← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 122

Sashe 94

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adewale na dawowa yacewa Nnenna ta had'a kayanta kala biyar wani bag ya bata madaidaici don shi bazai iya Zama dagashi sai ita a gidan ba in Kuma yaje dakunan abokan sa ita kadai a gidan Bai Dace ba shiyasa zaibi Lahab suje suga wasan da zasu bugan tunda shima student na school nasu ne, amma bai gaya Masa ba,don daman bazasu koma najeria ba sai karshen shekara Kuma yanzun watan su biyar a London.

Washe gari Suka d'auki hanya,Lahab baisan dawan garin ba kawai yana fita a fili Kamar ance ya d'aga idanunsa ya hangi Ade zaune da Nnenna sanye suke da rigan ball na team nasu, waro Ido yayi sai Kuma yayi saurin fitowa,wajen su ya nufa Yana mamakin zuwan su hannun Ade ya rike har Suka fita a wajen kafun ya Soma masifa akan me zai dauko Masa Mata ya jawota cikin arna haka"in baka da hankali Ni Ina dashi Kuma insu arna ne nima Arne ne Bai Kamata ka barta dani a gida d'aya ba harna tsawon kwanaki"ganin ran Ade ya baci yasa Lahab sauka ya basa hakuri sanann suka cigaba da Wasan.

Ana tashi Ade hotel Inda ya Kama yaje ya barwa Lahab Nnenna abinka da kasar turawa babu gulma babu sa Ido dakinsa Lahab ya wuce da ita har lokacin bai yarda sun had'a Ido ba tana Zama ya kawo Mata abinci,kafun ya Shiga yayi wanka ya sauya Kaya cikin t-shirt Mai kyau da wando dogo roba sai p-cap ya daura akan gashin kansa ya Yama wata arniyar aski, haraman fita yayi da sauri ta Mike ba tare da tayi magana ba kallonta yayi suka had'a ido,yayi saurin kauda nasa Yana magana cikin eiiieiiina yace"ya dai"?

"Zan bika"d'an zaro Ido yayi yace"muje Ina"Inda zaka"shuru yayi sai Kuma yace toh shirya muje mikewa tayi tayi wanka fita yayi a dakin ya zauna a kujera a kofar dakin Yana jiranta,wando tasa pencil Baki sai ta dau riga ta sanya ta kawo jacket ta d'aura akai gashinta ta daure ta sanya socks da boot nata,ta daura agogon hannnu ta daura, fitowa tayi a dakin wannan karon ma again Suka Kara had'a Ido dashi,kallonta yayi wannan Karo sosai sai itace ta kauda tata fuskar mikewa yayi ya koma cikin dakin sai gashi da veil medium baki matsowa yayi kusa da ita har Suna had'a numfashi da yake tana da tsaho tsakanin su babu nisa sosai amma dai yadan fita sosai,Yana kakkauda fuska yafa Mata yayi akai yayi rounded nasa a fuskarta ya gyara Mata tayi kyau kafun ya juya ya Soma tafiya binsa ta Soma a hankali a baya.

Motar wani abokin aikin su Lahab ya karba Suka wuce hotel insu Ade, daukar da sukayi daga nan Suka fita cikin gari sosai Suka ringa yawo a hankali-hankali Lahab da Nnenna suka dan sake jiki da juna har waya Lahab ya baiwa Ade yayita d'aukar su hoto da vedio duk Inda sukaje,sunje har cikin kankara, Suna ta hotona su kayi ciya ciye gashi Lahab ya Fara Zama popular yanzun suk Inda ya Shiga sai kaga ana Kiran sunan sa wasu su basa memo Koh wani Abu ya musu sign,Basu Suka dawo ba sai dare.

Daman sun riga sunyi dinner a waje Suna isowa wanka sukayi dukansu Suka sanya kayan bacci da yake daki d'aya ne babu yanda ya iya haka ya hau gadon ya kwanta itama kwanciyar tayi Suka bar space Mai yawa a tsakanin su a hankali bacci ya dauke Lahab,da misalin karfe 1 Lahab ya farka tare da dan juyawa zai gyara kwanciyar sa sai Kuma ya dan bude idanunsa da kyau ganin wajen Kamar ba mutum hannu yasa ya taba wajen kwanciyar ta Nan ma babu Nnenna,mikewa yayi zaune ya kunna hasken dakin.

Zaune take a kasan tiles ta tasa laidan da suka ci abinci Suka rage tun kafun su fita, ta lasheshi tass harda drinks in kana ta zauna tayi tagumi gabaki d'aya daga ka ganta kaga Wance take cikin damuwa hannu yaga tasa ta share hawaye da Suka saukomata a kumatun mikewa yayi a hankali ya sauka a gadon har lokacin bata San ya farka ba a hankali ya Soma taka kafafunsa a tiles in Yana nufar Inda take da Sauri yaga ta juya Suna had'a Ido ta Mike tsaye cikin kunya tana tattara kwalaye da laidodin abincin zata bar wajen,hannu yasa ya kamo nata Yana kallon ta sosai kana yace.........................

*Banyi Alkawarin na dare ba Amma Inna samu lokaci zanyi*

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*

Wai menene haka don Allah meyake damunki"?girgiza Kai tayi tana kokarin kaucewa zata aje laidodin sake Mata hannu yayi ya kwace laidan yaja hannunta ya Kamota Zama yayi da ita a bakin gadon shima ya zauna kana yace"Wai meke faruwa ne na ganki cikin damuwa Kuma kincemin babu kome"?matsa Mata yayi lalle saita fada Masa meke damunta kuka ta fashe dashi sosai cikin Sauri ya rungumeta gam a jikinsa ya koma baya-baya ya kwanta da ita a jikinsa,Yan@ kwance a dollof ita tana kwance a kansa,hannu yasa ya kashe wutan.

Labiba"ya Kira sunan ta a hankali kin amsawa tayi har lokacin hawaye bai tsaya a fuskarta ba,a hankali ya manna bakinsa a kumatunta hawayen Nata yake lashewa,lumshe Ido tayi tana d'an sake jikinta a nasa sosai ya lashe hawayen tas Kuma hawayen ya daina zuba,dan Jan lips nasa yayi a fuskarta har zuba gefen lip's nata sannan ya tsaya Yana bin fuskar da kallo,idanunta a lumshe suke jira kawai take taji saukan lips nata a nasa amma taji ya tsaya cak,dan bude idanunta tayi sai Kuma da Sauri ta kauda nata saboda tsayuwa da yayi kawai Yana kallon ta,"kin koshi da abincin Koh a kawo Miki wani"?girgiza Kai kawai tayi batace kome ba,sakin murmushi yayi a hankali ya zamar da ita a jikinsa ya kwantar tare da gyara Mata rufuwa shima ya rufu tare da kamo hannunta ya rike Yana bin fuskarta da kallo kawai.

A hankali ta matso kusa dashi tare da manna jikinta a nasa,waro Ido yayi da mamaki sai Kuma yasa hannu ya dagata jabal ya daura a kansa,lip's nata ya Kama amma bai tsotsa ba kawai mannawa yayi da nata,dan Jimm tayi sai Kuma ta Kama lips nasa na kasa cikin sanyi ta tsotsa,Kama nata yayi Suka hau bawa juna hot kissing sosai salon wasan ya chanja duk wani kunya kunya gabaki dayansu ajesa sukayi a gefe sosai Lahab ke sarrafa matarsa yayinda ita Kuma ke basa goyon Baya dari bisa dari,lokacin da kome ya kankama Lahab yasha mamaki matuka Kuma ya rude don dadin da yaji na yau ya d'ara na Ranan dadin da yaji sosai.

Lokacin da nutsuwar sa ta samu kokarin tashi yake a kanta da Sauri tasa hannu ta Kama waist nasa gam,Wanda hakan ya fahimtar dashi cewa itama tana bukatar nutsuwarta duk da akwai mutuwar jiki da gajiya a jikinsa hakan baisa sa kasa tallafawa matarsa ba sosai ya tallafeta har ta samu natsuwa,mikewa yayi a hankali ya d'auki towel NASA wanka yaje yayi kana ya fito mikewa tayi itama ta shiga toilet in kafun ta dawo Harya chanja zanin gadon ya kwanta,tana fitowa Zama tayi daga ita sai towel,shuru shuru yaji Bata hau Kan bed in ba kallonta yayi kana yace"lafiya bazaki kwanta ba kinsan karfe nawa yanzun"?shuru ta Masa Bata hauro Kan gadon ba,shima Bai Kara magana ba ya gyara kwanciyar sa so yake ya samu bacci kafun asuba don gobe Suna da training da sassafe,amma kasa baccin yayi ya sauka akan gadon d'aukarta yayi gabaki dayanta yazo ya kwantar akan gadon ba tare da ya damu da towel in jikinta ba ya lulluba Mata blanket.

************
tashi tayi ta zauna again Wanda hakan ya saka sa sake tashi agogo ya gani kusan 2:30 na dare tsaki kawai yayi yace"Wai don Allah wannan ai d'aukar alhakine ya Zaki kasa bacci ki hanani nima"?a fusace tace"toh ninace maka karka kwanta ne"toh Taya Zan kwanta kina zaune"a hankali tace"yunwa nakeji"wani kallo ya Mata sai Kuma ya tashi tsaye hannu yasa ya taba jikinta Jin sanyi babu zafi yasa sa komawa ya kwanta abinsa Bai Kara magana ba ya barta a zaune bacci barawo yayi awun gaba dashi.

da asuba Lahab daya farka da mamaki Nnenna ya gani d'aure da towel Kamar yanda ya kwanta ya Barta idanunta biyu da mugun mamaki yake tambayar ta Wai Bata kwanta ba?kin amsa Masa tayi yasa hannu zai tabata kawai ta turesa Saida ya koma Kan katifa ya kwanta,bata Kara magana ba shima gyada Kai yayi irin lallai innan ma, ya mike Alwala yayi yazo yayi sallah duk tana zaune,Kaya ya chanja ya fita waje da asuban amma shuru babu kowa shaguna duk a rurrufe dakin wani makwancin sa ya shiga yadau fresh milk guda biyu ya kawo Mata kin karba tayi Wai tayi fushi daker ya samu ta karba tana Sha Koh aje goran batayi ba ta Soma amai Kamar zata amayar da hanjin cikinta sosai tayi aman lokaci d'aya wani irin zazzafi ya rufeta,daukarta yayi ya Kai toilet tare da wawwanke Mata jikinta ya fito da ita, Kaya ya sanya Mata ya kwantar da ita akan gado kafun yazo ya gyara wajen da ta batan.

Wanka yayi da misalin karfe 6 zuwa lokacin wani irin bacci yayi gaba da ita so yake suje asibiti Kar ciwon yayi tsananin amma ganin tana bacci tunda bata samu na daren jiya ba sai yayi tunanin bari ya barta sai ya dawo,kayan ball yasa wando da riga sai takalmi ya fita a dakin, direct training ya wuce basu Suka bar wajen ba sai kusan 9 na safe daga wajen wajen Saida abinci ya wuce kaza yasai musu sai kayan ciye ciye na laida Incase kada ta bukace Abu lokacin da bazai samu ba shiyasa ya sama Mata irin su cake su pizza duk ya sassaya sosai ya Mata sayayya.
Chapter 94 · 0% Book details