← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 115

Sashe 112

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abban marwan kuka yake sossai yana Rokan yayan sa gafara...
Shugaban Adalai yace Sani baka min komai duk abunda yafaru sharrin matar ka ne...
Kusan karfe daya suka tashi taron inda Su Adamu suka fara shirye shiryen tafiya da dijat shida dangin sa da iyayen sa...
Tareda iya Firdausi da jakadiya...
Sossai khadijat ke kukan rabuwa da mamy..
Baba Salihu sossai Yayiwa Khadija nasiha akan biyayya Sannan Mamy ta daura da nata tana kuka sossai mai tsuma rai akan yar autan ta...
Mama karama itama nasihar tayi mata...
Koda zasu bar gidan da khadijat sossai Rahama da khadija suka rungume juna suna kuka sossai..
Adamu tsaye yake yana kallon Rahama yanda ta murje tayi mugun haske fatar ta tana wani sheki.....
Yarima Samad yana lura da kallon da Adamu kewa Rahama hakan yasa shi zuwa Jan Rahama Daga jikin Dijat yace yi shiru my wife yana rungume ta gaban Adamu yace karki damu kinji ai zaku ringa waya....
Maza kije wajen Asiya an barta ita kadai.....
Dawo da kallon sa akan dijat dake kuka yayi ya rungume ta cikin muryan lallashi yace dijat dîna kiyi hakuri kinji aure ke kawo rabuwa amma ai bamu rabu ba..kina taré damu kuma zamu kawo miki ziyara InshAllah nida Rahama da zaran ta haihu..
Da gayya ya fada dan Adamu yaji...
Shiko Adamu d'abe kawo komai aransa ba yace MashaAllah Allah yaraba lafiya...
Ahmad ne yafito cikin shigar sa na Alfarma sanye da Alkyabba yace har kun shirya ne Muje rakiyan nata Ko iyakar mu Airport...
Rungume dijat yayi yana kuka yana mata nasiha.
A'zuciyar sai fadi yake uhmm kema zumar zaki bayar kamar yanda n'a kwasa.
Afili kuma sai fadi yake yi hakuri Sister...

Shugaban kasar Niger tsaf shima ya shirya ze koma kasar sa..
Hakan yasa su waziri da hadimai zasu masu rakiya har filin airport din Samad Plan....
Kusan a tare motocin nasu suka bar gidan tareda Su Khadijat.....

Koda suka isa filin jirgin shugaban kasa shida Amarya sa Samad personnell suka Shiga...

Su Adamu kuwa sukabi Samad air plan wanda ake diban passgen A'ciki...

************************

MAKARFI

mama sossai ta rame batada kwanciyar hankali..
Dakin da take kwana Sam bata sake wa..
Saboda dakin tun ginin da ne kuma haryanzu ba'a gyara ba..
Ga Azaban Zafi ga tsauro..
Mahaifiyar ta zubaida tace Sam bazata kwana mata adaki ba...
Dan me yara basu kashe auren nasu ba..
Sai itace za'a koro Daga gidan miji kuma akan taurin kai..
Duk wasu nau'i n'a aikin gidan Mama ce takeyi babu sauki...
Motar ta data bâri ta tuna ta kira Abubakar tace dan Allah mota ta kasiyar mun ka aiko mini da kudin koda karamin gida ne insiya wallahi wahala nake ga zafi ga tsauro..
Abubakar cike da tausayawa Yace Mama wallahi nayiwa Abby Maganar Motar n'an yace wai Yarsa Rahama ce tabaki kudin..
Da dai da kudin Salma ne ze bada Asiyar..
Nikuma banda isashen kudi sai anyi Albashi kudin dake hannuna aka tura wajen kai gaisuwa...
Mama tace subuhannalah yanzu Abubakar nawa zan samu hannun ka wallahi tun safe banci wani abun kirki ba sai koko kuma wallahi dari biyar gareni gaba da baya inada kudi dubu dari takwas adakina amma mahaifin ka hanani shiga dakin yayi yazanyi da rayuwa ta...

Abubakar cike da sassaita nutsuwar sa yace karki damu inada dubu goma zanturo miki.... Yanzu nawa Abby yake turo miki d'uk Sati...

Cikin kasa da murya tace dubu biyar..
Kai kai Mama dubu biyar shine yake karewa a sati kauye ne ra..
Mama cikin bacin rai tace banson shashan ci dubu biyar arana sai incinye shi nidai inajiran ka....
Suna sallama ya zauna yana murmushi yace oh Mama ba'a Saba da wahala ba..

Salma sai a yau ta farfado Idanun ta d'uk sun kumbure '' fatar jikin ta yayi duhu sossai...
Ahankali ta bude Idanun ta tana kallon wayanda ke dakin Daga Abby sai Hassana dan cikin Ànty ya tsufa Sheik ya hanata yawo....
Hassana cikin hanzari taje tana shafa kan Salma tace d'aughter sannu Ko...

Gyada mata kai tayi tana Daga kwance...
Abby yace sannu kinji Salma ya jikin naki nan ma gyada masa kai tayi...

Shiko gyara zaman nasa yayi kan kujera ya zauna yace yawwa Salma yau za'a bamu Sallama.
Zankira Al'amin yazo yadauke ki yakaiki gidan nasa..
Tun safe nake kiran layin sa baya shiga kuma yace yau dawuri zezo daukar ki....
Zuru Zuru take kallon mahaifin ta..
Hassana tace Abban Rahama kamar yanda taji anty tana fadi please kabar ta mu koma gida taré inta warke saita koma gidan nata....

Sheik yace haba kina ganin yadace inkai wacce babu digon Imani agidana..
Sam bazeyu ba yata ce bazan iya canza ta ba..
Saide ina iya yimata iyaka da gidana....
Cikin rarrashi hassana tace dan girman Allah kayi hakuri wallahi yarinya ce tana iya canzawa duk da ance hali zanen dutse ne.
Amma inada yakiniin zata canza kodan ishara data gani....

Sheik yace Amarya tunda kince Allah angama amma tasani bata kara Jin dadi n'a...

Hassana tace naji n'a amince wataran zaka wuce ne uba da ya sai Allah tafada tana murmushi yawwa dafatan su Imran da kannen mahaifiyata sun isa lafiya Ko..
Dan nabar wayata gida..

Sheik cike da kallon so yake binta dashi yace eh sun isa lafiya Amarya ta...
Zanje indawo sai bayan Magrib sannu da kokari innadawo sai tattaara mu wuce gida Ko....

Hassana tace babu matsala habibi byee byee shima byee yake mata tareda barin Asibitin....

Al'amin zaune yake gaban shugaban tsafin nasu yana fada sossai..
Yace garin ya kabari Matar ka tara sa cikin jikin ta..
Kaida muka ce maka muna son Jinin t'a d'ana jariri..
Tunda babu dan yanzu muke bukatar kurwan ta....

Al'amin cike da damuwa yace tana Asibiti fa Ko farfadowa batayi ba...
Shugaban kallon banza yake binsa dashi ya dauko wani Katon kwarya ya zuba ruwa acikin sa...
Nan da nan saiga Salma ta bayyana tana kwance gadon Asibiti idanun ta abude yace kai shasha leko kagani tunda kace bata farkaba..
Kuma duk Alamu mahaifin ta gidan sa zekai ta jinya inhar tana cen bazamu iya daukan kurwan ta ba..
Yanzu da duhu yayi zamuje Asitin tare dukan mu ka kai mu har dakin da take ciki...
Cikin Rawar Murya yace babu matsala.....

Hassana bayan ta idar da Sallah zama tayi tana lazimi barci yafara daukan ta kasantuwa tana tattare da gajiya.....
Hakan yasa bataji karar bude kofa ba.....

Ahankali yaturo kofar nasa...
Ya leka sossai yaga barci Hassana take itama Salma Alamun barci take...
Hakan yasa shi komawa agurguje ya shigo da matsafan da suke sanye cikin jajayen kaya hannun shugaban su dauke da kwaryan jini......

Ahankali suke taku har suka karaso dakin..
Dube dube suke yi ganin babu kowa à bandakin....
Ogan nasu sai zazzare Idanu yake yana kallon mabiya bayan sa...
Da kowannen su Idanun sa zagaye yake da bakin abu....
Ahankali suka tura kofar kokarin dannawa dakin key suke yayi daidai da murda handle din kofar da Sheik yayi shida Aminin nasa....

Cike da tsoro Ogan Tsafin ke kallon wayanda ke shigowan ganin Sheik hankalin su yayi mugun tashi ba kadan ba musamman Al'amin da shima yake sanye cikin irin shigar su....

Cikin tsoro da gigita Sheik ke kallon kwaryan hannun su tunanin sa Ko sun kashe masa yar sa ne...
Arazane yace Isa maza ka kira mana sécurité..
Da likitoci harda yan sanda...
Ogan nasu uban dariya ya saka yace me zasu mana yanzu zamu bace agaban ka...
Sheik najin haka. Yafara adu'a ba kakkauta wa wanda yasa suka kasa bacewa adakin nasu........
Shigowar jami'an tsaro da Sécurité ya Daga hankalin Al'amin ita kanta Salma cike da tsoro take kallon matsafan...
Hassana firgit ta tashi tana salati tace innaliahi nashiga uku me zangani...
Kankace me jami'an tsaro sun saka musu ankwa a hannayen su..
Sheik cike da ban Mamaki yake kallon Al'amin shida Aminin sa..
Suka hada baki wajen Fadi kai Azzalumi maza ka sakar mana yar mu kafun kabar dakin nan...
Shiru yayi yana kuka yace sheik ba laifi n'a bane Salma ce ta jefani cikin wannan halin tace innemo kudi kota halin kaka ne da bazata iya zama da talaka ba.

Sheik tabi ya shiga yi yace Amma anyi Sakarai Salma batada wuta batada Aljanna.
Dan haka wannan ba hujja bace illa son zuciya da kwadayi...
Wani gigitaccen Mari Sheik ya sakar masa yace zaka sakar mun yata Ko sai nasa jami'an tsaron nan sun gyara mun kai....

Bakin sa narawa yace nasake ta Saki daya..
Sheik yace saki uku zaka mata mata..
Dole yacike sauran...
Jami'an tsaron figan su sukayi cikin zafin nama suka jefa su a motar su..
Wanda haka yajawo hankalin dumbun jama'a akan su.......

Salma kuka take sossai iya karfin ta Jin abunda yafaru tana jin rayuwar ta beda Amfani musamman da hassana ta gayamata bazata kara haihuwa ba..
Duk saitaji ta tsani mahaifiyar ta..
Kuka take iya karfin ta tana fadin wayyo Ni Salma haka rayuwa ta juya dani..
Yaya ta Rahama baki da hakki akaina shiyasa Allah yake kareki Allah kaban lafiya inroketa yafiya kafun nabar duniya tunda akace ciwo ya taba mahaifata dawuya in rayu....

Hassana tace Ah Ah InshAllah Salma zaki rayu kada ki karaya...

Katsina...

Bayan isha'i à bokan Adamu sukayi tsantsani wajen rako sa wajen Amaryar sa dijat........
Koda Abokan suka siye baki..
Iya Firdausi da Jakadiya masaukin su aka kaisu....

Adamu sossai yasa dijat sukayi nafila Sannan Dakyar tayi ciye ciye duk da tana jin yunwa.....
Aranar dai Dijat tasha kuka sossai dan Adamu be je da wasa kasancewa ya dade yana jiran wannan ranar....

Iya Firdausi tana masaukin nasu suna ta zuba soyayya ita da Abban Karima yana fadin gobe yakeso tazo Niger din..
Tace babu matsala megida duk hutawan da mukayi a hôtel be isheka ba..
Yace inafa ya isheni kece kawai nake gani yanzu agabana ban ganin kowa.........

**************************

Bayan kwana biyu...

Kwatano...

Ayau ne takama za'ayi zaman kotu..
Tunda sassafe kowa yashirya cikin gidan harda Asiya da Rahama...
Asiya Sam bata son hada idanu da Ahmad tunda abunnan yafaru Shiko hakan Ko ajikin sa dan fadi yake hutun kwana hudu nabaki babu ruwana à fili kuma sai janta da hira yake....
Baki Daga Bohicon duk sun hallara zuwa kotu....
Chapter 112 · 0% Book details