← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 122

Sashe 29

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu yasa ya sake fusgota domin yanzun ransa ya soma baci, da don baison zuwa gun mai shayi ba da wajen zaije yasai abinsa ya huta da takaici, kuma yasan muneera da ban haushi take amma ya Santa da shegen son yawo kamar masifa, rage murya yayi a hankali yace"ke wawuya yau kwad'ayin indomie nake kuma so nake me ki dafamun da kanki, inna dawo makaranta Zamu fita tare dake yawo"

Washe Baki tayi kamar gonar auduga cikin farin ciki tace da gaske uncle zamu fita zaka kaini gidan zoo da wajen shakatawa?

"Kwarai ma kuwa muneera harda ice cream zan sai miki kisha a gun"

Wani tsalle ta daka da Sauri ta nufi kitchen shima ya Mara mata baya, suna Shiga, ummu kam kala batace ba kamar d'azun sai aikin ta take duk da ta cika da mamaki amma batayi magana ba.

Nunawa muneera basket in yayi ya nemi waje ya zauna, yana kallon ta harta gaba dafa indomie da vegetables ga kwai data soya a gefe, ummu ta dade da FIFA, ganin itama miners ta kusa kammala wa yasasa mikewa ya Shiga store dake manne a kitchen in ya dauko roban takeaway, yazo ya juye indomie a dayan har sai da ya cika tam kafun ya rufe, haka d'aya roban ma ya zuba kwai soyayyan a ciki sai dan karamin flask mai d'aukan kofin shan shayi biyu a ciki, na Silva ne ya zuba coffee a ciki ya rufe, laida fari mai kyau na shopping ya dauka ya Jere abubuwan a ciki harda cups da spoon ya dauka yabar kitchen in.

dakin su ya Shiga a gurguje ya kalli agogon dake like a bangon ganin 7:00 yasa sa aje laidan da Sauri ya nufi toilet, kama kofar yayi zai bude yajisa a rufa, tsaki yaja jin saukar ruwa alamu wanka Rahab ya Shiga, tsabar sauri da yake yau yana Allah Allah ya bar gidan kafun Nnenna tabar gidan su.

*****************
Ta bangaren Nnenna Bata fargaba sai kusan shida na safe,mikewa tayi a hankali ta yayi blanket in dake jikin ta cikin natsuwa ta same kafafun ta izuwa Kasan tiles in, mika tayi sai kuma ta mike ta nufi toilet wanka tayi ta fitoh, jikin ta daure da towel fari, fuskar ta Sam babu walwala ga wani irin kasala dake damun ta da mutuwar jiki stool na mirror ta jawo ta zauna tana mai kallon kanta a madubi, sai kuma ta kalli hannun ta dake d'auke da Allurar ruwa.

Murmushi ta sake data tuna Da yaron jiya daya taimake ta gashi koh sunan sa bata rike ba, drowa ta bude ta dauko Cake in jiya, yaye laidan tayi a hankali tasa hannunta ta yanko kad'an tasa a bakin ta tana taunawa, fuskarta dauke da murmushi ta wani lumshe ido, ada ta d'auka musulmai mugayen mutane ne kamar yanda takeji a kauyen su amma ta hadu da mutane uku masu kirki Wanda hakan ya tabbatar mata ba duka bane aka taru aka lalace ba.

Da sauri ta ware idanun ta jin an sa makulli ata wajen kofar an murda mikewa tayi da Sauri jin yanda aka bangado kofar, bata kara tsinkewa ba saida taga mutanen da suka shigo Wanda koh ba'afada mata ba tasan babu imani a fuskar su kuma ba lafiya or kawo zuba, jiki na bari tace policeeeeeeee

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*

Page 35&36
Su biyu suka shigo ciki yan sanda ne mace dana miji sai mom da ta shigo a bayan su, tare da Jennifer da Sarah, gatanan Ku kamata don ubanta?mom tace tana pointing in Nnenna datayi mutuwar tsaye d'aure da towel mamaki na Neman hallaka ta.

d'ayar police in CE ta nuna Nnenna da yatsa, ke sa kayan ki, jikin Nnenna na bari ta bude baki har rawa yake ta soma bawa mom hakuri"pls mom am sorry karki sa su tafi dani pls"tana maganan tana kuka, wani kallon banza mom ta watsa mata, police in ta daka mata wani uban tsawa, keee kisa kayan ki muje shegiya barauniya.

Waro ido Nnenna tayi jin an kirata da barauniya ita yaushe ma ta dau abin wani harda za'a kirata da barauniya? jin matar ta sake daka mata tsawa yasa jiki na bari ta bude wardrobe inta ta zaro dogon Riga sai kuma ta nufi bandaki, ba musu suma basu hanata ba suka barta ta shiga.

Harta bude kofar sai kuma ta juya ta kalli kikin ta dake rabe a gefen gado don yau kwata-kwata bata gane yanayin jikin saba kamar baida lafiya.

Bude kofar tayi ta Shiga don harga Allah bata taba Shiga Matsala irin nayau ba, kayan tasa cikin rawan jiki ta zura dogon Rigan, amma ta kasa fita daga toilet in jingina tayi da kofar ta lumshe idanun ta bata son misbehave ta jawo wata matsala koh magana batason yi bare wani abin ya faru.

Ji kawai tayi an bankado kofar da karfin gaskiya Wanda ata dalilin bankadar har takai ga faduwa a kasa, mom ce ta shigo batayi wata-wata ba ta shakota tare da janta da karfin ta tafito da ita daga cikin toilet.

Kuka ta soma da karfi Amma sai da mom ta fito da ita daga toilet in ga hannun ta dake dauke da allura, da Sauri police in tazo ta tasa keyanta tana janta har suka fito falo, suka nufi kofa da ita, daidai lokacin Abraham ya turo kofar falon ya shigo, da mamaki ya tsaya rike da kofa yana bin su da kallo ganin Nnenna a hannun yan sanda ga mom a tsatsaye a falo alamu dai babu lafiya.

Mom Ya haka lafiya me Nnennan ta musu?

Koh kulasa mom batayi ba sai ma bawa police in daman fita a kofar ba tare da ta amsa masa ba, shima ganin da gaske fitan za'ayi da ita yasa sa sa hannu ya fizgo ta rai a bace ya sumo magana, haba mom wai menene haka me yarinyar nan ta tsare miki ne mom?

Wanke sa da mari mom tayi cikin zafin rai ta soma masifa, kai harka isa nace Abu kace ba haka ba, eh bana sonta kuma yau sai tasan ta taro March.

dafe kumatun sa yayi da mamaki yake kallon ta wai yau mom ce ta mare sa rabonsa da a mare sa ai harya manta, mom ni kika Mara?

Yes na made ka koh zaka ramane?

Girgiza Kansa yayi,mom bazan rama ba amma wallahi bazan bari a tafi da ita ba har sai an gayamin abinda tayi za'a tafi da ita.

Rike baki Sarah dake tsaye tun dazun tayi kafun tace, wai kai Abraham INA ruwan ka da itane?koh abinda mom ta mata toh sata tayi.

Kallon ta yayi sai kuma ya dubi Nnenna dake kuka, meta sata mata?

Wani shegen kallo ta jefa masa, baza'a fada ba, harsai munje station.

toh a gaskiya mom Indai hakane ba'a mata adalci ba ya za'a dau mutum baisan abinda yayi ba, sai kuma ya kalli yan sandan fuska a hade, tare da nuna muzu kofa, kunga yallaboi kuje kawai mu tattauna a waje, ba musu suka bisa waje,ga wannan ya mika musu kudin daya zare a Aljuhun sa kuyi hakuri abinda ya shafi family ne?don shikam harga Allah bai yarda da abinda mom tace ba, Ba musu suka karbi kudin suka tafi,

Dawowa falo yayi yanuna wa Nnenna kofar dakin ta yayi, shege kisa uniform kizo na sauke ki a school, da Sauri kuwa ta nufi kofar ta shiga, mom kam bakin ciki ne kamar zai kashe ta wai ya zatayi da Abraham ne yabar Shiga harkar yar iskan yarinyar nan rai a bace ta zauna a kujera tana mai bakin cikin rugujewar plan nata, Jennifer ma zama tayi tana wani langobe kafar data kone jiya, Sarah kam tsaki kawai tayi ta koma room nata Dan yau bata da lecture shikam yana tsaye yana jiran fitowarta.

*****************
tsabar sauri kasa hakuri lahab yayi ya sabi towel nasa ya fita a dakin ya nufi dakin uzaifa, da sallama ya tura kofar daidai lokacin shima uzaifa ya gama shirin sa tsap yana fefesa turaren sa ganin lahab yasa sa dakata wa ya bisa da kallo ganin sa d'aure da towel ya shigar masa bandaki, girgiza kai kawai yayi ya sabi jakansa yayi waje.

Shafshaf lahab yayi wanka da Sauri Sauri ya fito dakin ya nufi Nasu harda dan gudu gudun sa, daidai lokacin Rahab ma ya fito cikin shirin sa sanye da uniform a jikin sa, kallon lahab yayi kai yasa ya fita a dakin, shima lahab Shiga yayi da sauri yad'au uniform nasa yasa jakan sa da laidan abincin ya saba ya fita a dakin cikin hanzari ya maida kofar falon ya rufe, a sannu sannu take ratsa falon Nasu har kofar falon hannnu yasa ya bude kofar ya fitoh babban falon gidan.

Zazzaune suke kamar kullum akan dinning harya wuce su baiyi magana ba sai kuma ya dawo da baya tunawa da yayi da akwai fa uncle a dinning in,gashi ba addayiya bata fitoh ba, Dan rusuna wa yayi yana gaida Abbu"good morning yaya"?

Kallon sa Abbu yayi da mamaki yau shine sanye da uniform ba tare da anyi hali ba gashi wai harzashi makaranta, morning Lahab sai ina haka kake ta saurin nan?

Murmushi yayi ya dan tsosa keyar sa" wallahi yaya school zani Sauri nake na makara yana maganar yana kallon agogon dake manne a tsintsiyar hannun sa.

Dukan su suka zuba masa ido da mamaki wai yau lahab ke cewa zaiyi late, gyada kai kawai Abbu yayi bai kara magana ba, juyawa yayi ya gaida uncle dake hade da fuska yana cin abinci lahab yayi, kin amsa masa muzammil yayi sai nuna masa kujeran dake gefen sa da yatsa Wanda koh bai tambaya ba yasan me hakan yake nufi.

Kin zaman yayi cikin sanyi yace "uncle so nake daman na wuce da wuri ga abinci na nan a laida yana maganar yana daga laidan hannun sa.

Kallonsa muzammil yayi, kai wani Sabon salone cin abinci a kula ka fara koh me?
Chapter 29 · 0% Book details