← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 122

Sashe 1

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️🏵
🤹🏿‍♂️ *ALKAWARIN MASOYA* 🤹🏻‍♀️
~ Na ~

🍂 *Rukayya Ibrahim* 🍂

✨Tsokaci ALKAWARIN MASOYA na kudi ne gamai bukata naira 300 ne kacal ki zama mace mai aji ki karanta abinda kika saya👌
Free page🤧

*EXQUISITE WRITER'S FARUM*

Page1⃣&2⃣
Safiya ce da misalin karfe 7:10pm Ahlin gidan tsohon minister ne, zaune Akan daining babba mai d'auke da kujeru sama da 12 karyawa suke kowa ka gani cikin shirin sa yake na zuwa aiki koh makaranta inka cire matan gidan, Abba ne zaune a kujeran daining inda ke tsakiya, zaikai Akallah shekara 65

sai hajiyoyin dake zaune akan kujerun gefensa, manyan matane masu ji da aje naira da izzah, sanye suke cikin shiga na atamfa dukansu.

mamu uwar gida akallah zata kai 50 sai ummu Amarya mai shekaru 40 sai babban d'ansa Anwar d'an mamu ne zaikai shekara 35 zaune yake cikin shigar office(doctor).

sai mai binsa shareef mai shekara 31 shima yana sanye da suit baki (lauya), sai umaima dake sanye cikin dogon rigan kanti da gyelen sa, daga kaga irin wankan ta kasan yar jami'a ce, zata kai shekara 25 dukan su d'akinsu d'aya ne.

sai babban d'an ummu uzaifa da zaikai 20 yana sanye da jamfa da riga da wando na shadda, kansa babu hula(student).

sai munira mai shekara 17 sanye take da uniform tare da kanwarta zulaihat mai shekara 15 ita tana sanye da uniform, Abinci suke ci hankali kwance yayinda kujeru uku yakasance empty babu kowa akansa.

Addayiya dake zaune a tsakiyar falo ta mimmike kafa tsohowace sosai Amma jin dadi ya boye shekarun nata, sanye take da zani da riga sai d'an kwali data aje a gefe bata d'aura ba tulin gashenta daya rine zuwa fari a bayyane, Abinci take ci kwai ne da Arish sai tie ga bread a gefe, cin Abincin ta take hankali kwance.

Turo kofar da akayi shiya ja hankalin kattafanin su dake falon harda daining Area, duk da kamshin turaren sa ya sanar dasu wake shirin fitowa, Amma hakan bai hanasu juyawa don tabbatar wa kansu shin da uniform ya fitoh koh Ah ah.

Fitowa yayi a kofar, wow masha Allah watoh in Anace maka black is beauty, bazaka tabbatar ba sai kaga wannan Hallintar koh shakka bazakayi ba, bakine mai sheki irin bakikkirin nan, fatar nada masifar laushi har maiko-maiko fatar keyi sanye yake da wando baki, mai roba a kasar wandon, pencil ne ya kamasa sosai bai rufe masa idon sahu ba.

sai boot fari tas baisa wa kafarsa socks ba, hakan yasa ana kallon idon sahun nasa, t-shirt ne a jikinsa white sai rigan da ya daura akai mai hula da dogon hannu, Amma ya bude zip in wanda yasa ake kallon rigar ciki.

ga wani d'an iskan Aski dake kansa ya raruke gefe yabar sakiya da yawa, gashine mai laushi da yawan gaske irin na fulani, ga kwancecen sajensa mai hade da gemu, duk da bai cika masa fuskar ba, Amma daga gani Ana ji da gemun irin na tsiran farkon nan ne na tashe balaga.

Bakin sa pink ne mai kyau dan kankani, hancin sa mai tsahone sosai ga idanu manya kamar na mata, kwayar idanunsa bakine sosai wanda ke matukar rikita mutune a duk lokacin da ya zare maka su yayin da mabi da kwayar ya kasance fari tas gashin giransa mai yawane blutooth ne fari makale a kunnensa d'aya.

Yana da tsawo sosai Amma ba irin har shan innan ba, gashi da kira mai kyau duk da yanzun yake tashen sa, Amma kallo d'aya zaka masa ka gane za'ayi namiji, baxai wuce shekara 18 ba.

Taku yake irin na isasun yaran nan masu ji da lokacin su hade da kuruciya, duk da ya gansu zaune a falo, Amma hakan baisa sa ya nuna ya gansu ba nufar kofar falo kawai yayi.

Addayiya dake zaune a tsakar falo tana cin kaza da romonsa wanda yar aiki ta aje mata, ta mike kafa.

da gangan ya nufi ta saitin da take zaune kamar baiganta ba, ya d'aga kafarsa kamar zai taka kafarta da sauri taja abinta cikin masifa take kallon Lahab.

Amma yaron nan Anyi jarabebbe kai in gari ya waye baka sani surutu ba bakajin dadi, nida gidan mijina da d'ana, bani da sakat sai in baka nan, toh yau duk bala'inka bazan kulaka ba, d'an-banza kawai.

yi yayi kamar baisan ma tanayi ba tafiyarsa yaci gaba dayi.

Abbu dake zaune tunda lahab ya fitoh yake binsa da kallo Ganin yanda yazo ya wuce su, yau koh break in ma bai tsaya yiba, kwala masa kira yayi ganin yana kokarin bude kofar, Lahab!!!Lahab!!

*ALKAWARIN MASOYA Naira 300 ne vie 2185602275 Rukayya Ibrahim UBA bank, koh katin Airtel zaki tura ta wannan layin 08084453785 tare da shaidan biyan ki*

had'a fuska Lahab yayi jin yayansa na kiransa juyowa yayi ya dawo cikin falon har wajen daining Area, ya tsaya a bakin steps in.

Abbu ganin ba gaidashi Lahab zaiyi ba yasa sa kallonsa, Anya lahab rayuwa zaiyu a haka kuwa? kai kenan in gari ya waye sai an maka fad'a, daga safe zuwa dare sai ka samu surutu a gidan nan, mekake so Lahab da ban maka ba?

kara had'a fuska yayi jin Yayan nasa zai fara masa fad'ar daya saba a idon yaransa, "babu"

toh Yanzun ka kyauta kenan ina fa kallonka saura kad'an ka taka mini kafar mahaifiya da wa'inan shegun takalman nan naka?
Addayiya fa ba kakarka bace, koh su Anwar basa mata abinda kake mata a gidan nan.

jin Abinda Abbu yace yasa Addayiya fashewa da kuka, kuma fa umar tun farko saida na nunawa ubanka banason Auren sa da wannan figeggeyar yarinya, Amma dayake budurwar zuciya ne dashi,kaima kabi ka sani a gaba da wa'azi, gashi shi ya tafi ya barni da jaraba ga uwarsu shan tayi auren ta tana jin dadi ni An barni da ciwon baki, Allah sarki.

haushi ne ya kama lahab cikin masifa yace"oh Ashe kishi kike tayi aure bakiyi ba, kema ai bawanda ya hanaki saiki fitar da miji a miki"

kuka Addayiya ta sake, nikam na shiga uku ni Maryamu, toh bara kaji uwarka ce kwad'ayayiya ita da ubanta, ba kunya tazo ta likewa tsoho.

dariya jama'ar dake wajen suka sake Abbu ne kawai baiyi dariya ba saima haushi dayaji ya rasa meyasa kullun sai sunyi fad'a, kuma Lahab ke tsokanar ta daga karshe kuma ya sata kuka,
Habba don Allah Addayiya wannan wani irin magana ne a idon yara?

jin abinda Abbu yace yasa Addayiya had'a fuska taci gaba dacin Abincin ta, tana share hawaye.

kallon Lahab Abbu yayi, yanzun menene Amfanin abinda ka matan nan ta tsufa ma bazaka barta ta huta ba?koh so kake ka d'aura mata hawan jinine?

"kayi hakuri yaya bazan kara ba"

rufe mini baki karawa na nawa kuma lahab,kuma ban gane ba na ganka da wa'innan kayan ina uniform in?

kafun ma lahab yayi magana Umaimah tayi caraf tace Haba Abbu inda sabo yaci ka saba da halin small uncle ka hutawa ranka, kai yaranka basu baka ciwon kaiba zaka sawa kanka ciwo akan sa.

ai Lahab najin abinda tace cikin masifa ya nunata da yatsa"wallahi zanci uwarki umaimah daga yau in ana mini magana kika sake saka bakin ki a ciki yar iska kawai".

mikewa shareef yayi kai wallahi ya isheka haka Lahab mun gaji da iskancin ka a gidan nan?

wani hayyakowa lahab yayi cikin masifa kamar irin zai iyya dukansan nan"toh koh dukana zakayi matsiyacin lauya"

tura kujeran daining in shareef yayi zai sauko da sauri Abbu ya nuna masa kujera da hannu, go back to ur seat shareef, Lahab bappan kane respect him banason haka?

shi ya fara baka respect naka tukunnan kaida kake yayansa, kuma a girme ka haifesa Amma bayajin maganar ka, bayajin kunyar ma su ummu rashin mutunci saini ne dukan sa zai gaggareni.

ai jin yace duka yasa lahab harzuka zai zage shareef sai kuma yayi shuru jin takun sahun kafa a falon, wanda koh shakka babu yasan wanda ke tahowa.

Allahu Akbar tsarki ya tabbata ga Allah, hatta tafiyarsu iri d'ayace kai daga zaran ka gansu basai an fad'a maka ba, zaka bawa kanka amsa da tagwayene, babu abinda ya banbanta su sai abu biyu hali da kuma gyaran gashin su, Amma bayan wannan da koh a cikin gidan su baza'a samu mai banbantasu ba, a hakan ma mutanen waje ba iyya banbantasun suke ba.

karasowa yayi gaban daining in bayan sun gaisa da Addayiya a falo, gaida Abbu yayi da ummu da mamu, yaran Abbu suka gaidashi dukansu duk da mazan sun girmesa hakan bai hanasu basa girman saba.

kallonsa Abba yayi cikin farin ciki, sanye yake da uniform, wandone navy blue, sai riga fari da boot fari na makaranta a kafar sa, hannunsa sakale da school back sai wasu litattafai daya rike, Rahab na tura zuhaihat kafa biyu kazo mu karya, wai kana wanka?

murmushi yayi saida fararen hakoran sa sak irin na Lahab suka bayyana, Eh yaya Assigment nayi da safen nan shiyasa nad'an makara ban shiga wanka da wuri ba.

ok get a seat ka zauna oyya kayi break?

gaskiya Yaya nayi laten almost 7:32 yanzun fa?zan wuce kawai.

hannu Abbu yasa a Aljuhunsa ya zaro 1k mikawa Rahab yayi, gashi ka shiga school cafe ka sai abin break ka tabbatar kafun ka shiga aji ka karya?

d'an rusunawa Rahab yayi ya karbi 1k in hade dama yayan nasa godiya, kallon Anwar yayi, doctor Ya Alkawarin mu na kudin hadisi gobe islamiyya, in ka samu aban yanzun zanbi islamic bookshop in muna dawowa?

hannu Anwar yasa a Aljuhu ya zaro lalitarsa 10k ya zaro ya mikawa Rahab.

hannu yasa ya Amsa cikin murna yace, doctor kudin sunyi yawa hadisin fa 500 ne?

na sani Rahab sauran chengen ka rike a a hannunka.

Lahab dake tsaye a gefe tun fitowar Rahab bai kara magana ba, sai binsu da ido yake, ganin kudin da Aka bawa Rahab yasasa shammatar su ya fizge 11k in ya b'anb'ara da gudu ya nufi kofar falo, a tamanin Rahab ya bisa a guje zuciyar sa na tafarfasa don shi daman mutun ne mai karamin zuciya, duk irin kwala masa kira da suke akan ya dawo kin sauraron su yayi.
Chapter 1 · 0% Book details