← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 122

Sashe 49

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ganin zai fita yasa Inna dakatar dashi,tsaya Nabeel basai ka Kira bappan kuba zauna kaji abinda munafukar yarinyar Nan tace mini bayan ta gama munafurcinta sannan tazo tasa kanta a damuwa ai ba kuka zatayi ba Murna zatayi.

dan tsaki Nabeel yaja,Kinga Inna Ni kimin bayani yanda Zan gane Mana menene mubeenar tayi Kuma,kunzo kun hadu Kuna kuka Koh wanine ya mutu?

Jin tambayar da yayi yasa mubeena girgiza Kai ta Mike tsaye Shima mikewa yayi ganin ta nufi Kan taburma ta zauna Shima Zama yayi yasa hannu ya Kama nata sosai ya rike cikin nasa a tausashe Kamar ba Nabeel abokin Lahab ba ya soma magana,Kinga mubeena kibar kukan Nan haka ya Isa kimin bayani duk kunbi kun rudani meke faruwa ne?shuru mubeena batayi Masa magana ba sai kallon kasa da take har lokacin idanunta na zubar da hawaye,Taya zata maka magana bayan bata da gaskiya.

Kinga Inna in Zaki fadamin ki fadamin kawai Kuna dad'a rudani fa?

ba kome bane yasamu cikin wannan Hali illah abinda Yar uwarka da bata rike maraicin ta ba ta aikata Wai har yarinyar Nan zataga tsabar idanun yaron Nan Ahmadu tace bata sonsa yaron da yayi d'awainiya da ita tun bata Kai haka ba watoh yanzun ta Zama Yar collegi(college) zatazo ta nuna Masa wayewa banda rashin tunani irin nata ai shiya sata a makarantan.

sauke ajiyar zuciya Nabeel yayi Jin abin ba wani babba bane amma duk da haka Sosai abin ya basa mamaki har Saida ya kasa boyewa,Inna kikace Aunty mubeena tace Miki sun rabu da Ahmad Kuma ita tace bata sonsa?tunda Kika ga hakan Kika sani Koh akwai abinda ya Mata shiyasa tace bata sonsa,tsawon shekarun Nan batace bata sonsa ba sai wannan Karo gaskiya da sakel.

Jin amsar da Nabeel ya baiwa Inna yasa mubeena ta Fara magana a hankali har lokacin kanta a kasa,babu abinda ya hadamu da Ahmad daman bashi nake so ba Ina da Wanda nake sone.

Wakike son kenan sannan tsawon shekarun Nan bakisan baki sonsa ba kuke tare Koh yanzun ne kika ga Wanda kike son Inna tace

Aunty mubeena ki kwantar da hankalin ki ki Mana bayani d'aga Ni har Inna nakine babu bare in baki fada Mana damuwan ki ba wa Zaki fadawa kenan Yar uwa?kinsan mu masu goyon bayan abinda kike sone mundin zai saki farin ciki amma fa in bai sabawa shariya ba.

Sosai maganar Nabeel ya baiwa mubeena karfin gwuwar fadin abinda ke ranta daman tsoro take taya zasu d'auke al'amarin a hankali ta soma magana,daman tun da dadewa bashi nake so ba ku.............

🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785tare da shaidan biyan ki*

Page 61&62

Uhmm Aunty mubeena munajin ki ya kikayi shuru Kuma?

dan shuru tayi sannan a hankali tace,toh banace bana sonsa bane Kuma ban d'auka zaiji ba ashe yazo wajena a makaranta bansani ba shine ya yanke jiki ya Suma..........................................daga a har z mubeeena ta sanar dasu duk abinda ya faru amma bata sanar dasu Lahab ne take son ba ta boye musu tadai ce tana da Wanda take so,ajiyar zuciya Inna ta sauke Jin dogon bayanin da mubeena keyi,toh ke mubeena yanzun duk maye saki a damuwa?ai tunda ya hakura abinda ya dace yanzun saiki fitar da Wanda kike son yazo a muku aure bashi kenan ba Shima yaje ya aure takwarana in ba?

hawaye ne ya zubowa mubeena Jin abinda Inna tace,toh yanzun Inna fisabililahi sai Ruky tana kawata sai ta yarda zata aure sa kenan?

toh dan kaniyar ki sai taki ne Koh Yaya a zamanin da ake innan ana haba haba da mijin aure har zata ga bonus ta bari ne?kince baki sonsa don haka kicewa Wanda kike son ya fitoh, nagaji da ganin ki a zaune ba aure in ma karatunne ya ajeki bamuda kudin biya miki yanzun.

Haba Inna da wanne zataji ne Wai guda daya haka, Nabeel yafada wa Inna sannan ya juyo ga mubeena,Kinga Aunty mubeena yanzun kiyi shuru ki kwantar da hankalin ki ki Mana bayani shin Menene ya saki kuka da damuwan so kike Ahmad ya dawo ne?Koh Kuma bakison Rukayya ta aure sa wanne ne baki son guda daya?

girgiza Kai mubeena ta sake tare dajan numfashi Jin tambayar da Nabeel ya antayo Mata Wanda bazama tace eh ne Koh ah ah ba ta rasa wanne ne d'aya? tace bata son Ahmad amma tanajin haushin auren Ruky da xaiyi,nifa ba wa'innan ke damuna ba kawai dai makaranta nane gashi Rabin kayana duk shiya dinka min bazan iyya cigaba da amfani da abinsa ba,sai Kuma ta fashe da kuka Kuma Wanda nake son baisan Ina sonsa ba.

Ai Jin haka yasa Inna mikewa cikin masifa tace,keee maimuna don baki da hankali har kina maganar makaranta ai Ni koh Ni da kaina bazan sake barinki kije makaranta ba aure zakiyi,sannan Kuma kice Wanda kike son baisan kinayi ba, me kike nufi kenan mu Zaki mayar Yan iska Koh Yaya?

don girman Allah Inna ki barsu shiyasa Aunty mubeena bata son gaya Miki matsalan ta maimakon ki natsu ki bata shawara Koh Nasiya saiki Kama Mata ihu aikin gama dai ya gama Koh Ni Karan kaina banji dadin abinda tayi ba amma ya zanyi bazan iyya ganin Yar uwata ta aure Wanda bata so ba,shuru Inna tayi ta koma Kan kujeran da ta tashi ta zaune,ganin tayi shuru yasa Nabeel cigaba da magana,indai akan makaranta ne karkiji kome Aunty Ni Kuma insha Allah daga yau xanna xuwa shago xanyi aiki yanda ya Kamata xan nemi kudi na biya Miki kudin makaranta Koh da kuwa Ni Zan hakura da nawa karatun daman Lahab da Ade me biyamin, sannan Koh Ni bazan so ki cigaba da amfani da abinda Ahmad ya baki Koh yayi Miki,amma fa dole ne Zaki bar wasu kiyi amfani da wasu kamar sutura dole ne kisa nasa amma makaranta insha Allah Ni Zan cigaba da biya Miki ke Kuma ki maida hankali akan jarabawanki insha Allah kome zai daidai.

dan shuru mubeeena tayi tana kallon Nabeel in kafun tace,amma fa Ni babu ruwana da Rukayya daga yau, Kuma Zan maida Masa da wayarsa dake hannu na yanzun?

Inna ce ta tareta kafun ma Nabeel yayi magana,babu wani ba ruwanki da kawarki ai ita bata Miki kome ba, Kuma Koh tayi kece Kika ja maganar waya Kuma baza'a maida Masa ba ki bawa Nabeel yaje ya sayar dashi sai ya sayo Miki wani kala Kinga Koh anga waya a hannunki ba nasa bane.

gaskiya ne Inna bai Kamata ma ta nuna abin ya Mata zafi ba Kuma nima na tabbatar yaso auren kawartata ne don ya kuntata Mata badon Allah ba sai Kuma maganar Wanda take so, Aunty mubeena mu Maza Muna da wani dabi'a shine in mace ta nuna tana son mu Koh auren akayi bata mutunci a idanun mijin nata sai Wanda yasan abinda yake in Allah ya hadata da namiji Masanin Alkur'ani da hadisai don haka Ina Mai shawartar ki akan kibi kome a hankali sannan ki rike ajinki na y'a mace.

Insha Allah Nabeel Zan kiyaye tace cikin Jin dadi ganin basu matsa sai sun San wanda take son ba,Kuma taji dan sanyi data samu ta tofa abinda ke damunta.

Inna Kam cikin dan sake jiki datayi tace,toh yanzun mubeena haka Zan tasaki a gaba sai dai in gari ya waye kiyi wanka ki tafi makaranta Wai da sunan kina jiran Wanda yake sonki yazo auren ki wannan abune da xaiyo kuwa?,nidai Ina fada Miki gwara kiyi abinda zai fansheki Nabeel baisan kome ba sai shashanci.

Jin abinda Inna tace yasa mubeena mikewa ta shiga dakinta Cikin Jin haushi Nabeel yace haba Inna menene haka don Allah ya zakina fadar magana irin wannan yanzun Nasiya da magana Mai dadi Aunty take bukata amma abinda kike matan Nan baida kyau wallahi.

don Allah rufemin baki Wawa kawai.

Mikewa Nabeel yayi yasa takalmin sa zai bar gidan don yaga duk ta Inda zai bullowa Inna bazata hakura da masifar Nan ba dan dakatawa yayi Jin Inna na Masa zancen Lahab akan jiya muzammil yazo Neman sa baya Nan,Kai Inna inaga dai baikoma gida bane don yace min zashi gidan yayan sa jafar taima ma yanzun sun gansa amma bara nake gidan su Ade in yaso sai muje mu duba sa a gidan yayan nasa nima nayi missing nasa kwana biyun nan wallahi.

Ku dai kuka jiyo daman in kun hadu ba'ajin Alkhari amma daya ke kwana biyu baku haduba har dan hankali ka Fara,Jin abinda Inna tace, murmushi kawai yayi ya fita a gidan nasu,mubeeena dake daki tana jiyo duk abinda suke cewa dafa kirjinta tayi tana tari a cikin kwana biyu da bata sa Lahab a idanunta ba abin ba karamin nukurkusanta yake ba.

**********************
Mami Suna fita a gidan parking tayi a bakin titi tare da sauke ajiyar zuciya tana kallon Rahab dake zaune a sit in Mai zaban banza dake kusa da ita gabaki d'aya taga yaron nata yayi sanyi sosai wallahi,Rahab ta Kira sunansa amma shuru bai amsa ba hannu tasa ta shafa kumatun sa dan juyowa yayi Yana kallonta sai Kuma ya kalli titi shi baima San tayi parking ba,Mami ya Kika tsaya Kuma Koh motar ta lalace ne?

ba lalace wa tayi ba Rahab magana nake son muyi a gaskiya abinda kayi yau Innan banji dadi ba Sam, na kuma Yi shuru ne badon ka burgeni ba nayi shurun ne saboda na barka ka Fadi abinda ke nukurkusan ranka amma fa ka sani kaf duniya baka da gidan da yafi wannan gida da kake ciki sai Wanda zaka mallaka Nan gaba,baka da wasu Yan uwa Kuma Ado a gareka daya fisu barinka gidan Nan bazaiyu ba,in har kabar gidan toh burin mamu ya cika na rabaku da yan uwanku Kuma muzammil yayan Kane banji dadin abinda ka Masa ba.

da Sauri Rahab yace,nima Mami ai banjin dadin abinda yake Miki,meyasa Koh don albarkacin mu bazai mutuntaki ba kina matan baban sa taya Zan cigaba da basa girman sa Mami?
Chapter 49 · 0% Book details