← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 122

Sashe 63

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mika Masa card nasa kawai Rahab yayi yasan duk abinda sai gaya Masa Lahab ba ganewa zaiyi ba"amsar card in Lahab yayi da mamaki yace"a Ina ka dauko ATM nawa"?

Tashi tsaye Rahab yayi yace"ita ta bani a school"zaro Ido Lahab yayi yace"ita wa"?Wance ka baiwa card in Mana Koh kana nufin baka bata bane"?shuru Lahab yayi bai amsa Masa ba shima Rahab bai motsa ba sai Kuma ya koma ya zauna tare da fuskan tar dan uwan nasa yace"wacece don Allah"? remote Lahab ya d'auka ya Kara volume na TV ya mimmmike kafa ya cigaba da kallon sa Bai saurare Saba.

Bayan mangariba zazzaune suke akan dinning Suna dinner gabaki dayan su Lahab da Addayiya ne kawai basa dinning in don tunda Lahab ya dawo basu cika cin abincin da aka dafa ba shida tsohowar tsabar irin girke girken da ake kawo musu na namomi gashi yauma mamin sa ta turo su mahraz sun kawo Masa pepper chicken,ya jafar ne da iyalan sa Suka kwada sallama a falon amsa musu akayi gabaki d'aya cikin farin ciki zazzaunawa sukayi a falo mamu ta Mike taje ta dauko musu drink's da water ta aje musu gaggaisawa akayi Majid ya mike direct ya nufi dakin Addayiya don sunyi waya da lahab,tura kofar yayi Koh sallama babu zaune Lahab yake Yana cin kwai dafeffe,mikewa Addayiya tayi da plate na nama a hannunta ganin Majid yasa ta sakin tsaki amma batace kome ba ta koma ta zauna tana holo yashigo ba sallama Kamar dan kafurai shidai bai kulata ba sai zaman da yayi akan gadon ya kwace plate na kwai dake gaban Lahab ya d'auka ya Soma ci,da Sauri Addayiya ta kwace tace"Kai majidu baka da kunya Meka kawo Mana bare kazo ka samu dan marayan Allah Yana fama da jiki ba tausayi ka dau kayan jinya kana lashewa ai wannan mugunta ne?

Kala baice Mata ba sai kallon Lahab dake kallon sa yayi ya kalli Addayiya sai Kuma ya mike tsaye yace"don Allah ka tashi muje dakin ka menene na Zama a dakin tsohowar nan duk warin tsufa"uwarka da ubanka ne masu warin tsufa bani ba dan banza kawai gagare"ganin fad'an nason girma don sai CeCe kuce suke yasa Lahab mikewa ya nufi kofar Yana ma Majid magana akan suje sashen su,Majid Saida ya Bari Lahab yabar dakin kafun ya fizgo laidan kazar dake gefe ya fita da gudu a dakin.

***************
Kafun mangariba mubeena ta kammala girkin ta dankalin turawa ne ta soya sai ferfesun kifi ice fish,duba kwanukan nasu tayi gabaki d'aya sun tsufa Basu da kula sabo raba abincin tayi ta zubawa Inna nata da ban Nabeel da ban tasa nata sauran data keda niyar kaiwa lahab,hijab nata ta rufa ta fita gidan wata amarya dake kusa da gidan su,Kuma tayi sa'a ta samu Sabon kula guda biyu na tuwo dana Miya,sabo gal Mai kyau dawowa tayi ta zuba dankalin daban kifin daban ta aje a kwando,ita dai Inna da Ido kawai take binta,wanka tayi Koh abinci ta kasa ci bude akwatinta tayi ta dau wani less nata Mai kyau purple zani da riga gyale fari ta d'auka da takalmi ta yafa fitowa tayi a dakin a Karo na hudu tana duba Inna amma abin haushi har lokacin batayi niyar mikewa ba kasa hakuri tayi ta tama inna magana tana cewa"haba Inna dare fa nayi don Allah ki tashi mu tafi Mana Ina da karatun da zanyi fa"kallon ta da kyau Inna tayi tace Wai ke yaushe kuka Fara shiri da Lahab in har kike rawan kafa zakije ki duba sa ga wani uban cefene da kikayi Kamar Zaki gidan surkunaye"gabanta ne ya yanke ya Fadi Jin Inna ta jefo jirginta amma ta dake tace"shikenan nama hakura da zuwa"tayi Kamar zata koma daki amma a cikin zuciyar ta Allah Allah take kada Inna taki tsaidata.

Wallahi baki Isa ba tun yamma kike uzzuramin sannan yanzun kice kin fasa zuwa, bari ma nadau hijabina muje,dakatawa mubeena tayi ta hade rai ta tsaya tana jiran Inna data shiga daki dauko hijab nata,kulan abincin ta d'auka ganin Inna ta fito rurrufe kofofin su mubeena tayi Suka fita a gidan,tunda Suka dotse gate na gidan su Lahab gabanta ke faduwa rabon ta da ta Shiga gidan Harta manta tun wani Shiga da tayi Mami taci Mata mutunci tun Suna yara Bata sake taka gidan ba sai bana da zata yanda suke nufo gidan haka dukan da kirjinta keyi yake daduwa,wutan lantarki ne Kamar rana yake tsaye a kofar gidan ga flowers dake shiki,hannu Inna tasa ta bubbuga gate na gidan....................................................

🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*

Page 79&80

da Ido Mai gadin ya bisu sannan ya bude gate in tare da matsa musu saboda ya gane Inna ba yau ta Saba zuwa ba Akan Case in Lahab da Nabeel tun Suna yara,tafiya suke mubeena na binta a baya duk inda Suka wuce sai mubeena ta Kara waigawa ta kalla da kyau gidan gabaki d'aya ya chanja Mata ganin irin daular da yake ciki yanzun sama da da,tsayawa sukayi a kofar falo Inna nata kwada sallama dayake daman kofar in ba bell aka danna ba ba Jin mutum za'a Yi ba in Yana magana hannu mubeena tasa ta danna kararrawan.

Kallon ya Umar ya jafar yayi yace"gobe in Allah ya kaimu za'a kawo lefen yarinyar Nan umaima Koh"?kwarai ma kuwa gobe ne insha Allah"toh Allah ya kaimu saiku tashi mu tafi dare nayi sai Allah ya kaimu gobe in zaku dawo ma saiku dawo,mikewa dukansu sukayi harda nenne duk da yaran sunso a barsu su kwana amma ya jafar yaki yace gobe akwai school,kallon nanne yayi yace"Ina Majid in da Aisha kuma"mamu ce tace wata kil Majid na wajen Lahab ita Kuma Aisha bazai wuce tana can tana like da umaima ba, kasanta da zancen zuwa biki daga auren mutum ya tashi zata Fara like Masa"Addayiya dake zaune ne tace,kaji Shashashar banza ke zulai shiga ki kirata Kai Kuma uzaifa kirawo Majid in yazo mu tafi"ring na bell Inda sukaji shiyasa Anwar mikewa ya nufi kofar kamawa yayi ya bude sai Kuma ya waro Ido yace"innan Nabeel yau Kuma me Lahab yayi kin fa San baida lafiya Koh fita bayayi karma kice Yama Nabeel kaza"?hararan sa tayi da murmushi a fuskar sa ya matsa Mata ta shige mubeena na binta a baya tad'anji sanyi ganin yaran gidan har yanzun Basu da girman Kan masu kudi in ka cire Shareef yafi kowa mugun hali da murd'adden hali a gidan.

Ah ah sannu da zuwa wa nake gani Kamar Inna kayyu?da murmushi Inna ta karaso cikin falon ta zauna akan kujeran da Addayiya ta tashi tana nuna Mata ta zauna mubeena Kan kanta a kasa tazame ta zauna a kasan carfet"nice hajiya Asma'u"gaskiya ne barkanku da zuwa haba Yan Mata ya da Zama a kasa ki hau Kan kujera Mana kin hawan mubeena tayi sai wani susunkuyar da Kai take komawa zaune ya jafar yayi Suka gaggaisa dasu Inna, fitowa umaima tayi da hijab a jikinta sai Aisha dake gefenta Suna magana a hankali Suna dariya tare da muneera da aka aika ta Kira Aisha kallon umaima mamu tayi tace"ke Kuma meye haka Ina Zaki"dan rausayar da Kai umaima tayi batace kome ba sai Aisha ce tace"mamu Wai zata bimu gidan mune kinsan gobe za'a kawo Kaya shine Wai tanajin kunya"rike Baki Addayiya tayi tace"kunya Kuma Koh munafurci koma menene kwadaiji dashi,mikewa ya jafar yayi again Yana kallon uzaifa daya fito babu Majid kallon sa yayi ya tambaye sa Ina majid in?Wai shi Anan zai kwana"shuru kawai Addayiya tayi Albarkacin su Inna dake falon da wallahi Majid bazai kwana musu a gida ba,fita ya jafar da iyalan sa sukayi su ummu da sauran yaran Suka rakasu compound har gaban mototin su, Bismillah kuzo muje kugansa Yana dakin su,mikewa sukayi Suka bi bayan ta tana gaba Suna bayan ta har lokacin hannun mubeena d'auke da kwandon kwanuka gabaki d'aya jikinta yayi sanyi zuwa da tayi ta tarar da plates na kaji Baja Baja a falon da abinci Mai Rai da lafiya Wanda aka kawowa su nanne,sai taji ta muzanta ita da ferfesun kifin ta da dankali.

Zaune suke da Majid Suna Hira system na Rahab ne a gaban Lahab Yana chatt nasa sai Majid dake Masa Hira Yana cin kazar daya d'auka a dakin Addayiya,turo kofar dakin a kayi Addayiya ta shigo Inna na binta a baya waro Ido Lahab yayi da Suka had'a Ido da mubeena"Bismillah ku zauna ga waje Addayiya tace musu Zama sukayi"kallon Inna Lahab yayi ya gai data ta amsa tare da Masa ya jiki mubeena ce ta Fara Masa ya jiki ya amsa hade da cewa"big Aunty mekika kawo minine haka Naga kulan sabbi alamu dai abun ciki ba karamin dadi zaiyi ba"?dariya Inna tayi tace aiko ka canka daidai kasan Ni bazan tsaya bata lokaci wajen maka girki ba"da murmushi Lahab yace"kaiyya Inna Ina ma Kika iyya bare yayi dadi"dariya dukan su Yan dakin sukayi Majid Kam Inna kawai ya gaidar idanunsa Kam akan mubeena Wanda yasa Lahab sa hannu ya mintsine Naman cinyan sa dan Kara ya sake ya sauka akan katifar ya koma kasan carfet ya zauna Yana jama Lahab Allah ya Isa,kallon kulan Lahab yayi sai Kuma ya mike ya dawo kusa da mubeenar hannu yasa ya bude kulan sai Kuma da Sauri ya kalli mubeena,mikewa yayi ya dawo bakin gadon da kulan ya aje sai Kuma ya sake budewa yadau marfin ya zuba dankalin akai yasa miya ya Kama ci,Yana gyada Kai sosai mubeena taji wani mugun dadi ganin Lahab yaso abinda ta kawo duk da sunada fiye da hakan a gidan su,duk kankantan kyauta da mutum Yama Lahab baya botsaresa sosai yake nuna Masa ya kaunace abin Koh da kuwa bai Masa ba baya nunawa.
Chapter 63 · 0% Book details