← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 122

Sashe 81

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwantar da kanta tayi a bango ta rumtsa idanunta da karfi,Sun Dan Jima a haka kafun ya zare jikinsa a nata,ba tare da ta kallesa ba ta Mike tsaye sai Kuma da Sauri ta dafe bango Jin jiri nason ibanta,ta nufi kofar da Sauri yasha gabanta tare da Kare kofar da jikinsa,ba tare da ta Bari sun had'a Ido ba tace"ka ban hanya na wuce"Ina zakije"?shima ya tambaye ta.

"Zanje na gayama su mom bani na kashesa sa"cikin damuwa Lahab yace"tun farko kin Bata kome da ace lokacin da abin ya farune Kika tsaya Baki gudu ba duk abinda zai samesa kina da bakin kare kanki,amma yanzun kin taka sahun barawo ne kina zuwa saidai a yanke Miki hukuncin kisa"ban damu ba don rayuwa ta daman Bata da wani amfani"da Sauri ya rungumeta sosai ya manna bayansa da jikin kofar tana jikinsa dan dagata yayi a hankali Bai damu da fizge-fizge da take ba,har Saida ya dangana ta da bedroom turata yayi da Sauri ya dawo da kofar ya rufe ta Baya sannan ya fita a falon.

Fita yayi a dakin ya tsaya a bakin dakin dake kallon nasu in Bai manta ba jiya kusan tare Suka Kama dakin da couple in Suka shiga dakin su Kuma suka shigo Nan, knocking yayi Saida ya Jima kafun aka bude dakin mutumin ya tsaya Yana tambayar sa lafiya,dan kaikaya keyansa Lahab yayi a hankali yace"Dan Allah madam ta taimaka min da veil daya Dan Allah,kallon sa sosai mutumin yayi sai Kuma ya girgiza kansa Yana mamakin abinda ya had'a yaro da Bai wuce 18 years ba da mace a Hotel Amma baice kome ba ya koma dakin Yana kitsema iskancin yaran yanzun daga xaran balaga yazo musu dai macece a ransu.

hijab in ya kawo Masa babba har kasa sosai Lahab yayita godiya da Sauri ya shiga dakin bude kofar dakin yayi ya Shiga zaune ya saketa sai kuka take,jakanta dake yashe ya d'auka ya dau wayar ta ya maka da bango don yasan daker ne in ba'a bi diddigin layi ba shiyasa ya cire sim in ya karya yadau hijab in ya zura Mata akan jallabiyar dake jikinta irin hijaban Nan ne da akece musu Mai Corona ya rufe Mata Rabin fuska hannunta ya Kama ya goyi jakan nata a bayansa Wanda babu kome a ciki sai tarkacen takardunta fita sukayi a hotel in da Sauri ya tare musu Keke Suka shiga Yana tunanin Ina zai kaita to yasan dai yanzun fita a gari bazaiyu ba,kallonta yayi a cikin keken yace"akwai Wanda Kika sani anan ne"?girgiza Masa Kai tayi"Mika Mata wayan sa yayi yace kisa number parents naki muyi magana dasu don ya Kamata Susan abinda ke faruwa.

Kuka ta Soma a hankali Wanda yasa Mai Keke Dan juyawa ya kalleta,da Sauri Lahab yace"kimin shuru karki taramin jama'a"shurun tayi tana shesheka,"tsaya anan"Lahab yacema Mai keken ganin yanda yake juyowa Yana kallon Nnenna Bini-Bini duk da ba Dole bane mutum ya ganeta ba,sauka sukayi ya basa kudin sa wani keken ya tare ya fada Masa Inda zai kaisu,Suna Isa bakin layin Bai yarda ya shiga da Mai keken ba ya zare kudin sa ya basa hannu yasa ya kamo na Nnenna Suka Soma tafiya har Suka iso kofar wani gida Mai Jan tabo sosai irin gidan Nan na talakawa tsayawa yayi a bakin kofar gidan Yana sallama.

Amsawa akayi daga ciki babu Jimawa saiga yaro saurayin a kalla zaikai 25 ya fito sai Kuma ya waro Ido yace Rahab sannu da zuwa,shafa kansa Lahab yayi yace"Lahab ne"Aiko da Sauri yaron yace masa su shigo ciki Bismillah ba musu Lahab ya kama Nnenna Suka shiga ciki shimfida musu taburma yayi Suka zauna bin gidan Lahab yayi da Ido sai Kuma ya kalli yaron yace"goggoji ta tafi aiki ne"da Sauri saurayin daya mike ya ibo musu ruwa a kofi ya aje Yana amsa Masa da eh Lahab Bai barota a gida ba"?share tambayar Lahab yayi sannan ya nuna Nnenna yace"Dan Allah faruq in babu damuwa Ina son ta zauna anan zanje gida nayi magana da goggoji don Allah Kar a barta ta fita sannan ta zauna a daki banason mutane Suna shigowa Suna kallonta ga wannan ya Mika Masa 5k ka sama Mata abinda zataci pls,da Sauri faruq yace haba Lahab abinda zataci sai ka bani kudin karfa ka manta daga gidan ku goggoji ke zuwa da abinci haba haba wallahi bazan karba ba,duk yanda Lahab yaso faruq ya karbi kudin ki yayi,mikewa yayi zai tafi da Sauri Nnenna ta Mike hade da tsayawa a gefensa zaro Ido yayi yace"ya haka"?wani kallo take Masa duk da bataji abinda sukace ba don bajin hausa take ba Amma ta fahimci a gidan yake nufin zata zauna Taya zata zauna gida daya da faruq ba Mata a gidan.

da turanci take fada Masa bazata zauna gida babu mace ba,anan Lahab ke ce Mata ai matar gidan na tafiya aikine shima faruq Yana zuwa shago don haka ita kadai zatana wuni kin yarda Nnenna tayi da zaman sai da Lahab yayita Mata masifa kafun ta amince a idanunsa faruq ya bude Mata kofar dakin goggoji ta shiga shi Kuma yabi Lahab a baya ya rufe gidan ta baya kamar yanda Lahab yace Masa.

Lahab na Isa gida ya tarar da har Yan gidan sun karya masu zuwa aiki ma sun wuce aikinnsu Amma sauran yaran nagida tunda yanzun ana holiday ne, bayan dakunan gidan ya leka anan ya tarar da goggoji Zama yayi babu boye boye ya zayyana Mata abinda ya faru da Kuma Nnenna dake gidan ta tare da tabbatar Mata Batayi kisan Kai ba sanan Dan Allah duk abinda zaije ya dawo kada ta sanar da kowa Nnenna na gidan ta sanann tasa Mata ido,babu abinda lahabbl zai nema Wanda Bai sabawa shariya ba goggoji ta kasa Masa don ya taimake ta a rayuwa badon Shiba da d'anta kwalli daya faruq daya Zama tarihi.

da yamma saiga Adewale da Nabeel hankali tashe sukazo gidan su Lahab Nabeel zai tsinewa Nnenna yake Wai ashe makashiyace Mai fuska biyu shi wallahi tunda ya ganta shikenan yaji ya tsaneta Allah yasa a Kamata a ratayeta wani irin Abu Lahab yaji ya tsoki zuciyarsa hatta yawun bakinsa wani daci daci yake Masa wani Abu Mai kamasa gundura tsana yaji ya dirar Masa a makwashi na Nabeel,Amma baice kome ba Adewale ma kallon Nabeel kawai yake Saida ya Bari ya kammala zaginta tas kafun yace"haba Nabeel kana da tabbacin ita tayi kisan ne wai meyasa mutane suke hakane gashi duk gari ya gume ta kashe Dan marikinta ka sani Koh ba haka abin yake ba"hayayyako Masa Nabeel yayi yace cewa za'a Mata karyane in tasan tana da gaskiya meyasa ta gudu ana Neman ta, mikewa Lahab yayi ya nunawa Nabeel kofa hade da cewa"tashi ka fitar min a daki Nabeel"? Da mugun mamaki Nabeel ya mike tsaye yace"Ni kake kora Lahab"kofar lahab ya Kara nuna Masa a zafafe yace"tun Kan Raina ya baci Nabeel kabar dakin Nan"mikewa Nabeel yayi yace"insha Allah bazan Kara shigowa gidan bama bare dakin ka ya bude kofar ya fita"mikewa Adewale yayi ya matso kusa da Lahab tare dasa hannu ya dafa kafadar sa Yana bashi Baki akan ya kwantar da hankalin sa taima ma duk abinda ake fada akan ta karyane,shidai Lahab baice kome ba Harya Gama surutun sa yabar gidan.

Bayan kwana biyu Da yamma bayan Lahab yaje ball ya dawo kamar zaibi gidan goggoji yaga ya Nnenna ta kwana sai Kuma ya dawo gida yadau laptop nata,bayan yayi wanka yaje gidan goggoji ya duba Nnenna Kuma yaji dadin yanda yaje ya sameta tayi wanka harma ta sa Sabon Kaya daya baiwa goggoji kudi ta sai Mata,Amma dai tadan rame kad'an Zama yayi a kusa da ita tare dasa hannu ya taba wuyanta buge hannun tayi,shikam Dan murmushi yayi ya aje Mata laptop in a gefen ta Bata kallesa ba ta juya fuskar ta gefe daban irin tayi fushin Nan,sai da yayita faman lallama kafun ya samu ta hakura ta sauka daga fushin da take dashi na kwana biyar dabaizo ya dubata ba, faruq ne ya shigo gidan da Sauri ya karaso Kan taburman ya dau laptop in Yana jujjuyawa.

Washe garin ranan da yamma Lahab ne zaune a dakin sa Yana karanta littafin physics don yanzun da gaske ya dage Yana karatu, yaji an turo kofar dakin sa da Sauri da Sauri ya mike tsaye ganin uzaifa ya shiga hankali tashe Yana cewa Lahab ya fito ana Neman sa,shekeke lahab yayi yace "don ana nemana saika min irin wannan shiga daki cikin tashin hankali"Bai rufe Baki ba saiga Abbu ya shigo dakin da kansa hankali tashe yace"Wai Ina Lahab inne ka fito Mana fitowa lahab yayi da Sauri Abbu ya kamo hannun sa har babban falo,sake Baki Lahab yayi Yana bin wa'inda ke falon nasu sai Kuma idanun sa ya sauka akan Dan uwansa da ke tsakiyar wasu mutane guda uku cikin dumbin mamaki,yaji Abbu na cewa bakun ga dayan ba Y'an biyu ne,gaLahab in wannan dake wajen ku Rahab ne ince dai lafiya kuke neman sa,babu walwala a fuskar dayan ya kalli Lahab yace"Kaine Hassan Al'hassan dogo Mai naira?gyada Kai Lahab yayi sai Kuma wani daga cikin mutanen ya zaro ID card insa ya nuna tare da cewa"Ni sunan wisdom timoti jami'in sirri na farin Kaya zamu tafi da Lahab office in mu akwai tambayoyi da mukeso ya amsa mana"Lahab yaci niiii"? Yes ur under arrest................................................

Alhamdulilah Alhamdulilah Alhamdulilah

🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*

Book 2
Chapter 81 · 0% Book details