← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 115

Sashe 98

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cewa yayi yatara su ne akan yanda za'ayi adawo da Salihu gida..
Samad yace Sarki me ran karfe nayi magana da wani shahararren sojan n'an mataimakin shugaban kasa a harkan tsaro..
Yace inba nan zuwa gobe InshAllah ze gaya mana inda yake...

MashaAllah MashaAllah Sarki ya furta cike da Jin dadi yace Allah ya bayyana shi '' wallahi nakosa inga d'ana '' bansan da wani idanu zan kalle sa ba...
Sannan inason wannan matar nan Farida '' a je akamo ta akaita station banason tasamu labari ta gudu...
Habiba kiyi hakuri nasan bazaki ji dadi ba tunda yar uwar ki ce..
Amma dole ta fuskanci hukuncin cin Amana har cikin masarauta ba Daga waje ba..
Da bada shawara akan buga masa makami akai wanda da rai yana kusa yana iya zama ajalin sa...

Mamy cikin sanyin Murya tace A'a Sarki karka damu koni ce nayi laifi akamani.....

Mama karama tace gaskiya Habiba ke ya ce kuma ta gari '' wace mata ce za'a hana ta bin mijin ta kuma ta zauna babu ita awannan zamanin.
Shima Salihu yayi kokari da yayi biyayya yabar ta.... Allah yayi muku Albarka..
Da ameen kowa ya amsa...
Abban Marwan yace aini nafi kowa laifi nida sai abunda Fulani tace shinake yi '' 'tana juyani gashi tasa nayiwa dan uwana rashin mutunci...

Ahmad cikin kwantar da murya yace Abban Marwan ance rana dubu ta barawo rana daya tame kaya...

Yarima Samad yace hakane kanina..
Marwan cikin kuka yace Samad ka yafemun yanda n'a ringa diban kudaden ka''ina bawa Fulani duk a zatona daidai nake aikatawa duk da wani lokacin inajin ba dadi araina...

Yarima yace karka damu Marwan kaima ba yin kanka bane' ''

Sarki ne yayi gyaran Murya yace sai magana ta gaba..
Zancen auren Ahmad yataso nan da kwana 12.
Dan haka n'a gama hada lefe '' komai sashin nasa duk angyara shi...

Sannan inason ahada auren d'ana khadija..

Samad cikin zazzare idanu yace Khadija kuma Ah Ah nifa bayanzu zamu aurar da ita ba..

Sarki yace to uban me zatayi maka agida ne...
. Ahmad yace kaide Sarki kacika rigima inbanda abunka duka nawa Khadija take kuma wai waye zaka bata muji inbe mana ba Alkur'an ba za'a daura auren yanzu ba sai nan gaba intayi hankali......
Abban Marwan saida ya murmusa yace kam buhu lallai ma...
.
Sarki dake sauraren su yace kungama Ko...
Suka eh..
Yace uhmm daman Adamu dan Ambassador libya Abdullahi shine nabawa khadija..
Kunsan meyasa nayi haka..
Dukan su suka Girgiza kai da A'a suna sauraren shi...

Kunga dai abunda yafaru wajen auren Adamu yaro ya birkice kaman mai Aljanu kuma nayi Imani baya cikin hayyacin sa yayi haka..
Shiyasa bayan biki da Mahaifin sa yasauko Daga dokin fushi nace masa kawai abashi khadija kanwar Samad din '' tunda shi ya Auri muradin sa...
Hakan zekara mana karfin zumunci..

Yarima Samad yace ALLAHU Akbar kabiran.
Sarki sake da baki yace kaga Yarima banson iya Shege me kake nufi ne...

Mamy da Mama karama dariya suke ta kasa kasa..

Yarima gyaran Murya yayi yace tome laifina kayi abunda Alkhairi n'a jinjina maka...
Cewa kayi zumunci zaka hada '' naga aiga Marwan nan shine inka hada kayi auren zumunci wancen kam ba auren zumunci bane auren hadi ne irin wanda kamun...

Abban Marwan sossai ya d'ara yace yau dai naga Sarki da Yarima a fili mun ganku a rana..
Ahmad yace Abban marwan kabar shi yabashi Amsa muji me ze ce....

Sarki sake da baki yace Ahmad kaci uban naka kaida Samad din yan rainin hankali '' to naji auren hadi zanyi '' kai Samad d'anayi maka auren hadi ai kafi kowa samun Albarka..

Yarima Samad yace OK naji tunda bakada amsa ta..
Badai kaba Adamu ba to Allah yasa Alkhairi.
Tabe baki yayi yace inafatan kagama jawabin naka ni zan tafi...

Mamy cikin fada tace haba Yarima ya ana magana zaka tashi..
Komawa yayi ya zauna yace yi hakuri Mamy wallahi barci nakeji shiyasa bana fahimta bayanin sa sossai...

Sarki yace naji dai Yarima auren kuma ya badu '' kace kishi kake da Adamu.
Yarima Samad Dago kai yayi yana kallon Sarki tareda nazartan kalaman sa yayi murmushi yace ikon Allah indai haka zakabi da zancena tona amince dari bisa dari ya auri khadija kaikasan Inde banson auren nan bame yuwa bane kuma d kake cewa kishi akan me zanyi kishi dashi bayan '' be kasa ni ba a soyayya....
Sarki yace wayasani to..

Sossai sukayi tsare tsare yanda za'a gudanar da shagalin bikin.

Nan take Sarki yakira Ambassador Abdullahi ya sanar masa '' ga lokacin da ake bukatar à kawo lefe..
Sossai Ambassador yayi murna yace InshAllah muma jibi zamu dawo dukan mu Daga england..
Amma yakamata ahada Adamu da yarinyar daze aura tun kafun ranar auren sudan Saba...

Sarki yace InshAllah za'ayi haka yau za'a bata waya kuma 'za'a bashi lambar ta...
Daga haka sukayi sallama..

Hatta ankon zasu yi ranar bikin da wanda za'a raba wa bayi kyauta da jama'ar cikin gari duka an tsara komai..

Sarki yace nidai kam bazani daurin aure Kano ba... Zan tsaya anan ayi na khadija gaba n'a...
Kema Mamy bazaki je ba..

Mama Karama ce zata je ta wakilci Ahmad ita da Abban Marwan 'ga yarima Samad'' kuma nasan yan uwan mahaifiyar ku duk zasu tafi kanon gara araba biyu..
Kinga Mamy zaki zauna ku amshi suruka..
Kuma kibada Yar ki..

Mamy tace hakane Allah yasanya Alkhairi ya nuna mana lokacin lafiya da ameen kowa ya amsa....

Wuni Ranar Yusuf Sani yaro
bincike ya wuni sossai akan Sarkin Adalai '' amma d'uk kasar daya duba babu shi babu me kama dashi...
Hakan yasa ya shiga nauyin kasashen french dan yagani Ko ze dace..
Yabarshi akan gobe tunda Asuba zefara gudanar da binciken sa kafun lokacin daya diba yacika....

Kusan Karfe biyar n'a yamma Dakarun sojoji sukace gidan Maman Maryam..

Iske Abban maryam sukayi waje yana waya..
Cike da mamaki yake kallon motar sojoji yayi parking kofar gidan nasa...
Kashe wayar da yakeyi yayi yadawo da hankalin sa akan su dasuke durowa Daga motar sa..

Babban cikin su ne ya karaso gaban sa taréda cire madubin glas dake Idanun sa '' yace sunana Sulaiman gaba tareda nuna masa ID Card dinsa..
Munzo ne mu tafi da Hajiya Farida Akan zargin ta
Da ake yi tanada sa hannu wajen yiwa Shugaban Adalai sharri inkuna neman karin bayani kuzo office din mu..
Yanzu ina take ne...
Abban Maryam bakin sa na rawa yace tana cikin gidan ni Mijin ta ne..

Dan Allah kubari mu sasanta '' babban nasu yace zancen banza kaga wasa a tattare damu ne..
Maza kayi mana jagora Muje ciki...
Babu musu ya bude gidan jikin sa na rawa yashigar dasu har cikin gidan...

Koda suka isa Falon iske Maman Maryam sukayi tana dukan Yar aiki kishiyar ta..
Yarinya tana ihu tana fadin wallahi hajiya zan bar miki gidan in koma kauyen mu...

Sake da baki sojojin suke kallon junan su suna kada kai...
Ganin bata gansu ba.
Babban cikin su yace hajiya ayi mata rai hakanan Ko..

Cak ta Dago kai cikin gigita take kallon sojojin da suka kewaye dakin nata...

Sakin yar aikin tayi bakin ta na rawa tace ku kuma Daga ina haka....

Babban cikin su yace ina fatan kece hajiya Farida..
Kada kai tayi Alamun itace......

Hajiya munzo mu tafi dake Umarni ne Daga Sarkin kwatano...
.
Cikin Rawar murya tace what.............

Taku Har kullum Kyauta Daga Allah
3/21/22, 07:56 - Nuriyyat: 9️⃣3️⃣

Tace what laifin me nayi muku..
Angwa suka nuna mata cikin tsawa yace wannan ma dukar da kike wa yar aikin naki shima ya shiga laifi duk da bamusan me tayi ba amma hakan ya nuna duk cikin zalunci ne wannan dukar da ake mata....

KUKA tasoma tana kallon mijin nata tace Abban maryam dan Allah kace wani abu mana zasu tafi dani..

Abban maryam yace Farida mezan yi musu bayan sunce sai sun tafi dake kije kawai zan zo gashi Maryam bata gida inta dawo zamu zo taré....

Hijab din ta ya shiga daki ya dauko mata taréda mika mata '' tasaka tana kuka tace n'a bani wayyo ni Farida Nice za'a tafi dani gidan Maza...

Basu bata lokaci ba wajen sa mata ankwa ba hakan yasa nan da nan suka jata har cikin motar su....

....

Fulani tana zaune cikin dakin nata gangami yazo mata da abinci' 'hade da ruwa bakin ta na rawa tace nagode gangami saura lemu....

Tsawa ya daka mata yace shegiya munafuka ai ana bani lemu inbaki shanyewa nake' ''
Badan ba'a bani dokar zaneki ba dayau kinsha bulala..

Sossai take kuka tace waini yar kwalisa Nice ke kwana awannan dakin...
Gangami ya bushe da dariya harda rike ciki.
Yace sannu yar kwalisa '' bari ayi shari'a kigani inhar kotu ta daure ki..
Alkur'an saikin gwammance da nan fiye da cen shasha kawai yafice yabar ta yana wake waken sa hade da fito..

Yarima Samad mikawa Khadija wayar ta daya kwace yayi tanata murna yace uhmm yarinya bakisan aure zakiyi bane shiyasa kike kaudi...
Afili kuwa fadi yake yawwa khadija ta '' zauna muyi magana....
Zama tayi tana fuskantar shi tace yaya inajin ka.....

Yace khadija nasan kinsan kaddara mekyau Ko mara kyau..
Khadija cikin sanyin murya tace nasani yaya tunda malamin mu '' yana gaya mana...

Jawo ta yayi jikin sa yace yawwa yar kanwata..
Kinsan yayan ki Ahmed zeyi aure kuma Asiya kawar Rahama ze aura..
Kekuma Adamu zaki aura dan abokin Sarki ambassador libya....

Arazane ta Dago kai tana kallon sa ta maimaita aure a fili.
Make kafada tayi cikin kuka tace wayyo ni khadija yaushe nakai aure '' yaya kubari nakara girma wayyo Mamy banaso..

Kallon ta yake yana Murmushi da shikadai yasan ma'anar sa '' yace uhmm dijat dîna auren babu fashi banine n'a hadaba tsoho me ran karfe ne '' Inkinada ja je ki same shi.

Kawo wayar insaka miki lambar Adamun '' zan kira shi ince kinbude waya 'yakira ki' 'wallahi inkika masa rashin kunya zaki sani..
. Khadija sossai take kuka wai itace za'a ma aure kuma auren dole' 'mijin maci Amana' 'maganar zuci take ita kadai..
Chapter 98 · 0% Book details