Sashe 50
Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kaga Rahab wannan tsakanina da shine bana son kasa kanka a cikin wannan maganar,sannan bazan goyi bayan kabar cikin gidanku ba Yan uwanku zasuga Kamar Nike zugaku Koh Kuma so nake na karbe ku,don hakan yanzun dai muje station daga Nan sai na kaika gidan yayan ka jafar ka zauna acan.
Haba Mami ni wallahi bazan zauna a gidan Yaya jafar ba wata rana nanne tamin gori itama,baga irinsa ba Mami kinje kin aure tsoho karshe muntashi a wahale da ace mahaifin mu na raye na tabbata bazan tsaya tunanin Inda Zan...............daka Masa tsawa Mami tayi cikin Jin haushi tasoma magana,yanzun kaima Rahab maganar da zaka fadamin kenan Wai meyasa mutane suke min haka ne, watoh kaima ka kawo Kai har kana da bakin fadawa uwarka maganan ta aure tsoho Koh? sai Kuma ta kifa kanta a siterin motar tana Mai girgiza kanta tana alhenin abubuwan da Suka shude duk mahaifinta ne yaja Mata duk shiyasa ta cikin wannan matsalan,da Sauri ta kauda tunanin tare da istingefari tunawa tayi karfa tayi sabo kome na duniya dama Rubuceccen Al'amari ne.
don Allah Mami kiyi hakuri bazan Kara ba wallahi bawai rashin kunya na Miki ba amma abin na damuna Inna d'aga Ido Naga ya Umar da ya jafar da Aunty shamsiyya a matsayin yayuna ne su duka duk sun tsufa gwara gwara ma ya muzammil ga yawan gori da Addayiya da Mami ke Mana akanki abin baimin dadi Sam.
d'aga kanta Mami tayi daga Kan siterin ta kunna motar ba tare da tayi magana ba tafiya suke babu Mai magana har Suka Isa station Suka mikawa Yan santa case in Lahab daga station in titin gidan ta Mami ta nufa da Rahab,ganin haka yasa sa saurin dakatar da ita,Mami Ni bazan zauna a gidan ki ba ki kaini gidan uncle muneer saina zauna a wajen sa kafun Lahab ya dawo saimu koma gidan mu Koh?
tad'anji sanyi a ranta Jin yanda yaron nata ke Mata magana watoh ya hakura da fushin barin gidan nasu,amma bata nuna Masa ba sai Kara tamke fuska da tayi tayi rebas ta Kama hanyar unguwan su Uncle muneer in 30 minutes ya kaisu unguwar gangarawa tayi har kofar gidan tayi parking bude motar tayi ta fita Shima Rahab sauka yayi a motar ya bude baya yadau jakansa yabi Mami cikin gidan.
da sallama Mami ta Shiga gidan amsa Mata salamatu tayi,ah ah wa nake gani Kamar Hajiya Amina sannu da zuwa Bismillah,dan murmushi Mami tayi sannan ta shiga falon gidan Zama tayi a Kan kujera yayin da mustapha dake kwance Yana danna waya ya mike Yana gaidata tare da fita a falon Jin muryar Rahab a tsakar gidan Yana sallama,amsan kayan Rahab in yayi ya nufi dakin sa dake kusa da sauron gidan ya shigar da kayan wajen,dan leko falon Rahab yayi ya gaida salamatu sannan shima yabi mustapha dakin,bai bi mamin falo ba.
Salamatu daki ta Shiga bayan sun gaisa da Mami ta Kira Mata yayan ta muneer sannan ta basu waje sosai Mami Suka znta da yayan ta Kuma Shima ya Mata fada sosai data sanar dashi Lahab yaje wajenta Harya fusata yabar gidan nuna Mata yayi shi yaro Mai rawan Kai da lallama ake binsa daja a jiki daga karshe Kuma ya nuna Mata babu kome Rahab yazo su zauna ai dashi da mustaph duk daya suke a wajen sa sosai taji dadin hakan tare da mikewa tama yayan nata da matarsa sallama fitowa tayi a falon tasa takalminta ta nufi Sauro zata fita yayin da salamatu ke binta a baya Suna dan Hira,tsayawa tayi a kofar dakin mustapha ta kwalama d'an nata kira.
Rahab dake zaune a dakin mustapha nata zuba Masa hira,ya amsa Mata tare da mikewa ya fitoh ganin ya fiton yasa Mami nufar kofar gidan tana ma salamatu sallama itama salamatun asauka lafiya ta Mata ta koma cikin gidan,bayan sun fita wajen bude purse nata Mami tayi ta zaro ATM card nata guda daya ta mikawa Rahab ba tare da tayi magana ba,amsa yayi da Sauri Yana godiya,nasan zakaji sauyin rayuwa a gidan Nan don ba irin gidan ku bane daka Saba da laushi da AC ga card Nan Koh zaka bukace wani abin saika zare ka saya ban baka don kayi almubazzaranci dashi ba.
Insha Allah Mami Allah dai ya bayyana dan uwana duk da Ni Mami gani nake kamar wallahi ba b'ata Lahab yayi ba mu munsa Kan mu a damuwa,kindai San iyya shegen sa.
dan sassauta fuska Mami tayi,toh yanzun Rahab in ba b'ata yayi ba meyasa har yanzun bai dawo ba sannan tunda yake bai taba barin gida ya kwana wani waje ba tare da sanin yayan ku ba sai wannan Karo nidai gani nake Kamar akwai abinda ya samesa.
Mami ki kwantar da hankalin ki taima ma gidan wasu abokan nasa yaje yayi zaman sa kinsan fa yayi laifi Kuma ya tabbatar za'a hukuntashi Koh hakan ma zai hanasa zaman gidan.
Toh Allah ya shiryesa koma me ake ciki zanji a wajen Yan sanda.
Ameeen ya Allah Mami Rahab yace, Yana tsaye Harta shiga motar ta tabar layin unguwan sannan ya juya ya koma cikin gidan.
**********************
Dr ne ya shigo cikin fara'ar sa gaidashi Lahab yayi itama Nnenna ta gaidashi amsa musu yayi sai wani irin kallo yake Mata ganinta sanye cikin wando da riga sunyi azaban karbanta ta fito Ras da ita a cikin kayan,Lahab Kam ji yayi makokonsa ya cika amma baice kome ba,itama Nnenna aje bucker in tayi ta zauna a kujera.
Dr ne ya maida dubansa zuwa ga hannun Lahab Yana Masa ya jiki da mamaki yabi hannun da kallo sanna ya kalli karfen ganin ruwan Koh rabi baiyi ba gashi Kuma ya cire,ah ah Hassan ya haka yanaga an cire maka ruwan Kuma wace nurse ce ta cire?
cikin dan basarwa Lahab yace"am nine na cire naje nayi wanka ne naci abinci"
Meyasa ka cire sannan wani irin wanka kayi a irin wannan yanayin da kake ciki ai ba'ason kana wanka akai akai goge maka jiki za'a nayi ba wanka ba, muga hannu Koh ruwa ya shiga,ai saika bata Mana aiki.
Mika Masa hannu Lahab yayi likitan ya dudduba sai fad'a yake Kamar bashi ya shigo da fara'a ba shidai Lahab shuru kawai yayi har likitan ya karasa masifar sa kafun ya maida Masa da ruwan tare da Karin wasu Alluran,ya rubuta musu magani ya basu akan su sayo,amsan takardan Nnenna tayi sannan ta koma ta zauna,Shima likitan fita yayi a dakin.
Mikewa Nnenna tayi ta matso kusa da Lahab a hankali ta soma Masa magana"Lahab Lahab"ya jita Sarai amma yaki amsa wa haka kawai takejin haushin likitan ga masifar da ya gama surfa masa"kayi hakuri Lahab amma fa gaskiya Dr ya fad'a ya Kamata kabi ka'idar likita saika samu lafiya karfa ka manta tsagen kashine a hannunka kayi Wasa da hannun Nan sai kaga hannunka ya lalace"
Wani irin juyowa Lahab yayi cikin haushi Jin abinda tace Wai hannunsa ya lalace"aiko wallahi hannuna inya lalace kece sula Ina zaman xamana tsabar mugunta daga Miki abin arziki saiki sa hannun Nan naki na samudawa ki kwade hannun na Saida Kashi ya tsage sannan kice min innayi Wasa da hannu na ya lalace"?
Sake baki tayi tana kallon sa da mamaki tana Al'ajabin lamarin sa,dan Jan numfashi tayi kafun ta soma magana"toh shikenan"sai Kuma ta juya zata fita a dakin ganin hakan yasa sa tambayar ta"Ina zakije Kuma"?
tsayawa tayi bata juyo ba"zanje wajen likitane ya taimaka min da waya na kawo maka ka Kira gidan ku ka sanar dasu halin da kake ciki kada hankalin su ya tashi kaga nima saina samu na koma gidan mu"
"Zonan shine abinda Lahab yace Yana kallonta juyowa tayi ta dawo bakin gadon ta tsaya binta da Ido yayi sannan ya nuna ta da yatsa,"yanzun kina nufin a hakan Zaki fita kina yawo kina tallan jiki a cikin asibiti Maza na kallon ki Wai meke damunki ne baki da kayan da Zaki saya saina haukan Nan,bama wannan ba ce Miki nayi kije ki karbo min waya"?
bin jikinta tayi da kallo sannan ta Kara kallon sa"meya samu kayan jikin nawa da kake cewa Ina tallan jiki,sannan maganar ka aikeni Koh baka aikeni ba duk zanje na amsa wayar na kawo maka"tana karasa maganar bata jira Mai zaice ba ta juya zata bar wajen, hannun sa Mai lafiyar Kuma ke d'auke da laidan ruwa yasa da karfi ya riko hannunta tare da ingizata har Saida tayi baya tagaltagal zata Fadi Kara Jan nata yayi Saida ta Fado akansa.
Kallonsa tayi fuska a hade Kamar yanda Shima ke kallon ta"meyasa kake Wasa da lafiyarka ne"?
baibata amsar tambayar da ta Masa ba sai wani tambayar da Shima ya jefo Mata"kingaji da jinyata"?girgiza Masa Kai tayi tana son tashi akansa don har lokacin baisa riga a jikinsa ba"amma meyasa kikeson na Kira Yan gidan mu sannan kema kikeson ki koma gidan ku"?
"saboda hankalin Yan gidan ku ya kwanta na gidan mu ma ya kwanta"
Maidata kwancen yayi daga kokarin tashin da take yasa bakin sa a kunnenta"kinsan wanene Ni"?ya tambaye ta a hankali.
Ah ah bansani ba"toh bari kiji na fada miki Ni da kike ganin nan d'an tsohon minister ne sannan yayana babba,shararen dan kasuwa ne d'ayan Kuma gawurtancen soja ne dayan Kuma kusan gwannati ne,in Kika kuskura sukaji labarin kece Kika tsagamin Kashi burbudinki ma Y'an gidan ku bazasu gani ba bare gudan ki,gwara ki rufawa kanki asiri kiyi jinyata harna warke na koma da kafata hannuna sumul"
wani kallo take bin fuskar sa dashi kafun a hankali tace"Ni kasan wacece"?dan murmushi yayi sanna yace"wacece ke"bude Baki tayi a hankali zata Yi magana sukaji gyaran murya a dakin alamu mutum ne........................
🍀 *by Ruqeenjala* 🍀
*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*