← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 122

Sashe 64

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mikewa Inna tayi tace toh hajiya mu zamu tafi Allah ya kiyaye na gaba"Ameen Suka amsa duk da mubeena bata ji dadin tafiyar da Inna tace zasuyi yanzun ba amma ba yanda ta iya haka sukayi sallama da mutanen gidan Suka tafi,Suna fita a dakin Lahab ya aje plate in don harga Allah ba yunwa yakeji ba kawai dai yayi hakan ne don nuna Mata Jin dadin sa Sarai yasan halin mubeena haka zalika karon farko data dau Abu ta basa cikin mutunci babu masifa"da Sauri Majid ya dawo kusa dashi Yana bin kofar da kallo har lokacin sai Kuma yace"Kai wannan fa wacece Ni fuskar tama familiar ne gareni"hararan sa kawai Lahab yayi baice kome ba naci sosai Majid ya ringawa Lahab a Kan mubeena amma bai kulasa ba gajiya Lahab yayi yace Masa"kaga Majid banason surutu haba don Allah Kai baka Isa kaga Mata ba jikinka sai ya ringa rawa toh ka kiyaye kanka wallahi"tsaki kawai Majid yaja da Sauri Lahab yace"yauwa don Allah Ina so ka taimake Ni"wani banzan kallo Majid yayi Masa shima baice kala ba matsowa kusa dashi yayi Yana rokon sa.

Hannu Majid yasa ya hankada Lahab Sora kadan yafadi akan hannun sa mikewa Lahab yayi ya shiga toilet bucker ya cika da ruwa Majid na kwance kawai yaji an kwarara Masa ruwan sanyi kafun ma ya dawo hayyacin sa Lahab yabar dakin da gudu yayi dakin Addayiya tare da maida kofar ya rufe yahau Kan gadon ta ya kwanta sai bacci.

*****************
Zaune take rike da wayar da Abraham ya kawo Mata tare da dogon gargadi kada ta bari kowa ya gani sosai take jujjuya wayan babba be babu laifi Kiran Tecno danna wajen da yace Mata zatanayi in zata kunna tayi take haske ya kawo sosai take kallon screen in wayan tama rasa ta Ina zata Fara wannan shine Karo na farko data rike waya nata na kanta papa nada waya amma karamace ba irin wa'innan ba,shige shige ta Fara kasancewar ta Yar makaranta waya bazai bata wahala sosai ba shige shige tayi tayi har dare sosai,kafun ta kashe wayar kiki ta d'auka ta basa magani ta kwantar dashi itama ta kwanta abinta.

Washe gari da safe tun asuba ta tashi share gidan tayi da wuri Kamar kullum ta Gama aikin ta na safiya ta shirya ta tafi makaranta Kamar jiya yauma Abraham ne ya kaita duk da mom bata so amma babu yanda ta iyya ganin yanda Dad ya Soma chanjawa a Yan kwanakin Nan.

**********************
Bayan sallan asuba gabaki d'aya Yan gidan sun koma bacci sai kusan 7 Suka hallara akan dinning yaukam harda Lahab abinci sukeci Majid ya kalli Abbu yace"Abbu wallahi jiya Lahab jika katifar da Zan kwanta yayi ya jikani da ruwa karshe ma dakin Shareef na kwana"shuru Abbu yayi nadan wasu minutes kafun yace"Kaga Majid kaci abinci kawai ba'aci ana magana tsakanin ka da Lahab Kuma bansan Wanda yafi wani ba"yunkurin magana Majid yayi Abbu ya d'aga Masa hannu alamun ya mishi shuru kenan,shurun yayi Suka cigaba dacin abincin d'aga Ido Abbu yayi ya kalli mamu dake zaune fuska babu walwala hatta yaran Karan kansu sun fahimci akwai abinda ke damun ta,mikewa Abbu yayi cikin Sauri yadau jakan system nasa da Sauri muneera itama ta Mike hade da karban jakan ta nufi kofa,mikewa mamu tayi a fusace ta nufi sashen su ganin Abbu Harya nufi kofa baice Mata kome ba don jiya ma ba girkinta bane amma haka taje ta samesa akan kudin sayayya ya koreta gashi yau yayi ficewar sa bai bata ba,yaran Kam binta kawai sukayi da Ido Harta mule musu, amma basu ce kome ba duk da sunyi mamakin yau ranan kawo lefen umaima amma fuskar mamu ba walwala.

Mikewa sauran yaran sukayi Suna fiffitowa da d'ad'aya d'ad'aya Inka cire Majid da Lahab dake zaune har lokacin a dinning Kuma sune kadai bazasu makaranta ba(gagararu)Kamar an mintsine sa da Sauri ya mike gudu gudu Sauri Sauri ya fitoh a falon Aiko yayi sa'a su Rahab basu tafi ba, wajen sa ya matso yasa hannu ya jawo sa kusa dashi cikin kasa kasa da murya yace"don Allah Rahab so nake ka hadani da yarinyar da ta baka card jiya zamuyi magana ne a waya"wani juyawa Rahab yayi da kyau ya kallesa sai Kuma ya girgiza Kai ya shiga motar ya rufe baice kome ba aka ja motar Suka bar gidan komawa cikin gidan Lahab yayi ganin motar Dr ya shigo gidan nasu ya daura Masa ruwa da Allurai.

Mamu na shiga daki rai a bace ta zauna akan gadon ta tana kintsema irin wulakancin da Abbu ya Mata duk da tana da kudin itama Abba tanajin zafin kashe kudinta,Kamar ance ta d'aga Ido kawai taga card nasa akan pillow da Kuma pepar da Sauri ta matsa wajen ta dau card in take murmushin ya bayyana a fuskar ta ya yalwata sosai bude takardan tayi tana karantawa Kamar haka"toh sarkin son kudi Naga kin tashi sai wani harhada Rai kike waike Halima tunda nace Zan baki kina tunanin bazan bada bane toh ga card Nan banyar da ki kashe sama da dubu dari biyu ba don nasan ki"?da murmushi ta Mike ta dau wayar ta kiraye kirayen kawaye ta ta Shiga da kannen ta Akan suzo suje Mata cefene Kamar wani bikin ake.

Gidan su Lahab yanda kukasan gidan biki Kamar yau za'a daura aure saboda yawan kawaye da mamu ta gayyata karban Kaya sai zuzzuta zancen kayan take da kawayenta, Mami Kam batama San zancen kayan ba sai da azahar data shigo gidan taga Mata birjit gashi sai girke girke ake ana suyan kaji,da mamaki take gaida kawayen mamun da kannen ta amsa wa suke a daddage,Shiga cikin falon tayi hannunta dauke da laida hallo cikin ma da Mata gidasu tayi ta wuce sashen su Rahab zaune ta yarda Addayiya a falo sai ummu dake zaune Suna hira,karasowa falon tayi ta zauna Suka gaida sanan tace"Wai Addayiya meke faruwa ne Naga gidan a ciki"?meke Kuma faruwa banda Yar Nan umaima yau dangin yaron Nan sadeeq zasu kawo Kaya shine duk tazo ta cika Mana gida da jama'a Suna shewa Suna suya"da mamaki Mami tace"yanzun Addayiya haleema za'a kawo kayan yarta amma ba Wanda zai sanar dani"?ummu ne tace"Kinga Amina muma bamusan da maganar kayan ba sai da Addayiya ta fada"mikewa mamin tayi ta shiga dakin Lahab kwance yake hannunsa d'auke da ruwa shikadai ne don Majid ya fita,shigowa tayi ta zauna a bakin gadon tasa hannu ta taba wuyansa bude Ido yayi ganin Mami me yasa sa komawa baccin da yake.

Har zuwa yamma Mami na gidan duk da taso shiga ciki ayi aiki da ita Amma Jin yanda ake tsoka Mata magana yasa ta zame jikinta ta dawo tayi joining su Addayiya da ummu a falo Suka cigaba da zaman su,wanka yan Koran mamu sukayi akasha less da zanunuwa ansha d'auri ana jiran baki,da misalin karfe biyar na yamma lokacin yaran gidan wasu sun daddawo makaranta harsunyi wanka mazan Kam tuni Suka bar gidan bayan sunci lunch nasu.

Lahab sai hararan Rahab yake don bai hadasu da Nnenna ba bai kuma ce Masa kome ba,mami taso tafiya ganin har yamma ba'a kawo Kaya ba,amma ummu ta hanata gudun kada ummu tace hassada ce ya hanata Zama don tun safe zance daya mamu keyi yaudai makiyanta sai dai su mutu saidai su rufe idanun su yarinyar ta tayi goshi insha Allah kayan da za'a kawowa umaima har a gama aurar da yaran gidan baza'a kawo musu irin Shiba, danta Anwar ma akwatuna 12 ta had'a Masa za'a Kai wani sati Kuma tasan sadeeq zai had'a sama dashi.

Wangale gate na gidan akayi mota daya ya shigo rufe gate in Mai gadi yayi aka bude motar wasu matane guda uku Suka fito a motar,Jin mota ta shigo yasa mamu mikewa tabar falon ta shiga dakin ta Yan uwanta ne da kawaye suka tarbo bakin shigowa sukayi namijin daya kawosu shiya Fara shigo da akwatunan baza Ido manyan matan sukayi Suna kirga a kwatunan ganin mota daya ne ya shigo basu tsammace hakan ba Saida ma Suka ga an aje akwatunan duka,daidai Nan Mami da ummu Suka fito falon,kwata kwata guda biyar ne da karamin kit................................

🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*

Page 81&82

Zama Mami sukayi matan Suka Soma sauke kayan akwatunan, ba laifi sadeeq yayi kokari sosai zanunuwa kam masu kyau akwai na dubu hamsin da ishirin ga lace masu kyau babu laifi Kam, finda kayan suke su Mami na kirgawa sukam kawayen mamu Jan jiki sukayi Suna shan kamshi Koh kallon arziki basu ma bayin Allah Nan ba,mikewa kawar mamu tayi ta nufi sashen su Mamun zata Kai Mata rahoto da Sauri yayar mamu ta Mike tabi bayan matan Harta kusa isa kofa ta kwala Mata Kira tsayawa tayi har yayar mamu ta iso kusa da ita tana cewa"ina Zaki hajiya Hanifa badai wajen Halima Zaki ba"?wajen tane Mana zanje na sanar da ita abinda ke faruwa"da Sauri addanta tace"Kinga hanifa mu koma falo kinsan halin Halima Sarai zata iyya bamu kunya akan kayan nan muje ku ibo abinda aka tanadar musu ku Basu suyi Subar gidan kafun Haleema tasan zancen kayan lefen Nan"haba adda taya zamu d'au abinda muka had'a da kusan rabin kudin lefen da suka kawo mu d'auka mu Basu haba dan Allah"da Sauri Adda ta nufi kofar Jin ana kokarin bude kofar mamu itama Hanifa da Sauri tabi bayan Adda.
Chapter 64 · 0% Book details