← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 115

Sashe 48

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan batada tarbiyya an bata, ta zubar à titi ya za'ai tazo ta ringa buga mun kofa ina barci ta tashe ni ita bata Jira ne?

Rahama mutuwar tsaye tayi ganin yanda ya rufe Idanun sa yana zazzaga ruwan masifa dan sosai yaji haushin ta inda ze iya Zane ta tabbas daya Zane ta.

Cikin rawar murya Salma tayi kasa da kanta a duke tace dan Allah kayi hakuri ban san kana barci ba.

Kallon banza ya watsa mata tare da yin tsaki.

Yabar wajen a zuciye tare da komawa dakin nasa zuciyar sa na tafasa.

Faruk da Aminu kallon Rahama sukai Amma basu ga a'lamun bacin rai a tattare da ita ba wannan yana Daga cikin dabi'ar ta baka gane fushin ta sai inhar ta bude baki tayi lafazin da zai sa a gane Ranta ya baci ba.

Faruk yace" Madam Samad kiba kanwar ki hakuri muma mun dauka yana farke ne shiyasa da tace bata iya jira muka nuna mata dakin naku.

Salma ba k'aramin bakin cikin wulakancin da Samad yayi mata takeji ba.

Rahama cikin cool voice din ta tace "My kanwaty am sorry bai san ki bane shiyasa amma zan mai bayani"

Kusan a tare suka sauka Daga kan matakalan( Steps) d'in.

Farruk ya ja Aminu suka fita compound din gidan dukansu wayoyin su n'a hannun a rike sukabar falon.

Itakuwa Rahama zama tayi cikin muryan rarrashi tace haba kanwata kiyi hakuri n'a kin hade rai tun dazu.

Salma kallon Rahama take tana jin mugun tsanar ta a cikin rain ta ayyana a ranta dole saita raba Rahama da Samad daman cikin wannan daulan take jibi fa dakin sa ta fito Girgiza kai tashiga yi.

Rahama dake kallon ta tace haba Salma har yanzu baki huce bane?

Murmushin yake tayi cikin salo n'a bariki tace ayya karki damu ai yana da ikon yamin fada yayana ne shima.

Rahama murmusawa tayi tare da tashi zuwa gaban TV ta kunna mata kallo.

Remote ta mik'awa Salma tace gashi ki canza tashar da kikeso bara inje kitchen in daura mana girki Ko Salma tace Tom maza ki je tana yatsine fuska.

Kallon Rahama take yanda take tafiya cikin saurin ta.

Harara tabita dashi tace wahalalliya mai bakin hali irin n'a Ànty sai kinyi kuka wlh InshaaAllah ba dai ni bace zaki sani ne.....

Samad yana komawa cikin dakin zaune yayi bakin gado rike da kansa dake Sara masa hade da wani zazzabi banda haushin Salma ba abunda yake ji tabbas itace silan wargaza mishi cikar Burin shi.

Agogon dake makale jikin bangon dakin ya kalla ganin time yatafi yasa cikin kasala ya shiga bandaki rage kayan jikin sa yayi ya sakar wa kansa shaya wannan ruwan dake sauka bisa kansa izuwa gangar jikin sa ba k'aramin tasiri sukai ba wajen rage masa abun yake ji ba.

Lumshe Idanun sa yayi abunda ya faru tsakanin da Rahama ne yafara dawo masa ji yake kamar yayi tariya ya koma baya cike da takaicin Salma yafito daga bandaki tareda sane jikin sa da towel.

Gaban miror yaje yana kallon kansa ta cikin madubi Murmushi yayi cikin maganar zuci yace ya Allah kanuna mun cikar burina na tabbatar inna same ta zata kula dani yanda ya kamata,
tsaki yayi a ransa yace to ya'akai ne duk aji n'a amma gaban wannan yarinyar sai in kasa rike shi?

Barin wanan tunanin yayi tare da dauko mayukan sa ya fara bin jikin sa dashi,
wasu tsadaddun kayan sa ya dauko Daga wadrobe d'in sa kallon kayan yake yana tunanin Ko ya canza su ne wata zuciyar tace tunda baka taba saka su ''l
sa abunka kila rabo yayi yau ka hadu da zanen hoton ka.

Da wannan tunanin yayi maza ya saka wannan babban shaddar daya haddaden dinki Daga gun kwararen tela sossai rigar ta zauna masa a jiki,

kasancewa bleu ne shaddar hula bleu ya saka ya dauko wanda yayi macin sosai da kayan jikin sa.

Cikin dan hanzari ya zura agogo tareda saka takalmin sa half cover.

Sosai shigar tayi masa kyau kara koma gaban miror yayi yana kallon kansa tareda dauko turaren one love ya feshe jikin sa dashi.

wayar sa dake ajiye kan miror ya dauka tareda yiwa kansa hoto.

Kallon kayan break din Da Rahama ta kawo masa yayi wanda ga sunan bata kwasheba kwabe baki yayi yace uhmm badai an hadani da aiki ba,
In ba haka ina ni ina aure garin kano kuma a kanon ma wacce ban taba mafarkin samun ta ba.

Rahama dawowa falon tayi ganin Salma ta daura kafa daya kan tebur din tsakiyar falo 'kuma tasan Yarima in yagani to sai yayi magana musamman da yake jin haushin su.

Su Faruk ma baya barin su daura kafar su akai ce musu yake suje su nemo nasu wannan nashi ne.

Cikin sanyi murya da dabara tace uhmm Salma zo mu danje kitchen ki tayani aiki mana?

Salma cikin hada rai tace au har wani aiki zan tayaki inzo gidan naki ni dai ki dafa kiba ni.

Kalamin Salma caraf a kunnen Samad dake saukowa kan matakalan (steps)din Jin karar tafiyar sa yasa Salma da Rahama kallon sa.

Salma tabarakallah Masha Allah take ta furtawa ji take kamar taje ta rungume shi wanda haddaden gayen shine mijin Rahama ah lallai tana girgiza kai.

Rahama kasa da kai tayi ganin ya karaso falon.

Fuskar sa a hade babu ya hada rai kallon Salma yake yanda kafafun ta ke yawo akan wannan tebur din nashi.

Karasowa wajen yayi yana kallon ta cikin idanu yace keee!

Da kakkausar murya yake magana wanda yasa gaga Rahama har Salma tsorata.

Cikin bacin rai yake magana yace "ke waya baki damar ki daura kafafun ki anan?

Rike da kugun sa ya fara zazzaga mata ruwan masifa
wanda ya jawo hankalin su Faruk da daki suka fito dan Jin ba'asi.

Cikin sauri Salma ta sauke kafafun ta.

Ta boye bayan Rahama dan gani take kamar bugun ta zeyi.

Faruk yace" Yarima wai me yake damun ka ne?

Tunda ka kwanta ciwon nan shikenan sai ka fara dawo da halin ka na baya"

"Wannan fa kanwar matar ka Rahama ce ba kaga suna kama bane haba dan Allah ka sassauta mata"

Yarima Samad da yakai wuya wajen bacin rai ya fuskanci Faruk cikin muryan sa dake nuna zallan bakin ciki yace.

"Ina ruwana da ita wacece Ko da tare suka zo duniya da Rahama karshe kenan ba abunda ya dameni akan me zata zo mun gida irin wannan lokacin kuma tazo da hauka ace bazan magana ba"

Kallon Rahama yayi wacce tayi kasa da kan ta.

Yace ki bude kunnen ki da kyau ki saurareni,
Wannan yarinyar in har tazo gidan nan ki ringa sauke ta a dakin ki Ko dakin baki ba na son inyi tozali da ita"

Rahama cikin kasa da murya dan yanzu ya fara bata tsoro tace" Insha Allah zan kiyaye"

Kallon sa ya maida akan su Faruk yace kuzo Muje aina ga ku shirya Ko?

Aminu yace ai dole kace haka jibi yanda ka kure adaka shine zaka ja mu kamar wasu raguna babu kyaun gani.

Samad gaba yayi yace to ina compund din gidan da kun gama ku same ni bai san me yasa kwata-kwata baya son zaman falon tunda yaga Salma inda khadija ce daya zane ta wannan abun haushin ka.

Niko nace Yarima ya da daukan zafi haka daga ta buga maka kofa shikenan sai ka sa ta a gaba.

Kallona yayi yace ke kuma Daga ina haka cikin yin kasa da Murya nace suna n'a *kyauta Daga Allah* wani kallo yabini da masu tarin ma'anoni yace suwaye ba n'a Allah ba?

Ganin kansa n'a hayaki yasa n'a wuce sadaf sadaf batareda ya ganni ba n'a boye wani lungu dan cigaba da kawo maku labari.

Kallon agogon hannunsa yake ya na buga uban tsaki
Har ya zangaya ze shige motar yasa Su Aminu har, sun fito suna ta buga uban sauri suma.

Samad yace yawwa Faruk wannan yarinya nan ya ma sunanta ?

Faruk yace Samira kenan kake nufi?

Eh ita ya bashi amsa à takaice.

"Dan kira ta ka tambaye ta yaushe zata raka ka?

Faruk zaro wayar sa Daga cikin Aljihun sa yayi tareda dannawa Samira kira.

Wayar tayi ring har ta yanke bata Daga ba.

Aminu yace" tunda bata d'aga ba muna iya tafiya unguwar da tace"

"Amma fa kamar unguwa sheik Imam ne"

Samad yace "au haba unguwar ce aikuwa tazo gidan sauki"

Samad yace," kamar ya kenan?

Aminu yace ,"akwai wata kawar Rahama mai suna Asiya unguwa take inada nombar ta sai intura mata zanen ta whsap zata bincika mana basai mun;sha wahala saka yarinyar nan agaba ba"

Ajiyar zuciya Samad ya sauke" yace to dan gwada tura mata"

Bude datar shi Aminu yayi ganin kamar Asiya bata online yau kwana hudu kenan.

Samad da Faruk da suka tsaresa da idanu suka ce ya ne katura mata.?

Aminu yace "eh natura mata saide ta kwana biyu bata hau ba"

Faruk yace karka damu da ta hau zata gani.

Samad shiga motar yayi yana kokarin shiga mazaunin drever.

Faruk ya tareshi cikin hada fuska a wasa yace tabe tabe ya da haka ne
Wai?

Da mamaki Samad yake kallon sa yace waye tabe_tabe ne wai rannan naji kuna fadi kuma yanzu naga kuna yawan fadin haka.
Aminu ne ya tuntsire da dariya yace" haba Samad dani yake fa wai ni ne tabe tabe.

Samad dake masu kallon rashin yarda da zancen Aminu yace "ku gaya min Ma'anar tabe tabe nace tareda hade fuska tamau.

Faruk kokarin shiga mota yake Samad ya jawo shi ya dawo da baya suna face din juna.

Murmushi Faruk yayi yace ka basar wani film ne muka kalla nida Aminu sosai wannan shirin ya kayatar damu kuma sunan film din tabe tabe shiyasa nasawa Aminu sunan ya karashe zancen yana Murmushi tareda bude mota yashige.

Samad tsaye yayi yana nazarin wani Daga bisani shima shiga motar yayi shida Aminu suka bar unguwar cikin gidan.

************************

🇧🇯

Mamy zaune falo Ahmad na kusa da ita.

Cikin Fada take magana tace "haba Ahmad meye hujjar ka na fadin kai baka yarda da wannan matar ba?

Ahmad fuskantar Mamy yayi cikin yin kasa da murya yace
Chapter 48 · 0% Book details