← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 122

Sashe 61

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai akayi treatment in kiki harda allurai aka Masa Dr n yace a bar Masa shi taje school ta dawo, Abraham ne ya biya duk kudin da aka kashe a clinic in daga Nan makaranta ya kaita tare da sanar da ita akan ta jirasa zaizo ya dauketa in aka tashi,zaune take a class tana tunanin yanda Lahab ya kwana da jiki taci burin zuwa ta dubasa sannan ta Kai Masa card nasa amma Bata samu hakan ba gashi tsoro take ji kada ace bazata Kara ganin sa ba tunda ance an koresu gashi yanzun batasan gidan su ba,ga Dad zai nema Mata driver tunawa da zulaihat data taba zuwa ta karbi jakan Lahab a hannun ta in bata manta ba Yar junior set ce Kuma ba shakka zata game fuskar ta da Sauri ta Mike ta fita a class in ta sauka a barandan su.

Block in junior ta shiga class by class amma koh Mai Kama da zulaihat bata gani ba sauka tayi a baranda har tazo tsakar compound na makaranta motar gidan su Lahab ta danno Kai cikin makarantan muneera ce ta balle marfin motar sai Rahab daya fitoh a gidan gaba sosai Nnenna ta daskare a wajen tana bin dan uwan nasa da kallo cikin Al'ajabi don ita a zatonta Lahab ne yazo makaranta da Sauri ta nufesa ganin zai hau block in class nasu tace"Lahab tsayawa yayi Yana kallon ta da mamaki duk da yasan ba shi ta sani ba amma ya cika da mamakin Inda tasan Lahab don shidai bai taba ganinta a school in ba"ya jikin naka Wai har an kunce hannun ne"?ta ce tana kallon sa, murmushi kawai yayi yace Mata"da sauki sosai amma baizo ba"waro Ido tayi kenan wannan ba Lahab bane lallai kam,card data dauko da niyar baiwa zulai ta Mika masa tace"gashi na Lahab ne Inka koma ka basa" hannu yasa ya karbi ATM in Yana jujjuyawa juyawa tayi tana tafiya shidai Yana tsaye har lokacin Yana binta da kallo Harta shiga aji shima juyawa yayi ya wuce nasu ajin.

***************
Adewale na barin makarantan su mubeena gidan su Lahab ya wuce,zaune suke a daki Suna Hira kallon Adewale Lahab yayi yace"Wai Ade lafiya yanaga duk kabi ka ramene ga wani fara'a daka shigo dashi Kamar Wanda aka baiwa auren mubeena"kyelkyelewa da wata bazawaran dariya Ade yayi shima Lahab dariya yayi a hankali Yana kallon abokin nasa Addayiya ce ta turo kofar dakin fuska a hade tace"Kai Kunga banson hauka ya zaku zo ku zauna min a daki kunamin ihu bare ma Kai Mara lafiya surkuwar haleema tazo dubaka tana falon su zata shigo sannan kazo kana dariya a sama sama Kamar zararu"shuru sukayi gabaki dayan su basu kulata ba itama juyawa tayi ta bar dakin.

"Bazaka gayamin meke maka Dadi Yana saka rama be Wai"?cikin murmushi Adewale yace"kasan yau Nina Kai mubeena makaranta a mota"waro Ido Lahab yace mota kwal uba yaushe ka samu mota Ni ban samu ba ai wallahi da sakel"kaga kwantar da hankalin ka Lahab ba nawa bane na David ne"?

"Toh ya akai ta yarda ka dauketa wannan sarkin taurin Kai"murmushin dake fuskar sa har lokacin na Nan yace"Nabeel ya kirani Nan take ya sanar dashi yanda Suka Kaya,sosai Lahab yaji dadi ganin abokin nasa na cikin farin ciki yace"aiko aiki ya sameka Ade sai kayita fama aiki ya sameka soyayya ne Koh wahala"hararan sa Ade yayi ya zaro wayar ta ya nunawa Lahab yace"tabbas zata kirani kaga na samu hanyar communication da ita"gyada Kai kawai Lahab yayi Yana murmushi don shi soyayyar su dariya yake basa.

muryan Addayiya sukaji tana cewa"Bismillah ki shigo Yana ciki shigo farida Sannu da zuwa,sai Kuma aka turo kofar Addayiya na gaba farida dake sanye da hijab har kasa babba sai socks dake kafarta kanwarta na gefe sanye da gyale,Suka shigo Zama farida tayi a kasan carpet in dakin duk yanda Addayiya taso ta zauna a kujera ki tayi shikam Lahab tunda ta shigo ya mugun hada rai Yana Mata wani kallo na bacin rai gata dai a fuska mutuniyar kirki har kwatance iyaye keyi da ita akan yaransu suyi koyi da halinta a unguwan amma basusan Kura bace da fatar akuya,ita Karan kanta jikinta yayi sanyi don kaf gidan Banda Anwar babu Wanda yake supporting in soyayyar su sosai irin Lahab so dubu in Suka hadu ya ringa tsokanar ta kenan San bai rike girman sa na surkinta bappan mijin da zata aura ba,amma abin mamaki yau Koh kallon arziki bata samuba amma ta alakanta abin da ciwon dake damunsa ne kawai amma ganin yanda ya juya ya Kama hira da Ade sai taji ranta ya baci sallama Tama Addayiya Suka tafi.

Bayan fitar su juyawa Ade yayi ya kalli Lahab yace"Wai Lahab wannan ba Amiran islamiyyar ku bace ustaziyar unguwan Nan Kuma matar da Anwar zai aura Kodai ba ita bace"ita ce Ade Meka gani"?da mamaki yace gani nayi kana Mata magana kamar maijin haushin ta Kuma Naga ba hakan kuka Saba magana ba last haduwar da nasan munyi da ita ma in ban manta ba ta fito islamiyya mu Kuma mun fito ball har kake cewa dole a auren su ayi program Kai babu ruwan ka da ustazanci ta ajesa sai bayan aure"?

Kai wallahi Ade yanzun nayi mugun tsabar yarinyar munafuka ce Mai 2face ce"Kamar Yaya ban gane ba ya Kara tambayar sa nan Lahab ya zayyana Masa duk abubuwan da suka faru tare da kudurinsa akan wargaxa auren sai Kuma warning da Mami ta buga Masa akan zancen"rike Baki Ade yayi yace"gaskiya Lahab ba haka zakayi ba kawai ka rabu dashi ya aureta taima watakil auren ya zamo tsular shiriyarta sai kaga ta shiryu"wani kallo Lahab yayi Masa yace"kana nufin auren ta da Anwar zai nutsar da ita macen da aka sa date na auren ta har zata iyya fita hotel tsakar dare tana can akan me Koh kaffara bazanyi ba Anwar ba mazinaci bane akan me Zan bude Ido Ina kallo ya aure Mai dattin Mara tazo ta Haifa Masa yara Yan iska karfa ka manta duk abinda mace ta aikata zata gani a kwartar tuwon ta sai Wanda Allah ya sosu suke ganin daidai amma mace batayi iskanci bama ya ta Kare bare tayi Kuma Ni abinda ke dad'a batamin Rai shine fuskar mutanen kirki da take dashi wallahi saina tona Mata asiri don ubanta"

Sosai Ade ke kallon Lahab Yana mamakin soyayar dake tsakanin su da Yan uwan sa yace"kaga nifa yanzun shawaran da Zan baka d'aya ne karka tona Mata asiri a bayyyane baka da hujja in dai baka iyya Kama barawo ba shi saiya Kama ka Mami nada gaskiya gwara kayi shurun kawai"wallahi bazanyi shuru ba"Lahab yace,ok in bazakayi shuru ba toh kasani indai zaka Hana auren ka Hana a zahiran ce ba a nuni ba kasa Anwar ya ganta da kansa"sosai Lahab ya zagu yace toh ta Yaya kenan"Baki Ade ya bude zaiyi magana saiga Kira ya shigo wayar mubeena dake aljuhun sa zaro wayar yayi Yana kallon screen in waya.

Mubeena mikewa tayi tayi summit na paper ta da wuri tana Allah Allah Kar Rukayya itama ta Mike tana mikawa da Sauri gudu gudu ta fita a class in rataye da jakan ta bayan hall Inda ba mutane sosai ta nufa don ta tabbatar in taje cafe Ruky zata iyya ganinta itakuma yanzun batason wani alaka ya sake shiga tsakanin su da juna tafison tayi rayuwarta Kamar da Kamar batasan Ruky a duniya ba Zama tayi akan kututturen itace dake gindin bishiyar leam dake wajen jakan ta ta bude tasa hannu zata dau wayarta wayam kake ji bataga waya ba hankalin tane ya tashi ta shiga dube dube tana zaro material nata dake cikin jakan dan dakatawa tayi tana wani nazari in dai bata manta ba Kamar lokacin da suke tawowa Yana hannunta time to time tana duba lokaci sai Kuma kusan accident in da sukayi daga lokacin Kuma ta kasa tuna yaya wayar ma yayi "Allah dai ya Soni Kar a wani wajen na yatsar da wayar" da Sauri ta Mike ta Kama hanyar hall tana shiga lokacin an gama summit gabaki d'aya ajin sai dalibai daidaiku dake tsattsaye wasu a zaune Suna jiran next paper ganin ba Ruky a cikin hall in ya sata karasowa wajen da ta zauna tana dudduba wajen Koh Ta bar wayanta a wajen amma babu,lawiza dake zaune ita da wani Suna duba jotter ta matso wajen su tayi da sallama tare da rokon lawizan ta Ara Mata wayarta zata Kira wayarta,Mika Mata lawizan tayi da Sauri ta amsa ta loda number ta a ciki tare da karawa a kunne,daidai lokacin Ruky da tunda mubeena ta fita itama ta kammala da Sauri tabar ajin sosai tayi ta yawon Neman mubeena Amma Bata ganta ba tana ta tambayar mutane,sai Kuma ta hango mubeenar ta shiga Hall na exam da Sauri tamike daaga Inda suke tsaye ta nufi hall in.....................

🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*

Page 77&78

Kauda idanunta tayi daga Kan na Ruky Jin an d'aga wayar tayi sallama, Adewale dake Kare da wayar a kunne amsawa yayi cikin Jin dadi Jin muryarsa yasa ta tamke fuska ta sabe jakanta a kafa hade dama lawiza nuni da hannu tana dawowa,tare ta Ruky dake tsaye tayi tace"haba mubeena yau throughout nayi ta neman ki a school Nan ban ganki ba sannan yanzun kin gannin Zaki wuce"?fuska mubeena ta sake Kamar ba kome tace"waya zanyi Kuma Ina bukatar sirri tana karasa maganar ta rabata ta wuce Ruky Baki ta sake tana binta da Ido hartabar hall in mamaki na cikata Koh Ahmad a gabanta mubeena ke waya dashi tunda suke mubeena bata tana zakud'awa da sunan amsa call ba koma waye ya kirata sai yau Zama tayi a kusa dasu lawiza tana sauke a jiyar zuciya kallon ta lawiza tayi sai Kuma ta tabe Baki batace kome ba.
Chapter 61 · 0% Book details