← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 122

Sashe 58

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Manna Masa hauka Rahab yayi bai basa amsa ba hakan ya Sasa kallonta yace"waini don Allah kumin magana Mana menene haka na Mannin hauka,turo kofar akayi zulaihat ce ta shigo hannunta dauke da plate,uncle sannu ya jiki sai Kuma ta Mika Masa plate in hannunta gashi inji ummu waina kawo maka,karbar plate in yayi yace"gaskiya kice Mata na gode"budewa yayi gasheshen Naman ragone yasha yaji sosai yana kamshi ga cabbage a Kai rufewa yayi ya aje don harga Allah ya gaji da ciman Nan yau yaci nama haryafi a kirga hannun zulai ya rike ya ajeta a gefen sa yace"zauna anan muyi magana"zaman tayi cikin Jin dadi tana kallon sa"meya faru jiya a gidan Nan har Uncle muzammil ya tafi meya had'asa da Rahab"shuru tayi tana kallon sa tunani take ta fad'ane Koh karta fada ga Kuma Rahab da Addayiya dake wajen fahimtar hakan yasa sa mikewa hade da kamo hannunta Suka bar dakin,Zama yayi akan kujeran falo itama ya ajeta yace"toh yanzun ai saiki fadamin abinda ya faru naji"Zama ta gyara a hankali ta soma magana,ba jiya bane Wai Mami ta Mari mamu shine sai Mami ta zageta ran Uncle Rahab ya baci ya tattara kayansa zaibar gidan zaibi Mami shine uncle Rahab yace............................tass ta mayar Masa da yanda abin ya faru duk da a farko Lahab yayi farin cikin barin muzammil gidan Amma yaji haushin abinda Rahab ya Masa,sai kuma ya basar yace"Ni gaba ta kaini tunda bani na zagesa ba bare a sani a gaba"ya mike ya koma dakin yayi kwanciyar sa abinsa.

***********************
Fuskar dady babu walwala daga hospital in station sukaje yayi sign sannan Yama mutumin da yakai rahoton ya ganta a asabiti kyautar 3k amma mutumin yaki karba Sam yace ya yafe wallahi daga Nan gida Suka nufa har lokacin Dad baice Mata kome ba parking yayi a kofar gate na gidan su,bude kofar motar Nnenna tayi da Sauri ta sauka ta tura karamin gate in ta shiga a take karnuka Suka mimmmike Suka nufota itama bata wani damu ba ta soma kiciniyar bude babban gate tsuntsunata sukayi sannan Suka koma Suka kwanta wangale gate in tayi dad ya shigo da motar sa parking yayi ya bude ya fita baibi ta kanta ba ya bude kofar falo ya shiga,binsa tayi a baya a hankali jikinta duk yayi sanyi bataso ta Bata Masa ba itama batasan ransa zai baci har haka ba,mikewa su mom sukayi dake zazzaune a falo cikin alhini,shigowar dad da Nnenna yasa Suka Mike Suna tambayar sa a Ina yaganta kala baice musu ba sai tura kofar Nnenna da yayi ya shiga ya zauna akan stoll na dakin yayi shuru,kanta a kasa ta gaida mom kasa amsawa tayi itama Nnenna Bata damu ba tabi dad dakin nata shiga tayi tana tafiya Kamar Wance kwai ya fashewa a ciki zamowa tayi ta zauna akan tiles har lokacin kanta a duke wani irin tsawa da bata tabajin dad Yama Koda yaran cikinsa bane ya sake Mata"keeee meya hadaki da wannan yaro Mara kunya dan hausa people innan am asking you for the last time wallahi ki gayamin gaskiya.

A hankali tace"am so so sorry Dad ban d'auka haka yake ba don Allah kayi hakuri nima ban Sansa ba accident muka samu lokacin baya hayyacin sa shiyasa na d'auke sa da taimakon Mai Keke mukaje asibiti bai farfado ba sai yau"tana gama maganar ta rumtsa idanunta da karfi saboda karya data fetsawa mahaifin nata duk da ba dabi'arta bane karya amma yau Lahab ya saya tayi.

A fusace dad yace,watoh kece uwar tausayi duk musulmai dake wajen a rasa Mai taimaka Masa saike uwar gwaninta sannan da wani kudi kike kula dashi a hospital in tunda har waya ma baidashi?

Duk da taso tadan rikice amma ta dake tace"akwai kudi a Aljuhunsa masu yawa dasu nayi amfani"Jin abinda tace Sam baiyarda ba ga wani bacin Rai daya tinkaro sa don shi a rayuwar sa yaki jinin musalmai da Christian ta taimakawa dayafi kowa murna,d'aga hannu yayi zai mare ta da Sauri ta Kare fuskarta shima hannun nasa tsayawa yayi Bai mare ta ba don sai Kuma yaji baison Marin nata komawa yayi ya zauna ya sassauta muryar sa ya Soma Mata magana,Kinga Nnenna Nan ba Enugu bane rayuwar Nan daban dana Shan banason ki jajibowa kanki matsala bana son kina mu'amala da ire iren mutanen Nan Baki ganin su Sarah da Jennifer kin taba ganin Koh maganar kirki ya hadasu da musulmai kina ganin layin mun Nan kwata kwata christoti Bamu da yawa Amma bama shiga harkan su don haka bana so karki Kara karki sake daga yau ma Zan nema miki drive da zaina kaiki makaranta tunda Naga Gloria da Abraham amanar da na Basu na tafi ba iyya rikewa suke ba,Yana Gama magana ya mike yabar dakin.

shuru tayi tana tunanin meyasa Wai kowa yake cewa musulmai Basu da kirki ne amma ita Bata ga rashin kirkin su ba ta hadu da shayibu(mijin ma'u) da Lahab Bata ga wani abin aibu a tare dasu ba amma tunda uncle Nata yace ta bari toh zata barin tunda bata San dalilin da yasa yace Mata haka ba wata Kila Suna da wani haline da ita Bata gane ba,mikewa tayi ta soma dube dube a dakin tana Neman Kiki kiransan ta somayi a hankali tana dubasa,,banko kofar dakin akayi mom ce ta shigo ranta a bace ta Soma magana harke kin Isa a dauko Miki d.............................

🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*

Page 73&74

A d'auko Miki driver Jennifer da take Yar masu gida ba'a kawo Mata drive ba saike banza toh wallahi Baki Isa ba ita dai Nnenna na tsaye kanta a kasa shako wuyanta tayi tace,kee magana nake Miki fa kin manna min hauka watoh kin gama karuwan cin ki shine Zaki dawo kuma a nema miki who a u?fisge riganta Nnenna tayi ta bude kofar toilet ta shiga tare da banko Mata kofa,sosai mom ke masifa ita dai Nnenna batace kome ba hartaji mom ta fita a dakin kafun ta fito tana kuka tana Kiran kiki,tsunguna wa tayi tana leka kasan gado duhu ne babu kome bayan wardrobe duk ta dudduba amma Bata gansa ba.

gajiya tayi ta koma bakin gado ta zauna tare da zuba tagumi tana tunanin Koh dai Kiki ya mutune da yunwa toh amma inya mutu Ina gawan sa ai da zata gani,kuka ta Soma a hankali tana cewa"ka taimaka Kiki ka fitoh tsawon shekara 10 Muna tare sanan yau kawai saika tafi ka barni,ta sake sabon kuka da karfi turo kofar akayi Abraham ya shigo dakin da Sauri ya karaso bakin gadon ya zauna hannu yasa zai Kama nata cikin tashin hankali Yana tambayar ta meyake faruwa hannu tasa ta buge nasa tare da mikewa rai a bace tace"fita mini a daki banason ganin ka ka fita nace"tana magana tana kuka sosai.

zamowa yayi daga Kan gadon yayi kneel a kasa ya Soma magana,haba sister meyayi zafi haka zakice Baki son ganina menene laifina kinsan irin tashin hankali dana Shiga kuwa?na rashin ki a kusa dani naji tsoro sosai,komawa tayi ta zauna tana cigaba da kuka Koh banza tad'anji sanyi ashe akwai wa'inda Suka damu da rashinta a duniya,matsowa kusa da ita yayi sosai cikin lallami yace,kiyi hakuri ki sanar dani Ina Kika shiga wallahi na damu rashin ki na samu Dad amma yaki ya kulani pls tell me Ina Kika shiga?

dan shuru tayi sai Kuma tace"accident muka samu a hanyan toh Wanda mukayi accident in dashi ya samu rauni sosai shine na taimaka na zauna agunsa Ina jinyar sa"da mamaki yace toh meyasa ran Dad ya baci saboda dan abinda kikayi Nan sannan nasan saboda baki da wayane da Zaki Kira ki fada Mana amma Bari na fita Zan sayo Miki Sabon system?girgiza Masa Kai tayi shima girgiza Mata yayi yace,saboda me?meyasa duk lokacin da Zan Baki Abu saikin Raina ne?da mamaki tace"raini Kuma"eh mana ya bata amsa dan rufe fuska tayi tace"nifa ba Raina wa nayi ba kawai ka barshi don nasan in mom ta sani ranka da nawa ne zai baci.

Mikewa yayi daga durkusen da yake har lokacin idanunsa na kanta yace,kawai amsa nake son naji kinaso Koh ah ah?nifa bawai bana so bane kawai dai.........dakatar da ita yayi ta hanyar cewa,nifa banson kice kome waya dai Zan sayo Miki sauran aiki ya rage naki,dubeki Kamar Mai wayo amma babu,Yar kauye kawai duk abinda aka baki dole ne saikin nuna an gani kawai boyewa zakiyi kina amfani da abinki Koh su Sarah karki bari su gani kinji ?"toh nagode"tace tana Kara zuba tagumi har ya bude kofar zai fita sai Kuma ya dawo ya tsaya again yace,meke faruwa ne sister Naga Kamar kina cikin damuwa?

"Banga cat nawa ba brother"tace tana Kara fashewa da kuka tana dad'a rufe fuskar ta da hannu, murmushi yayi yace,kiyi hakuri toh Zan samo Miki wani new cat in,d'aga kafada tayi tace"Ni bana son wani kawai so nake na gansa"bude kofar kawai yayi ya fita baice kome ba,jakan makarantan ta ta bude ta dauko uniform nata dake ciki ta aje akan gadon takardunta ta Soma fitarwa sai Kuma ta zaro Ido ganin abinda ya Fadi hannu tasa ta d'aga tana duddubawa ATM in Lahab ne"wash na manta dashi kwata kwata ban basa ba toh yanzun ya zaiyi da bill na hospital gashi babu kowa nasa?"sai Kuma ta danyi murmushi idanunta na zubda kwalla tace"ashe fa ya Kira Yan gidan su,gobe Zan Kai Masa a hospital in duba jikin nasa.

********************
bayan isha'i umaima dake dakin ta a zaune wayarta ne yayi tsowa mikewa tayi ta dau wayar ta Kara a kunnen ta,sallama akayi ta amsa cikin happy tace"ok harka iso ok toh ganinan fitowa,katse wayar tayi ta aje mikewa tayi ta dau hijab nata ta dau turare ta feffesa a jiki sannan ta zura,ta fitoh a dakin nasu kallon su muneera dake zaune a falo tayi ta nufi kofar ta fita.

Tsaye yake Kamar kullum a kusa da motar sa karasowa tayi tana murmushi"barka da warhaka Rabin Raina",da murmushi yace"yauwa dear ya Mai jikin?
Chapter 58 · 0% Book details