← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 122

Sashe 32

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zulaihat Kam tana fita ajin su Rahab ta nufa ta Kai Masa jakan Kamar yanda ya umurceta kafun ta wuce masallaci domin sallan la'asar suci abinci kafun su Fara hadda by 4 O'clock.

Harta nufi gate sai ta tuna Lahab yace taje clinic juyawa tayi ta nufi clinic in,tana Hawa block in ta samu wasu Yan coper guda biyu sun fitoh d'aga ciki suna yare, alamu dai ya nuna wajen uncle physics nasu Suka fitoh shiga clinic in tayi direct ta nufi office in likitan knocking tayi shuru ba'a Bata izinin Shiga ba,gajiya tayi da tsayuwa kawai saita yanke shawarar tafiya abinta, juyawa tayi saura kadan suci Karo da Dr daya kawo Kai,da Sauri tayi baya hade da dukawa, "good afternoon Dr"?

Afternoon Nnenna Koh?

gyada Masa Kai tayi, toh muje ciki sai muyi maganar,Yana karasa maganar ya bude kofar office in ya shiga,biyosa tayi a baya Zama yayi a kan kujerar sa tare da nuna nata kujeran kaban Des nasa,sit down Mana Nnenna?

gyada Masa Kai tayi hade da Zama akan kujeran dake gaidashi tayi Shima ya sake amsawa kafun ya daura da cewa,gaskiya Naga jikin yayi kyau sosai ashe shiyasa ban ganki da safe ba.

"Sorry Dr naji saukine sosai shiyasa"

Ok Amma ai zakizo mu cire kanula in Aiko,ya karasa maganar Yana kallon hannnunta.

"Dr Na zare Allurar ai"ta karasa maganar tana kallon sa

What???meyasa Zaki cire kina aikin asibitine ban hannun mu gani.

Mika Masa hannun tayi,da kansa ya warware tsumman zare Ido yayi Ganin yanda hannnun ya kubura alamu ma sun nuna jini ya zuba,Aiko take yahau masifa irin dai yanda Dr kema majinyata in suka jika musu aiki,take yadau waya yayi magana ba'ajima ba sai Suka ji knocking izinin Shiga ya bada,aka turo kofar wata kyakyawar budurwace sanye da kayan asibiti.

Cike da girmamawa tace,sir gani

Yauwa sister farida ga wannan kuje da ita pharmacy kusai Allurar Nan saiki Mata tare da dressing in hannun nan nata Kisa Mata plaster,yakarasa maganar da Mika Mata Dan paper daya rubuta Mata allurar.

da Sauri ta karba cikin girmamawa.

Am sannan ke Nnenna kina Shan magani akan Kari Kam Koh? karki kuskura kiyi Wasa da magani kinji Koh?

Gyada Kai Nnenna tayi tare da mikewa tabi nurse in a baya,fuskarta a hade don wallahi ta tsane Allura.

Haka ba yanda ta iya ana kammala Mata allurar aka wanke hannun nata aka manna Mata plaster ta fita a clinic in, lokacin kusan 3:30 yayi haka ta fita a makarantan Koh sisi Bata dashi haka ta ringa takawa da kafa har gida duk tabi ta gaji ta jirkita gabaki d'aya.

Ta bangaren su Lahab haka Suka ringa yawon su har rana yunwa data Kama Lahab abinci Suka saya dukansu Suka ci,d'aga Nan sai Kuma yamma Suka Kama hanyar gidan su Nabeel.

Da sallama dukansu suka shiga gidan Inna ce zaune tana kwaba lalle zata daura sai yayar Nabeel dake rataye da jakan makaranta a kafadar ta sanye take da dogon riga na atamfa Wanda yasha wanki da guga duk da yasha ruwa Amma tas yake sai gelenta fari medium rataye a kafadar ta,ta rataya hand bag nata maikyau a kafadarta fuskar ta ba kome sai powder data shafa,tunda Suka shigo Adewale ke binta da kallo itakam kallo daya ta musu ta kauda kanta tare da zura takalmin ta ta nufi kofar fita.

"Ah ah big Aunty sai Ina Lahab yace Yana kallonta"

Mtwss Inda ka aikeni, shine amsan da ta bashi tana fita a gidan Inna Kam Ido kawai ta zuba musu irin kallon Nan na tuhuma da haushi don haryanzun Bata bar Jin haushin abinda Lahab yama jikanta ba gashi Kuma yau ta gansu tare duk buga Masa gargadi datayi bashi ba Lahab d'aga yau.

Adewale Kam saurin juyawa yayi tare da zaro wayarsa yahau wayar karya Yana fita a gidan Lahab Kam da kallon tuhuma ya bisa Amma Nabeel bai kawo kome a ransa ba ya nufi dakin sa Lahab na binsa a baya harsun kusa Isa dakin da Sauri Inna ta Mike kaiii lahabu dakata Ina zakaje badai dakin jikana ba kamko???Mara mutunci.

Dakatawa dukansu sukayi suna kallonta da mamaki bare ma Lahab Inda sabo dai ya Saba da masifar ta Amma bata taba koransa ba,"oh Inna yanzun ni kike kora a gidan Nan"?

Eh na koreka lahab,shine amsar da ta basa tana Masa kallon uku saura kwata.

"Kaga Nabeel shiga ka dauko mini kayana na shanja"

Shiga dakin Nabeel yayi Kamar yanda Lahab yace Masa don baison shiga rigimar su da Inna,kayan ball in Lahab da yake bari a gidan su ya dauko Masa da takalma duk ya fitoh masa dashi,kallon Inna yayi dake tsaye ta rike kugu yayi kawai ya girgiza Kai tare ta mikawa Lahab kayan,gasunan Lahab.

Amsa Lahab yayi ya aje akan dogon igiya dake tsakiyar gidan ya makala kayan ya aje takalmin a gefe,rigan uniform dake jikinsa ya cire tare da vest ganin addan Nabeel Bata gida yasashi Kwabe wando ya rage dagashi sai gajeren wandon jikinsa salati Inna ta buga,innalilahi wa'inna'ilahu raji'un mezan ganin nan dan duniya tsirara kayi a gaban jama'a nashiga ukuna,tana maganar tana tafa hannaye.

Shikaran kansa Nabeel mamakin iskancin Lahab yake wallahi ace mutum baya shakkan kowa.

Bucket Lahab ya d'auka batare dayabi takan masifar Inna ba yaja ruwan sa ya wuce bayi bayan yadau kayan daya makala a igiyan, wanka yayi ya zura kayan ball in abinsa ya fitoh daidai lokacin Nabeel ya dauko musu kwanon alele da Inna tayi a kitchen aje musu yayi a tsakar gida ya shimfida musu taburma,Lahab ga abinci fa ka fara ci Bari nima nayi wanka.

gyada Masa Kai Lahab yayi ya zauna tare da tambayar sa"wai har yanzun Adewale bai shigo bane"?

Nabeel najan ruwan Yana basa amsa,wallahi bai dawo ba nayi tunanin Koh fa ya wuce gidane.

"Anya kuwa Nabeel kasan yaufa akwai show bazai koma gida ba"

Kai gaskiya hakane fa Bara nayi wanka kaci alelen ka rage Mana daidai na fito wanka maybe ya dawo.

Bandaki Nabeel ya Shiga yayinda Lahab ya bude kwanon yayi Bismillah ya Soma cin alelen da Miya Inna Kam sai hararansa take makokonta cike yake tam da haushi ita da gidan ta ta kasa koransa.

Ta bangaren Adewale Kam Yana fita ya hangeta a bakin titi da Sauri ya nufeta,Assalamu Alaikum Gimbiya mubeena sai Ina haka.

Kallon sa mubeena tayi, waalaikumu Salam lafiya Kam?

Lafiya mubeena nace Ina Zaki?

Cikin yanga tace school zani wani abun me?

No ba kome Kuma in ba damuwa Zan iyya rakaki?

Kallon sa tayi da kyau itafa lamarin dan yarobawan Nan ya Fara isarta,akan me zaka rakani cema akayi bansan hanyar bane Koh me?

No ba hakan bane mubeena me laifi dan na nuna Zan rakaki school Naga dai duk Inda kaga kyautatawa da kulawa alamune na.................sai Kuma yayi shuru Yana kallonta kamar yarda ita ma ta juyo gabaki daya tana mamakin mezai ce kenan.

Uhmm uhmm a gaskiya mubeena nagaji da boye abinda ke Raina na gaji da hakuri da abinda ke cutar dani,nagaji da lallashin kaina wallahi Ina cutuwa mubeena bazan iyya daurewa ba nayi iyya yina Amma nakasa juriyar hakan.

Zuciyar ta bugawa take sosai Wanda har Saida ta dafe kirjin ta kafun ta daga idanunta tazuba Masa a hankalin ta bude bakinta ta Kara tambayarsa a Karo na biyu,menene wannan abin Adewale??...........

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*

Page 39&40

Ina sonki Ina kaunar ki Ina bukatar ki a rayuwata,dan Allah karkice ah ah zuciyata bazata jure hakan ba ki tausaya min, Adewale yakarasa maganar cikin wani yanayi na fargaba.

Wani irin gyara tsayuwa mubeena tayi cikin Al'ajabi da mamaki take bin yaron da kallo don Koh a cikin su ukun shine karami su Lahab da Nabeel sun Dan girmesa kusan da shekara daya ma Koh watannni,Amma Kai dai baka da hankali Koh ince baka da mutunci yanzun Kai Inba tsaurin Ido da samun wuri ba ka rasa wance zaka kalla kace kanaso sai ni? sa'ar kace Koh tsarar kace ni toh wallahi d'aga yau sai yau magana makamancin wannan ta sake shiga tsakanin mu sai nayi mummunan Saba ma aikin banza kawai da wufe,ta karasa maganar tare da juyawa tana tsaida Mai keken da zai wuce.

Adewale dayayi mutuwar tsaye a wajen ganin Mai keken ya tsaya har tana kokarin Shiga yasasa saurin Kama Mata hannu,pls Mubeena ki tsaya ki saurare ni don Allah zuciyata bazata juri wannan horon da kike Mata ba.

Tasss kakeji mubeena ta wanke Adewale da Mari tare da fizge hannunta ta shiga keken tare da cewa Mai keken,malami dan Allah ja muje.

Adewale na dafe da kumatunsa Yana bin keken da kallo Harta cila,dafe kansa yayi a take yaji Kan na Masa wani irin ciwo kirjinsa na mugun bugawa juyawa yayi zai tsallaka titin,Sukayi Ido biyu da Lahab dake tsaye a nesa ya zuba Masa Ido alamu ma ya Jima agun.

Lahab Kam tunda Nabeel ya Shiga bandakin haka kawai taji hankalin sa ya kasa kwanciya ta fitar Adewale Kuma ya tabbatar bin mubeena yayi,hakan yasasa kasa hakuri har Saida ya rufe kwanon alelen yasa silifas din mubeena dake waje duk da ya Masa kadan Amma haka yasa.

Inna sai masifa take,Kai lahabu cire takalmin Nan wannan kafa naka kamar doya manya manya zaka saka Mata a takalmin ta Mai number 10 da rabi so kake ka tsinka Mata ai kafarka sai number 11 da rabi.

Kin kulata yayi ya wuce ya fita don ya gaji dasa boot takalmin ball in Kuma so yake inyasa Kar ya cire saiya dawo ball,fita yayi a gidan sanye da kayan ball in jikinsa tun d'aga nesa ya hangesu tsaye Suna magana hakan yasa shi jingina da ginin kofar gidan su Nabeel in ya hade hannu a kirjin Yana kallon su Amma baijin abinda suke cewa,bai Gama Shan mamaki ba Saida yaga mubeena ta wanke fuskar Adewale da Mari.
Chapter 32 · 0% Book details