← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 122

Sashe 11

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su biyune da bawan Allanan da zaikai shekara 40 jijiga yarinyar Nnenna kiyi Amma ina yarinya taki shuru mutumin ma ya karbeta ya jijiga Amma ina kuka take bilhakki da gaskiya abin ya kwabe musu sun rasa yaya zasuyi da ransu Ga dare ga kukan yarinya.

Mutumin ne ya mike hade da cewa Nnenna bara ya dubo koh ruwane a samu a bata tunda kamar sun shigo kauyukan Gombe babu musu tace masa toh.

Yana tafiya yarinya sai kuka take harda had'a gumi sosai ta bawa Nnenna tausayi tunawa da tayi ana baiwa jarirai nono yasata saurin kwantar da yarinyar a cinyanta ta sauke kulenta ta aje a gefe.

Riganta ta matsar kasa kad'an hannu tasa ta zaro breast nata manya kuma tsayayu, babu wani tsoro ta kafawa yarinyar nipple a baki, jikin yarinyar har bari yake ta kama da sauri sauir take jan maman.

Duk da babu kome a cikin nono babu ruwa Amma hakan baisa yarinyar ta sake ba, sai ma Nnenna da zafi ya dameta ta zare bakin nonon ta, aiko yarinyar cinyara kara tayi da karfi, Nnenna ma da sauri ta maida mata tana rumtsa ido saboda zafi.

A haka har yarinyar tayi bacci mutumin bai dawo ba ita ma bata damuwa ba ta maida kirjinta ciki, tana mai tausaya ma jaririyar, sai da ta sake jimawa sosai kafun mutumin ya dawo d'auke da ruwa a tundi.

Da mamaki yake tambayar Nnenna ya haka yarinyar tayi bacci, Amsa kawai ta basa da yarinyar ta gaji da kukane har tayi baccin, ruwan ta karba shima ya cire rigansa ga baiwa Nnenna tana tsomawa a ruwa tana gogewa yarinyar jiki harta gogeta ta fita kamar yanda yace tayi.

A wajen suka kwana yarinyar ta farka da dare haka Nnenna ta damka mata nono a cikin duhu ba tare da mutumin ya gane ba a tunaninta batasan shikam yasan me take ba, washe gari mutumin ya fita bakin titi ya tare musu motar suka shiga har cikin gari.

Tunda Nnanna ta shigo cikin gombe take bin koh ina da kallo duk da bata kallo garau Amma tana iyya gani dishi dishi, ji take kamar ta shigo sabuwar duniya gata rike da kule da jaririya ga riganta a bace kaca kaca station mutumin yace su nufa gudun matsala.

Report mutumin ya shigar akan suna d'aya daga cikin matafiya da aka ma fashi daren jiya a mashigar gari, daman yan sandan sunsan da fashin, jakan hannunsa daya d'auka wanda matar ta baiwa Nnenna ya bude ID card na matar ya fitar ya baiwa yan sandan, tare da musu bayanin jaririyar.

Akan su nema musu matar ga jaririyar ta a hannun su koh wani yan uwan ta kona mijinta, babu musu yan sanda suka karba aka fara bincike basu bar Station in ba saida aka samo Iyayen matar ashe ma ba boyayyu bane manyan mutane ne, karbar jaririyar su sukayi suna ta godiya, jin Abinda Nnenna tayi, wasu sai kuka suke don tun jiya hankalin su yake a tashe gashi basu san halin da yarsu da mijinta suka shiga ba, daman garin su mijin suka fitoh.

Nnenna kamar tasa kuka don haka kawai taji tana son jaririyar Amma ya ta iyya haka ta basu yarsu, kakan jaririyar kudi ta baiwa Nnenna masu yawa akalla zai kai 500k kin karba tayi sai da mutumin yasa baki kafun ta karba tana musu godiya.

Mutumin ya mata sallama zai tafi sai kuma ya dawo ya tsaya ganin yanda ta rike kudi a hannu sannan tana bakke da kule ta tsaya a gefen station.

Tambayar ta yayi lafiya take tsaye bataza ta tafi gida ba?

Kuka Nnenna ta sake cikin jimami take sanar dashi ita bakuwa ce kuma bata san kowa ba takarda kawai baban ta ya bata ta taho wajen uncle nata daga Enugu, kuma yanzun bata gani sosai, bata da glass a ido.

Karban paper mutumin yayi yana dubawa sai kuma yace mata tazo suje kudin ma karba yayi yasa A Aljuhunsa ba musu ta bisa a baya, Abinci yasai mata a tsallaken titi Amma taki ci sai kulenta kawai yaci don batacin nama sam koh Abinci mai nama, ya sai mata medicated glass a wani shago ta sanya a idanunta.

Keke napep mutumin ya tare musu suka hau ba musu tana ta binsa.

Sunyi tafiya mai d'an nisa kafun suka iso wani unguwan talakawa har kofar wani gida sukayi packing,mutumin sauka yayi kamar d'azun ya zaro change daya saya mata abinci ya biya mai machine in tare dama Nnenna iso a cikin wani kwarmadeden gidan jan kasa.......

*********************
Lahab yana d'aki a kwace bayan ya rufe kofar dakin su, yanajin lokacin da Anwar ke ihu har zuwan su Addayiya da Abbu yana cewa yaga bakin Anwar in, sai kuma yaji Rahab nace wa ashe ba hakorin sa bane yacire, bakine da Goshi ya fashe duk yanajin Ana ta hidimar Anwar har kaisa asibiti da akayi da irin zagin da Mamu da Addayiya keyi Amma koh a jikinsa kofar ya sama kwado.

Ranan Rahab ma a dakin su Uxaifa ya kwana, washe gari da Asuba Lahab koh a jikinsa ya fita da asuban yaje masallaci agun ya hadu dasu Abbu Ga bakin Anwar ya sunduma gwanin tausayi, Lahab kam koh a jikinsa yayi kamar ma bai gansu ba.

Daga masallaci gidan su adewale ya wuce suka fita jogging, sai 8:00pm suka dawo,gidan su nabeel ya shiga yayi wanka ya sanya kayan sa da yake bari a gidan su nabeel wata rana in yayi wanka a gidan.

Adewale gida ya koma ya ibo musu abincin karyawa a kula lafiyayye suka karya daganan suka shiga gari yawo.

Bashi ya dawo ba sai yamma ya kamo hanyar gida don duk rashin jin Lahab baya wuce mangariba a waje haka baya fita koh ina da dare shiyasa suke kara godewa Allah baya yawon dare iyyakar sa rana.

Turo kofar falon yayi ya shiga ciki har yayi rabin falon sai kuma ya tsaya ganin mamin sa zaune a falon tana hira da Addayiya, tsayawa yayi yana kallon Addayiya da mamaki ganin yanda take washe baki, kamar ba ita ke zagin mamin su ba kullum.

Mami dake kallon sa ita ma tun shigowar sa jin baiyi sallama ba yasa ta nuna masa kofa ba tare da tayi magana ba, shima baice kome ba ya koma bakin falon ya tsaya amma baiyi sallamar ba, meya tunane oho ya juya ya zagaya ta bayan ginin flat nasu, ya shigo sashen su ta d'ayan kofar falon su.

D'aki ya wuce yayi wanka abinsa wando yasa 3quater sai Armless, jin an kira sallah yasasa yin Alwala ya fita masallaci ta kofar da ya shigo ana idar da sallan shagon mai Abincin tsallaken titin su ya shiga yasai abinci Agun ya zauna yace har isha'i yayi sallah ya shigo gida kamar d'azun yabi kofar baya.

Kwanciyar sa yayi abinsa yana chat gabaki d'aya hankalin sa nakan wayar sa.

Mami dake bakin kofar dakin hannu tasa ta tura kofar da sallama ta shigo, da sauri Lahab ya mike zaune daga kan katifar sa yana kallon mami sosai cikin sa ya duri ruwa ganin fuskar ta babu koh digon walwala.

Wallahi Lahab kabi duniya a Hankali Lahab kaji tsoron bakin jama'a lahab ina rabaka da Halima da yaranta, Lahab bakama jin Abinda nake fad'a maka koh? inka ma Addayiya koh yayan ku Umar su naka ne babu yanda suka iyya,hakuri ya zamo musu dole Amma wallahi ina rabaka da Halima(mamu)da taba mata yara don baka da hankali zaka d'aukar mata kudi har 300k sannan ka buga mata fuskar yaro sai da ya kumbura, Anwar Abokin wasan kane, bafa cousin naka bane d'an yayan kane akan me zakayi wasan banza dashi.

"Habba mami nifa bani na d'auka mata kudi ba, wani munafukin ne ma yaje ya sanar dake wannan sharbeben karyan"?

Ungo naka?mami ta masa dakuwa.

Kumbura fuska yayi "nifa mami ban d'aukar mata kudi ba"

Rufe mini baki in bansan halinka bane sai na yarda baka d'auka ba, wallahi Lahab ka shiga hankalin ka ka jima yaro ciwo Amma bazaka iyya zuwa ka duba sa ba, bare ma ka basa hakuri koh neman yafiyarsa.

"Kai mami" yace yana kallon ta

Duka mami ta kaimai da karfi a baya ji kake domm, ihu ya sake yana sosa bayan sai kuma da sauri ya sauko a katifar.

Bar kallona rasa kunya beran danga, wuce muje ka duba Anwar in kuma wallahi ka basa hakuri.

Ba yanda ya iyya haka yanaji yana gani mami ta saka sa a gaba har d'akin Anwar da sallama suka shiga d'akin.

Zaune yake a bakin gado ga abinci a gabansa saman center table, Amma ya kasa ci inka gansa sai ka tausaya masa kofar ta buge fuskar sa sosai ga goshi ya kumbura, Amma lahab koh a jikinsa tsayawa yayi a gefe yayin da mami ta nemi kujera dake dakin ta zauna tana kara ma Anwar ya jiki tare ba basa hakuri Akan rashin Hankali da Lahab ya masa.

Murmushi kawai yayi cikin sanyin jiki yake sanar da ita babu kome, kome ya wuce wallahi sai a lokacin Lahab yaji tausayin d'an-d'an uwansa, Jin yanda yayi maganar gwanin tausaya, takowa yayi a hankali ya matsa wajen da Anwar ke zaune a bakin gado shikam tsungunawa yayi a gaban Anwar in ya kama hannunsa, Cikin wasa yace "Son Am so sorry for what uncle do it for u, nasan Abinda ke damunka kar fa'iza ta ganka haka da kumburarun lebuna koh, tace a sauke sartin biki"? Ya karasa maganar yana dariya

Shima Anwar d'an dariya yayi a hankali saboda bakin sa, jin turancin da Lahab ya masa kamar wani d'an primary, kaga koh Lahab shiyasa nace ka koma makaranta turanci babu dadi.

Dariya lahab yayi daman shima burinsa kenan yaga Anwar ya sake jikinsa, hira suka soma akan budurwar Anwar fa'iza, Abincin da aka kawo wa Anwar lahab ya d'auka yaja kujera ya zauna yana bawa Anwar kadan kadan A baki ganin haka yasa mami yima Anwar sallama jin mijinta yazo zasu tafi.
Chapter 11 · 0% Book details