← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 122

Sashe 76

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kunya Kamar ya kashe Alhaji sai lallabata yake ta tashi su fita surkinsa ne karta kunyata shi amma abin bakin ciki mikewa Amina tayi tasa kafa ta shurar da kulolin abincin dake gaban sarki ta Soma masifa akan bazata tafi ba saiya saketa bazata zauna dashi ba,dafe kansa yayi cikin takaici sai Kuma ya sulale ya Fadi Koh motse bayayi salati muzammil daya shigo gidan kenan dawowar sa daga makaranta Addayiya ke sanar dashi sarki na falon babansu yaje ya gaidashi,ya jima a bakin kofar Yana Jin duk abinda ke faruwa amma baice kome ba don yasan Koh yayi magana baban sa zai gwatsele sa akan Amina.

da gudu ya shigo dakin yayi Kan mahaifin nasu sai Kuma ya sake kuka yana kwalama mutanen gidan Kira ya mike da gudu yabar falon sarki ma mikewa yayi yana salati ya matso wajen alhassan in bayan ya dauko ruwa yana shafa Masa amma ina shuru,saiga muzammil da fadawa da suke tsatsaye a kofar flat in da sauran Yan gidan suka shigo falon da gudu cikin tashin hankali Amina dake gefe da Sauri tayi hanyar kofa jikinta na rawa bata taba Shiga tashin hankalin da ta shiga ba, karfa mutuwa Alhaji yayi.

Mikewa muzammil yayi yabi bayan ta da gudu tana kokarim dannawa kofa sakata ya bango kofar ya shigo bell nasa lafiyayye ya Soma lafta Mata da iyya karfin sa Daman ya girmeta da shekara biyar a lokacin Yana da 21year,mugun duka ya rufeta dashi baji ba gani duk takaicin da take dura Masa a gidan yau shiyake sauke Mata, dukanta Yake Yama cewa kafun ta kashe Masa uba shi zai Fara kasheta har lahira inyaso ana binne ubansa ana tona kabarinta a gefe.................................

🍀*By Ruqeenjalal*🍀

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*

Page 96&97

babu Wanda hankalin sa ya kawo wajen dukan da muzammil kema Amina asibiti aka wuce da minister,mamu ce ta hankalta bayan an wuce da Alhajin asibiti Kara zuga muzammil tayi,shikuma yayi ta kirban Amina ba karamin duka Yama Amina ba Saida ya faffasawa Yar Fulani jiki kaca-kaca kafun ya Barta korata shida mamu sukayi a gidan har bakin titi mamu ta yafa mayafinta ta kora Amina muzammil na rike da bulala, sulaiman daya maida kofar gidan wajen zaman sa tunda aka Hana kanwarsa shiga shikenan ya maida wajen wajen zaman sa kullum Yana tsumayen wata Rana Amina zata fito Kamar a mafarki yaga Mai Kama da ita an hankadota daga cikin gidan,hankali tashe ya mike ya bi bayan su daidai lokacin muzammil ya watsa Mata bell da Sauri ya tare dukan tare da cakumar muzammil da dambe security dake kofar gidan da gudu Suka nufosu ganin wani na dambe da Dan minister a takaice dai daga Amina har sulaiman ranan jikin su yayi tsami bana Wasa ba.

Allah yaso sulaiman yana da kudi a wajen sa,dashi Suka hau mota zuwa kauyen su gabaki daya zance ya baza kauye sulaiman ya kashewa Amina aure inno batayi binciken kome ba ta hau fushi da Amina Koh sauraron raunukan dake jikinta batayi ba,sai muneeru dake Kai kawo a kanta.

ta bangaren gidan minister sai bayan tafiyar Amina sukaji labarin dukan da Muzammil Yama Amina,Amma babu Wanda ya damu don ba sonta suke ba Daman Kuma abinda tama mahaifinsu ya musu zafi,hawan jini ya samu sosai Koh hayyacin sa Bai dawo ba sai bayan kwana biyu ya Fara bude Ido,a ranan daya bude Ido da zancen Amina ya farka sosai ran Addayiya ya baci ita ta sakasa a wannan Hali sannan har Yana da bakin Kiran sunan ta bama yaki taba,baida magana saina Amina batazo ta dubasa ba Koh Bata da lafiya ne,da haushi ya ishi muzammil Anan yake ce Masa tana garin su ya koreta Aiko ranan sunga me ake Kira bacin Rai iya bacin Rai rikice musu yayi akan lalle lalle sai an sallamesa yaje ya dauko matar sa a kauye.

Abin fa ya wuce tunanin Mai tunani dole tasa alhussan tashi tare da basa Baki akan shi zaije ya daukota shi Kuma yayi hakuri ya zauna a asibiti sai jikin sa yayi sauki kafun yace zai bar asibitin.

Alhussan badon ransa yaso ba yaje garin su Amina,sosai inno tayita basa hakuri lokacin da ya zana Mata abinda Amina ke musu, daki ta Shiga ta jawo Amina tare da Mata kashedi Koh bayan ranta ta sake Masa makamancin abinda akace, indai ta rabu da Alhaji Allah ya Isa Bata yafe Mata ba Amina tasha jinin jikinta bana Wasa ba especially furucin inno gareta haka ta bi alhussan har asibitin halin da taga bawan Allan a ciki sosai jikinta yayi sanyi shikam cewa yayi ta zauna a asibitin kin Zama tayi saboda yanda kowa yazo sai taga irin tsanar da yake nuna Mata abayyane, komawa gida tayi sai dai tazo ta dubasa ta koma shikam yad'anji dadi kad'an ganin ta dan sauya Hali tayi sanyi ba Kamar da ba, ba'a San garin Yaya ba wani ya sanar da Alhaji dukan da Muzammil ya Mata sosai ya birkice yace muzammil kada ya sake taka Masa gida ya tattara yanasa yanasa ya koma hostel,wannan shine mafarin gabar da muzammil keyi da Amina ata dalilinta mahaifin sa ya bude Baki yace kada ya tako Masa gida akanta.

Alhaji yaji sauki inno da muneeru sunzo sun dubasa Kuma sun Kara basa hakuri akan abinda ya faru,su Umar hankalin su ya tashi haka zalika ransu ya baci na abinda mahaifin su yayi na korin muzammil,gashi yaran duka sun tsani Amina sosai,Umar jafar su Suka tattara yaran su da Suka Fara wayo sosai, muzammil Anwar Shareef da Hashim Suka turasu abroad karatu gabaki d'aya bama sun sanar da mahaifin nasu ba Saida yaran Suka tafi,sosai Alhassan yaji ba dadi Amma baice kome ba, gidan ya kasance yarane kananu kadai a cikin sa masu wayon duka basa Nan.

Amina tayi sanyi kad'an Kuma ta Soma kula Alhassan harma suyi Hira hakan ya samu mafari ne da takardu Koh jaridu dayake kawo Mata Yana karanta Mana tare da koya Mata yanda ake wasu abubuwan a boko shikenan ta Soma sanyi haka zai sayo littatafai in yana gida su zauna Yana karanta Mata Yana fassara masa,ganin yanda take kaunar karatu yasa sa shigar da itama makarantan secondary akaita a daukota, a sannu sannu soyayyar sulaiman tayi sanyi aranta bawai son alhassan ta Fara ba ah ah tanajin farin ciki yanzun in tana tare dashi a hankali hankali zaman su ya sauya daga tsana zuwa kulawa.

Bayan wasu watan Ni saiga ciki kusam ya fito daga wajen Amina abinda ya zamo abin mamaki da Al'ajabi da kunya a wajen ahlin gidan Inka cire uban gayyan dayafi kowa murna murna yake Kamar Bai taba samun Y'ay'a a duniya ba sai Nan Nan yake da Amina kome take so jiki na Bari yake Mata,itakam Amina kunya sosai yake damunta haka zata kunshe ciki musamman lokacin da ya fito tayita boye boye batason Koh fita tsakar gidan.

Lokacin da cikin ya girma hatta tafiya Amina bata iyyawa sosai duk tsanar da Addayiya da sauran yan Gidan Suke Mata Saida Suka dawo tausaya Mata Amma Banda Mamu dake ta radawa mutane cikin jikin Amina bana surkinta bane,saurayinta ke binta makaranta daga Nan su wuce iskancin su shine tayi ciki ana cewa Wai na alhassan ne,magana fa ya fito fili Wanda yasa alhassan mugun fusata tare da jawa Umar dogon layi akan ya Shiga tsakanin matar sa da Amina maganar datayi girma Saida Umar ya sake halima,ganin yaka yasa jafar tattara matarsa da yaransa Suka koma cotes na ma'aikatan gonnati Suka bar gidan.

daker da sudin goshi mamu ta dawo dakin ta,cikin Amina ya girma girma bana Wasa b,sosai alhassan yake kula da ita da abinda ke cikin ta baya duba tsufansa Koh girma yake tattalan matar sa,lokacin da cikin Amina ya shiga wata tara,Alhassan ya Soma ciwon da ba'a gane kansa ba,da fari ciwon ciki ya Fara anje asibiti sukayi gwaje gwaje aka basa magana Koh sati baiyi ba sai Kuma tashi ya gaggara haka aka ciccibesa aka Kai asibitin likitoti sukace su basuga ciwo ba,hankalin family Nan ya tashi bana Wasa ba dawo dashi gida sukayi ganin yanda yake ramewa.

Alhassan ya rame ya Kade gashi a kwance sai abinda aka Masa magana ma ya daina saidai kawai aga yana zabura Yana Shure Shure hawaye Nabin kumatun sa,abun fa ya d'agawa Amina hankali ganin tunda ya kwanta sai aka hanata shiga Koh dakin da yake,mamu ta Soma zuga Addayiya Wai Koh Amina ce da saurayin ta Suka Masa asiri,Nan fa Addayiya ta tada hankalin ta aka Fara Neman maganin hausa,Koh wani malami aka kawo daga yace iska sai yace asiri aka Masa,Nan danan magana ya Fara nisa Amina ce ta Masa aSiri ai Fulani daji me(shiyasa akeson Koh baka son mutum ka boye kiyayyar a idanun mutane inko ka bayyana toh Koh Abune ya samu mutumin in badai Yana da tauyidi ba kana cikin matsala).

Yau Amina ta tashi da nakuda sosai take cikin halin ciwo,tun safe tana daki tana fama da jikinta don tunda Alhaji ya kwanta ciwo babu Wanda yake bi ta kanta abinci ma kuku zata kawo Mata ta aje Mata ta fita duke take a bakin gado sai jujjuya kanta take tana damke da bakin gadon sai salati take tana kuka.

Muzammil dasu Anwar da labarin ciwon Alhassan ya riskesu duk da Muzammil na fushi da abinda mahaifin nasa ya Masa Amma halinda akace yake ciki ya tada Masa da hankali bayan isarsune suka tsinci zancen ai Amina ne ta Masa asiri abinka da maza su Basu wani yarda da zancen ba,amma Mata Kan sosai suke zuzuta abin,cikin wannan halin da Amina take ciki badawiyya(matar Hussain)ta shiga falonta da sallama don ita Sam yau hankalinta Bai kwanta da shurun Amina tun safe Koh tsakar gida Bata fita ba.
Chapter 76 · 0% Book details