← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 122

Sashe 121

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tashi muje na kaiki gida"girgiza kanta tayi a hankali tana cewa"no basai ka kaini ba nida kaina Zan koma ka koma wajen iyalinka"girgiza Mata Kai yayi a hankali yasa hannu ya rike nata ya Soma magana"mubeena ki manta da kome daya wuce a baya mu fuskance gaba Koh da Inna Koh Babu Inna mun riga mun Zama Yan uwa pls feel free with me kinji big Aunty"?

A hankali ta gyada Kai tana share hawayen idanunta sake Mata hannu yayi kana yace suje ya maidata 9:00 na dare yayi tuntuni, tafiya suke Lahab Kamar ance ya d'aga Ido kawai ya had'a Ido da Nnenna dake tsaye a bakin hall in tana Masa wani irin kallo da Bai taba ganin ta dashi ba haka kawai yaji mugun shakkanta ya shigesa,amma ya basar bude motar sa yayi mubeena ta shiga kana shima ya Shiga yaja Suka bar wajen,har unguwan su ya kaita lokacin da zasu rabu kudi kusan 100k ya Bata Amma mubeena taki karba yayi yayi taki.

Lahab na dawowa yaga wani kallon harara da Ade ke aika Masa,kallon yaran nasa yayi yace su taso su tafi Nnenna kin tashi tayi har Saida nazeefi ya Kara Mata magana kafun ta tashi Albarkacin yaron nasu kada ya fiskanci akwai wani abu,shikad'an sa yake Hira da y'ay'an sa itakam bakinta kus Kama wata hanyar taga yayi hakan yasa ta kalle sa Amma batayi magana ba,gidane Mai kyau Kuma kerarre bude kofar sukayi dukan su Suka shiga haurawa upstairs yayi da yaran Koh wannen su ya nuna Masa dakin kwanan sa Babu abinda Babu a dakin nasu Kama daga man shafawa zuwa sutura duk ya tanadar musu.

A ranan bacci ma Lahab basuyi tare da Nnenna ba saboda masifar data yitayi Masa akan mubeena harda cewa in son mubeena yake bazai burgeta ba sai taga ya aureta abu dai baiyi dadi ba ranan.

***************
Washe gari da safe Addayiya ta turo ma yaran kayayyakin su don ta fahimci Lahab Kam ya Kai matar sa dakin tane sun koma gidan su,Yan uwan Nnenna da suka zo aure dukan su sunzo sunga gidan ta Kuma gaskiya sun yaba wa Lahab,Mami tazo tayi ta Neman gafarar Nnenna amma Nnenna tace Mata Babu kome yanzun kome ya wuce ai Suma da laifin su a wancan lokacin,vedion auren Ade da aka had'a dana Lahab Sosai mutane suka ringa tofa Albarkacin bakin su.

Bayan aure bai Jima ba saiga Usman (cousin in Deyana)daga kasar su ya taso har NAGERIA gidan su Lahab yazo da hoton mubeena Wanda a cikin hotonan biki aka d'auka Bata ma sani ba tana zaune akan kujera ga hawaye cike a idanunta,yace fa shi duk duniya yaga matar aure ta tafi dashi,ai ba karamin dadi Deyana(Nnenna) taji ba Koh hankali ta zai kwanta saboda yanda Lahab ke shiga harkan mubeena abin na jaza musu rikici akanta.

Anyi bikin mubeena bukin da d'angi da jama'ar gari basu taba tsammani ba tabbas sunga ikon Allah daman akace Mai hakuri na tare da riba Allah ya kawo wa mubeena Miki balarabe Kuma saurayi ba magidanci ba,bugu da Kari Yana tsananin sonta da kaunar ta a bikin su ba karamin bajinta Lahab yayi ba duk da su basa kayan aure Koh gara Amma bikin yayi armashi kudi yayi kuka kome daya shafe mubeena Lahab ne yadau nauyin sa har aka kammala biki lafiya aka dagata daga naija zuwa Libya.

Iyayen Deyana sunzo bikin don haka Basu koma ba Suka nemi dady(baban Abraham) Wanda kunya ya hanashi Koh zuwa Inda Deyana(Nnenna)take,haka zalika momy itama tayi dana sani sosai,dady shiya dau iyayen Nnenna ya kaisu har Enugu daga nan Ya wuce dasu Edo state duk da dangin papa(marikin Nnenna daya rasu )Basu rike Nnenna ba amma iyayen ta sun musu goma na arziki wa'inda Nnenna ta sani da wa'inda Bata sani ba duk an musu abin Alkhari anan Nnenna take Jin labarin matar papa data rasu Ashe tunda ta dawo Libya da yarinyar(Nnenna)Kuma tace yarta ce ta Fara kudi Kamar na hauka yaranta data tafi Libya ta barsu su uku kaf Suka mutu saura Nnenna kawai Kamar tsafi saiga arzikin matar papa ya Soma karewa wata Rana kawai aka waye gari gidanta da ita ya Kama da wuta ta mutu murus Amma Nnenna Babu abinda ya sameta duk da kuwa tana cikin gidan wannan ne musabbabin rikon Nnenna ya dawo hannun papa,Kuma da iya gaskiya suka rike Nnenna Babu Wanda ya taba tsammanin ba yarsu bane.

Papa yasha tsangoma da tsana akan Nnenna saboda lakaba Mata maita da ake Amma Bai hanasa cigaba da rikon taba.

Bayan tafiyar iyayen Deyana Lahab yaje London ya tattaro duk wani Abu nasa dake can Mai amfani ya dawo nageria ball ma yace yanzun yayi girmeta bazai cigaba da bugawa ba ya barwa yara shi yanzun uban matasa ne, hospital babba ya budewa Deyana tana aiki ga yaran sa na zuwa makaranta duk karshen hutu zasu koma wajen Mami su Mata kwana biyu Su karasa sauran kwanakin a wajen Addayiya.

Labarin Alhaji sulaiman kutsam aka samu wata Rana,sakamakon wani tsoho daya kawowa Yan Sanda rahoto Kuma ya musu jagora,lokacin da aka shiga gidan dake dukar daji sulaiman aka samu rashe rashe dashi da Yan kungiyar su Suna Shan jinin jariri ga gawar yaron a kwance akan table nasu dukan su sanye da jajayen Kaya abin d'aga hankali Amma su Bako Imani, kamosu Yan Sandan sukayi a haka aka fito dasu cikin gari a kallah sun Kai su 10 Kuma dukan su Babu karamin mutan a cikin su, masu kudine sosai d'aga mazan har matan.

Makasu akayi a kotu a ranan dubun al'umma Suka shaida fuskokin mugaye da siffan mutanen kirki Mami tayi kuka bana Wasa ba lokacin da sulaiman ya Fadi dalilin sa na tsanar su Lahab Ashe tun lokacin da Al'hassan ya aure Mami yayi Alkawarin ganin bayan sa da duk abinda Mami zata Haifa Kuma saita Zama mallakin sa,amfani kawai yayi da kiyayyar su Lahab a zuciyar farida da Nabeel yasasu wannan aiki Wanda haka ya bayyana cewa Mami tafison y'ay'an Al'hassan akan nasa y'ay'an shiyasa yayi niyar kashesu yaga Koh in Babu su zata fi son y'ay'an sa sama da kome Daman tuntuni yayi niyar kashesun.

Zancen Nnenna Kuma Ashe kungiyar sune,asalin matar papa tana da mukami Mai tsoka a kungiyar don ta riga sulaiman shiga kungiyar tasu don shi sulaiman wani abokin sane dayaje service inyamuri suka hadu shine ya kawosa kungiyar,bayan matar papa ta dawo Libya kungiya ta bata mukami Mai girma sakamakon yaranta data bayar har uku,Saida Kuma rikici ya barkene lokacin da kungiya ta bukace,ta bata jinin Nnenna anan tace Nnenna Amana ce aka Bata bazata taba cutar da ita ba iyayen ta sun Mata halacci an buga an buga Abu yaki ta kafe akan bazata taba data jininta ba.

Hakan ya fusata shugaba su ya Aiko Mata da annoba Rana tsaka ya Kama gidan ta don duk barazanan da zasu Mata sun Mata amma ta nuna musu saidai tabar kungiyar akan ta bada Nnenna, amma abin Al'ajabi babu abinda ya samu Nnenna cikin yardan Allah saboda marabai dake jikinta sosai suke Bata kariya Amma da izinin Allah (tunda malam ya Bata magani shikenan Bata tare dasu yanxun)bayan mutuwar matar papa, sun gano jinin Nnenna ba karamin karawa kungiyar su shahara zatayi ba duk wani hanya da Suka San zasu bi suga bayanta sun bi Allah baya Basu sa'a lokacin da ta girma sai Suka Soma janta zuwa cikin kungiyya a nufin su ta gaji karagan mulkin matar papa Kuma ta dalmaya dasu saboda Karin shahara da daukaka da zasu samu amma sun rasa meyasa Nnenna tafi karfin su karshe ma duk lokacin da Suka yunkuro Mata sai sunga tashin hankali shiyasa suka sanya Mata kaunar Kule Kuma suka hadata da kiki Yana gadinta.

Jin wa'innan labaren ya d'aga hankalin jama'ar NAGERIA Inda wasu gaggan matasa Suka bankawa motar su sulaiman petur da wuta lokacin da aka fitar dasu daga kotu Basu ma Bari shariya ta kare akan su ba,mutuwar su Babu abinda jama'a ke tofawa sai Allah ya Kara nauyin kasa,mahraz da kannen sa harma da Mami ha karamin kuka sukasha ba uba ubane Koh yaya mutum zaiji zafin abin a ransa.

Su Lahab sun koma rugan su malam Inda Suka tarar Allah Yama malam rasuwa Lahab ya d'auki dawainiyar matar malam nayau da kullum ya gyara Mata gidan ya koma na zamani haka zalika ya kaita haji duk wata Kuma sai ya turo Mata da kayan abinci,mama da Muhammad Ashe iyalan bubaja ne mama ta sake aure ne,lokacin da Suka hadu ba karamin kuka mama tasha ba shima bubaja ya Barta da Sabon mijinta don yaji matukar dadi daya hadu da gudan jinin sa,sannan mijinta ya rike dansa Kamar na cikin sa,ashe lokacin da Suka fita a gidan haka kawai Suka manta da kome da kowa nasu sai mutuwar su sulaiman ne abubuwan Suka dawo musu.

Rayuwa ta koma sabuwa sai abinda ba za'a rasa ba daman shi dan Adam kulum cikin jarabawa da tawakkali yake yau dadi gobe akasinsa,mubeena Amarya ta haihu Allah ya azurta ta da samun ya mace,haka zalika matar Ade ma ta haifi namiji,amma Deyana shuru kake ji har yara sun gima kusan 15years kafun Allah ya saukar Mata da rabon ta,itama ta Kara haihuwar namiji yaro yaci sunan Rahab duk da ba tagwaye bane amma Lahab yasa Masa Hussain Kuma ana Kiran sa da Rahab,saboda har lokacin Kewan Dan uwan sa da har gobe yake damun sa Bai barsa ba, Y'ay'an Mami kaf sunyi sure Yusuf autane kad'ai ya rage shima ya Zama saurayi.

Abotar Adewale da Lahab sai Kara gaba gaba yake har Kuma lokacin iyayen Ade basu musulunta ba sai dai hakan baisa eshat da yaranta sun guje jinin ubansu ba haka suke zuwa wajen kakanayen nasu Kuma Alhamdulilah Suma Suna kaunar y'ay'an d'an nasu(jikokin su) Kamar me ga yara Kamar larabawa kamannin uwar su Suka d'auka hatta launin fatar su.
Chapter 121 · 0% Book details