Sashe 43
Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cikin zafin nama Nnenna ta damko hannun Lahab dake Kan cinyanta har lokacin Yana shashafa wa don ya gaza ganin jikin wa yake tabawa don bai kawo a ransa itace be sai da yaji muryar ta, bayan ta rike Masa hannu tace"Lahab ka tashi"?
Shuru yayi bai bata amsa ba sai ma yanzun ya tsoma Jin haushin abinda ta Masa gashi Nan taje ta karyasa a banza d'aga make Masa hannu sai tsagewar Kashi mace Kamar Mai Kashi daya amma ta wani bangaren yaji dad'i kula data nuna Masa gashi har kwana zatayi dashi,Koh dayake ma ai ita ta raunana sa,,Yana jinta tana Kara tambayarsa amma baibata amsa ba,sai kokarin sauka yake akan gadon,itama da Sauri ta sauka ta nufi switch na dakin ta ketta take haske ya gauraye dakin d'aga Ido yayi ya kalleta sai Kuma ya maida kansa a tiles in Yana Neman takalminsa don baison taka tiles in asibiti.
Fahimtar abinda yake nema yasa ta saurin matsowa garesa ta cire sandal in kafarta ta tsunguna hade da kama kafar nasa Wai zata saka Masa takalmin, shuru kawai yayi baiyi magana ba Harta gama sawa mikewa yayi ya nufi toilet,itama Zama tayi akan kujera tayi shuru duk sai taji ya shiga damuwa sosai wallahi,bai wani Jima a bandakin ba ya fitoh Hawa Kan kadon yayi ya kwanta tare dasa hannunsa Mai lafiyar ya lulube jikinsa duka harda Kai.
Mikewa tayi ganin ya kwanta taje ta kashe wutan dakin duk da Dr yace inya tashi takirawo nurse kin kiransu tayi,a hakan dai tana Kan kujera ga kafarta a waje har bacci ya dauketa shikam kasa baccin yayi dan zazzabi zazzabine a jikinsa kwata kwata yaji baccin ya Kare Masa,a hakan yayita jujjuyawa har aka Kira sallan asuba mikewa yayi daga Kan gadon ba tare daya kunna wutan ba ya Shiga ban daki Alwala yayi duk da zazzabin da yake ji Amma bai sawa hannun ruwa ba.
Dudu ba dakin yayi baiga sallaya ba dan tsaki kawai yayi yakai dubansa ga Nnenna dake bacci a zaune gashi bazai iyya zuwa masallaci ba har lokacin ana yayyafin ruwa rigansa ya d'auka ya shimfida a kasan tiles in ya Kama sallah Yana idarwa daidai lokacin nurse ta shigo ganin ya farka yasa ta cikin fara'arta tace,ah ah Hassan ka farka ne?
"Eh na farka sister"Yana mamakin Ina tasan asalin sunan sa waya fada Mata sunansa?
Ok Baku da sallaya ne Naga kana sallah da riga bara na kawo muku amma yanzun akwai Inda ke maka ciwo ne?
"dan zazzabi zazzabi nakeji ga nauyin da kaina ke mini"
Ok toh bara na Kira doctor,tace tana fita a dakin, Nnenna da tun tashin Lahab ta farka shuru kawai tayi Harya idar da sallan,bude Ido tayi ta kallesa a hankali ta sauka akan kujerar tasa gwuwuwinta a kasa ta hade hannayinta sannan ta soma magana"kayi hakuri Lahab badon niba badon halina ba ka yafe mini nasan ban kyauta ba Kuma wallahi Koh Ni ban d'auka zaka cutu har hakanba pls forgive me"
Kauda fuska yayi Koh kala baice Mata ba,itama ganin hakan yasa jiki a sanyaye tace"ya jikin naka"?Nan ma shuru ya Mata Kamar ta shuka dusa,turo kofar da akayi yasata mikewa ta koma Kan kujerar da ta tashi likitane ya shigo nurse in dazun na binsa a baya hannunta d'auke da sallaya, Assalamu Alaikum
"Waalaikumu Salam"Lahab ya amsa tare da gaishe da likitan.
Amsawa likitan yayi ya daura Masa laidan ruwa ita Kuma nurse in ta aje sallayan a gefe tace, sister ga sallayan Nan sai Kuna amfani dashi daidai.
Lahab ne ya Mata godiyan don ita Kam Nnenna bama tasan me take cewa bama sai wani harhada fuska take ganin yanda likitan sai binta yake da Ido duk yabi yasata susuce,ashe Shima Lahab ya lura da hakan sosai ya had'a fuska tare da kallon laidan ruwa da aka saka Masa tunda yake ball kullum mami na Masa bariya akan yabar ball yana Karya mutum Amma gashi yau ball bai karyashi ba Nnenna ta tsaga Masa Kashi ba'a taba daura Masa laidan ruwa ba tunda yake har wani fariya yake babu kamarsa a gidan su gashi yau tasa an daura Masa sannan ga wani shegen kallo da yaga likitan ke Mata ita Kuma tabar kafafu a wajen ganin likitan ya fita yasa sa CE mata,"keee
dan kallon sa tayi ganin yanda ya wani had'a rai irin ba wasan Nan yana kiranta mikewa tayi tazo bakin gadon ta saya batayi magana ba,"in tambaye ki Mana?
"Ina jinka"
"Wai a addinin ki ance ki ringa saka suturan da zaina fallasa tsiraicin kune"?
Itama had'a ran tayi tana Masa kallon mamaki amma batace kome ba Shima ganin bata da niyar basa amsa yasa ta ce Mata"ATM nawa da Kika amsa jiya ki fita bakin asibiti baza'a rasa shagon Kaya a wajen ba kije ki sayamin Kaya so nake na chanja na jikinta,kema ki sai naki kibar daukar Alhakin Maza.
Jin ya gama maganar yasata juyawa kawai Bata ce kome ba ta bude jakan makarantan ta ta zaro card in da flask nasa dayake school dashi ta nufi kofar"zo taji yace dawowa tayi ta tsaya tana sauraron sa"ki sayi abinci"toh tace ta fita a dakin komawa yayi ya kwanta .
****************
Hmmm gidan su Lahab da sun shiga tashin hankali na rashin d'ansu domin Wasa Wasa Saida muzammil ya ringa bin gida gidan Yan uwa Yana tambaya Amma sai suce Basu ga Koh keyar Lahab ba,Mami ma ta Kira Addayiya ta sanar da ita Lahab yazo wajen ta amma ya fita,Wasa Wasa har dare ba labarin bawan Allah Nan Addayiya kuka ta Soma tana amanar umaru ya bata me zaicewa ubangiji an basa amana yaro ya Bata gidan su Adewale da Nabeel duk anje sunce su rabon su da Lahab tun shekaran jiya da Suka bugi malami a school
Rahab shi Karan kansa kuka yake amma fa Abbu ya bada guarantee Lahab ba bata yayi ba,akwai dai Inda ya shiga yanzun yanda kowa ke ruruta rashin jinsa aka fitar da zancen ba'a gansa ba wasu zasu ce duniya ya shiga Koh Kuma yafi karfin iyaye da yayunsa tunda daman shi dan Adam baka iyya masa haka baka guje masa kome abin magana ne.
Muzammil Kam yasha alwashi idonsa idon Lahab kashesa ne kawai bazaiyi ba Amma Shima ya mugu mugun shiga damuwa sosai.
ta bangaren gidan su Nnenna Suma sunsha mamaki ganin har dare babu Nnenna especially da yanzun ita ke musu girki gashi dady zai dawo gobe duk mom ta rikice batasan me zatace wa Dad ba tunda Bata San takamemmen Inda ta shiga ba a daren haka yayita sake sake,washe gari da safe Dad ya Kira ta ya sanar da ita Yana Kan hanya kitchen ta shiga ta girka musu breakfast sukaci kafun Sarah da Jennifer Suka tafi makaranta.
Mubeena a daren nan ta kwana a zaune ga wani irin bugawa da kirjinta yake ta rasa meke Mata dadi tabbas da tasan Ahmad zaiji abinda tace wallahi da Bata fadawa kowa ba tabar abin a ranta yanzun wani hukunci Ahmad zai yankewa alakarsu Koh banza Mai kyautata maka randa bashinan sai kaji ba dadi,bare Ahmad daya Mata kome a rayuwar baicacanci wulakanci Koh ki ba haka bataso yaji kome ba,washe gari hakan ta tashi idanunta a kumbure sosai Wanda hakan ya matukar damun Inna ajeta tayi ta tambayeta meke damun ta Amma kememen mubeeena tace ba kome.
Toh Koh kunyi fada da Ahmadun ne?Inna tace Mata.
Babu abinda ya hadamu Inna.
Toh Amma Naga jiya baizo ba Kuma nasan Ahmad in ba ruwa ake ba babu abinda ke hanasa zuwa.
Inna nace Miki babu kome fa shuru kawai Inna tayi bawai don ta yarda babu abinda ke damun ta bane,da misalin karfe 8 na safe sai ga Rukayya ta doka sallama a kofar gidan nasu tare da turawa ta shigo.
Waalaikumu Salam barka da zuwa takwara,Inna ta amsa Mata tana shimfida Mata taburma,yauwa Inna Ina kwana mun tashi lafiya tayi maganar tana Zama a taburman Zama itama innar tayi tana amsawa lafiya Alhamdulilah ya jatumar Taki?
tana lafiya Inna mubeeena na Nan kuwa?
tana Nan yarnan gata can kunshe a daki duk abin duniya na damunta Kuma Taki fadamin ki shiga ai in akace maka mutum bafulatani an gama magana.
Murmushi Rukayya tayi ta nufi dakin tana tsokanar Inna,ai kawancen ne aka daina dake kin tsufa Bari Kiga na shiga fadamin zatayi.
dariya kawai Inna tayi yayinda Rukayya ta Shiga dakin kwance ta tarar da mubeena Koh sallamar da tayi ma Bata amsa ba Zama tayi a bakin gadon a hankali tasa hannu ta girgiza ta,firgigit ta farka d'aga nannauyan tunanin data tafi,Haba mubeeena Zaki kashe kanki ne Koh Yaya irin wannan tunanin da damuwa da Kika daurawa kanki da wannan kwanciya naki da Alwala kikayi kikayi sallah Kika roki Allah ya yaye Miki dayafi?
Uhmmm Ruky bazaki gane halinda nake ciki ba ni kadai nasan yanda nake ji.
Koma me kikeji ba daidai bane ace kina sakanki a damuwa har kinsa tsohowa ma a cikin damuwa haba mubeena?
Ruky dole na damu bantaba Jin kunya irin na jiya ba da wani Ido Zan Kara ganin Ahmad tana maganar tana kuka.
Mubeeena ki kwantar da hankalinki yanzun ma zuwa nayi ki tashi muje asibiti mu duba jikin nasa ya ya kwana tunda yau bamu da exam.
Haba Ruky wallahi bazan iyya zuwa ba innaje nace meye?
Kinga mubeena gwara dai ki tashi muje ki dubasa Amma rashin zuwanki ma wani rauni Kika fame Koh iyayen sa zasuyi mamakin ki in Baki je ba karfa ki manta Koh ciwon Kai kikayi haka Yan uwansa zasu yita zuwa dubaki dan Allah ki daure muje kinji Koh?
Mikewa zaune mubeena tayi jiki ba kware ta fita a dakin tabar Ruky ita kadai ruwa ta Iba tayi wanka ta shirya Suka ma Inna sallama Suka fita a gidan,tun d'aga nesa ta hangesa tsaye a wajen jiya gabaki d'aya yabi ya rame itama Kara had'a fuskarta tayi daman a hade yake tafiya suke yayinda ya zuba Mata Ido shi Kuma tun d'aga nesa,har suka karaso Inda yake zasu shari kwana matsowa yayi kusa dasu tare da musu sallama Kamar cikekken musulmi, Assalamu Alaikum