← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 122

Sashe 36

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kara Ware Ido yayi dakyau ya Kara kallon ta sai Kuma ya mike tsaye don Kamar mafarki yake ba a zahiri bane daman haka takee.........................

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*

Page 43&44

Ba kowa bace face farida budurwan Anwar Koh ince matar da Anwar zai aure don har date na auren an yanka,mamaki ne ya kusa kashe Lahab don itace Amira a islamiyyar su Kuma sosai iyaye ke Alfahari da ita ana nuna wa Yan Matan islamiyyar su suyi koyi da halayen ta ashe abin ba haka yake ba kullum tana cikin hijab har kasa ana taboda zatace Allah yace annabi yace Ashe fuska biyu gareta lokacin da Anwar ya fitar da ita akan matar da zai aura babu Wanda baiyi na'am da abin ba.

da Sauri ya juya musu baya ganin ta kusa kamasa Yana kallon ta gashi hall in Suka nufa agogon hannun sa ya duba karfe 10:39am,mikewa yayi da Sauri yabar wajen tsayawa yayi a jikin mototin dake pack Yana kallon ta harta shiga ciki,hannu yasa a Aljuhunsa wayam babu waya sai yanzun yake Jin haushin rashin waya a hannun sa yabar wayan sa a gidansu.

Shiga ciki yayi Yana bin hall in da kallo Maza da matane ana ta rawa ga yan matan musulmai da Cristian nan cikin bad dress sai faman Mika wuya yake Yana Neman su Majid Aiko acan wani table ya gansu zazzaune da Yan Mata ana ta Hira ana mammatse su tacan gefensu ma faridan ne tsaye Suna magana da wani,Wanda a dukkan alamu birthdayn nasa ne,dole yasa sa bin cikin mutane Yana tafiya Yana sunkuyar da Kai Harya iso kusa da Majid juya Mata baya yayi yanda baza taga fuskar Saba sai bayan sa,ya zauna akan kujerar ya Bata baya,amsar wayar Majid in yayi ya kunna camera tare da karban hulan faruk pcap ya rufe fuskarsa sosai.

Tashi yayi ya koma tables in baya ya zauna sosai yake bin duk wani abinda take,mc ne ya Soma magana bayan an Saida kid'a,Muna ma manyan bakin mu barka da zuwa,sannan Muna son ganin shi kb uban gayyan a fili tare da zazzafar budurwar sa fereey su karaso Muna son ganin su.

farida ne ta shigo fili da wani yaro da bazai wuce 23 ba Yana rike da hannun ta Suka Haura Kan step in,zasu yanka cake,aka kawo aka aje musu kb ya d'auki wuka ya saita Kan cake in yayin da farida ta daura hannunta akan nasa,shi Kuma Lahab sai daukar hoto yake da vedio tunda Suka taso,gashi jama'a sun mimmmike tsaye Suna musu wakan we wish u happy birthday.

Yanka cake in sukayi kb ya d'auka ya Samata a baki itama ta basa kafun ya Kama bakin ta ya bata hot kiss take wajen ya kashame ta ihun su Majid da tafin su,Waka aka sake Wanda mutum zaijishi har tsakiyar kansa kafun aka kashe wutan Hall in habawa basai aka Kama iskanci ba, duk namijin da ya Kama mace take zai danneta a wajen, Lahab da zuciyar sa ke bugawa da Sauri ya ringa lalube Yana Neman hanyar kofa Jin wani ya kamasa Yana ta jansa ihu ya Fara Yana namiji ne ba mace ba Amma ina sai ma ji da yayi mutane biyu sun shuresa sama.

Wani irin wainuwa yayi ya kadawa dayan cizo har sai da wayar hannusa ta Fadi kasa garin Sauri yaji ya taka ta ta subuce tayi wani wajen,dole baida wani zabi sai na fita a hall in da gudu Yana tattaka mutane ya samu ya fita a ciki duk yabi ya had'a gumi jakaf ya fitoh, direct gate ya nufa Amma abin bakin ciki bai samu Koh tsuntsu a titi ba garin shuru babu motsen kome,agogo ya duba karfe 12:19 na dare hankalin sane ya Kara tashi ba dan kadan ba, daya sani dayasani dabai biyo Majid ba da hankalinsa kwance a gida Kai dama ya sani da gidan su ya koma Koh kasheshi muzammil zaiyi yayi da wannan tashin hankali,gashi bata kofar gate Suka fita ba baisan ta Ina zai shiga ba in yaje ya buga kofa aka bude Masa baisan amsar da zai baya yayan Saba Kuma Koh giyan wake yasha bazai kuskura ya koma gidan suba jingina yayi da ginin hotel in duk abin duniya ya damesa.

Yana Nan tsaye a wajen har 1 na dare kafun ya Fara ganin yara na fitowa daya bayan daya dayake darene babu Wanda ya lura da mutun agun sai can kusan 1:27 yaga motar su Majid na kokarin fita a gate in da Sauri yazo yasha gaban su tsayawa faruk yayi a mugun zuciya Lahab ya bude kofar ya shiga ya maida kofar ya rufe da karfi"Amma wallahi Majid Allah wadaren ka Ashe iskancin da kukasan zakuzo kuyi kenan kace na biyoka sai yanzun na gane dalilin dayasa Yaya baison xamana tare da Kai ashe hakan Alkhari ne"

Kaga Lahab dakata bafa jawoka nayi da karfi ba Kuma in kasan Kai karamin dan iskane meyasa ka shiga ciki.

"Majid Ni kake Kira dan iska"?Lahab ya tambaye sa ransa na kara soyuwa,ga bakin cikin batar wayar Nan ta Majid shikenan ya rasa wannan vedio,yasan duk abinda zai fada akan farida bamai yarda don kaf unguwan su yabonta ake,yaso yayi amfani da vedio wajen Hana auren ta da Anwar saboda baya kaunar ta yanzun yaji ya tsane ta kwata kwata Kuma baya fatan ta aure dan dan uwan sa.

Keeeeee kakeji faruk ya taka birki da karfi suna salati da Majid don saura kadan ya buge wani tsoho Allah ya Sosa.

Lahab Kam dafe kirjinsa yayi haka kawai zuciyar sa ta tsinke da Sauri su Majid Suka fita a motar Suka nufi tsohon dake duke a kasa jikinsa na rawa.

dagosa faruk yayi yana basa hakuri tare da tambayar sa abinda yafin dashi a daren nan shikam tsohon sai kallon glass in motan yake ta Inda Lahab ke zaune yayi sumar zaune ganin tsohon jiya da Nnenna ta hanasa basa kudi Kuma yazo yayi mafarkin sa kin fita yayi a motar Yana dai ganin su Suka basa hakuri tare da tsallakar dashi titi Suka taho motar ja faruk yayi Suka bar wajen.

Kamar yanda faruk ya daukosu haka ya maidasu lokacin dare yayi sosai wajen shuru babu motsen kowa gabaki d'aya Lahab ya shiga damuwa Allah Allah yake yagansa a daki Kar wani ya gansu.

Bude back door in Majid yayi Suka shiga ya maida kofar ya rufe kirim Kamar yanda ya bude tafiya suke a garden kaman barayi Suna zazzare Ido,suwaye a garden Nan su wanene???sukaji muryan daya d'aga cikin security na gidan ya nufo garden in da toshi Mai haske.

Habbawa Majid da Lahab kafa me naci ban baka ba gudu saka saka Jin gudun kafafu yasa security hura usur dake wuyan sa a take sauran ma suka nufo garden in tashin hankali yasa su Lahab kasa bude kofar ganin an kusan cin musu yasasu Hawa bishiya suka labe Lahab sai tsinewa Majid kawai yake a ransa.

Security's Kam sosai sukayita checking na gidan Amma basu samu kowa ba sunyi iyya dudubawan su Amma shuru sai daga baya wani yaga shatin takalma a tabon dake garden in hakan ya Kara tabbatar musu akwai mutanen da Suka shigo garden in bin shatin sukayi har hanyar back door duk da Basu Zargi wani bane ya shigo kofa a rufe sai dai a Yan gidan.

Hakan yasa Suka Kara tsananta tsaro da sa Ido Suka yada zango a garden in wannan tashin hankali duk su Lahab nakan bishiya Suna jinsa,hannu ya d'aga yaga time dayake agogon Mai wutane 2:31am na dare.

Wannan dare dai mutane uku sun kasa bacci Mubeena Lahab Adewale don shi Majid tuni ya jingina da jikin reshe ya Kama bacci abinsa Koh a jikinsa Kamar a gadon sa yake kwance Banda Lahab da Sauro suka tasa sa a gaba ga fargaba dake damun sa.

Su Lahab na garden a zaune akan bishiya d'an bacci ne ya sace Lahab.

Mafarki............
Kwance yake Yana bacci akan bishiya wani gawurtancen macijina Mai girman gaske Baki kirim Yana ratso ganye da reshe Yana tafiya Yana fidda harshe Hawa Kan Lahab yayi yasa bindinsa yasa ya nade Lahab kamar taya yayin da tsohon Nan ya bayyana a gaban Lahab Shima hannnun yasa cikin dariya ya damko makogoron Lahab da karfe gaske Wanda yasa sa farkawa a cikin mafarkin.

Ihu yake yana Neman taimako yayin da tsohon yake Kara damkar Masa makogoro har Yana Jin numfashin sa na d'auke wa.

Bayyana tayi a kasan bishiyan Wanda ya kasance Mai Nisan d'aga kasa zuwa saman bishiyan haryakai sai dai a ringa hangan mutum dan kadan a kasa,ihu take tana cewa Lahab, "Lahab ka farka Lahab ka farka ka farka na rokeka bazan iyya kwacan ka ba ka farka kamin nisa sai Kuma ta Kama bishiyar tana Hawa Amma tamkar ana Kara Nisan tsakanin gindin bishiyar da ganye.

Wani ihu ta Masa da karfe Wanda Lahab yaji sa har tsakiyar kansa,a take ya farka a zahiri ya jika sharkaf kallon Inda yake yayi da gaske a bishiyar yake ga wani motse da yakeji a saman reshen gefensa wuyansa da aka Shaka gani yake kamar da gaske don wani irin radade yake ji a wuyan nasa hannu yasa Yana shafa wuyan ai da Sauri ya dirko d'aga Kan bishiyan Jin ana kiraye kirayen sallan asuba jikinsa sai rawa yake.

Bai Koh tashe Majid ba ya wuce cikin massalacin dake gidan yayi Alwala a pampo ya shiga ya zauna,Kamar 30 minutes sai ga Yaya jafar da Hashim sun shigo da mamaki suke kallon sa ganin ya fitoh da wure Amma sai suka kauda mamakin tunawa da Lahab nason ibadah bai cika Wasa da sallah ba,Kai Lahab Ina Majid kun kwana tare Amma kazo massallaci Ina yake?

"Yana daki na barsa Yana Alwala zai fitoh"shine abinda yace kawai yaja bakinsa yayi shuru security ma sun shigo aka tada sallah dasu ana idarwa aka gaggaisa anan daya daga cikin security ke sanar da Yaya jafar akwai Wanda ya fita a deren jiya don sai karfe 1 ya dawo Amma sun rasa ta Ina ya shiga Koh ya fita.
Chapter 36 · 0% Book details