← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 122

Sashe 38

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mikewa yayi Yana yamusa fuska haba Inna wannan wani irin zalunci ne ace mutum na kwance Amma zakizo ki tasheshi da sassafen Nan Kamar na daukar Miki kudi Koh naci bashi?

rufe min Baki shashasha ba gwara ma ka daukar min kudin ba Koh fitinan zata tsaya iyya kaina.

toh yanzun dai menene da Zaki ta dani.

Bappa Ado dake sauraron duk abinda suke cewa daga waje, d'aga murya yayi yace,melene dan kaniyanka innar tamu kake fadawa haka don baka da mutunci toh Maza saka kayan makarantan ka ka fitoh muje muji Kiran me ake Mana.

Waro Ido Nabeel yayi da Sauri Jin muryar bappan sa da Kuma abinda yake cewa Wai suje school shap? ya tabbatar yau Ade da Lahab ba zuwa zasuyi ba karshe hukunci ya Kare a kansa shi kadai wallahi Bai Isa ba wane shi.

Wai Ina nabeelu ne,ganinan bappa Ina zuwa ,sai Kuma yayi kasa da murya cikin magiya yace,don Allah innata kice Masa bari nayi wanka kinji dan Allah?

Hararan sa Inna tayi tare da fita a dakin,Shima mikewa yayi ya dau rigansa yasa wayar sa dake zaune a gefe ya d'auka yasa a Aljuhu tare da daukar soson wankan sa Kamar gaske,ya fitoh a dakin tsungunawa yayi ya gaida bappan nasa,amsawa yayi sama sama,lafiya kaga Nabeel kayi Sauri kayi wankan kazo mu tafi nabar shagona a rufe fa.

toh bappa yace da Sauri ya Mike yadau bokati ya ibi ruwa ya wuce bayan gida,Yana shiga aje ruwan yayi ya Kama ginin bayan gidansu daman guntune ya d'ale abinsa ya dirka ta lungun unguwan su,karkade wandonsa yayi ya Kara gaba abinsa.

Yau ne gobe ne Nabeel bai fito ba tun bappa Ado na tsaki Harya Fara mita Yana kwalawa Nabeel Kira,gajiya yayi da jiran nasa ya tashi ya tsaya a hanyan kofar bandakin,Kai Nabeel chanja fata kake ne Kome?wanka Kamar wankan amarya,shuru make ji ba'a amsa ba.

Inna Kam wani tunanin tayi sai Kuma ta girgiza Kai,Ado shiga ban dakin nan ka duba in dai na canki daidai toh Nabeel baya gidan Nan yanzun.

da mamaki Ado yace kamar ya Inna baya gidan Nan?

Kaidai shiga ka duba,ba musu ya shiga Aiko ba kowa sai ruwa da soso fitowa yayi Yana masifa,wallahi Inna Nabeel ya Raina Ni Sam baya ganina da gashi harni zai rainawa wayo toh na fasa zuwa makarantan ina da abinyi Amma saboda shi nabar kome nawa nazo muje naji dalilin Neman sa shine zai min iskanci?

Ah ah baza'ayi haka ba kayi hakuri kaje kaji dalilin Neman naka karka Zama irin sa Mana shi yaki zuwa Kai kaki zuwa ai sai ran shugaban makarantan ya Kara baci kaje kaji in.

Shikenan Inna saina dawo,toh Allah ya dawo dakai lafiya Ado,fita a gidan bappa Ado yayi.

***********

Mubeena Keke napep na tsaidata a kofar school nasu ta d'auka biyan sa kudin sa tayi ta Soma takawa a hankali jiki a sanyaye tana ratsa makarantan tafiya tayi Mai nisa sosai kafun ta iso department nasu,Hawa block in tayi ta shiga Hall in lokacin dalibai sun cika tim a ajin ana jiran lokaci yayi wasu na zaune wasu na karatu wasu na hira wasu na tsatsaye a window d'aga kaga irin cikan nan kasan lokacin jarabawane Koh test kawai ake wannan sammakon da yawan,acan kujerun tsakiya ta hangi kawarta Ruky zaune da wasu friends nasu biyu Suna Hira ana dariya.

Nufarsu tayi tana kiyastawa Ina ma inama itama tana da daman walwala Mana kamar da,ai data mure,Assalamu Alaikum.

Amsa Mata sukayi dukansu Suna had'a Baki tare da kallon ta hannu Suka Bata Suka gaisa tare da matsa Mata itama ta zauna,kallon ta Ruky tayi,ya fama da karatu bestie?

Alhamdulilah Ruky,shuru tayi kawai tana sauraron surutun su Ruky Amma ita Bata saka musu baki ba illa takardan ta data fitar tana bita kafun lokacin shiga jarabawan su ya cika.

Misalin karfe 10 lecture in ya shigo,Suka Soma jarabawan,Basu Suka fitoh ba sai 11:30 gabaki dayan su suka zazzauna akan kujerun dake gindin bishiyar gefen block nasu don Suna da jarabawa anjima,daya kawar tasu ce ta Mike tare da musu sallama zataje hostel ta dawo.

Kallon mubeena Ruky tayi sannan ta Soma Mata magana cikin hikima,mubeena meke faruwa? na fahimci tun jiya kike cikin damuwa duk da kina kokarin boye mini Amma ai labarin zuciya a tambaye fuska meya faru?

dan murmushin yake mubeena tayi,babu kome Ruky kawai dai gajiyane da rashin samun isheshen bacci kinsan in exam yazo bani da nutsuwa sai anyi an gama?

Haba mubeena Koh Zaki boyewa kowa kome bazaki iyya boye mini ba sai dai in Baki yarda dani ba, Koh Baki daukeni a matsayin aminiyar da Zan Baki shawara ba?ta karasa maganar ranta adan bace don tana Jin matukar haushin halin mubeena wasu lokacin akwai zurfin ciki da muku muku.

Mubeena sauke ajiyar zuciya tayi Uhmm Ruky bansan ta Ina Zan Fara ba kinsan kaf duniya bani da kawa Kuma aminiya sama dake Amma akwai abinda baki sani ba guda d'aya, daya Jima Yana damuna Ina boyewa saboda kunya kaina da kaina nake,amma a Y'an kwanakin Nan na rasa meke tadomin dashi ga wani irin tsoro da fargaban rasa abun da nake.

Wani Abu kenan da ban sani ba?

gyara Zama mubeena tayi,tace Ruky a gaskiya bazan boye Miki ba zuciyata bata kaunar Ahmad?

Kamar ya mubeena bata kaunar Ahmad daman bason Ahmad in kike don Allah ba kike tare dashi kike nuna wa duniya kina sonsa?Koh dai kin samu Wanda ya fisa kin wuce chaptern sa yanzun kina son sauyawa da wani? bara na fada Miki wallahi mubeena zakiyi dana sani a rayuwar ki ki dubi irin d'awainiya da Ahmad yake dake duk wani fadi tashi nasa akanki ne shine yau rana tsaka Zaki kawo min wani zance Wai baki sonsa?

a zahiri ne Ruky kuke ganin haka amma a can cikin zuciyata bashi nake so ba na saurare Ahmad ne saboda nace mini da yake da irin yanda yake nuna tsananin Sona,na karbesa ne a matsayin masoyi saboda a tunanina Koh bashi dama da zanyi a rayuwata ya canja min ra'ayin dake zuciya ta amma fa ki sani tun kafun nasan Ahmad na Fara sonsa.

Son waye kenan kike Kuma? bangane kin baiwa Ahmad dama dan ya chanja ra'ayinki ba kimin bayani yanda Zan gane manufarki da kyau.

Mikewa mubeena tayi tsaye ta juyawa Ruky baya tayi dan taku kadan kafun ta tsaya hade da hade hannayen ta biyu waje daya hawaye ne Suka cika a idanunta har Suna sheki da zummar saukowar Kan farin kumatunta.

Itama Ruky mikewa tayi ta matso gareta ta dafa kafadun ta,lalle wannan al'amari Mai girmane mubeena wakike ma wannan so haka wanene shi.

Juyawa tayi Suna fuskar tan juna, hawaye Nabin fuskarta ta Soma magana,Ina sonsa najima da sonsa Ina Jin kunyar sa nayi iyya kokarina na ganin na binne abinda ke Raina ba tare da kowa ya sani ba amma Ina na kasa.

Ki sani mubeena barin Kashi a ciki baya maganin yunwa wa kike son?

Ba kowa bane illah lahabbbbbbb.............

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*

Page 47&48
Wani Lahab kike nufi mubeena ban gane ba?

daman bazaki taba ganewa ba Ruky ni Karan kaina ban ganewa kaina ba.

Ki fahimtar dani wani Lahab kuma.

Kinsan kanina Nabeel?

Kwarai nasan Nabeel Mana sau nawa Ina zuwa gidanku Ina samun sa Yana tsananin Kama dake fari sol kamarke in ban manta ba?.

Yauwa akwai wasu yara biyu da Zakina ganinsu tare da dashi yawanci a gidan mu ma mutum yazo da wuya yatafi bai gansu ba.

gyada Kai Ruky tayi,tabbas na gansu su biyu sa'o'in juna dayan black beauty sosai handsome dashi ruwan Fulani sai dayan Kuma wankan tarwad'a amma Kamar kabila kabila.

Yauwa Ruky kin musu kyakkyawan sani,wannan black in shine Lahab Brown in shine Adewale,wannan Lahab in nake so sannan jiya Kuma Adewale ya tare Ni da wata magana daya matukar tayarmin da hankali don furtashi baraza nane gareni da Kara nisan tani da abinda nake so.

Ruky Kam tama rasa wani hauka ne mubeena take,yanzun mubeena kina nufin wannan yaro friend na kaninki inne kike so sannan wannan kabilar daba musulmi bama kikace yace Yana sonki?

Eh Ruky na Fara son Lahab ne tun da jimawa dayake tare Suka taso da Nabeel Kuma rashin jinsu daya tun Suna yara suka Soma abota,lokacin da Lahab yakai shekara 16 a lokacin sai na Fara Jin wani yanayi daban a tare dashi in har baizo gidan muba sai naji na matukar damu duk lokacin da yazo sai in jini cikin farin ciki na tsane Naga yazo gidan mu zai tafi sai inji tamkar na bisa mu rayu tare a duk lokacin da Suka samu matsala da Nabeel Suka daina ma juna magana Koda kuwa na wuni gudane sai naji tamkar na shekara ne, gashi ba zuwa nake gidan suba duk saina birkice na rasa meke damuwa har sai na gansa natsuwata take dawowa.

A lokacin da na Kara girma saina fahimci babu abinda ke d'awainiya dani face son Lahab,nashiga tashin hankali nayi kuka na roke Allah ya ciremin sonsa a raina Amma Ina kullum Kara Jin sonsa nake na jiya yafi na yau,Yaya zanyi Ruky taya Zan fuskance duniya in d'aga yatsa in nuna Lahab a matsayin Wanda nake so So ma irin na aure?

dole tasa na daina sakar musu fuska na ringa nuna Masa hali Koh Allah zaisa na daina damuwa dashi Amma na kasa na kasa Rukayya,sai kuma ta fashe da matsananci kukan tana dukawa akan gwuwuwin ta.

Itama Rukayya dukawa tayi ta kamo kafadar mubeena ta mikar da ita,hannunta ta Kama suka koma Kan kujera Suka zauna ganin hankalin mutane ya Fara dawowa kansu.

Ke share hawayen ki mubeena shifa so haddin Rabbine,Allah shike dasa so a zukatan bayinsa ba wayonki Koh dabarar ki bace zai rabaki da abinda kikeji ba, illah Addu'an Allah ya zaba Miki abinda yafi Zama Alkhari a gareki.
Chapter 38 · 0% Book details