← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 122

Sashe 59

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da sauki Rabin Raina Yana ciki muje Bismillah

Bude motar yayi ya dau laidodi manya dake ciki,da Sauri umaima ta matso tasa hannu zata karbi laidan,kaucewa yayi Yana dariya ya rufe motar yace"Kinga Bari Zan idar da ladana basai kin tayani ba"kaga ka bani kawai bakon ka annabin ka kana son mu shiga ciki Addayiya tamin fada ban karbe abin hannu Bako ba, murmushi kawai yayi ya bata laida daya shima ya rike daya Suka jera tare Suna tafiya itace a gaba Yana binta a baya.

Zaune suke a dakin Addayiya kansa a kasa irin anzo gidan surkunayen Nan kansa a kasa suke gaisawa da Addayiya sai umaima dake zaune a bakin gado,Lahab da Rahab nakan gadon a zaune"gaskiya mungode Abubakar Allah yabar zumunci Allah dai ya nuna Mana ranan bikin Nan ayi a wuce wajen, Addayiya tace Kara sunkuyar da Kai sadeeq yayi Yana ma Lahab ya jiki amsawa yayi rahab ya gaidashi ya amsa da fara'a mikewa umaima tayi da Sauri Addayiya tace"Ina Kuma Zaki kibar Abubakar in kuma"zanje na sanar dasu mamu Wai zai shiga falo ya gaidasu" ta bata amsa ba tare data jira abinda zata ceba tafita a dakin,itama Addayiya mikewa tayi tadau laidan daya kawo Mata ta bude wardrobe nata tasa ta rufe tare da fita a dakin,ganin babu kowa daga shi sai tagwaye yasa sa d'aga kansa ya kalli Lahab yace"am in babu damuwa small uncle Niko so nake muyi magana da Kai wata Alfarma nake nema.

"Wace irin Alfarma kenan sadeeq ince dai lafiya"? Lafiya Lahab daman akan maganar kawo lefe ne abinda ma ya dagoni kenan zuwa gombe nazo na sanar Mata akan ranan talata za'a kawo lefe toh saina zo na tarar da abinda ya faru Allah ya kiyaye na gaba,Ameen Lahab da Rahab sukace Suna cigaba da sauraron sa,shine tace a aje maganar kawowa, yau na tashi da niyar wuce wa sai ga kiranta tace min an ganka harma ka dawo gida,dana Mata maganan kawo Kaya shine tace Wai babu Rana sai Randa kaji sauki gashi mom nata kirana akan maganar lefen nakasa ce musu kome pls kasa baki akan maganar na rasa wazan tinkara ga umaima da taurin Kai?

Rahab ne yace kana nufin ita tace babu maganar lefe ba ranna kawowa bayan Kuma date na biki saura wata daya"?cikin dan annashuwa ganin ya samu goyon baya yace"eh wallahi nima shine hankalina yadan tashi"karka damu Zan ma Addayiya magana karku fasa kawowa ranan Tuesday in Ina jibine ma"?eh sadeeq yace sai Kuma yayi shuru ya fasa maganar da zaiyi ganin umaima ta shigo tsayawa tayi tana kallon su ganin Kamar wani abin suke kullawa tace"ka taso muje ku gaisa"mikewa yayi yabi bayan ta Suka fita a dakin,Suna fita saiga Addayiya ta dawo a lokacin Lahab ya sanar da ita abinda ke faru Aiko tace zata samu mamu da Abbu duk da ajesu akan maganar lefen.

Mamu taji haushi matuka na zuwan sadeeq gaida Lahab amma bata nuna Masa a fuska ba sai bayan ya fita sosai tayita zagin umaima,washe gari da safe Rahab da sauran yaran Suka shirya cikin kayan makaranta suka tafi Abbu ya gama Shirin office NASA harzai fita Addayiya ta kirasa shida mamu ta musu bayanin akan za'a kawo lefen umaima gobe Tuesday sosai abin ya baiwa mamu mamaki ace Kamar ita uwar umaima bata San da zancen lefe ba sai da Addayiya ta Kira ta ta sanar da ita lallai yau zataci uban umaima,mikewa tayi a fusace zata bar dakin Abbu ya daka Mata tsawa tare da Bata izinin komawa ta zauna komawar tayi ta zauna Rai a bace Abbu yace"Abba haleema bazaki taba hankali ba tunda har yanzun Baki da hankali ya uwata na tsaka da magana Zaki tashi ki fita wannan ai raini ne"?

Rabu da ita ai haleema halinta sai Allah Inda sabo na Saba da shi nasan babu abinda ya Bata Mata Rai sai zancen lefe gobe Kuma ta Fara ji a bakina Addayiya tace tana girgiza Kai,Abbu yace haba Addayiya ai a tunani na Koh ke Zaki iyya tarban masu kawowan basai haleema tasa Baki ba Amma menene don kin sanar da ita Kuma ni naji dadin hakan Koh banza iyayen yaron Nan sun girmama mahaifiyata"bama su bane Umar yaron ne daya zo duba Lahab yau yake sanar dani akan Suna so zasu kawo Kaya Amma umaima tace karsu kawo sai Lahab yaji sauki.......ai bata gama magana ba mamu ta amshe da cewa"yanzun akan yaron Nan har umaima na cewa a d'aga kawo lefen don bata da hankali Ni na tabbatar wallahi Koh mutuwa nayi na tabbata yayan Amina bazasu fasa abinda sukayi niyar Yi ba akan me zatace haka wallahi yau sai ta gane kuranta.

Addayiya tace don Allah haleema inkin tashi Mata hukunci ki kasheta har lahira bake kince baki da kunya ba Bismillah jeki tabata Ni Kuma Zan nuna Miki karfin ikona a gidan Nan ShaShashar banza Mara hankali,Abbune ya Soma bawa mamar tasa hakuri itakam mamu mikewa tayi tabar dakin,tasan Koh hauka take yanzun dai bazata lakato wata maganar ba shiyasa ma bata bi takan umaimar ba Kuma batace Mata kome ba sai dai fuskarta kawai mutum zai gani ya gane tana cikin bacin Rai,d'aga waya tayi ta Soma kiraye kirayen kawaye da Yan uwanta akan gobe za'a kawo kayan auren umaima,duk Wanda ta Kira sai yayi Mata mitan akan sai yau za'a sanar dasu hakuri kawai take basu.

Abbu na fita a dakin Addayiya compound ya nufa zai bar gidan da Sauri mamu tabi bayan sa har ya shiga mota ya hangota yaso yaki tsayawa amma ya daure yaji dame tazo,abinka da Mai jiki dan Sauri da Tayi yasa ta sauke numfashi akai akai bayan isarta jikin motar sa ta Soma magana daker daker"daman Alhaji Naga fita zakayi bakace min kome ba?kallon banza ya Mata kafun yace toh me kike son nace Miki haleema?

Haba Alhaji kana fa zaune kanaji Addayiya tace gobe za'a kawo lefe amma baka bani kudin da zanyi sayyayyan abubuwan tarban Baki ba kasan wannan shine aure na farko da zamu d'aga a gidan Nan auren umaima da Anwar gaskiya bana son Abinda zaisa a Raina mu nafison kome a wadace,shikam Abbu Yana mamakin irin jaraban karya dason kudi da Haleema ke dashi a rayuwar ta amma baice Mata kome ba har Saida yaja dan lokaci ita dai tana tsaye tana kallon sa yace"Haleema wa'inda zasu kawo kayan Nan fa ba a gombe suke ba a bauchi ne Koh danko zaku dafa musu ai kye bari gobe yayi a dafa xuwa yamma ai ya dafu Koh?

Jin abinda yace yasa ta hade rai tace"haba dan Allah kafa San yau nake son naje nayi sayyayyan kayan aiki irin su kaji da sauran su kaga gobe in Yan uwa Suka hallata sai su Fara aiki kawai,zaro Ido yayi ya nunata da yatsa yace"yanzun haleema da bakin ki kike cewa Zaki kasuwa sayyayyan kayan abinci wallahi karki kuskura Kuma kudi ne dai bazan bayar ba saina dawo office Yana karasa maganar yaja motarsa yayi gaba ya barta a tsaye agun tana juyawa zata koma cikin gida Kamar ance ta kalli bini sukayi Ido hudu da ummu dake saman bini tana kallon su,a fusace mamu ta shiga falo ta nufi upstairs don wallahi yau saita nunawa ummu bacin ranta na sa Mata Ido da take a gidan.

Ummu dake sama da Sauri ta Soma saukowar daga saman jin takun steps a fusace yasa ta bude dakinta dake sama ta shiga tare da maida shi ta rufe da karfi ta murza key harga Allah masifar mamu ya isheta haka bata son cecekuce a gaban yara.

********************
tun da sassafen mubeena ta kasa nutsuwa yau Monday sunada paper batason zuwa makarantan balle ta hadu da Rukayya ita Soma tayi Inna ta tashi suje su duba Lahab amma tace sai ta dawo makaranta sai suje ga Nabeel dake ta surfa Mata nacin ta shirya yau da kansa zai Rakata makaranta lura da yayi duk jikinta a sanyaye,ruwa ta Iba taje tayi wanka shima Nabeel wanka yayi ya goge kayan sa bayan ta shirya dumamen tuwon daren jiya sukaci,Nabeel ya dauko kayan daya dinka jiya da niyar kaima Mai kayan tunda jiya bai samu ya karasa da wori ba sallama Suka ma Inna dukan su Suka fita a gidan tafiya suke Suna dan taba Hira kowa ya gansu yaga Yan uwa gasu farare tass farin nasu daya ne ga Kama na jini,sunkai almost 30 minutes basu samu Keke da zai kaisu makarantan su mubeena ba in Kuma Suka ce drobe basa samun Wanda ba mutane kowa yasan yanayin garin gombe in gari ya waye especially ranakun makaranta akwai go slow sosai hakan ya taimaka wajen Kara lattin nasu sosai hankalin ta ya tashi ganin lokacin shiga jarabawan bai wuce 40 minutes ya rage ba,Nabeel wayar sa ya zaro a Aljuhu ya lalube number Ade ya Kara a kunnen sa.
Chapter 59 · 0% Book details