← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 122

Sashe 10

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da mamaki kowa ke kallon Rahab kiri kiri Lahab xaiyi abu Amma haka xai goya masa baya kuma sun tabbatar lahab ne kad'ai xai iyya aikata abin nan.

Kuka mamu ta sake da karfi tana nuna Lahab, cikin masifa take cewa, wallahi kai zaka aikata tunda naga Rashida tace mini zata tafi bayan shigan ka kitchen zuciya ta ta rayamin kaine zaka sace mini kudi?

Da mamaki shareef yace mamu me kike nufi bamu gane ba?

Kwashe yanda sukayi da Gogoji mamu tayi ta sanar dasu, salati abbu ya sake ya farama mamu holo akan abinda tayi da wasa da rayuwar wasu wannan ai rashin imani ne taya d'an mata na cikin Ciwo tazo a taimaka mata Amma har tana mata barazana da rasa aikin ta, aiko kyauta yaci ta baiwa gogoji tayiwa d'anta jinya, sosai fad'a ya koma kan mamu maimakon Lahab da ya baro ta.

Sosai taji bakin ciki da kara tsanar Lahab a ranta fiye da da, especially da Abbu yace su shirya bayan isha'i suje su duba yaron gogoji su bata kudi tayi hidimar jinya.

Lahab cikin murna ya cinna mamu ya wuce d'akin su yau koh holo bai Amsa ba, wanka yayi ya ibi abincin da Rahab ya kawo masa yaci abinsa bayan isha'i sukaje asibitin, sun samu jikin yaron da sauki, Abbu ma ya bawa gogoji kudi sosai haka ma ummu da Addayiya, tare da sanar da ita babu zancen kori a tsakanin su sun zama d'aya ai tsawon shekaru ba wasa bane.

Itama bata fad'a musu Lahab ya bata kudi ba.

Suna dawowa lahab ya xauna a falon su yana kallon ball, don ya manta da wayan sa a gidan su nabeel, gabaki d'aya ya tattara hankalin sa akan kallon.

Anwar daya fito dakin sa sanye da rigan bacci da wando, hannu yasa ya d'auki remote ya chanja tasha zuwa news, da mamaki Lahab ke kallonsa ganin ya zauna yana wani abu isa-isa,mikewa yayi yana kallon Anwar ya mika masa hannu hade da cewa"bani remote"?

Innaki baka fa sai me?

"Sai kowa ma ya rasa"lahab ya basa Amsa

Au haka koh toh a rasa kace koh? karamin mara kunya d'an iskan karya wallahi tarawa nake ina jiran uncle muzammil ya dawo ya mana maganin shege.

"badai shege ba kace shegu, kuma inya dawo in sai me mala'ikane shi da zanji tsoron dawowar sa koh gidan ubansa ne"?

Kama Baki Anwar yayi, ubansa ka zaga lallai abin naka nayi ne lahab wallahi kadaiji kunya baza'aje boko ba baza'aje arabic ba ahaka dai za'a kare

"Inna kare a haka uwarka ce ta kare"

Jin Amsar da lahab ya basa yasa bacin ransa karuwa akan nada, don yaji haushin abinda lahab da rahab suka ma mahaifiyar sa, da kunyatata da sukayi a gaban kishiyar ta da surkuwar ta ga yara, gashi kowa baiga laifin saba saina mamu, hannu yasa zai tsinke lahab da mari.

Da sauri lahab ya cabe hannun Anwar hade da wurgarwa, da gudu ya b'anb'ara, sanin da yayi koh ya saya in zasu daku ma shine zaiji a jikinsa, shima Anwar da gudu yabisa.

Gudu Lahab keyi Anwar na binsa harya nufi kofar d'akin su da sauri yasa kafa ya bangaje kofar ya shiga, cikin sauri ya maida kofar zai rufe daidai lokacin shima Anwar ya kawo kai zai shiga, buga masa kofar Lahab yayi a fuska ji kake kauuu sai salatin Anwar dake tashi da karfi yana innalilahi Lahab ya cire masa hakoriiiiiii

*******************
Nnenna sai da asuba ta mike a hankali jin muryoyi na tashi a tasha, bakko mai datti ta gani a gonar d'auka tayi ta tsunduma kulenta a ciki ta fita a gonar ta nufi tashan, Abinci ta saya hade da kifi ta baiwa kulenta itakam ta kasa cin kome don mutuwar papa ya shiga jikinta bana wasa ba.

Duba takardan da papa ya bata tayi wanda jiya ta cusa a Aljuhun riganta, budewa tayi tana dubawa gani tayi ya rubuta mata Gombe state da kuma unguwa da address na gida hade da sunan mutumin Coulis Appa, nunawa masu motar tayi akan tana neman motar gombe?

Bata samu ba sai dai sunce ta shiga a sauke ta a wani state, ta hau wani mota ba musu ta shiga ganin wannan ya amince zai kaita don wasu mutanen koh magana ta musu sai dai suki kulata haka mai abinci ta koreta wai tana warin petur karta jaza mata masifa, wasu yarane ta roka suka sayo mata, haka motar ma tana shiga mutane suka ringa toshe hanci wasu na tufar da yawo.

Ganin haka yasa driver ce mata ta sauka, kuka ta sake tana basa hakuri daker ta samu ya yarda Amma sai dai ta zauna akan injin mota daman bus ne.

Ba musu haka ta zauna tana maijin azaba bad'an kad'an ba,kafun mita ya cika, karshe dai da taga za'a tada motar Kawai tace zata koma boot cikin kaya ta zauna agun bazata iyya zaman kan inji ba, da murna mutanen motan sukace ta shiga boot in, a haka akayi ta tafi sai kusan 4 aka sauke su a wani gari wanda itama batasan ina bane agun inyamuri mai motar ya had'ata da wani akan zata gombe.

Tana bakke da bakkonta ta shiga motar gombe akaja suka kama hanya gabaki d'aya
tayi ligis kafufunta sun kukkumbura don ita bata taba tafiya irin na yau ba, shiyasa sai zare ido take, tana kallon mutane, suma suna kallonta sauran abincin data saima kulenta yaci ya rage shitasamu ta afa a bakinta jin yunwa na shirin kasheta.

Har dare suna kan hanya basu isa ba, ga dare ya fara rabuwa wasu har bacci suke Amma banda Nnenna dake zaune rungume da bakkon ta, suna gaf da shiga garin gombe, kamar daga sama sukaji karan bindiga tauuutauuutauuu sai sukaji tayan motarsu ya fashe, musulmai dake cikin motar ne suka fara Ambaton Allah, yayin da Christoti na ihu suna kiran jesus, Alamudai sun shiga riskun yan Fashiiiiiii

✨Ruqeenjalal✨

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🤹🏿‍♂️ *ALKAWARIN MASOYA* 🤹🏻‍♀️
~ Na ~

🍃 *Rukayya Ibrahim*🍃

Free page🤧

*EXQUISITE WRITER'S FARUM*

page 1⃣5⃣&1⃣6⃣
Nnenna kam jikin ta rawa ya fara ganin yanda hankalin jama'ar motar ya tashi don ita ba fahimtar kome tayi ba tadai san Tabbas akwai abinda ke faruwa.

Motar ce ta tsaya a take barayin suka saitasu da bindiga tare da basu izinin fitowa daga motar, ba musu duk jama'ar motar suka fifita harda Nnenna.

Ashe basu kadai aka tare ba ga mototi da yawa har biyar, kallon wata mata Nnenna tayi da mijinta da gani dai musulmai ne masu arziki matar na d'auke da ciki babba, haihuwar yau koh gobe ga mijinta a kusa da ita sai rokon barayin yake akan suyi hakuri akwai kudi a mota, Amma karsu cutar masa da mata.

Wani daga cikin sune ya daga ma su Nnenna tsawa akan su kwanta, kamar sauran babu musu duk suka kwanta, mutumin kuma wani ya buga masa gindin bindiga a kafad'a.

Matar ganin Halinda mijin ta ya shiga a take hankalinta ya tashi nakuda ya ballo mata sabo, Salati take sauran matan dake gefen tane suka fahimci haihuwa zatayi da sauri wata ta miki zata nufe ta ganin tana nakuda kuma a zaune.

Tsawa suka kwadawa matar akan ta koma inda take mijin ma jansa akai gefe aka bar matar ita kadai tana ta fama da azaba.

Caji suka fara daga mota har jikin mutane An samu wasu da kudi sai a ware su a gefe wanda ba'a samu kome agun saba Harbesa ake, Hakan yasa wasu da dama mutuwa tun ma ba'azo kansu ba suka hadeye rai suka musu.

Nnenna karan kanta Hankalinta ya tashi don ta fahimce Abinda ke faruwa a wajen watoh bakin rai bakin fama, Allah sarki mai nakuda nan nata fama da wahala kowa agun saida ya tausaya mata kuma da gani haihuwar fari ce.

Gaskiya Yan fashin nan basuda imani suna gani matar nan ta haihu Amma koh a jikinsu daker suka bari wata tsohowa ta yanke ma jaririya Cibi, Uban yarinyar ne ya roke Alfarmar a barsa yaga yarsa, Amma barayin nan haka suka ki.

Nnenna dake gefe a kwance Wani kato yazo kanta yana lalubar ta aiko banda naira dubu uku dake hannunta bai samu kome ba, janta yayi ita da bakkon ta gefe tare da bada izinin akai masa ita ciki tunda bata da kudi dole su fanshe kaya.

Kamata wasu sukayi wani yaja bakkon ya yar a take kulenta ya bayyana, Fizgo kanta Nnenna tayi da gudu ta nufi matar dake kwance cikin jini ga jaririyar a gefe dukawa tayi ta d'au jaririyan tare dama matar magana da turanci akan zata kai mata yarta har inda suke ta fad'a mata inane garin su?

Da mamaki barayin da mutanen wajen suke kallon Nnenna ita kamma koh a jikinta babu Alamun tsoro koh tashin Hankali, wani daga cikin sune ya harzuka da sauri ya nufi wajen da Nnenna ke duke tana jin maganar da matar ke fad'a mata, ga jakanta purse data bata akan inta shiga gombe sai ta binciki jakan tare da bata d'ankwalin kanta ta sanya jaririyar a ciki.

Ba musu ta Amsa daida lokacin barawon ya daga bindiga da karfi zai buga ma Nnenna akai cikin hanzari ta gauce ba tare da ya dame taba.

"Karka kuskura ka fusatani nama mahaifina Alkawarin xan danne xuciyata karka hasalani" tace tana nuna mutumin da hannu.

Hannu kawai yasa ya kwasheta da mari tau saida ta fadi a kasa daga tsungune, mikewa tayi da jaririyan a hannunta sai kuma ta daga kanta da karfi jin yana mugun sara mata.

Bata dawo hayyacin taba saida taji guje gujen mutane Ana ihu ana gudu daga maza har mata ga karan harsashe kamar ruwa, d'ago kanta tayi cikin matsanan cin Nauyi tana kallo dishi-dishi kamar dai Nnennan da babu glass.

Bata Ankara ba taji An kama hannunta da sauri an jata sun kama gudu Ashe wai yan sandane suka diro suke musanyan wuta da yan fashi.

Tsungunawa tayi da gudu ta sabe kulenta da jinjira a haka suka ringa gudu bata masan wanene ya riketa ba, ga jaririyar sai kuka take kamar ranta zai fita dole tasa suka tsaya a wani wajen ganin sun tsira sunyi nisa da Dajin.
Chapter 10 · 0% Book details