← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 115

Sashe 45

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zomu shige ciki inya gama ya fito dan kansa.
Barin sa wajen sukai..
Tareda shiga cikin gidan.
Rahma zaune take duk hankalin ta yatashi sossai Saboda mummunar mafarkin da tayi.
Ganin su Faruk sun shigo Daga cikin gidan '' cikin sauri sauri ta nufo su.
Fuskar ta babu walwala tace sannu ku da dawowa
Yawwa suka amsa mata.
baza idanu takeyi inda zata ga Yarima Samad ya bullo sai gani tayi shiru ne..
Kallon ta tamaida akan su Faruk dasuke kokarin hawa kan matakalan step..
Da kakkausar murya tace ku daka ta nace Ko ?
Da mamaki suka juyo suke kallon yanda Idanun ta suka kada lokaci daya.
Faruk yace Madam Samad lfy kuwa ?
Tace ina fa lafiya kunshigo gida babu bayanin da kuka mun.

Ina Mijina yake kuka dawo ku kadai bayan taré kuka fita kallon agogo tayi tace karfe goma d'a rabi n'a d'are..
Ina magana kunyi shiru.

Aminu yace yana cikin mota zaune muka barshi.
Be gama rufe bakin sa.
Tayi hanyar wajen aguje..
Har buge kafar ta tayi dan sauri.
Wajen motar tasa ta nufa mutuwar tsaye tayi ganin..

Taku har kullum kyauta Daga Allah
3/21/22, 07:44 - Nuriyyat: 4️⃣9️⃣

Mutuwar tsaye tayi ganin Yarima Samad hancin shi n'a fitar da jini ya jingina kansa jikin kujerar mota numfashin sa nata fisga sama_sama harya fara fita hayyacin sa.
Sossai hankalin ta ya tashi batasan lokacin data shiga taba jikin sa ba, jikin ta na rawa aguje takoma gidan gudu take bata ganin inda take jefa kafafun ta.

Faruk takira sunan sa da karfi har gidan ya amsa da sautin muryan ta.
Faruk dake kokarin canza kayan jikin sa.
Jin muryan Rahama yasa suka fito cikin hanzari shida Aminu.
Da sauri sauri suke saukowa Daga kan matakalan Stép.

Rahama n'a ganin sunfito.
Cikin fita hayyacin ta datayi tace Dan Allah kuzo Muje bakin ta na rawa '' ku taimaka mun mijina bata jira cewar su ba tayi wajen a guje.

Cikin hanzari suka take mata baya kokan su Iso
Har tana kokarin fiddo shi Daga motar da iya karfin ta.
Faruk a razane yace Abdul Samad cikin tsananin tashin hankali suka tara hannu shida Aminu wajen ciccibar sa zuwa daki...
Daga shi sukai cikin tashin hankali Rahama tace ina zaku kaishi ne.
Ku dawo dashi muje asibiti ta fada cikin raunin murya.
Faruk yace kibari à dai fara du bashi mugani suna cigaba da shiga ciki dashi.
Kan kujerar 3str din falon suka ajiye shi..
Aminu yace yanzu wani likita ne zamu kira ya duba shi.
Rahama dake arude shafa fuskar Samad tayi tace akwai docto family house din mu zan kira Abbana ya turo mana shi..
Cikin hanzari tadauko wayar ta tareda dannawa sheik kira.
Wayar sa tayi ring har ta katse ba'a Daga ba.
Tallafo kansa tayi tana ta masa fifita.
Ganin Zufa yake tayi duk karfin Ac dake dakin.

Aminu yace basu Daga bane yana tambayar ta.

Eh be Daga ba kila ya kwanta ne amma bari inkara mama ta.
Takarashe zancen tana mai dannawa ànty kira.
Bugu daya ànty ta Daga.
Cikin sheshekar kuka tace ànty dafatan kuna lfy dan Allah nombar docto ishaq zaki bamu nakira Abba n'a be Daga ba.
Ànty cikin kidima tace subuhannalah daughter meyake samun ki ne bakida lfy ne wayyo gayamin kinyi shiru cikin gigita take magana duk tabi ta rude.
Rahama cikin sassauta murya tace bani bace.
Shine beda lafiya.
Idanun ta na
Shiru tayi Jin yana motsa hannun sa na dama.
Jefar da wayar tayi ta nufesa hannun ta Daga cikin kuka tace Faruk dan Allah kabani ruwan zam_zam in akwai agidan nan in babu kaban ruwa pls tafada cike da bukatuwa..
Faruk cikin hanzari yatafi dan cika umarnin ta.

Ànty sai hello hello take ta fadi amma shiru take ji sai tashin maganar da suke yi a falon take ji.
Hakan yasa ta kasa kunnen ta..
Ganin Rahama ta ma mance da ita hakan yasa ta katse wayar tareda lalubar lambar docto ishaq.....

Faruk hannun sa dauke da ruwan zam zam ahannu cikin hanzari yakaraso falon yana mai kokarin mika mata..

Bata karba Daga hannun sa cikin sanyin murya tace dan juye mun a kofi.
Adu'oi take ta karantowa tana tofah masa a ilah'irin jikin sa..
Samad Idanun sa a lumshe.
Ajiyar zuciya ya soma saukewa ahankali yake kokarin Daga hannayen sa.
Ganin haka yasa Rahama tayi saurin Daga shi tareda daura kansa kan cinyar ta.
Faruk miko mata ruwan yayi ta karba cikin sauri.
Nan m'a ta shiga karanto adu'a sossai take yi wanda saida ta dauki minti shabiyar.
Sannan ta dan dan Daga shi da taimakon Farruk.

Cikin sanyi murya tace Amjad ga ruwa n'a kawo maka kasha dan Allah..
Ahankali yake bude Idanun sa yana kallon yanda duk tabi ta susu ce.
Hannun yayi mata Alamun tabashi dan shi kansa kishi yake ji sossai..
Mika masa ruwan adu'ar tayi tana kallon yanda hannun sa ke rawa ya kasa rike kofin cikin hanzari tasa hannayen ta cikin nashi tareda kai masa kofin abaki.
Shanye shi yayi tass.
Yunkurin Amai yasoma cikin hanzari tace Aminu dan bamu roba a bandaki.
Ganin Aminu ze bata mata lokaci hakan yasa ta tashi aguje ta tafi tadauko tana kokarin tara masa agaban sa daidai da saukan Aman.
Amai yakeyi ba kakkauta har Idanun sa sunjuye.
Wani ciwon ciki mai uban Azaba ya turnuke shi tun daga kan mara zuwa cikin izuwa kirjin sa
Nishi Nishi mai wahala yake fitar wa.
Rahama n'a kokarin tashi taje ta zubar da Aman wani riko yayi mata yanda Kasan mace tana nakuda irin haihuwa tazo Gadan Gadan.
Sabon yunkurin Amai ne yataso masa.
Yanayin Aman 'hankalin su yayi mummunar tashi ganin bakaken zare da Allurori hade da bakaken kyankyasai ya amayo.
Nan da nan.
Yafara sauke Ajiyar zuciya akai akai.
Rahama da su Faruk kallon abunda ya amayo suke da mamaki.
Faruk yace innaliahi wa'inna il rajun.
Samad me wannan kuma nashiga uku ni Umar wayyo Allah n'a
Aminu cikin tashin hankali yace wannan abun sai mun dauki hoton sa dan wlh bamu yarda ba.
Nida ataba Samad wllh gwamma ni aka taba.
Daukar wayar sa yayi yadau hoto.
Rahama gabadaya bakin ta yamutu Idanun ta sun kada jajir '' kallon Samad take saita ji yabata tausayi.
Cikin aro jarumta tace Faruk ku taimaka mun inshigar dashi daki yayi wanka yakwanta kai kuma Faruk Zam _zam zaka karo mun su.
Angama Ranki ya dade yafada daukar roban Aman Samad yayi tareda fita dashi Daga falon zuwa bandaki n'a baki
Dan ya zubar ya tsaftace falon..
Aminu ya taimaka mata wajen shigar da shi daki.
Duk abunda ake Samad yana Jin su saide babu wani kuzari a tattare dashi bare ya taimaka wa kansa..
Kallon Aminu tayi cikin sanyi murya tace kana iya fita dan yasamu yayi wanka.
Aminu yace babu damuwa inda abunda kike bukata ki sanar muna.
Kallon shi take harya fice Daga dakin
Tunani take taya zata taimaka masa yayi wanka.
Cikin tausayin sa daya darar mata lokaci daya tasoma kiciniyar cire masa riga '' lafaffen cikin sa take kallo yanda gashi ya kwanta luf à jikin sa...

Tunani take to taya zata cire masa duka kayan jikin sa.
Wata zuciyar tace anya zaki iya yiwa wannan wanka kedai akwai sa kai rigima..
Barin wani Tunani tayi cikin hanzari tasoma kokarin tadashi.
Duk ya sake mata nauyin shi kallon ta yake yanda yanayin ta ya canza sossai..
Tana kaishi bandaki taimaka masa tayi wajen cire dogon wandon nasa.
Karamin wando dake jikin sa tabar masa.
Ahakan m'a ta kasa jure kallon sa..
Ganin banda kallon ta babu abunda yake yi kuma ya kasa yin komai.
Uhmm Allah mai iko wannan wankan ma bazeyi ba saina masa...
Barin wani tunanin tayi tareda yi masa wanka.
Babu bata lokaci tadawo dashi cikin daki.
Kaya masu dan nauyi tasaka masa Saboda tsabar sanyin da ake yi.
Kwantar dashi tayi cikin muryan rarrashi tace inhada maka coffe ne kasha.
Shiru babu Amsa sai kallon ta dayake yi.
Hakann yasa tafita tareda zuwa kitchen ta daura ruwan zafi coffe ta hada masa.
Tana kokarin kai masa à daki taci karo da Faruk da Aminu.
Ganin Docto Ishaq a gefen su zaune..
Cikin yanayin damuwa yace Rahama yakike ya mai jiki Alhmdulilah tabashi amsa dasauki. tace Docto à tsohon daren nan kazo.
Mun saka ka aiki nasan kila kana hutawa ne ànty takira ka tafada cike da kulawa.
Docto Ishaq yace karki damu ai d'are beyi ba sossai ina pection din yake.
Ganin Abdul jalil n'a kokarin shigowa da mamaki take kallon sa tace kaikuma daga ina.. Murmushi yayi mata yace antina aini n'a rako Docto n'a tsaya Daga waje ne ina waya.
Chapter 45 · 0% Book details