← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 122

Sashe 111

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Lahab yayi Wanda Rabon yayi irinsa tun ranan da Nnenna tabar sa,dukan su kallon sa sukayi sai Kuma Rahab ya hau dariya ya nufi kofa zaikarbo abin Yana cewa"in bazakici ba ai nida kanina zamuci,mikewa Lahab yayi da gudu yadau pillow yabi Rahab Wai zai buga Masa duk da ba karfin jikinsa yakeji ba Amma haka kawai yau yakejin kaunar Dan uwan nasa sama da da, yaji baida buri daya wuce ya gansa cikin happy shiyasa yana mikewa ya Soma bin Rahab dariya Rahab ya Fara Suka ringa zagaya falon Addayiya Kam sai magana take sun bar mutum tsaye a kofa,sosai Lahab ke gudu Yana bin Rahab shima gudun yake Yana kakkaucewa da Sauri ya bude dakin su ya Shiga Yana kokarin rufe kofa,Lahab ya turo kofar da karfi Aiko Nan yasa Kara yayi Kan gadon binsa Lahab yayi ya dannesa kana yad'au filon Yana ta buga Masa Yana cewa"nine kaninka ni"?da Allah kayi hakuri toh ba Kai bane haba"d'an sayawa Lahab yayi yace toh kacemin Yaya"da Sauri Rahab yace Yaya dan Allah gani ka matsemin hannu fa zafi yake min,mikewa Lahab yayi shima ya mike zaune Yana duba hannun nasa,hannu Lahab yasa ya rike hannun dan uwan nasa Yana dubawa.

Kallon sa Rahab yayi yace"ya Allah ka dauwamar da zuciyar d'an uwana cikin gaskiya da aminci"d'ago Kai Lahab yayi ya kallesa tare da amsawa da Amin"Lahab ka rame sosai kayi hakuri da kaddarar aduk yanda tazo maka Mai kyau Koh Mara kyau kayi hakuri kome ya faru jarabawa ne daga ubangiji zanji dadi Inka kasance cikin happy Kamar rayuwarka tada"girgiza Kai Lahab yayi kana ya zame ya kwanta a cinyan Rahab Yana cewa"Anya kuwa wannan geben zai cika abinda ya wuce ya wuce bazai taba dawowa ba, Rahab yanzun Kaine kad'ai farin ciki na Kuma nawa dake kusa dani"shafa kansa Rahab yayi yace toh inka waye gari babu Ni ya zakayi bazaka iya hakuri ba kenan"?

d'ago Kai Lahab yayi da sauri yace"banason haka karka karamin wasa irin wannan banason ai duk Randa Babu Rahab Babu Lahab Koh ka manta Abu dayane mu guda biyu"?haka ne Lahab Allah ya baka hakuri kaji"nuna min hoton yaran namu na Kara gani naji ance Suna Kama damu Niko sai Inga Kamar sun fimu kyau"da Sauri Lahab ya mike system nasa ya d'auka ya mikawa Rahab Aiko Nan Rahab ya kwanta Lahab ma ya kwanta tare da daura Rabin jikinsa ana Dan uwan nasa,kallon hotonan Rahab yake Yana yaba kyawon yaran da tsamtsam kamannin su dasu sai dai yaran farare ne"smma sunan da ka sawa yaran baimin ba Ina laifin kamin tagwara Lahab"?

Kasan fa sunan mu sunan iyayen mune kana nima na sake sawa yarana haba abin yayi yawa shiyasa nasa Musu nazeefi da nazeeefa Ni sunan yamun Kuma Ina Jin dadin sa"kyebe Baki kawai Rahab yayi Yana cewa lallai masu yara manya Allah nifa dariya kake bani Inna ganka na tuna Wai yara biyu gareka,make sa Lahab yayi shima yasa hannu ya hambare Lahab in Saida ya Fado daga Kan gado zuwa kasa,turo kofar Addayiya tayi hannunta d'auke da laidan ordern ajewa tayi tana cewa Kai ga abin naku nidai bazanci ba"mikewa Rahab yayi yazo ya amshi laidan ya koma Kan gado ya zauna bude laidan yayi ya dau roban takeAway in ya mikawa Lahab amsa Lahab yayi shima Rahab ya dau sabo ya bude sai Kuma ya kalli na Lahab ya kalli nasa.

"Yaya dai haka"?tsaki Rahab yaja yace nace takeAway uku biyu shinkafa daya gasheshen nama Kuma Ni Naman nafiso fa"kallon takeAway gabansa Lahab yayi sai Kuma ya dauka ya mikawa Rahab Yana cewa"anything for u brother gashi daman Ni nama bai wani dameni ba yanzun ban shinkafan naci,Mika Masa Rahab yayi sai Kuma yadau takeAway Naman ya aje a gabansa ya ibi guda bakwai ya sama Lahab a cikin shinkafan sa,iba a spoon Lahab yayi zaikai Baki haka kawai sai yaji abincin ya fita akan sa yaji baya kaunar cin abincin sauke spoon in yayi Yana kallon Rahab dake ta cin nama Yana kada Kai irin ya Masa dadin Nan,had'a Ido sukayi Rahab ya d'aga Masa gira daya"?

A hankali Lahab yace"Rahab na rasa meyasa nakejin wani iri a jikina Kamar Zan rasa abinda nafi so"?amsa Rahab ya basa,sai kayita astagafurullah na rasa meyasa Lahab ka kasa hakuri da abinda ya faru yanzun dai kaci abinci tukunna sai muyi magana dan Ni yunwa nakeji"shuru Lahab yayi Yana ta kallon dan uwan nasa"bazakaci bane Lahab girgiza Masa Kai yayi da sauri Rahab ya cire hannusa a naman Yana tambayar sa meyasa Koh Naman yakeso ba shinkafa ba sai Kuma ya tura Masa Naman duka a gabansa"toh gashi karba kaci"hawayen da Lahab baisan na menene bane ya cika masa Ido yace"nima bansan meya faruba haka kawai nake jina incomplete wallahi"

Murmushi Rahab yayi sai Kuma ya yamutsa fuska kana Kuma ya Fara tari a hankali Abu Kamar kiftawar Ido saiga Rahab ya rikice da wani irin mugun tari,hankali tashe Lahab ya mike Yana Masa sannu a zatonsa Koh kwarewa yayi,Amma Ina Rahab tari yake Yana sarkewa wani hararwa da yayi ya yunkura zaiyi amai Aiko sai gani Lahab yayi gudan jini bakki Kirin ya Fado daga bakin dan uwan nasa a rude ya mike Yana salati Yana kamasa ganin ya Soma wani irin aman jini Yana wani irin mimmikewa,ihunsa da salati shiya shigo da Addayiya cikin dakin a rikice.

Salati ta sake hade da kamo Rahab in Lahab saban rikita rasa ma mezaiyi yayi da gudu ya fitoh cikin dakin sai Kuma ya koma da Sauri waya ya d'auka ya Kira ambulance sai kuma ya kasa hakuri yadau keyn mota ya dauka yazo ya ciccibi Rahab daya sandare baya Koh motse sai Kuma kunfa dayake fitowa a bakin sa bayan jini ya tsaya,gudu yake Yana kuka Koh takalmi babu a kafarsa ya fita tsakar gidan motarsa ya bude yasa Rahab Addayiya daga ita sai dankwali itama Shiga tayi yaja motar da karfin gaske ya fita a gidan da mugun gudu,daidai lokacin Adewale ya shigo arean ganin yanda Lahab ya fito gidan yasa sa bin bayan sa da motarsa shima.........................

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*

gudu kawai Lahab yake shararawa Addayiya na baya ta daura kan Rahab a cinyar ta tana tofa Masa duk Addu'an da yazo bakinta"ruwa ruwa zansha ruwa"shine kalmar dake fita a bakin Rahab cikin magagin fitan Rai wani irin Jan birki Lahab yayi da gudu ya balle marfin motar don Babu ruwa a ciki kafa Koh takalmi Babu ya Soma gudu Akan kwalta saura kad'an wani Mai mota ya kadesa shagon wata Mata ya Shiga Babu magana ba kome kawai ya bude freezer ya dau ruwa ya fita da gudu cikin motan ya dawo ya shiga baya Kan d'an uwan nasa ya kama ya balle marfin Goran ya kafa Masa,gadai ruwa ya cika bakin sa Amma Koh kad'an Bai wuce ba sai dawowa da yayi Yana zuba,adaden ruwan da ubangiji ya rubuta Masa zaisha a duniya ya kare,ganin haka yasa Lahab ya Soma kuka,zai fita a sit in ya koma driver sit,sai Kuma yaji an rike Masa hannu da Sauri ya kalli hannun sai Kuma yace"sakeni Rahab sakeni muje asibiti babu abinda zai sameka.

"Lahab kayi hakuri da rayuwa kome yayi farko yana da karshe tabbas nikam ajalina yazo amma nagode Allah daba kaci abincin Nan ba da yanzun dukan mune a cikin wannan hali"kayi shuru sakeni mu tafi kaji Babu abinda zai sameka dan uwa ka manta tare aka haifemu tare zamu rayu Kuma mu mutu tare"?girgiza masa Kai Rahab yayi cikin azaba yace"wannan tsarine na ubangiji duk abinda ya tsara shine daidai Allah ya riga ya rubuta iyakacin rayuwar da zanyi a duniya kenan,naso kafun nabar duniya na Kara ganin mamina amma Dan Allah in tazo bayan babuni kuce ta yafemin duk abinda tasan na Mata Wanda nasani da Wanda ban sani ba kuce Mata Ina sonta,Kamar yanda nakeson ka kaida Addayiya Ina maka fatan Alkhari a rayuwar ka zan kwanta cikin salama mundin na mutu Lahab baka zubda hawaye ba,banason ganin ka kana kuka,sai wata rana"Yana karasa maganar yahau sassakewa la'ilaha'illahlah la'ilaha'illahlah............ Addayiya ta Soma cewa cikin kuka cikin yardan Allah Rahab ya karbi kalmar shahara"la'ilaha'illahlah Muhammadu rasulilah sallalahu allaihi wa sallam,wannan shine kalmarasa ta karshe daya furta a duniya Rai yayi halinsa.

Wani irin kafewa Lahab yayi a cikin motar jijiyoyin kansa kwayar idanunsa wani irin tashi sukayi suka zazzaro saiga jini ya Soma bulbulowa a hancinsa amma Babu Koh digon hawaye Sam babi hawaye a idanun sa, Addayiya kuka take tana maimaita innalilah wa'inna'ilahu raji'un, police ne suka matso kusa da motar ganinta a no packing matsowa sukayi daidai lokacin Adewale ya karaso fitowa yayi a motar shima ya nufi motan su Lahab in,kansa police yasa ta glass ganin wa'inda ke ciki yasa da Sauri ya Soma tambayar lafiya"?Addayiya na kuka ta musu bayani a take sukace Bari su dau Rahab akai hospital girgiza Kai Addayiya tayi tana cewa wani irin hospital Kuma bayan Rai yayi halinsa,Kinga ma wannan babban case ne gubafa yaci,daukar Rahab akazoyi Amma Lahab na damke da hannun dan uwan nasa anyi anyi a banbare yaki sai hakuri ake basa zuwa lokacin zama'a sun cika makil an zagaye motan daker da Nasiya Lahab ya sake dan uwansa da jagoran Yan Sanda aka kaisa asibiti,Lahab na zaune a kofar dakin da aka shiga da dan uwan sa gabaki d'aya kamannin sa ya sauka sai jini dake zuba a hancin sa anyi anyi ya shiga likitoti su dubasa yaki yace a barsa in ma mutuwa zaiyi ya mutu amma yaki kula kowa.
Chapter 111 · 0% Book details