← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 115

Sashe 91

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sossai wani zufar wahala ya ketowa Samad da Rahama kusan a tare suke kallon juna suna kallon takardan

Yarima Samad tashi tsaye yayi hannun sa rike da takardan yace uhmm Rahama ke Jaruma ce..
Kin jure gwagwarmaya akaina ga wani yanzu kindakko wannan karan taré zamuyi meye mafita Rahamatullah ke nake sauraro..
Tareda dafata '' kallon sa take cikin kunan Rai tace Ancuci Sarkin Adalai bazamu kyale su ba..

Dole mu d'au Fansa..

Yarima yace hakane yanzu lokaci yayi da zasu gane kuren su ina case dayawa agaba n'a..

Amma case din Saratu shine babba itace lomar farko...

Rahama tace bayan Saratu waye agaban naka...
Bakin sa na rawa yace..

Marwan da Salma...

Cikin Rawar Murya tace Salma kuma kardai kace KANWATA...

Kwarai kuwa kanwar taki yanzu ba lokacin maganar ta bane '' yakatse zancen da neman mafita akan Saratu.....

Tunani yashigayi sossai '' cikin tabe Baki yace nasan wani Soja À buja babban soja ne. Mataimakin shugaban kasa ne...

Rahama tace '' ya sunan shi Ko wannan sojan nan mai rikon gaskiya da Amana wanda yayi fice akan harkan bincike da bin diddigi '' Yusuf Sani Yaro...

Yarima Samad yace kwarai kuwa shi nake nufi '' zan masa magana Akan Saratu '' yana zaune a abujar zeyi komai tunda tana nijeria tazo gidan sauki....

Rahama tace gaskiya kasa shi agaba dan wanda yakama mahaifin sa '' akan laifi to kaga baze yi shayin kamo mana Saratu ba..

Cike da jinjina Al'amarin Ya rungume Rahama yana kuka yace Rahamatullah tun ranar danayi tozali da mugun abu akan mahaifina adaren ranar ne nafara mafarki akan ki Rahama....

Cike da zare idanu tace Amjad kamarya kenan dan fahimtar dani yanda zangane......

Rahma à wannan Ranar nafara ganin ki à mafarki n'a kina zuwa min fuskar ki dauke da nikabi''' kullum abu daya kike fadamin shine inyi hakuri da jarabawa zanyi nasara...
Kullum fadamin kike Amjad inason ka '' inason ka amma akwai tazara à tsakanin mu...
Niko nace dan Allah meye tazarar sai kika gayamin À mafarkina tazarar b kasa daya muke ba '' idan zan iya inzo kano neman ki '' kuma mahaifina yana cikin garin kanon kusa da wani shahararren malamin Addini..

Koda naje kano duk inda nasan manyan malamai sainaje neman sa. Amma babu nasara...

Ajiyar zuciya Rahama tasauke tace Amjad '' Iskar dake taré dakai itace take nuna maka hanyoyi acikin mafarkin ki itace take zuwa maka da suffa ta dan tasan lallai zamu hadu kuma zamu zama mata da miji tasan taré nidakai zamu kawo karshen duk wani makirci shiyasa tayi amfani da wannan damar tun ranar data bude maka idanu a mafarki da fuska ta ka kara ganin ta??

Girgiza kai yayi yace Ah Ah bankara ganin ta ba...

Uhmmm tunda Daga Ranar Burin ta yacika shine tabar jikin ka tabar rayuwar ka tadau Alwashin taimaka maka ne bisa zaluncin da taga anshuka muku ta turo ka gareni ne dan mu taimaki Sarkin Adalai....

Yarima Samad jinjina Al'amarin yayi yace nayarda da bayananki hubby n'a wai ya akayi kike ganin Aljani bayan mu bama gani...

Murmushi ta sakar masa wanda yake sanya ya m'asa zuciya...

Amjad kakana Sheik Kabeer Hizqeel Makarfi shine wanda yake bani sirrin abubuwa da makaman su' 'da kariyar su...

Duk sanda zamu hadu saiya koyae dani abunda mahaifina be koya mun ba...
Ita Salma Sam taki maida hankali''' kaga nida Abubakar da Abdul jalil mune muke daukan darusan dayake koya mana...

Tun ina gida ake kawo mun irin yaran mata da Aljanu suka aure su..
Da wayanda iska ke damun su...

Ninan Rahama ana kawo mun mara lafiya daga wata kasa dan neman magani akan warware sihiri Ko muguwar cuta.....
Ina bada magani da ayoyin Allah kuma Alhmdulilah ana dacewa dan abun ba dagani bane Daga Allah ne '' kuma Nice sila..

Amjad tunda nataso agidan namu bansamu shakuwa irin ta uwa ba..
Ànty itace ta zame min uwa itace ta zame tamkar uba n'a.. Duk da mahaifina yana kula dani...
Da karatun mu..

Ànty ta koyar dani Addini da koyamin yanda zan mu'amallanci mutane..
Ta koya mun yanda ake zama da miji tun ina karama...

Agidan mu Salma itace babban matsalata inason ta sossai kuma har gobe ina sonta...
Matsalar da Aka samu mahaifiyar mu batason ganin laifin Salma akan ta zata bugeni '' Salma tana iya fadin abu wajen ma maman mu kuma maganar ta zauna kenan babu wanda ya isa yace ba haka bane...

Salma itace silan raba aurena da Adamu da za'a daura '' wanda yakawo mai Martaba ya karbar maka aurena...

Hakan n'a dauke shi à matsayin kaddara sai gashi nasamu wanda nafi so game da komai sai yanzu n'a tabbata Adamu kaunar sa nake a lokacin...

Kaine ainihin wanda nakewa pur love Amjad......

Farkon haduwata dakai tun daga ranar nakasa sukuni '' duk da bawai n'a gane ainihin me nakeji a tare dakai bane......

Zagin da kai mun n'a rashin kamun kai shine ya hanani barci...

Kayaitaceen murmushi yayi saida kuncin sa ya lotsa yace Rahamatullah '' ranar naji bakin ciki ganin ki da wannan Adamun hakanan naji kamar in shake shi...

Nikaina n'a dauka rashin kamun kai ne yasa naji haushin ganin ku...
Saida ga baya nagane ashe kishi nakeyi....

Sossai suka d'ara har lakuta mata hanci yace Uhmmm shine nace mun a airport Ko...

Uhmmm n'a nace maka koka nace mun harda wani d'anne fitananne kawai tana murguda baki....

Bawani Fitina kice kinsha dadi '' dariya tayi sossai saida fararen hakoran ta suka bayyana tace uhmm kaida ka afkamun amma ka tashi kanata zuba ruwan masifa harda wani ka fasa tafiya kasan à ranar bama ka isheni kallo ba....

Uhmm inban isheki kallo ba aina ishe Salma Ko...
Tunda suka dauki hoton mu sanda muke kwance a wayar Marwan.....

Cikin zazzare idanu tace hoto kuma.........

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah
3/21/22, 07:55 - Nuriyyat: 8️⃣6️⃣

Tace hoto kuma bangane ba '' Marwan din ya dauke mu hoto nidakai ''

Eh shine yadauke mu'' matso kiga hoton' 'gallery Din wayar sa ya shiga ya maida hankalin sa gun nemar hoton...

Murmushi yayi yace uhmm zokiga' 'matso da ita yayi kusa dashi tareda nuna mata hoton...

Cikin gigita take kallon hoto cike da zallan mamaki tace Marwan din ne yadauki hoton tana kallon hoton bakin ta abude...

Eh Marwan yadauka ya turawa Salma' ' itakuma Salma ta nunawa Adamu ranar daurin auren naku shikuma ya janye...

Wataran Salma takira Marwan saina n'a dauki wayar agaban sa' 'n'a Daga inajin muryan mace nace masa kenan kafara bin mata....

Wannan dalilin yasa nabi diddigin sa nadau wayar tasa naga hoton daya tura mata saida nashiga shock cikin tsananin tashin hankali nasan wannan hoton' 'yanada Burin ya yada shi duniya tagani kinga za'a halin mu daya da ubana...

Goge duk wasu hotuna nayi a wayar tasa dan kada yayi zargin Ko angano shi ne...

Innaliahi Rahama ta shiga maimaitawa tace Salma nashiga uku kanwata' cikin kuka tace Amjad bansan menayi wa Salma ba take tsanata ba '' n'a dauka kuruciya ce ''wallahi innaga yaya da kanwa suna kusanci' 'sossai kuma suna kaunar junan su 'burgeni suke.....

Hannayen sa yasa yafara goge mata hawayen nata yace Hubby kiyi hakuri fa..

Azuciyar sa sai fadi yake dan ma bakisan abunda Salma take shirin aikatawa bane''' uhmm InshAllah zan kareki mata ta cikin maganar zuci yake Rahamaa ta zuba masa idanu tace yadai Amjad tunanin me kake..

Murmushi ya sakar mata hade da lakacar hancin ta '' uhmm Hubby kinsan in inajin dumin jikin ki..
Kashe min jiki kike...

Zazzare idanu Rahama tasoma tana neman hanyar guduwa cikin kukan shagwaba tace Amjad dîna....

Ni d'ai ka kyaleni ba abunda zan iya maka...
Tashi tayi tana kokarin zillewa hade da masa gwalo '' sossai ya d'ara yace uhmm Allah yakaimu ai daren yau namu ne..

Tabe baki tayi tace uhmm kaga bankira Asiya ba tunda ta tafi ba...

Kuma yakamata ki kirata ita da mamar ki '' anty kike kiran ta...

Eh Ànty nake kiran ta my Amjad ''...

Kusan Azahar Samad yana makale da Rahama adakin Dakyar yabar ta '' ta shiga kitchen da kan ta dan daura musu girki....

Isowar Karima ne yasa Samad barin Sashin yafita dan gudanar da wasu Ayyukan sa...

Yana Fita ya tura wa Yusuf Sani Yaro sako akan whsap dinsa...

Ya tura masa da :

Salam Alhaji yusuf dafatan kana Lafiya..

Kwana biyu baka nemana ya kake yame dakin naka Sumayya...

Cikin Sa'a kuwa yau yana online dan sai yayi sati behau online ba '' amma datar sa tana kunne da zakayi masa '' whsap call ze shiga amma baza'a Daga ba.....

Ganin Sakon Yarima Samad yasa shi kai tsaye shiga cikin sakon yasan duk yanda akayi Ko zumunci zasu yi Ko kuma aiki ne yazo dashi...

Hakan yasa yayi maka reply tareda bashi damar su sauka Daga kan whsap '' yakira direct..

Babu Musu Samad yasauka Daga kan whsap dîn..

Kiran sa yayi direct Daga cen bangaren yana wayar amma kuma yana magana da wasu alamu cikin tarin Ayyuka yake '' kuma manyan yan majalisu ne kusa dashi....
Cikin da fada fada yake musu magana yace dan Allah ku fita '' waje ku dawo nan da Sati daya '' Samad dake sauraren yanda yake zuba ruwan masifa àcen din yace kaga namijin zaki '' wanda beson takura.....

Muryan Yusuf yadawo dashi duniyar tunanin daya shiga..

Yusuf yace dan uwa Dan Sarki. Jikan Sarki wai kana nufin har yanzu bakaga Sarkin Adalai ba...

Samad yace ban ganshi ba nasan kaine kadai zaka iya binciko mun shi..
Amma kafun nan wannan baiwar nan wacce Al'amarin yafaru da ita '' ita nake nema ance ta buya à garin kano.....

Kasaitaccen Murmushi Yusuf yayi yace uhmm '' lallai tayi karamar hauka tarasa inda zata buya sai kano..

Amerika ne kadai zata je inkyale ta..
Tura mun hoton ta '' kaban awa 48 duk inda take zakaji inma kanon Ko wajen kano...

Sossai Samad yaji dadin bayanan Yusuf hakan yasa yaringa masa adu'oi à karshe yace shine bakazo biki n'a ba..

Yusuf yace A'h Ah kabari ta haihu mana InshAllah da Mata ta zan zo.
Sossai Samad ya d'ara yace to Allah yabata cikin da Ameen suka Amsa taré........

''
Chapter 91 · 0% Book details