Sashe 9
Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin tashin hankali papa ya daura hannu akai yana kiran jesus, sai kuma ya ruga da gudu yayi d'akin Nnenna biro da takarda ya d'auko yayi rubutu a ciki da sauri ya fitoh falon.
Nnenna dake kuka a jikin matar ya mika hannu ya kamata ba tare dayayi magana ba ya nufi kofa da ita da sauri ta fizge hannunta tayi wajen kulenta dake zaune kansa a kasa kamar mutum haka ya duka, d'aukar sa tayi da sauri tabi papa a baya.
Suna fita a kofar su da gudu suka kama hanya zasu bar gari koh rabin kauyen basu fitaba suka ga tawaga na binsu na matasa da mata da mazan kauye wasu na rike da sanda wasu wuka wasu jarkan petur.
Gudu papa suke da Nnenna jama'a na binsu ganin suna basu wahala yasa wasu bin shunkut suka tarosu ta gaba sosai jama'a suka kewaye su, wasu mazaje majiya karfine suka tinkare Obinna(papa) suka kamasa rike sa sukayi a gefe suka bar Nnenna a fili tsaye da kule a hannunta idanunta koh glass babu kuma ba kallonsu ma take sosai ba tadai san yau suna cikin tashin hankali da ba'a saka masa rana.
Tana cikin tunanin halinda yau xata kasance kawai taji ihun papa yana had'asu da jesus karsu kona masa yarinya suyi hakuri zasu bar kauyen zasu tafi a garin suyi musu gafara.
Bata ma gama fahimtar kome ba taji an kamata janta sukayi tana kuka tana kome suka daureta da jikin bishiya wasu suka kwarara mata petur a jiki daga sama har kasa,Nnenna kuka ta saka tare da rimtsa idanunta gudun kar ya shigar mata ido.
Kara papa ya sake ganin wani ya kunna leta tun daga nesa ya jifo mata, Amma abin mamaki wutan na faduwa a cikin petur kawai ya musu, sun gwada hakan yafi sau biyar Amma wuta yaki kamata.
Wani daga cikinsu ne ya zaro sharbebeyar wuka cikin zafin rai yake cewa tunda bazaki kama da wuta ba wallahi sai nayi ajalinki jinin sister na bazaki sha bulus ba, da gudu yayi kanta baiyi wata wata ba kawai ya d'aga wukar ya burma mata, kara ta sake da karfi ganin wanda wukar ya caka shima yaron ihu ya sake hade da kama kansa ganin abinda ya aikata wa............................
✨Ruqeenjalal✨
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🤹🏿♂️ *ALKAWARIN MASOYA* 🤹🏻♀️
~ Na ~
🍃 *Rukayya Ibrahim*🍃
Free page🤧
*EXQUISITE WRITER'S FARUM*
page1⃣3⃣&1⃣4⃣
Papane wukar ya caka a ciki ashe lokacin da wannan guy in ya tinkare Nnenna papa ya rugo da gudu unexpected ya shiga gaban Ta, wukar ya sauka a cikinsa.
Ihu Nnenna ta sake da karfi a take tayi tsalle ta fizge igiyoyin dake jikinta, a take suka tsintsinke, cikin hanzari ta taro papa dake kokarin kaiwa kasa.
Kuka take cikin yare take magana, pls papa karka tafi ka barni bani da kowa sai kai, me yasa baka bari An kasheni ba kai kayi rayuwar ka Meyasa??meyasa?? tana maganar tana kuka.
Cikin magagen mutuwa papa ya kama hannunta yasa mata paper dake hannunsa, a hannunta cikin Azaba ya soma mata wasiya, Nnenna ke ya dace ki rayu bani ba, don ni tawa ta kare wannan Address na d'an uwa nane yabar kauyen nan shekaru da dama ki bar garin nan ki tafi wajensa, sai kuma tari ya sarke masa.
Sai da ya sakaita kafun ya cigaba da magana jini na biyo bakinsa, ki rike Addininki kinga AREWA zaki tafi, zakiga abubuwan da suka sabawa Al'adun mu ki iyye bakin ki aduk inda kika tsinci kanki, kiyi hakuri da rayuwa sannan ki xamo mai kawaici domin fushin ki Ajalin wasu ne, naso na sanar dake koh da wani abune a game dake kafun nabar duniya Amma hakan baxaiyu ba lokaci na yayi, Amma nasan wata rana zaki san kome koh bajima koh ba dade, in jesus name?
"Emeen papa bazaka mutu ba asibiti zan kaika" ta karasa maganar hade da kokarin kamasa ya mike tsaye, Amma ina rai yayi halinsa.
Ihu ta sake da karfi sai da ya Amsa amo kuka take da karfi tana rungume da papa.
Inyamuran nan basu wani ji d'ard'ar ba, suka sake yunkurin d'aureta Amma abin mamaki duk wanda ya taho gareta sai dai kawai aga yana faduwa macece yayin da ita kuma ke duke cikin tsananin bacin rai.
Ganin abinda ke faruwa yasa sauran mutanen gudu sosai, kauye ya kashame da guje guje, yayin da Nnenna ke tsungune a gindin bishiyar rike da papa har lokacin kuka take tana maijin wani irin ciwo da fushi a ranta.
Dafata taji anyi da sauri ta d'ago domin ganin wanda ke tsaye a kanta, tsohowar d'azun datazo ta sanar da papa za'a kasheta ne, tsaye tana hawaye, Nnenna kiyi hakuri kinji rayuwa haka take tafiya da kaddara iri iri abinda yafi miki ana shine kiji maganar Obinna kibar garin nan ki tafi inda ya turaki.
D'aga mata kai Nnenna tayi tana mamakin kallon matar da take zarzar tunda aka cakama papa wuka ta koma kallo kamar kowa gashi ba glass a idanunta"bani da kudi ki dubi kayan jikina akwai petur bazan iyya tafiya a haka ba "?
Ina zuwa kawai tace, ta koma cikin kauye, ba'a jima ba sai gata da kaya dogon riga ta had'a da kudi 10k ta mikawa Nnenna, gashi kisa kayan wannan kudi kiyi kudin mota.
Karba Nnenna tayi sai kuma ta kara kallon matar, momy ni zan jira a binne papa dani kar abar gawansa a wulakance"?
Karki damu daughter ki tafi na miki Alkawari gawan papan ki zai kwanta a mutunce?
Mikewa tayi a hankali ta juya ta kama hanyar fita a kauyen gabaki d'aya, daman sun riga sunyi nisa tana kuka tana tafiya rike da kaya da kudi a hannu sai da ta kusan fita a kauyen kafun ta shanja kaya, kudin ta saka a Aljuhun rigan har lokacin warin petur take.
A haka ta ringa fasa hanya zuwa lokacin At least 5 na yamma zaiyi tana fita bakin titin ta samu machine mai kafa biyu, ta tare akan tanaso ya fitar da ita zuwa tasha, shikam mai machinen haka kawai yaji shakkan ta da tsoron d'aukar ta ganin kyau inta yayi yawa karfa yaje ya d'auki Aljana gashi hanyar ba mutane.
Ganin kamar bazai d'auke ta ba yasa ta zaro masa 2k ta nuna masa akan zata biyasa mundin ya kaita, inyamuri da kudi ba musu yace ta hau, harta hau machine zai ja da mamaki kawai taga kulenta a gindin machine a zaune yana kallonta ita harga Allah ta manta da zancen kulen ma tsabar tashin Hankali.
Da sauri ta sauka ta ciccibesa ta hau suka ja, basu suka isa tasha ba sai 6 gashi babu mototi kowa ya tashi kudi ta biya mai machine in ta koma wani rumfa ta xauna a bakin shagunan wasu masu manja da suka kulle.
Har dare ya raba tana wajen a zaune koh motsawa batayi ba har aka fara yayyafi kamar wasa aka fara zuga ruwan sama sosai tun baya samunta har ya fara tabata.
Ruwa akayita jugawa har 9 na dare zuwa lokacin gabaki d'aya tashan babu kowani maluki sai ita kad'an ta kowa ya kara gaba ga sanyi ga yayyafi.
Tana zaune kanta a duke sai digar da hawaye take tana tuno Abubuwan dake faruwa a rayuwar ta, wai menene laifin ta meyasa sai ita kad'ai Abubuwan nan ke faruwa da ita, avinda ke yawo a ranta kenan, jikawai tayi an haskata da touch, Amma koh d'ago kai batayi ba tanajin sahon kafar mutane, Amma hakan baisa taji koda d'an tsoro ba, don zuciyarta yanzun yariga ya kekashe duk wani tashin hankali, gani take kamar ta riga ta gama ganinsa a kauyen su, tunda har wanka da petur aka mata za'a cinna mata wuta.
Kamar da wasa taga maza hudu akan ta dagani dai irin yan iskan nan ne, kama mata hannu dayan yayi cikin maganar yan kwaya yake cewa, kai baby ya haka naji kina warin petur Amma dai duk da haka bamu damu ba, zamu iyya a hakan ma.
Fizge hannunta tayi kawai ta mike tsaye kulenta ta d'auka, Zata kara gaba da sauri d'ayan ya sha gabanta hannu yakai zai taba mata kirji, ai ji kawai yayi anyi sama dashi an buga a kasa ya sake kara da karfi jin kamar kafarsa ya karye, ita karan kanta a tsorace take ganin abinda ya faru duk da a duhune, tsere suka shigayi ita da yan kwayan ana rige-rige kowa gudu yake don ita ma arcewa tayi, bata tsaya ba sai gonan wani dake yankin wajen ta shiga ta kwanta a cikin ciyayi.
Har asuba Nnenna idanunta biyu, yau dai idanunta sun koma kallo kamar ko wani mai lafiyar ido, sai kuma ta tsinci kanta da rashin jin bacci kwata kwata koh tashin Hankali ne yasa ta kasa baccin ne oho.
****************
Lahab basu dawo daga ball ba sai kusan 6 na yamma, bai saya bin gidan su nabeel ba direct ya nufi gidan su, haka ma adewale gidan su ya shiga, da sallama ya shigo babban falon sai kuma ya saya yana bin kowa da kallo ganin gabaki d'ayan su a tsatsaye alamu dai shi ake jira ya shigo.
Basarwa yayi kawai ya shigo falon irin koh a jikinsan nan ya kama hanyar bangaren su.
Lahab!!!Abbu ya kira sunan sa tsayawa yayi yana kallonsa ba tare da ya Amsa ba, jin abinda Abbun ya cigaba da fad'a, Lahab ka d'auko card in Halima ka bata sannan ka fitoh mata da kudin ta?
Hade fuska yayi sosai ya tamke tamau irin ba wasa a cikin nan"A gaskiya a gidan nan ana mini abinda bai kamata ba, ace ni shikenan an mai dani agola nida gidan ubana bani da sakat, yanzun rabona da cikin gidan nan tun yaushe Amma a rasa wanda za'a d'aurawa sata sai Lahab saboda an mai dani barawo"?
Da sauri Addayiya ta cebe zancen ai barawon ne, koh karya aka maka baka sata?
"Karki kara cema d'an uwana barawo Addayiya kikiyaye bakin ki? tayaya zakuce shiya d'auka mata abu batare da anyi bincike ba, kuma taya ma zai d'auki ATM nata Alhalin baisan pin in ba, ai sai a tuhume ni da yaranta tunda muke cire mata kudi bashi ba?