← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 122

Sashe 109

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wai me hakan yake nufi kina nufin tafiya zakiyi ki barni"?Lahab ya Zama dole,kana ta karbi evalope in ta d'au ATM nasa ta Mika Masa ya karba,kudin dake cikin account nawa ya Isa in Kula dasu"no ki amsa in kika ki karba bazan ji dadi ba,maidawa tayi cikin akwatin kana ta dau macen ta Goya da majanyi hannu tasa zata karbi namijin,da Sauri Lahab ya mike tsaye Yana kallon ta kana yace"Wai da gaske tafiya zakiyi"Dole na tafi lahab"amma dan Allah kada kiyi nisa dani zamuyi waya ki Kama gida cikin tsohon unguwa da Muka Bari zanzo na sameki agun ki kular Mana da yaran mu sannan dan Allah inaso yarana su tashi cikin addinin musulunci Ina son su kasance musulmai ki Basu tarbiya daidai gwargwado,na Miki Alkawarin insha Allah kome zai daidaita wata rana ga wannan"ya Mika Mata wani golden box Mai sheki hannu tasa ta karba kana ta dau akwatinta a hankali sai Kuma ta tsaya tare da Mika Masa daya hannun ya bata yaron ta amma Lahab bai Mika mata nazeefi ba Kuma har lokacin yaron baibar kuka ba da ajiyar zuciya.

Lahab na maka ALKAWARIN yaran ka zasu tashi cikin musulunci Zan Basu tarbiya daidai gwargwado Zan sasu a makaranta da ake koyar da ilimin addinin ka,Koda Allah yasa bamu Hade yanzun ba, haka zalika Zan jira ka tsawon Rai amma bana tunanin zamu cigaba da rayuwa Nan kusa,nima inaso Koh bayan babuni dan Allah ka ringajin maganar iyayen ka Kama mahaifiyarka biyayya duk abinda tace maka kayi mata,kaga nida bani da iyaye wazai min Holo innayi ba daidai ba koh kuskure?babu bana dashi"

amma Labiba taya zakice bazamu ray..............bauuu kakeji an turo kofar da karfi mami ce ta shigo"toh karuwa an nuke da yaro a daki ana kitsa Masa magana ke Koh kunya bakiji ki rasa zaki bi sai wannan yaro"?Koda yake daman Ina Arne Ina kunya"maza shege ki fita tunda ba gidan ubanki bane,aje a nemi wani daderon bada d'ana ba,anga yaro yayi kudi ana Shirin d'auke Masa hankali"Mika Mata shegen ta ta Kara gaba dashi kin mikawa yayi da Sauri Mami ta karaso cikin dakin ta fizge yaron ta wurgawa Nnenna da karfi,saura kad'an yaron ya subuce baiwar Allah ta canke abinta salati Lahab y sake ya rumtsa idanunsa donshi a tunanin sa yaron ya Fadi akan tiles,a gaba Mami ta tasa Nnenna Kamar wata Shaniya tana zaginta tana turata da karfi ita da akwatin nata,Lahab na binsu a baya shima hawayen yake Yana rokonta.

Har wajen compound Mami ta fita da ita da Sauri Lahab ya sake kneel down batare da gajiyawa ba yahau baiwa uwar tasa hakuri amma Mami ta rantse bazata hakura ba"wallahi Lahab kaji yau sai rantsuwa nake ba? toh bazanyi a banza ba Koh bayan Raina hajiya Khadija ki shaida ban yarda ya Kara rayuwa da yarinyar Nan ba,haka zalika Inka sake Koh magana ya hadaka da ita Koh neman Inda take Koh a bayan idanunsa ne,Allah ya Isa Lahab Allah ya Isa,Kuma saina d'aga maka no-no in yaso kabi duniya,wani irin daskarewa Lahab yayi Yana tsaye harta fita a gate in,da gudu Ade yabi bayanta da niyar ya bita cakumosa Mami tayi tana zaginsa tana cewa babu Inda zaije wato zai bita su hadawa danta munafurci Koh? ai daman Arne bai iya samun waje ba"Lahab dai na tsaye Kamar gunki da Sauri Ade ya samu ya b'anb'are kwalarsa ana Mami da gudu ya nufi kofar gidan amma abin mamaki babu Nnenna Babu Mai Kama da ita,haka ya wuce hospital dake unguwan nasu amma Bata Nan,duk wani bus stop daya sani yaje amma Babu Nnenna.

*****************
Yayyafin aka Soma da karfi Mai hade da iska a hankali Lahab ya zame ya zauna akasan compound in Yana wani irin kuka maicin rai,sosai yaji tsoro ya darsu Masa a ransa kada Nnenna tashiga wani matsalar Kuma gashi baisan ya lafiyar dansa ba Ashe haka Y'ay'a suke da dadi? Mami tuni Suka shiga ciki Suka barsa a wajen tunda ya kafa idanunsa a gate tun fitarta har yanzun bai kauda ba,ruwa aka Soma dakarfi haka ruwan nan ke sauka akan Lahab amma Koh gezau ko alamun tashi baiyi ba,yanzun Kam kukan ma ya tsaya hawaye ya bushe,fitowa kawar Mami tayi tana cewa Lahab ya taso a wajen Kar wani ciwon ya kamasa"ki barsa inyaso ya mutu a wajen da irin wannan yaro ai gwara baka haihu ba"abinda Mami tace kenan taja kawarta Suka sake komawa ciki so take ta nunawa Lahab true colourn ta yanda gaba bazai Kara yunkurin tafka wannan kuskure ba.

Ruwan sama na kusan 2 hour's kaf suka Kare akan Lahab daman ba isheshen lafiya bane dashi gashi yaki rufe idanunsa har lokacin idanun nakan gate na gidan ruwa ya shishiga cikinsu sunyi jazur dasu,turo gate in akayi a hankali Adewale ne ya Shiga jikinsa a jike shima a hankali ya Soma nufo wajen da Lahab ke zaune a hankali lahab ya dago idanunsa ya kalle Adewale irin kallon Nan na tambaya?girgiza Masa Kai Ade yayi watoh baiganta ba, lumshe idanunsa Lahab yayi a hankali,kawai sai Ade yaga Lahab na sulalewa a hankali da Sauri ya tarosa da hannayen sa gudun kada kansa ya sauka da kasa,amma Ina Lahab Kam gabaki d'aya ya zube a jikinsa baya Koh motse.

A hankali ya Soma bude idanunsa sai Kuma ya maida ya rufe kirim ganin wani irin duhu daya mamaye dakin,Jin ana Kiran sunan sa a hankali yasa sa Kara bude idanun nashi dishi dishi ya Soma kallon sama sai Kuma ya Wulla idanunsa ga wajen da yaji ana Kiran nasa,Abbu ne da uncle muzammil sai Mami,maida idanun yayi ya rufe Koh tantama bayayi a gadon asibiti yake,toh amma yaushe su Abbu suka zo?Jin an rike hannunsa yasa sa Kara bude idanun,ya saukesa akan Addayiya dake zaune abakin gadon da yake,bude baki yayi a hankali yana Mata magana amma saboda dishewar da muryarsa yayi yasa Addayiya bataji abinda yake cewa ba matso da kunnenta tayi Kan bakinsa"Addayiya kwana na nawa anan"?

A hanakli Addayiya tace"yau kwanan ka uku Lahab a gadon asibiti"?.....................

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*

Lumshe idanun nasa yayi ya koma ya kwanta,matsowa kusa dashi muzammil yayi yasa hannu ya taba wuyansa sai Kuma ya fita a dakin bai Jima ba sai gasa ya dawo tare da Dr, ta basa Dr yayi Lahab yaki bude idanun sa tambayar sa yayi akwai Inda yake Masa ciwo?girgiza Kai yayi a hankali ruwan Dr ya cire masa kana yace ya wanke Baki ya samu yasa Abu Mara nauyi a cikin sa,sannu Yan dakin Suka Soma wa Lahab shidai gyada musu Kai yake kansa na kasa don wani irin kunyar yayun nasa yake daman Mami Kam Koh kallon Inda yake batayi ba.

Kamasa muzammil yayi a hankali ya mike tsaye sai Kuma yace uncle ka sakeni Zan iya zuwa toilet in da kaina sakin sa muzammil yayi Aiko saura kad'an Lahab ya zube a kasa ya tarosa Yana cewa ba bayaji ba shiyasa ya barsa yaga gudun ruwan sa mutum kwana uku a kwance har Yana da kuzarin cewa zai mike ya taka,Kai muzammil ka bisa a hankali Mana kafun yaji saukin tukunna"Addayiya tace tana mikewa tabi bayan su cikin toilet in ruwa ta hadawa Lahab yayi wanka ta basa Sabon toothpaste da brush ya wanke bakinsa Sabon uniform na hospital in da aka aje musu a goge Addayiya ta dauka ta basa ya sanya Wanda ya ciren Kuma aka saka a basket.

dawowa Lahab yayi ya zauna a bakin gadon gabaki d'aya ya zube,ya Kare kowa ya gansa yaga Wanda yakejin jiki,tea Addayiya ta had'a Masa tare da Mika Masa,gizgiza Kai yayi kana yace"Addayiya banajin yunwa bazan iya Sha ba"aiko Dole kasha Taya zaka zauna babu kome a cikin ka har kwana uku Allah yaso ma ana daura maka ruwa"duk yanda Addayiya tayi Lahab yaki Shan tea Nan gajiya Mami tayi ta daka Masa tsawa akan ya karbi shayin yasha hannu Lahab yasa ya karbi shayin bawai don tsawar data buga Masa ba sai don kudurin da ya daukarwa kansa akanta,tunda ya kafa kofin shayin Bai sauke ba Saida ya karar duka Yana aje kofin amai ya tasar Masa kafun ma ya Isa toilet tuni ya kwarara a tsakar dakin.

Sai da Lahab yayi kwana biyar a hospital kafun aka sallame su Kuma abinda ya bawa kowa mamaki shine,tunda ya farka baiyi zancen rashin ganin Ade ba Koh Kuma zancen Nnenna asalima Lahab gabaki d'aya ya sauya inya zauna ya lumshe idanun sa sai yakai awa uku Koh hudu Bai bude ba sai ka gama surutun ka akansa bai d'ago ya kalleka ba,indai ba Mami bace ta Masa magana Koh Abbu Koh muzammil wannan Kam Koh Bai Basu amsa ba yanayin abinda sukace Koh abinci Suka basa Koh baison ci ci yake inyaso amai ya biyo baya,bazai hanasa sake ci ba.

Gabaki d'aya jikin dangin sa yayi sanyi yau aka sallame sa,zaune yake Akan gadon hospital in ya chanja uniform nasu zuwa kayan sa kallon sa Addayiya tayi, guri daya ya kurawa Ido zuru magana take Masa Amma baimasan tanayi ba hannu tasa ta tabasa,da Sauri ya zabura sai Kuma ya kauda fuska,shigowa dakin Abbu yayi yace ya tashi su tafi an sallame sa,mikewa kawai yayi kansa a kasa har Suka fita,mota Suka hau sai gidan Lahab.
Chapter 109 · 0% Book details