← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 122

Sashe 15

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana shiga kitchen in ta tsaya tana kallon peace dake shirya Abinci a kuloli, tana gama zubawa ta bawa Nnenna umurni akan taje ta jera a daining don duk abinda ke wakana a falon tana ji, ba musu ta cicibe kulolin takai daining ta jerasu, tare da su plante suna gamawa kimtsawa, familin suka zo suka zazzauna akan daining, saving nasu peace take Amma Ibraham yace lallai sai dai Nnenna tazo ta zuba masa.

Ba musu Momy tace tazo ta zuba masa matsawa tayi fuska ba walwala sam, tazo ta d'auki plate kaman yanda taga peace tayi haka itama take, zuba masa tuwon tayi da miyar naman Alade, sai kauda fuska take saboda bata koh son ganin naman.

Shikam kafa yasa ta karkashin table in ya taba mata tsintsiyar kafa, sake plate in tayi jikinta na wani irin bari kamar mazari, da sauri ta juya ta dafa jikin bangon Area in kanta na wani irin sarawa kamar zai rabe biyu.

Da sauri suka mimmike suna tambayar ta menene..............

✨Ruqeenjalal✨

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🤹🏿‍♂️ *ALKAWARIN MASOYA* 🤹🏻‍♀️
~ Na ~

🍃 *Rukayya Ibrahim*🍃

✨Tsokaci ALKAWARIN MASOYA na kudi ne gamai bukata naira 300 ne kacal ki tuntube ni ta layin nan whatsApp only 07044407979👌

Free page🤧

*EXQUISITE WRITER'S FARUM*

page2⃣1⃣&2⃣2⃣
Kasa Amsa musu tayi saboda tsananin ciwo da kanta keyi ga wani irin fushi dake taso mata tana kokarin dannewa.

Tsawa mom ta daka mata,kee ba magana ake miki ba kin wa mutane banza?

Shuru kawai Nnenna tayi jin jirin ya lafa mata yasa ta nufi barin Area in cikin damuwa, sukam da ido suka bita suna mamakin halinta na ko in kula ga had'a fuska da mannin hauka.

Tura kofar d'akin ta tayi ta shiga da sauri ta zauna a bakin gado, ranta a jagule ta kwanta tare da lumshe idanunta, anya zaman nan zai mata dadi kuwa?wai itakam bazata samu farin ciki bane a rayuwar ta, shikenan bata da sukuni, wai menene a jikinta da yake rud'ar maza harsu kasa hakuri sai sun nuna maitar su a fili tayi tunanin koh in ta dawo Birni zata ga change ashe abun ba haka bane.

A haka tana kwance har bacci ya d'auke ta ba tare dataci na dare ba daga ita har abin kiwon nata.

********************
Lahab kam gantali suka tafi abinsu bashi ya dawo gida ba sai yamma kamar kullum yau ma xama yayi a masallaci, agun yayi Alwala ya shiga harsu Abbu ma suka shigo suka same sa daga yanayin kallon da abbu ya masa sai da yaji cikin sa yayi kuka.

Suna idar da sallah yabi bayan su har cikin gida tsaya yayi a falo yana bin falon da kallo, mamu ne zaune ita da umaimah inka gansu a lokacin kad'ai ya isa ya sanar da kai akwai matsala, tsawa abbu ya buga masa, Lahab nemi waje ka zauna.

Ba musu ya nemi gefen kujera ya zauna kamar na Allah ya hade kafa waje d'aya, zama Abbu yayi haka ma su Uxaifa, saiga Addayiya ta fitoh sanye da hijab, yauwa Umaru jarabebben ya samu isowa kenan, ai tunda naji muryarka nace d'an kusan wa ya dawo, ta karasa maganar da zama a 1 sita.

Hararan ta Lahab yayi da suka had'a ido Amma batace kome ba, sai maida hankalin ta da tayi a wajen abbu dake magana, wallahi wallahi lahab ka shiga taitayinka dani a gidan nan, kar kaga duk abinda kakeyi an zuba maka ido babu mai hukunta ka sai muxammil, ka d'auka koh tsoron ka akeji.

kallon Abba yayi cikin hade fuska yace"toh ni me nayi koma?koh nace me aka sake kullamin"?

Tsawa abbu ya kara daka masa sai da ya razana wallahi irin unexpected in nan, wallahi summa tallahi lahab ka kiyaye kanka da bacin raina zaka ga ba daidai ba randa ka kaini bango?banda rashin hankali da rashin tunani ace saurayin diyarka yazo, ta masa girki sai kazo ka sabe ka kara gaba dashi?

Muna barin ka da yunwa ne a gidan nan koh me? da bazaka tambayi abinci ba saika d'auki abinda ba naka ba ina rabaka da d'aukar kayan mu a gidan nan.

Kayi hakuri Abbu, Rahab yace hawaye na cika a idanunsa ji yake kamar shi yayi laifin, sabanin lahab dako a jikinsa TV kawai ya kurawa ido kamar pusta.

Amma dai kai Lahabu anyi shegen gari ana maka fad'a shine zaka basa keya kana kallon d'an iskan TV?

Juyawa yayi yana kallon Addayiya cikin masifa da haushi yace, "wallahi addayiya ki fita harkana nace miki koh? koh dole ne sai kin shiga abinda babu ruwan ki"?

Kai na shiga!! nace na shiga!! d'an batalon uba, yanda kake baki haka zuciyar ka take.

Kwarai kuwa addayiya ni wallahi inso samu ne ma kawai a mayar dashi wajen dadyn su Taimiya.

Kama baki Addayiya tayi tana kallon mamu dake maganar nan, Eh lallai halima sai yanzun nasan zaman da kike da yaran nan, sai kuma ta fashe da kuka tana rufe fuska da gefen hijabi, toh wallahi bari kiji na sanar dake da kowa ma na gidan nan wallahi koh bayan raina ban yafe maka ba umar in yaran nan tagwaye suka bar gidan nan mundin ba aure koh karatu koh son ransu bane yasa su fita sai masifar Matan ka koh yaranka.
Wallahi koh bayan Ran mijina bazan wufantar da amanar da ya bamu nida umar ba, ai yasan da Jafar in yace umar ya kular masa da yaransa,ta nuna mamu ke asuwa da zakice yabar gidan uban sa? ai kece ma zaice ki kara gaba, in kin manta bara na tuna miki lokacin da umaru ya tashi auren ki yar haka kike kamar kishiyar mayya.

Amma dubeki yanzun kin zama buhu kici ki koshi kiyi kashi kice zaki raba zumunci, wallahi baki isa ba kai lahab tashi ka tafi abunka ka d'au abincin dan uwar ki umaimah bazaiici kayan yayan sa ba, sai ya zama zaraba toh yaci din Lahab tashi ka tafi.

Mikewa Lahab yayi cikin kuri ya nufi kofa yayin da mamu taji kamar ta tona kasa ta shiga musamman ma dariyar da ummu ta sake, irin dariyar nan na jin dadi.

Abbu kam sai ido, ya rasa meke damun Mamar tasa itace tayita uzzura Abinda lahab yayi, sannan yanzun tazo ta juya zance kuma, duk da abinda mamu tace bai dace ba sam shima baiji dadin abinba d'an uwa ba wasa bane.

Lahab na shiga d'aki kwanciyar sa yayi koh abinci baici ba.

Washe gari jafar da babban d'ansa, Taimiya suka diro tun safiya a d'akin su Anwar Taimiya ya sauka dayake duk sa'o'ine, sai abokan Abbu, tun safe su mamu ke shirye shiryen tarban baki.

Sai da yamma iyayen sadeeq suka zo anyi kome a mutunce sun kawo goro da Sadaki tare da yanka sarti duka, saboda nisan dake tsakanin sun, gari ba daya ba. sonyi kome lokaci d'aya, ya rage saura kayan aure da rana, daman sadeeq da umaimah sun jima tare jira yake ta kammala karatu gashi yanzun har ta fara zana final exam nata.

A Ranan ma Lahab koh wuni baiyi a gidan ba sanin da yayi mamin sa na zuwa kuma yasan tabbas tazo ta samesa zuwa school ya kamasa kenan.

*****************
Nnenna dake bacci hankali kwance ji tayi kamar ana son tabata kamar da mutum a kanta don ita duk nauyin bacci muddin mutum ya tsaya akan ta tana farkawa, bude idanunta tayi da sauri yayin da ta damko hannun mutum dake kokarin kaiwa jikinta.

Ware ido tayi da kyau ganin Abraham ne duke akan ta sanye yake da gajeren wando da single, wantsalowa tayi gefe tana kare jikinta, hade da masa mugun kallo.

Shikam sai kara matsowa kusa da ita yake, baby ya naga kina kwana da wuta gashi koh sleeping dress babu?

Mikewa tayi tsaye tare da nuna masa kofa cikin bacin rai tace," get out Abraham wallahi ka fita koh na illataka"

Da mamaki yace nida gidan mu zakice zaki illata ni kina mace ina namiji har akwai wata illar data wuce nina miki?

"Tabbas akwai don ni illar da zan maka na har abada ne babu sauran gani bare wata rana ka manta, fitar miki a wajen kwana naji gidan kune amma d'akin nan ance nashiga don haka fita kaban waje"tana maganar cikin fad'a fad'a tsawa tsawa.

Zaro ido yayi da mamaki don shikam bai d'auka haka yarinyar take ba gashi dare ne kar tayi ajisu da sauri yayi mata magana kasa kasa, ke menene haka?

"Fita"!!!!!!!!!!

Da sauri ya juya ya fita, itama Nnenna mikewa tayi ta rufe kofar duk da bata iyya ba amma haka ta tura da karambani ta murd'a ki tare da zarewa ta aje a gaban katifar ta koma, zata kwanta sai kuma ta kalli makwancin kulenta, zaune yake yana kallonta alamu madai ya jima da farkawa.

Wutar d'akin ta kashe ta kwanta tare da rungumar kulenta.

Washe gari da misalin karfe 3 na asuba taji ana buga mata kofa da karfi ana kiran sunan ta, mikewa tayi ido duk bacci, haka ta mike zaune da lalube ta kunna hasken d'akin, key ta d'auka tana kokarin bude kofar aka bankosa ta waje, sai da ya buge mata goshi kara ta sake tana dafe wajen, kafun ma ta dawo hayyacinta taji an sake mata dundu mai zafi a baya hade da zagi.

Ke yar kauye ai bacci bai kamaki ba yar wahala muna bacci kina bacci fita zakiyi ki share gidan nan tsaf, har compound kiyi mooping kiyi wanke wanke in peace ta fitoh breakfast zata had'a miki d'aurayan da zakiyi.

Gyada kai kawai tayi amma batace kome ba sai bin bayan jennifer tayi har tsakar falon tsintsiya ta watso mata da sandan mooping da sauran kayan gyara, ta koma dakin ta ta kwanta, Allah ya kyauta don ta azabtar da baiwar Allah kawai ta tashi.

Tsintsiyar Nnenna ta d'auka ta share falon har wajen compound unguwan tsit babu motsen kowa sai kukan karnuka ga sanyin asuba dake tashi haka Nnenna ta share gidan tas da falo, amma ta rasa ya xatayi mooping karshe ma jika musu falo tayi da ruwa tirim.
Chapter 15 · 0% Book details