Sashe 6
Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sumui sumui suka juya suka kama hanyan layinsu gabaki d'ayansu basu sake magana ba koh gulman baban ade, don su haka suke gabaki d'ayan su suna girmama iyayen abokan su, sam don d'aya daga cikin su don iyayen su sun zage dayan su baya damun su duk da zagin da baban adewale ke musu yayi yawa harya wuce iyyaka.
Gidan su nabeel suka je aje kayan sa shima lahab yayi a wajen nabeel kafun ya nufi gida.
Tafiya yake hankalinsa kwance harya iso kofar gidan su, hannu yasa xai tura kofar get, sai kuma yaja da baya ganin ana kokarin bude kofar ta ciki, Abbu ne ya fitoh cikin jallabiya hannunsa rike da calbi sai yaransa dake binsa a baya harda Rahab dagani dai masallaci zasu don an fara kiran sallan mangariba, sunkuyar da kai yayi ya basu hanya.
Dubesa kamar mutumin kirki, shige mu tafi masalaci, Abbu yace yana masa pointing da yatsar sa, ba musu lahab ya juya yabi bayan su.
Bayan an idar da sallah haka Abbu ya sakasu a gaba suka kamo hanyar gida don masallacin baida nisa da gidan su, asalima ginin gidan su manne yake da masallacin, tun a hanya yaga yanda Rahab yayi banza dashi sai wani shamasa kamshi yake amma koh a jikinsa.
Don shi harya ma manta da zancen 11k na safiya wallahi sai yanzun dayaga yanda rahab ke had'e da fuska ya tuna amma dai baice kome ba har suka shiga gida.
Bude kofar lahab yayi don wannan karo shine a gaba, mamu da ummu ne zaune a falo dukan su suna sanye da hijab dagani dai sun idar da sallan mangari bane, wuce su lahab yayi, ya nufi kofar daya fitoh da safe.
Tura kofar yayi ya shiga wow babban falone mai dauke da manyan kujeru na gani na fad'a sai d'akuna sama da bakwai dake falon, nufar d'aya daga cikin kofofin dake falon yayi, tura kofar yayi ya shiga d'akin da sallama.
Dakine babba mai d'auke da kayyaya ki irin na samaru kan zamani, wardrop ne guda biyu sai manyan katifu guda biyu d'aya a kusurwar daki, dayan ma haka an gyara katifun sun matukar kayatu da zanin gado, sai mirrow dake d'auke da kayan kamshi irin su turare da mayuka, labuleye sun kewaye rabin d'akin, shiga yayi ya tura kofar ya rufe.
Toilet direct ya nufa wanka yayi babu jimawa sai gasa ya fitoh, wardrop in ya bude wando da riga na bacci ya d'auka ya saka fisa turare yayi ya koma d'aya daga cikin katifar dake kwance akasan tiles na d'akin ya kwanta, lumshe idanunsa yayi kawai yayi shuru duk da yasan yanzun ne lokacin cin Abincin dare Amma bayaji zai iyya cin kome gaskiya.
Turo kofar d'akin Akayi da sallama, bai bude idanunsa ba ya amsa.
Tsayawa umaimah tayi tana kallonsa ganinsa da kayan bacci kuma a kwance, small uncle wai inji Abbu kazo muci abinci?
Kallonta yayi irin kallo mai kama da hararan nan"ke kuma munafuka watoh gidan mamina kike zuwa kina kai gulma koh"?
Hhh dariya ta sake da karfi tana rufe bakin ta, ashe yau gidan mami akaje shiyasa ya shareef yace min yaganka da jallabiya kum......da sauri ta kwala kara ta ruga a guje ta bar d'akin, ganin lahab ya mike harya sabi bell nasa zai nufota.
Kwafa kawai yayi cikin jin haushi ya koma ya kwanta, sai kuma ya mike da sauri jakan makarantan Rahab ya bude takardunsa ya fitar English And maths ya d'auko yana dudubawa.
Bude kofar d'akin akayi, Amma bai dago ya dubi waye ya shigo in ba, ji kawai yayi an fizge littafin Hannun sa, da sauri ya d'ago yana dubansa, Amma baice kome ba.
Wallahi karka sake taba mini littafi lahab?daga yau sai yau tunda baka da mutunci bakasan idon sani ba harni zaka fizgewa kudi? don kaje ka kashe a banza da abokan banzan ka?in karatu kake so kaje makaranta ni ba bawanka bane.
"Don Allah ya isheka haka d'an iyayi kawai zakazo kana tsayamin akai zaka mini rashin mutunci, lahab sosai ya rufe D'an uwansa da masifa, shuru kawai Rahab yayi ya koma kan katifarsa da littata fansa, Aje littatafan yayi ya d'au system yana dannawa.
Tsaki lahab ya sake ya koma ya kwanta cikin bacin rai don shi ya tsani abin haushi a rayuwar sa, shi gabaki d'aya ma ya manta da zancen fad'arsu na safiya, tuni ya watsar Abinsa, kwanciya shima yayi yana kallon d'an uwansa dake rike da system haushi yakeji sosai don sam Kin saya masa akayi, aka saima d'an uwansa kome aka tashi Rahab ake bawa koh a basa abu, Amma shi ba'a masa.
*************
Nnenna zaune take akan kujera, kwalli d'ayan dake falonsu,littatata fanta take dubawa Ta rasa me zatayi ga yunwa ga kewa, ita kad'anta take rayuwa a d'akinsu Babu uwa ba kawaye Babu kowa sai kulenta dake gefe a zaune,ji kawai tayi an banko kofar falon.
Da sauri ta mike papane ya shigo cikin mayye Yana tangadi hannunsa rike da laida baki karami,cikin magana irin na Yan kwaya yake k'wala Mata Kira,Nnenna!!
"Yes papa"tace tana toshe hanci Jin irin gasar da mahaifin nata keyi ga wari,Mika Mata laidan yayi da sauri ta karba don Wallahi yunwa takeji Tana Kai hannu ta Amshi laidan kawai ya kwararo Mata Amai a jiki da sauri ta matsa gefe tana fashewa da kuka ganin Alelen Akwai dake laidan ma ya Fadi a kasa Amai ya tabasa ga jikinta duk Amai,da kuka ta fita waje da gudu.
Papa dabaya cikin Hayyacin sa kiranta kawai yake Nnenna!!Nnenna!!Ina zaki??
Kasa basa Amsa tayi da sauri ta kwabe rigan dake jikinta. Tabar vest don ita ba brz bane da ita,ruwa ta iba da sauri tayi bandaki.
Tana wanka tana kuka a hakan harta kammala, ita abinda yafi Bata Takaici Abinda zataci Daya baci da Amai yafi kome Mata ciwo,falon ta shiga tana kallon Papa dake kwance Kamar macece Ga Amai a zube a gefe.
Tsumma ta d'auko da ruwa ta share simintin don d'akin ba kome a kasa sai simintin kwashe Aman tayi ta rufe musu kofar falo,kulenta dake gefe a rakube ta d'aukosa hawaye na cika Mata ido, yau hakan zasu kwana da yunwa kenan.
Kwanciya tayi tare da zare glass nata ta aje a gefe,kulen ta d'auka ta kwantar a gefenta,A sannu sannu har bacci ya d'auke ta.
Misalin karfe 1:30am na dare,dare ya tsaga, A hankali kulen Nnenna(Kiki)ya mike daga kwance, sauka yayi akan taburmar ya girgiza jikinsa da karfe a take ya sauya Kama daga fari zuwa baki kirim, kwayar idanunsa ya sauya shima zuwa jajazur,da hanzari yayi hanyar kofar d'akin fita yayi Zuwa falo, kallon Papa yayi sai Kuma y..............
✨Ruqeenjalal✨
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🤹🏿♂️ *ALKAWARIN MASOYA* 🤹🏻♀️
~ Na ~
🍃 *Rukayya Ibrahim*🍃
Free page🤧
*EXQUISITE WRITER'S FARUM*
page 9⃣&🔟
Sai kuma ya ruga yayi kofar falon ganin papa na motsi kamar xai farka, yana isa kofar kamar walkiya a take ya bace batt.
Nnenna dake bacci jin wani irin sarawa da kanta yayi wanda yasata farkawa a gegece kama kan tayi gam tana Kiran jesus, ji take kamar ana tsikara mata kwakwalwa da Allura, gashi d'akin duhu don koh touch basu dashi mai kyau sai fitila shima ya mutu.
Jin abin ya saketa kad'an yasa ta mikewa a hankali hannu tasa a duhun tana lalubar glass nata har Allah yasa ta gane, d'auka tayi tasa a idanunta Amma abanza don kamar yanda bata kallon kome da bata saka ba haka ma yanxun.
Cire glass in kawai tayi ta lallaba ta mike tsaye da sauri ta dafe kanta jin juya mata da kan keyi, ga wani irin jiri dake dibarta, da sauri ta dafe jikin falangen d'akin nata, da babu shakka zatasha kasa.
Kuka ta fara a hankali ta rarrafe zuwa kan katifar ta, kwanciya tayi sai kuma ta mika hannunta zata taba kulenta, amma bata jisa ba kiransa tayi cikin muryarta mai dadin sauraro cikin rauni"kiki!!kiki!!"
Ke Nnenna bazaki mini shuru ba saikin cikamin kunne aikin banza, taji muryar papa daga falo cikin magagin bacci.
Shuru tayi tana tunanin taima kulen ya chanja wajen kwanciya ne.
Haka tayita fama da motsen kai har 3 na dare kafun ta samu bacci ya d'auke ta.
****************
Asuban farko Lahab dake kwance a katifarsa lulube da blanket ga sanyin AC dake dukansa, ware idanunsa yayi a hankali ya yaye blanket inda ke kansa, bakinsa d'auke da Addu'an tashi daga bacci ya mike zaune.
Hannu yasa a drower dake gefen katifar ya kunna hasken wayansa,zuro kafarsa yayi a kasan cafet inda ke shimfid'e a kasan tiles na d'akin, mikewa yayi tsaye a hankali hade da mika, toilet ya nufa, ya bude ya shiga kunna hasken ban d'akin yayi,brush yayi ya hada ruwan dumi ya watsa a jikinsa, Ya d'auro Alwala ya fita a bandakin.
Kan katifar da d'an uwansa ke kwance ya matsa sai kuma ya koma toilet in da sauri, ruwa ya tara a buta yana zuwa yaja kafar Rahab kasan tiles ya dundula masa ruwan sanyin.
Ihu Rahab ya tsake hade da salati ya mike tsaye ganin Lahab ne, ya masa wannan rashin mutunci daman ya saba masa.
Tsaki kawai yayi ya juya ya wuce toilet don shi sam bai iyya fad'a irin lahab ba sai zuciya.
Shimfid'a sallaya lahab yayi ya sauya kaya zuwa wando da riga, hawa sallayan yayi ya tada sallan nafila,Rahab na fitowa a daidai lokacin yajin An fara kokarin shiga masallaci hakan yasa Lahab sallamewa.
Masallaci suka wuce dukansu mazan gidan, basu dawo ba sai 6:30 Abbu kam komawa bacci yayi haka yaran giyan kaf daga matan har maxa inka cire tagwaye sai ma'aikata ke zarya, Rahab zaune yake yana bitan haddansa, yayinda lahab ya sanya kayan ball wandone dogo na roba, sai riga da boot ya sanya sai towel ya rataya a wuyansa fita yayi a d'akin.
Firij na falo ya bude ruwa gora d'aya ya d'auka ya nufi kofa da jogging, gudu yake a hankali harya fita a gidan su a haka ya gangara layinsu har kofar gidansu adewale.
Aiko yana tsaye sanye da wandon ball guntu da riga sai takalmi alamu shima jiransa yake hannu ya bawa lahab suka kashe, tare da tambayar ya suka waye garin yau, daga nan gidansu Nabeel suka nufa da sallama suka shiga gidan.