← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 122

Sashe 103

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mikewa yayi ya dauko kayan baccinta dogon riga saka Mata yayi kana ya kwantar da ita ya sanya mata socks na bacci,ya tashi zai fita a dakin hannu tasa ta Kama nasa amma batayi magana ba sai Kuma tace"idan abinci zaka sayo ka Bari kawai a koshe nake banajin yunwa"zame hannunsa yayi yace"na sani inna kawo kada kici"yasa Kai ya fita a dakin.

Yana fita falo ya waro Ido ganin tsohowar Nan dake falo ta wani rungume kuloli a hannu,dan kallon sa tayi sai Kuma tace"Dan ball Aina Jima a falon Nan naku nayita sallama shuru shine nace taima sallah kuke Bari na jiraku,Lahab Kam d'an kunya yaji ganin babu riga a jikinsa da Sauri ya bude kofar dakin sa ya Shiga riga ya d'auka ya dawo falon Zama yayi Yana gaidata amsawa tayi kana ta aje kulan hade da cewa"wannan abincin garin mune,tuwon masara miyan lawashi da kifi harda gyada kasan lokacin da akace min hauwa'u zata haihu duk Saida na tanadi abincin masu jego na tawo dashi,shine nace Bari na zubawa yayarka mema sunan ta"?dafe Kai Lahab yayi yace"Labiba"Labiba Kuma sunane wani irin sunane haka Ina ma laifin a karasa da Habiban ta ai yafi"mikewa yayi yadau kulan kana yace Mata sun gode sai Kuma ya juya zai bar falon.

Am nace ba Ina mamar taku Ina Mai cikin"mama duk Suna bacci ne"bacci Kuma haka da isha'innan Koda yake nasani Koh Yan gayune ku"shuru yayi Yana cigaba da tafiya da abincin yasa hannu zai bude kofar dakin daidai lokacin Nnenna ma ta bude kofar zata fito Jin surutai kad'an kad'an a falo"lai kin tashi"mama tace cikin farin ciki karasowa falon Nnenna tayi tazo ta zauna a kasan carfet da Sauri mama tadau pillown kujera tana cewa maza ta tashi tasa Mata bakyau tana Zama dabas haka a kasa.

Shidai Lahab na tsaya da kula a hannu Nnenna nata Hira da mama mikewa mama tayi ta nufesa hannu tasa ta kwace kulan tazo ta aje a gaban Nnenna babu tambaya ta nufi kitchen Wai zata dauko plates,kallon Nnenna yayi yace"kiyi taka tsamtsam da wannan Mata kinji na fadamiki"shuru ta masa har mama ta dawo Iba Mata tuwon tayi da Miya Nnenna Kam sosai ta zage tayita cin abinta Suna Hira rabonta dacin irin wanann abinci ai anfi shekara.

Lahab na daki a kwance Yana Jin surutansu a falo,har kusan 10 na dare mama Bata koma ba,ya zubawa sarautan Allah ido yaga iya gudun ruwan su, knocking na kofa yaji akayi,da Sauri ya mike ya fito falon kallon mama yayi Wance ta kwanta akan kujera harda filo ana ta Hira,bude kofar yayi Muhammad Ne nan dai Muhammad ya tasata a gaba suka bar gidan duk da ranta baiso ba,washe gari da safe lahab na gida da gangan ya sawa kofarsu key gudun kada mama ta sake dawowa,da misalin karfe uku na yamma ya tafi airport dauko Ade.

Da dare zaune suke dukan su a falo ana hiran yaushe gamo anan Ade ke Basu labarin nageria jakansa daya shigo falonsu dashi ya jawo budewa yayi ya dauko laida babba Bakin laidan ya bude ya fito da maganin kulli kulli Yana cewa"ga wannan gogojice ta ban Wai inji malam Nnenna tana Sha a shayi Koh kunu sai Kuma wannan yace na wankan Kane wa'innan Kuma yace Wai in ta haihu a baiwa yaran susha kafun a Fara Basu nono,a had'a musu da ruwan zamzam"da mamaki Lahab yace"ya akai malam yasan tana da cikine Wai"wallahu alamu shine abinda Ade yace sai Kuma ya dauko wani laidan yace gashi inji mubeena abaka"dariya Lahab yayi yace lallai big Aunty gabaki d'aya na manta da ita wallahi Amma yanzun tayi aure koh"girgiza Kai Ade yayi yace batayi ba.

"Toh ya maganar soyayyar ku"kaima dai Lahab Wasa kake Koh aini inaga na hakura kawai wannan karon ma wulakanci na Tara Saida nazo Mata bankwana na samu fuskar da tacemin na kawo maka sako"bude letter Lahab yayi gaisuwa ne sai Kuma number ta data aje Masa a karshe tare da fatan Alkhari, murmushi kawai yayi lokacin da ya Gama karantawa Yana dago Kai sukayi Ido hudu da Nnenna dake hararansa da Ido Kamar zasu bullokuto waje mikewa tayi cakal cakal irin saurin masu cikin Nan ta nufi daki"

Kallon juna kawai Ade sukayi sai Kuma Lahab yadau laidan maganin ya bita cikin daki,zaune ya sameta ta had'a gabas da yamma Zama yayi a bakin gadon da mamaki yake tambayar ta meya Bata mata rai"tura hannunsa tayi a jikinta ta kwanta hade dajan bargo Bata Kara magana ba,aje magangunan yayi ya fita a dakin,da misalin tagwas na dare Nnenna mikewa tayi Jin Karan bude kofar da rufewa fita tayi a dakin Lahab directly ta wuce budewa tayi ta Shiga sannan ta shiga dube duben abinda take nema da Sauri ta dau lettern dake Kan gadon ta warware kana ta Soma karantawa,cikin haushi ta yayyaga paper tana Jan tsaki,daga Ido da zatayi sukayi four eyes da Lahab dake tsaye harde da hannu.

"Meyasa Kika yaga"shuru tayi Bata ce kome ba"meyasa Kika shigomin daki Ina mun riga mun raba daki bake bane?"Nan ma shuru ta Masa"nuna Mata kofa yayi"fita"a hankali ta Soma takawa sai Kuma ta fashe da kuka tana dafa bango da Sauri ya matso gareta Yana tambayar ta lafiya kasa amsa Masa tayi sai kokarin dukawa da tayi,da Sauri ya tallafota akan cinyarsa Suka zauna,yamutsa fuska ta somayi tana Dan juya Kai a hankali hankali tashe yake cewa meke damunta Amma shuru babu amsa sai lip nata na Kasa data Kama da karfi tana taunasu,mikewa yayi ganin jini ya biyo sahunta da Sauri ya Soma sanati hade da ciccibarta suka fito daga flat nasu da Sauri ta bude motar ya sata tare da zagayowa ya shiga yaja da karfi tunkan ya Isa hospital in ya Kirasu akan Suna zuwa ya sake kiran Ade ya sanar dashi,Suna Isa hospital aka shiga da ita labour room,iya wahala Nnenna Tasha Amma haihuwa shuru Kamar zata mutu tace a Kira Mata mijinta ya yafeta karta mutu Yana Jin haushinta, lokacin da Lahab ya shigo dakin kuka kawai ya Soma Nnenna na kuka tanacewa ya yafe Mata mutuwa kawai zatayi,shi Kuma sai cewa yake bazata mutu ba.

Dr cewa yayi Lahab yasa hannu za'a Mata operation,saboda kasa haihuwa da tayi da kanta ga karfinta ya Kare,hannun Lahab na rawa yayi sign cikin fargaba sai Addu'a yake Allah ya sauketa lafiya,fitowa yayi a dakin Yana hawaye da Sauri Ade dake zaune a waje tuntuni ya mike zuwa yayi ya Fara basa Baki akan yayi hakuri,insha Allah zata sauka lafiya ya Mata Addu'a shitafi bukata.

Zaune suke gabaki dayan su hankalin su a tashe yake cikin damuwa, fitowa nurse tayi ta ce Lahab ya shigo,mikewa yayi yabita har dakin da aka kwantar da babies in tunda yasa hannu ya daukesu kuka kawai ya fashe dashi ya mannasu a kirjinsa mace ne Dana miji aka Haifa yara farare tass Kamar mahaifiyarsa,Saidai fuskar sak na ubansu ne,kuka yake hawaye shabe shabe dagasa nurse in tayi tana cewa kukan ya Isa haka yaran sa kyawawane don ita Bata taba ganin Miji ya kawo matarsa Yana kuka haka ba sai yau tunda daman sun riga Sunsan Lahab da Nnenna yanzun basa mamakin auren nasu,,kiss ya manna musu a kumatun kana ya kalli nurse in"Ya jikin nata?sunkuyar da Kai tayi sai Kuma tace am sorry ka kwantar da hankalin ka muna iya bakin kokarin mu Amma jininta ya tsinke yanzun ma jini ake sa Mata jini na zuba a jikinta sosai ka Mata Addu'a zataji sauki amma maganan operation anyi nasara sai na tsayuwar jini,zaro Ido Lahab yayi yace"tsinkewar jin.......???? Bai karasa ba yaga nurse tasa hannu ta amshi yaran hannun sa tana Kiran Jesus ganin numfashin yara na sarkewa akai akai dukan su biyu................................................

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*

Salati Lahab ya sake da karfi itama nurse hankali tashe ta kwantar da yaran tare da Kiran likita da telephone Inda ke manne a dakin Koh minutes biyu ba'a Yi ba saiga Dr ya shigo harda gudun sa Suka Soma bawa yaran taimakon gaggawa oxygen Suka saka musu a hanci har lokacin numfashin su Bai daidaita yanda ake so ba,Allah sarki d'a Mai dadi Lahab Bai tabajin yanason wani Abu farar d'aya Kamar yanda yaji wani irin kaunar yaran Nan ba, hankalin sa sosai ya tashi Wanda yasa likitoti koransa waje,Ade Karan kansa ya shiga tashin hankali bare da Lahab ya shiga dakin da Nnenna ke ciki yaga yanda ta jirkita laidan jinine hannu biyu aka saka Mata tsaban irin zuba da jini keyi a jikinta"

Kamar an mintsine sa da gudu ya fita a hospital in gida ya koma ya Soma neme nemen maganin da Ade ya kawo Masa saban tashin hankali daker ya gane maganin fitowar sa kenan a gida zai Shiga mota saiga Muhammad anan Suka gaisa yake sanar dashi d'azun mama tayita zuwa gidan su a rufe lafiya Kam,a damuwan ce lahab yake cewa haihuwa Nnenna tayi tana hospital babu wani kawaici Muhammad yabi Lahab hospital lokacin da ya tsinkawo lamarin sosai ya tausaya wa Lahab don shi Karan kansa yasan tashin hankali daya Shiga lokacin haihuwar matarshi,bare Lahab da aka ma Matarsa tiyata ga tsinkewar jini ga yara babu lafiya Kuma sosai yasha mamakin kasancewar su couple Bai taba tsammanin hakan ba.
Chapter 103 · 0% Book details