daurin zaninta hade da daukar hijab a jikin kofa tasa tana kokarin fita a dakin sai surutai take,shagon sa zanje saina ci Masa mutunci sai yasan ya taba kayyu yau Innan don ubansa har gun uwarsa sai naje na shata Mata layi Ni za'a rainawa wayo in gama tattali Ina jiran biki zaizo yace ya fasa.

Inna ki dakata don Allah,Amma Ina Inna bata saurare mubeena ba sai takalmin ta data saka tsabar Sauri ma hagu ta sama dama dama ta sawa hagu ta nufi kofar gida.

Inna ki dakata nace Miki Koh kunje shagon sa bazaki samesa ba haka zalika gidan su saboda yana asibiti,dakatawa Inna tayi ta juya tana kallon mubeena,wani asibitine kenan har can Zan bisa Koh Yana danjan mutuwa ne saina nuna Masa bacin Raina harni zai cutarwa Jika,ta juya abinta zata fita.

Inna ki dawo Nina ce bana sonsa bana sonsa ne don bashi bane a zuciya.............

***************
Alhaji sulaiman da Mami da yaranta ne zaune akan dinning dayake yau weekend ne babu makaranta gabaki dayan su abinci suke ci Kuma d'aga yanayin cin kadai zaka gane Suna Jin dadin sa,sabanin Mami dake ta sai jujjuya shukali take abin duniya ya dameta gabaki d'aya jin abincin take Kamar mad'aci,Mami Mami Mami mahraz ya kirata har baki uku Amma shuru Bata ma San yanayi ba.

Mufeeda dake kusa da itane tasa hannu tadan tabata,Mami ya mahraz nata Miki magana baki amsa Masa ba?dan firgigit tayi cikin yake ta kalli mahraz , na'am mahraz Meka ce?

Mami meke damunki ne Koh Baki da lafiya ne?

Ah ah mahraz lafiyata klau Meka gani?

Uhmm kawai yace bai Kara magana ba don Shima yanzun ya Fara wayo sosai yasan me ake Kira tunanin shiyasa daya fahimci bata son tambayar ya Barta kawai badon ya yarda ba,Alhaji sulaiman Kam girgiza Kai kawai yayi tare da kallon mamin,mamin mahraz tunda yau weekend ne sai kije gidan su lahab in ki barmin yaran a gida.

Dan dago Kai tayi ta kallesa watoh Koh bata fada Masa ba ya fahimci matsalar Lahab ne,toh shikenan dadyn mahraz,tsagal wasila tayi tace,nidai gaskiya Mami Zan biki kinji?

kallon ta Mami tayi Jin mahraz da mufeeda ma sunce Suma zasu,Kinga bafa jimawa zanyi ba Kai Kuma mahraz da girmanka zaka wani cewa zaka bini toh Yusuf ma a gida Zan barsa,Aiko Yusuf dake Kan cinyar wasila Kamar yasan me mamin ta fada Kwabe fuska yayi sai Kuma ya sake kuka da karfi Yana kokarin sauka d'aga Kan kafar wasila Yana mikawa Mami hannu,gabaki dayan su Saida sukayi dariya hannu tasa ta dau Yusuf in ta daura akan kafarta Aiko take yayi shuru abinsa Costan sa da aka dama Masa a cup ta janyo daga gaban wasila tana Iba tana basa.

Suna gama cin abincin mufeeda ta goya Yusuf ganin yayi bacci a bayanta yasa Mami ta tashi ta shirya fitowa tayi hannunta d'auke da car key's,toh Ni Zan wuce sai na dawo tace tana kallon Alhaji dake zaune rike da jarida ga yaransa a kusa dashi,toh a dawo lafiya Mami yaran suka had'a baki,yauwa Yan Albarka sannan Kai mahraz ka karbi Yusuf a bayan mufeeda ka kwantar dashi a tsakar gado kasa Masa filo a gaba da bayan sa Karya fadi?

toh Mami saikin dawo,Allah yasa tace tana bude kofar falon ta fitoh compound na gidan parking space ta wuce ta bude motar ta ta shiga tare da maida murfin ta rufe ta tada motar.

da Sauri gate man ya walgale Mata gate Yana Mata a sauka lafiya.

*****************
a gaskiya sadeeq kayi hakuri maganar kawo laifen Nan a ajesa a gefe yanzun hankalin gidan mu ba'a kwance yake ba bare ayi wata maganar lefe,umaima dake jingine da motar sadeeq a cikin compound na gidan su tace fuskar ta babu walwala.

Sadeeq dake zaune a gaban mota kofa a bude fitowa yayi gabaki d'aya a motar Yana kallon umaima,Wai umaima Mike faruwa ne na kasa gane kanki tun fa jiya na shigo garin ku na kiraki a waya akan ina zuwa da daddare Zan Miki Albishir na musamman saboda maganan Nan na taso daga baushi nazo gombe amma har zakice Wai a sauke maganan kawo laife ranan Monday bangane me kike nufi ba?

Unmmmmm sadeeq kenan bazaka gane bane shiyasa amma nidai na riga na gama magana.

Wai tsaya umaima bangane Kin gama magana ba akan me zakice Kar a kawo Kuma baki gayamin gamsheshen amsa da Zan Kai gidan mu nace ba, meke faruwa ne?Koh dai son nawa ne Kika daina d'aga jiya zuwa yau?

dan murmushi tayi tana kallon sa watoh shi tanan ma tunanin sa ya sako Masa Kenan,sadeeq dan uwan mahaifina yau kwana biyu bai kwana a gida ba sannan ba'asan Inda ya shigaba taya hankalin mu zai kwanta har a karbi kayan auren ka?

Subhanallah wanene a cikin su ya batan?ya tambaye ta don yasan bazai wuce small uncle's nata ba.

Wallahi hubby Lahab ne ya bata ta basa amsa tana kallon gate Jin horn na mota Mai gani ne ya taso ya bude kofar.

ton Allah ya bayyana sa,sannan Kayan aure na Koh na auren ki ai inta nine a yafe kayan.

Shuru tayi bata basa amsa ba tana kallon Mami data shigo da motar ta gidan parking tayi a kusa dasu ta fitoh a motar tsungunawa sadeeq yayi har kasa ya Soma gaidata.

Amsa wa Mami tayi umaima ma ta gaidata ta amsa sama Sama ta nufi flat nasu don hankalin ta ba'a kwance yake ba da sallama ta bude kofar ta shiga Addayiya ce zaune a kasan cafet sai rusa kuka take yayinda muzammil dasu Abbu keta bata hakuri amma Ina sai Kara volume take Jin sallamar Mami yasa ta share hawayanta tare da amsa sallamar Kamar yanda sauran Yan falon Suka amsa shigowa Mami tayi ta nemi waje ta zauna gaggausawa sukayi anan ake ta jajanta lamarin.

toh Ni anawa shawarar uncle Mai zai Hana akai case Nan hannun Yan sanda babu amfanin muyi shuru da sunan gudun magana shifa mutum ba'a iyya masa kome aka Masa baza'a gujewa maganar sa ba,shareef dake zaune Akan 1 sita yace Yana kallon uncle.

da Sauri Mami ma tace eh wannan gaskiya ne nima nayi tunanin haka Kar Muna tunanin wuta a makera mu ganta a masaka Muna tunanin Lahab gudu yayi Alhalin Kuma b'ata yayi Koh wani abin ne ya samesa don Ni wallahi jikina ya bani ba lafiya bane jiya Koh bacci ma banyi ba.

Wani dogon tsaki mamu tayi cikin makirci ta soma magana,Haba Amina wani irin magana akai ga Yan sanda waye baisan halin Lahab ba aje asa hukuma a ciki karshe a kamasa a logi(hotel) Koh club ya kunyata mu abarshi dai ai duniya ce tafi gabaruwa jimawa Kuma duk Wanda yabar gida da kafarsa zai dawo.

Wani irin bacin rai ne ya ziyarci Mami Jin munanan kalamai da take fadawa gudan jikinta,keee Haleema dakata banason shshigi ai basai kinyi haka Zaki nunawa duniya baki kauna ta da y'ay'ana ba wannan Kam kowa ya Jima da sani,Ina d'aga Miki kafane Albarkacin yayan ki amma wallahi wannan karon in Kika Kara shiga harkata wallahi Zan nuna Miki shuru shuru ba tsoro bane.

Itama mamu mikewa tayi Koh kunyar su Anwar batayi ba,keee Amina inkin fasa baki cika yar halas ba sannan menene abin ki a tsotsonki banda kwadayi dason abin duniya in ba kwadayi ba meya shigo dake tsakar rana cikin ahli Kika Haifa musu masif........tas tas kake ji Mami ta wanke fuskar Mami da wasu mahaukatan Mari guda biyu daidai lokacin umaima ta shigo falon mikewa Anwar yayi jikinsa har rawa yake ya nuna Mami da yatsa,mahaifiyata Kika Mar..............
Chapter 45 · 0% Book details